GADAR TSAUTSAYI 18
by @nusybee143
Page 18
Hankalin Arfa ya kwanta sosai,don ta san wacece yayar Tata Hajiya Ruƙayya,har ma ta saki jiki ta ci abincin da masu aiki suka jera mata
Da daddare ta shirya cikin ƙananan kaya da suka bayyanar da surar jikinta ta tafi sashen Muyassar,wanda ya dawo nan tun bayan kammala karatunsa na tertiary da ya yi a abroad, Abba ya buɗe masa babban Company ya naɗa shi CEO
Yana zaune yana duba wasu file yana shan green tea ɗin da ya sa a dafo masa ya ji knocking,da farko ya yi tsammanin Shaheeda ce, wadda ta ce zata kawo masa abincin da ta dafa masa,don haka ko kallon sashen bai yi ba ya ce"come in!"
Shiga ta yi tana girgiza jikinta cikin salon jan hankalin ɗa namiji, yadda ta lafta turare da yadda ya ji ba'a yi sallama ba ya sa ya ɗaga kai da sauri yana kallonta,ya ɓoye mamaki da ɓacin ran da ya ji sun saukar masa a lokaci ɗaya ya bi ta da kallo, kafin ya dake ya ce"welcome!"
Murmushi ta yi ta samu waje ta zauna,ta zare siririn mayafin da yake kanta, dogon gashin ta ya sauka har bayanta,a hankali ta cire rigar da take jikinta ta after dress tana kallonsa tana murmushi
Fuska a ɗaure yake kallonta, kafin ya ce"lafiya dai ko?"
Cikin narke murya ta ce "ziyara na kawo maka,na zo taya ka hira"
Taɓe baki ya yi sannan ya ce"na gode,amma da kin ɗan koma, kin ga aiki nake yi,idan na gama zan zo na same ki"
Tana shirin yin magana Shaheeda ta yi sallama,ya ɗaga kai yana kallonta yana amsawa da murmushi akan fuskarsa, ta ƙaraso tana gyara riƙon tray ɗin hannunta
Tashi ya yi ya amshi tray ɗin yana murmushi yana faɗin "birthday girl!
Ya taron?"
Dariya ta yi ta ce "kai yaya!
Wani ma ya ji fa sai ya ce ba da kai aka sha shagali ba,ka cinye min cake,don ma dai kai ka siya"
Dariya ya yi ya ce"ba zan kula ki ba Fatsima,ya gajiya?"
Harararshi ta yi tana tura baki ta ce"nice Fatsima?"
"A'a ba ke ba,waccan"suka yi dariya a tare cike da nishaɗi
Zama suka yi suka fara cin abincin da ta kawo a tare, Arfa da ta ƙule ta bi su da kallo ta kawo wuya,ta dube shi cikin fushi ta ce"amma Muyassar wannan wanne irin wulaƙanci ne?
Na zo wajenka amma za ka bagarar da ni kana kula wannan yarinyar mara kunya mara tarbiyya!"
Muyassar ya dube ta,amma kafin ya yi magana Shaheeda ta yi shewa ta ce"cassss!
Wato ma nice mara tarbiyya ba ma ke ba ko?
Ko don an ce gwano baya jin warin jikinsa?"
Rai a ɓace Arfa ta kalli Shaheeda ta ce"ke yi min shiru kafin na ɗauke ki da mari,mara kunya mara tarbiyya kawai!"
Muyassar ya riƙe hannun Shaheeda da sauri yana faɗin"enough Shaheeda,bana son sake jin wani abu daga bakinki idan har na isa da ke,kuma idan har kina amfani da tarbiyyar da Ummeey ta ba ki"
Shaheeda ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce"kuma fa maganarka gaskiya ne babban yaya,idan ina da tarbiyya babu dalilin da zai saka na rinƙa kula karnuka suna yi min haushi,kai ma ya kamata ka san yadda za ka yi da su kar a gansu a tare da kai mutuncinka ya zube"
Muyassar ya dafe kai ya bi Shaheeda da kallo cike da takaici,bai yi mamakin wannan ɗanyen aikin nata ba in dai ita ce, abin da ya fi haka ma zata yi, saboda sam bata taɓa barin bashin magana a rayuwarta,bata da haƙuri ko kaɗan idan aka taɓo ta,a hakan ma don Ummeey tana tanƙwarata ne
A nutse ta juya zata fita, Arfa da ta je ƙarshe ta shaƙo mata wuya, ba tare da ɓata lokaci ba suka kacame da dambe,don duk da cewa Arfa ta girmi Shaheeda da wajen shekaru huɗu zuwa biyar hakan ba ya ba wa Shaheedan tsoro ko kaɗan
Da ƙyar Muyassar ya raba damben, sannan ya ja Shaheeda gefe ya rufe ta da faɗa
"Ba cewa na yi ki yi shiru ki wuce ba?
