GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 19

by @nusybee143

Page 19


Ƴar dariya Shaheeda ta yi tana faɗin "A'a fa Mummy,gida dai na ubana ne,kawai dai ba'a ciki yake ba ne,kuma ma,ni da na zo don na tafi?ai tafiya tawa ce"

Bin ta suka yi da kallo cike mamaki da takaici,sanannen abu ne cewa Shaheeda bata da kunya,shine dalilin da ya sa kaf matan ubanta babu mai ɗaga mata yatsa,amma ba su yi tsammanin zata iya kallonsu ta yi musu wannan wulaƙancin ba

"Ke Shaheeda!uwata da yayar tawa kike gayawa magana?ba ki da kunya?"

Yatsina fuska ta yi ta ce"aunty yi haƙuri"

Mummy cikin kufula ta ce"sai na yi maganinki mara mutunci matsiyaciya kawai!

Shegiya mara amfani"miƙewa ta yi tsaye tana mayar da wayarta jaka tana faɗin "a'a fa Mummy!ina da amfani wallahi"daidai lokacin Muyassar ya shigo 

A kunnensa ta faɗa,don haka a kufule ya fara faɗin "Shaheeda mahaifiyata kike yi wa rashin kunya?"

Babu tsoro ko shakka ta ce "cewa ta yi bani da amfani,ni kuma na san ina da amfani,ni gida ma zan tafi ba zan zauna a rinƙa tsine min ana kwashe min albarka ba,bayan uwata da ubana ba su kwashe min ba,sai anjumanku"ta wuce ta gaban Muyassar ta fice daga parlourn,suka bi ta da kallo

Shima bin ta ya yi ganin ta ɗauki hanyar gate,ya ce"Shaheeda dakata anan,idan kika fice daga gidan nan sai na yi mugun saɓa miki"babu musu ta ja ta tsaya fuska a murtuke 

Mota ya koma ya ɗauko,yana zuwa daidai saitin da take ta buɗe ta shiga tana kumbure-kumbure

Faɗa ya yi ta yi mata har suka isa super market ɗin da za su je,sai huci take yi amma bata yi magana ba,shima daga baya ya gaji ya yi banza da ita

Duk da fushin da take yi hakan bai hana ta sakin jiki ta yi siyayyarta ba, Muyassar ya biya kuɗin suka kwashi kayan zuwa mota 

Har cikin gidan ya shigar da motarshi,har suka shiga babu wanda ya yiwa wani magana,sai da ya tsayar da motarshi ya juya yana dubanta,ko kallonshi bata yi ba ta fara yunƙurin buɗe motar ta fita 

Naɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana kallon yadda take ta kokawa da mota, saboda bai cire lock ba,kuma ta san da hakan,amma saboda neman magana irin nata take ta kokawa da motar 

"Zan fita,ka buɗe min motar"ta faɗa tana sake ɗaure fuska 

"Ba zan buɗe ba, ba kina da hannu ba? buɗe da kanki"

Tura baki ta yi,ya sauke numfashi sannan ya kira sunanta"Fatima!"

Tana kumburi ta ce "na'am!"

"Ba ni hankalinki my Teema"

Bata yi magana ba ta juyo amma bata kalle shi ba,ya fara yi mata nasiha cikin nutsuwa da kwantar da kai,ta yi shiru tana jin shi, duk da cewa jin shi kawai take yi,amma gaba ɗaya nasihar iska take bi 

Sai da ya ga alamu kamar bata tare da shi sannan ya ce"Shaheeda anya kina ji na kuwa?"

Gyara zama ta yi ta ce"ina jin ka mana,ka ce na daina faɗa manya suna faɗa ko?ko da ace sune suka yi min laifi na yi haƙuri"sai kuma dariya ta ƙwace mata, don maganar tashi gaba ɗaya a gwaranci ma take jin ta

"Au dariya ma na ba ki Shaheeda?

Ina magana kina yi min dariya?"

Girgiza kai ta yi tana murmushi ta ce"a'a,wani abu na tuna,na gode yayana "kallonta kawai ya yi yana girgiza kai,ya san halinta abu ne mai wahala ta sauya 

Tana shiga part ɗin su kai tsaye ta wuce zuwa ɗakinta ta ajiye kayanta,ta fito tana ƙokarin kiran Ummeey, wadda ta san bata nan,tana gidan aminiyarta Hajiya jameela, wadda ta zama tamkar ƴar'uwarta uwa ɗaya uba ɗaya 

Bugu biyu ta ɗaga,ta shagwaɓe fuska tana faɗin"Ummeey har yanzu ba ki dawo ba?"

"Ke bana son iskancin nan naki!ke ba yanzu kika dawo ba?kar ki ɓata min rai,ki ɗauki abinci ki ci, sannan ki ƙarasa gyara min kitchen ɗina,sai na dawo"ta kashe wayar

Shaheeda ta miƙe tana murmushi ta ce"wai abinci,sai ka ce wata cus!ga chaculate da yaya ya siya min me zan yi da wani abinci?"ta ɗebo chaculate ta dawo parlourn ta kunna TV tana kallo tana cin abinta 

Da daddare bayan ta idar da sallar isha'i, tana zaune akan dardumar tana game a wayarta Ummeey ta leƙo,ta dube ta ta ce"Shaheeda sako hijabinki,ki zo abbanku yana son ganinki"babu musu ta miƙe,ta janyo hijabin da ta yi Sallah ta saka,suka fice zuwa sashen mahaifinta Alhaji Yusuf 

Da sallama suka shiga parlourn abban nata, Shaheeda ta bi mutanen parlourn da kallo,bata yi mamaki ba,don ta san hakan zai iya faruwa dabam

Ummeey ce dai ta tsorata, saboda da ganin yanayin fuskokinsu ta san akwai abin da ya kawo su wanda ba mai daɗi ba, musamman da ya kasance Shaheeda ta je gidan nasu yau 

Har ƙasa ummeey ta kai ta gaida innayyo, wadda ta amsa ciki-ciki,ta dubi Hajiya Sa'adatu da fara'a tana faɗin "maraba da zuwa Hajiya!

Sannunku da zuwa"

"Yawwa sannu! yarki ce ta ɗago mu ai"ta bata amsa kai tsaye 

Hajiya Zainab ta samu kujera ta zauna tana kallon Shaheeda da ta zauna a kan carpet ɗin parlourn ta ce"kayya! Allah ya sa dai lafiya"

"Duk wani abu da ya danganci wannan iblishiyar ƴar taki ai ba na lafiya bane Hajiya Zainab, Allah ya kyauta dai"da sauri Hajiya Zainab ta kalli Shaheeda, wadda ta yi tamkar bata ji abin da Hajiya Sa'adatu ta ce ba,itama ta ja bakinta ta yi shiru 

Alhaji Yusuf da ya gama amsa waya yanzu,ya dawo da hankalinsa kan mutanen parlourn yana kallon Shaheeda da ta takure waje ɗaya kanta a ƙasa,ya ce"ke Shaheeda ba ki iya gaisuwa bane?"

Babu musu ta fara gaida innayyo, innayyo ta yi mata banza,bata damu ba ta gaida Hajiya Sa'adatu,caraf Hajiya Sa'adatu ta ce"Shaheeda ai ni yanzu ai ban isa komai ba,tunda ban wuce ki kalle ni ki zage ni ba"

Ko a jikin Shaheeda, Abba ya dube ta cikin fushi ya ce"wato Shaheeda nunawa duniya kike yi mu mutanen banza ne ko?

Mahaifiyar tawa da ƴar'uwata za ki je har gida ki zaga?"

Hankali kwance ta riƙe haɓa ta ce"tooo! Abba yaushe aka yi haka kuma?

Kowa fa ya san ba na zagin babba,kuma kai ma ka san haka Abba "

"Au ƙarya aka yi miki tabbatacciya?"a cewar innayyo cikin fushi, Shaheeda ta yi kamar bata ji ta ba, innayyo ta cigaba da magana a fusace 

"Wato dai ba ki da ishashshiyar tarbiyya,na yarda da hakan tabbas,ke kuma jarrabawar da kika samu kenan,rashin tarbiyya,amma wallahi Zainab ba ki kyauta mana ba wallahi"

"A'a fa innayyo!babu ruwan uwata,ya kamata ku rinƙa adalci,ba komai zai faru ku rinƙa ɗaukar alhakin baiwar Allah ba"

"Ke Shaheeda! Shaheeda!!a gabana kike ƙaryata mahaifiyata?

Irin rashin albarkar da kike yi kenan?"

Kai tsaye ta ce"yi haƙuri Abba, Allah ya huci zuciyarka"

Hajiya Sa'adatu ta ce"shegiya ƴar banza annoba!"

"A'a fa Mummy,da ubana dai gashi kina gani, sannan kuma idan ni Annoba ce....."dukan da Abba ya kai mata ne ya sa ta yi shiru tana shafa fuskarta da ta sha mari, Abba cikin fusata ya ce"jaira kawai mara kunya,tashi ki bani waje "babu musu ta miƙe ta fice daga sashen hankalinta a kwance 

Tana fita gaba ɗaya parlourn aka mayar da akalar faɗan kan Hajiya Zainab da take zaune cikin fargaba,babu kalar maganar da innayyo bata faɗa mata ba, don ma dai Alhaji Yusuf yana tausarta, kuma ya hana Hajiya Sa'adatu magana 

Ranta a ɓace ta koma sashenta,kai tsaye ta nufi ɗakin Shaheeda wadda tuni ta manta abin da ya faru ma, chat ɗinta take yi da ƙawayenta tana sanar musu lokacin tafiyarta zuwa Belgium,sai ga ummeey ta banko kofar 

Tashi zaune ta yi tana kallonta, kafin ta nemi ba'asi Ummeey ta fara sauke mata mari a fusace,sai da ta yi mata biyu sannan ta fara masifa cikin fitar hayyaci 

"Shaheeda kashe ni kike son yi kenan?