Ke dole dai sai kin nemi magana hankalinki zai kwanta? wai meyasa ba ki da haƙuri ne ko kaɗan?a haka kike son ki tafi Belgium ɗin da wannan shiriritar?
To su ba za su ɗauka ba,idan kika yi musu wannan rashin hankalin zane ki za su yi,silly girl kawai!!"
Tana huci ta ce"amma yaya kana kallo ta rufe ni da duka ko?ko ni jaka ce irinta da zan rufe idanu ta rinƙa dukana?
Wallahi ko yanzu ta sake dukana sai na rama!"
Arfa da ke gefe tana mayar da numfashi,don bata saba dambe ba,ta ce"sai dai uwarki ce jaka,ba ni ba"
Babu ɓata lokaci Shaheeda ta ce"uwarki ta fi kama da jaka wadda babu abin da ta iya sai sakin ki kamar tinkiya kina liƙewa maza"
Muyassar ya buge mata baki ya ce "ba na ce ki yi shiru bane Shaheeda?"
Ƙwalla tana taruwa a kwarmin idanunta,amma don masifa da ƙi-faɗi ta hana ta zuba ta dube shi tana kumbura fuska ta ce"to ba kana jinta tana zagin uwata ba sai na zuba mata idanu?
To wallahi ta sake zagina sai na dake ta"
Muyassar ya dafe kai ya ce"Shaheeda wuce cikin gida,bana son ɓacin rai "babu musu ta wuce tana waƙar"mai wasa da maza karya! tunda na ganta na raina ta"
Girgiza kai kawai Muyassar ya yi, cikin ɓacin rai ya mayar da kallonsa ga Arfa wadda ta sake ƙanƙance idanu alamun Masifa, saboda waƙar da ta ji Shaheeda tana yi,amma kafin ta fara magana Muyassar ya daka mata tsawa
"What's wrong with you Arfa?
Kin zo kamar abin arziƙi kin kama dambe da Shaheeda?wannan wacce iriyar wauta ce?"
Cikin ɓacin rai ya ce"oh duk zagi da maganganun da ta gaya min ba ka gani ba sai nawa da na so sauke mata dattin kanta?"
Kai tsaye ya ce"na san me nake yi Arfa, lokacin da Shaheeda ta shigo parlourn nan ko kallonki ba tayi ba,amma sai da kika shiga sabgarta kika janyowa kanki magana"
Kuka Arfa ta saka ta ce"lallai ma Muyassar!
Wato goya mata baya za kayi ko?
Na gode!"ta miƙe a fusace ta bar wajen,shima ya ja tsaki sannan ya zauna don fara abincinsa da ya fara sandarewa
Ita dai Shaheeda bata sanar da Ummeey abin da ya faru ba,asalima ko a fuska bata bari wata alama ta bayyana ba, musamman ma da ta samu ta rama abin da Arfa ta yi mata, wannan ya fi komai yi mata daɗi
Ita kuwa Arfa tana kuka ta shiga sashen Hajiya Ruƙayya, Hajiya Ruƙayya ta ɗago daga sakawa Usman diaper da take yi ta zuba mata idanu da mamaki, Arfa tana shiga ɗakin ta zube a gefen gado tana gursheƙen kuka
"Me kuma ya faru?"
"Aunty ba ki ga irin wulaƙancin da Muyassar ya yi min ba saboda waccan tsilar koɗaɗɗiyar yarinyar
Har zagina fa ya yi ya hankaɗa ni waje, gaskiya ni ba zan iya lamuntar wannan rashin mutuncin ba"
Hajiya Ruƙayya ta ce"a'a dole gaskiya a ɗauki mataki kam,kuma ke ma ai sai da na ce ki bar komai a hannuna,za mu tattauna da uwar amma kika ƙi,idan kuma kika cigaba da zuwa yana ci miki mutunci ni babu ruwana"
"Amma aunty kin san irin son da nake yi masa,kuma shima ba ga alamu yana so na,kawai wani ƙulumboton waccan tsinanniyar yarinyar da uwarta suka yi ya guje ni"
"Idan ma ƙulumboton ne ni na san yadda zan yi ai
Yanzu ki kwantar da hankalinki,da kaina zan yi masa magana in sha Allah,idan kika ga bai aure ki ba to sai dai idan mutuwa ya yi,amma in sha Allah aure tsakaninku kamar an yi an gama ne
Ki daina damuwa da wannan ƙwailar yarinyar, saboda ko da ace sonta yake yi kamar yadda kike zargi ni na san Mahaifiyarsa ba zata taɓa bari ya aure ta ba"
Wata wawiyar ajiyar zuciya Arfa ta yi,ta ce"ko aunty?
Amma menene dalilin?"
Kai tsaye Hajiya Ruƙayya ta ce"babu jituwa tsakanin Hajiya Zainab da Hajiya Sa'adatu ne,shine dalilin
Shekarun baya da Hajiya Sa'adatu ta zauna anan Alhaji ya fifita matarshi akanta, shine ya sa take jin haushinta "shiru Arfa ta yi tana taɓe baki
Daga lokacin babu wanda ya sake shiga harkar wani tsakanin Shaheeda da Arfa, musamman da Muyassar ya samu Shaheeda ya yi mata faɗan duk abin da Arfa zata yi mata kar ta sake tayar da kai ta kalle ta, murmushi dai kawai Shaheedan ta yi masa a lokacin,amma ta gama ƙudurcewa a ranta duk lokacin da Arfa ta sake shiga harkarta sai ta ganar da ita kurenta, don wallahi sai ta yi mata duka a tsakiyar gidan,sai dai komai zai faru sai ya faru daga baya
Sai kuma aka yi sa'a babu wanda ya sake shiga harkar juna a cikin su biyun,asalima kwanan Arfa biyu da zuwa ta koma gidansu
Tafiya ta miƙa, lokaci ya yi ta ƙaratowa na tafiyar Shaheeda zuwa Belgium, murna da farin ciki kuwa a wajen Shaheeda ba'a magana,ji take yi babu ya ita a farin ciki,ga Muyassar mai sake zuga ta
Sai dai a matan gidan babu wadda take farin ciki da wannan tafiyar,amma babu halin bayyanawa,duk da cewa Shaheeda ta san da cewa ummeey bata son tafiyar Tata amma ko a jikinta
Kwana biyu ya rage jirgin su Aneesa ya ɗaga zuwa garin Ghent da ke ƙasar Belgium inda zata fara karatunta na course ɗin software engineering,idan Muyassar yana kiranta da software engineer har wani blushing take yi
Yau zata koma kasuwa don siyan kayan tsarabarta kafin ta saba da Belgium,dangin su chaculate da biscuits da suka zama sune farin cikinta, Muyassar baya nan,yana gidansu,don haka ta kira shi a waya,kai tsaye ya ce ta biyo ta gidansu sai ya kai ta
Driver ne ya kai ta har bakin gate ɗin,ta kalli drivern ta ce"baba Nuhu kawai ka tafi, babban yaya zai dawo da ni idan mun gama"
Drivern ya ce "to babu matsala Hajiya"Shaheeda ta fice daga motar ta kutsa kai cikin gidan
Hajiya Sa'adatu mahaifiyar Muyassar tana zaune a parlourn,tare da innayyo,kakarsu,ta daɗe da sanin su dukkansu babu mai ƙaunarta,amma ko a jikinta,tana ganin yadda mahaifiyarta take kuka saboda sun yi mata wani abin,amma ita gani take yi Ummeey bata yi niyyar ramawa bane,ta kan ce"gaskiya Ummeey wani lokacin gani suke yi kin cika yi musu shiru shiyasa suke yi miki abin da suka ga dama,amma wallahi da ni ce babu wadda ta isa ta taka ni ban murza ta ba,ko wacece kuwa, innayyo kawai zan iya ɗagawa ƙafa darajar auren ɗanta da nice ke"
Ummeey ta kan ce"ke ƴarinya ce Shaheeda,da kin gane da kin ɗauka, haƙuri shine komai, shine maganin komai,da sannu komai zai wuce, duniyar ma nawa take?"Shaheeda ta kan taɓe baki, wannan azancin na Ummeey ba wani gane kansa take yi ba
Sau uku tana yin sallama amma babu mai niyyar amsa mata,asalima cigaba da hira suka yi tamkar ba su san da Allah ya yi halittarta a wajen ba, Shaheeda ta taɓe baki ta ce"Allah ma ya gani na yi domin shi"ba tare da tunanin komai ba ta kutsa kai cikin falon ba tare da ta sake yin wata sallamar ba
A fusace Mummy mahaifiyar Muyassar ta ɗago tana kallonta kafin ta ce"mara tarbiyya uban wanene ya ba ki izinin shigowa cikin falon nan?"
Tana da abin faɗa,amma sai ta danne ta ce"yaya Muyassar ne ya ce na zo zai kai ni kasuwa,za mu ƙarasa siyayyar da za mu tafi Belgium "aunty Salma da ta shigo ta yi ƴar dariya tana faɗin "ai kuwa bakin naki ya iya faɗar Belgium ɗin!
Ke dai ubanki ya dage sai kin bar ƙasa,bayan ga makarantu nan masu kyau a Nigeria,to Allah ya bada sa'a,don Allah kar ki ba su kunya Shaheeda, kin ga dai uban kuɗin da ya kashe wajen nemar miki gurbin nan"ta karasa magana tana zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon
Shaheeda ta yi murmushi,amma kafin ta yi magana a fusace Mummy ta ce"wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar dama kin daina bata bakinki Salma,amma ni ban ga alamun wani karatu da za'a yi anan wajen ba, sannan ki tashi ki fice daga gidan nan idan dai ba na ubanki bane"
#Nusy_bee