Ke yanzu ba za ki zame min sanyin idanu ba?ke kenan a cikin neman masifa,kawai burinki ki ganni ina ɓacin rai? da gaske annoba kike son zame min?

To wallahi idan kika cigaba da yi min wannan halin sai kin fasa tafiyar, tunda da alamun ma idan kin je can abin da za ki rinƙa yi kenan, shashasha kawai!"ta fice cikin ɓacin rai 

Ƙwalla ta fara taruwa a idanun Shaheeda tana ƙoƙarin mayarwa, ɗabi'arta ce tun tana ƴar ƙaramar yarinya bata taɓa yarda ta yi faɗa ta yi kuka ko da ace an yi galaba akanta, yanzu kuma kuma bata kuka akan duk wani mutum da ta tabbatar ta fi shi gaskiya 

Wayarta ce ta yi ƙara, ganin Muyassar ne sai ta ɗaga ta kai kunne tana sauke numfashi, Muyassar yana jin yanayinta ya kwantar da murya ya ce"da wani abu ne Shaheeda?"

"Ummeey ce ta mammare ni saboda su innayyo sun ce bani da tarbiyya na ce ina da ita"

"Kayya!ke ma bakinki ba ya bari ki ci riba,kai mata wayar mu yi magana"a kufule ta ce"itama tana da waya"

Ƴar dariya Muyassar ya yi,ya ce"haka ne,to bari na kira ta"kafin ma ya rufe baki Shaheeda ta kashe wayar ta 

Muyassar kuwa haƙuri ya yi ta bawa Ummeey yana gaya mata gaskiyar abin da ya faru lokacin da Shaheeda ta je gidan, Ummeey ta ce"ni ba wani abu nake jiyewa Shaheeda ba,mace ce, watarana zata yi aure,zata tafi gidan wani da wannan tsinin bakin ne?

Ga taurin kai da gardama har ta yi mata yawa tun tana ƙaramarta, gashi sam bata da kunya ta yi ta ja min magana,ya kamata ka rinƙa yi mata faɗa "Muyassar ya rissina kamar wadda take gabanshi ya ce"in sha Allah Ummeey zata daina, yarinta ce kawai"

"To Muyassar, Allah ya sa hakan"

Muyassar yana ɗan murmushi ya ce"Ameen Ummeey "

Washe gari da neman magana Shaheeda ta tashi, saboda baƙin cikin abin da aka yi mata jiya, shiyasa yau take neman wanda zata huce akanshi,don haka bayan ta gama karyawa ta koma wajen lambun gidan ta zauna 

A wajen lambun gidan sashen Hajiya Atika, wadda suke kira da Ammi yake,kaf gidan ta fi kowa yara,kuma ta fi son yara 

Tana zaune tana jin waƙar Alingo ta p-square tana bin waƙar Safwan ya zo zai wuce,yana ganinta ya yi murmushi ya ce "su yaya Shaheeda yan ƙasar Belgium"

Yana direwa ta ɗora"su Safwan yan zaman gida Nigeria "

Safwan ya ce"ai nima Ammi ta ce ina kammala karatun secondary za'a kai ni ƙasar waje na yi karatu "

Shaheeda tana murmushi ta ce"ai dole ka je yaro tunda kishiyar gidanku ta je,kai dai ka buɗe ƙwakwalwar ko sau ɗaya ne don ka samu Sa'a ka tafi,ka san Abba ba ya biyawa daƙiƙi kuɗin makaranta har ƙasar waje,amma ni ka ga mahaifiyata na biyo"da kallo Safwan ya bi ta, kafin ya ce "ai nima ba daƙiƙi bane,kuma nima mahaifiyata na biyo"

Ƴar dariya ta yi ta ce "kayya!yaro man kaza,kai dai je ka,kar allura ta tono garma"babu musu Safwan ya wuce zuwa sashensu 

Ƴan mintuna da shigarsu sai ga Ammi ta fito riƙe da hannun Safwan fuskarta a ɗaure, hankali a kwance Shaheeda ta ɗaga kai ta kalle ta, Ammi ta ƙaraso tana faɗin "ke Shaheeda! menene manufar tambayoyin da kika saka yaron nan a gaba kina yi masa?

Wanne irin sakarci ne hakan?"

Yatsine fuska ta yi tana yi mata kallon hadarin kaji ta ce"tambaya kuma?

Ni?kuma a ina ma tambaya ta zama laifi?na tambaya an ba ni amsa, menene abin da ya kawo tuhuma kuma?"

"Ke yarinya!

Dama ana faɗin ba ki da kunya ba ki da tarbiyya,to ni na fi ƙarfin in yi da ke sai dai da uwarki,yar banza mara mutunci "

"A'a ni ɗin dai,nice nake da lokacinki,amma dai ita waccan da kike ambata ki bar ta ta ji da abubuwan da suke gabanta, ƙasar waje ce dai sai na je,duk da zuga da busa da zungure da hankaɗe da ake yi wa malam Yusuf,babu mai shiga tsakanin hanta da jini,ni da ubana kenan"ta miƙe tana waƙar hanta da jini ba sa rabuwa ta wuce sashensu zuciyarta fes 

Hajiya Atika ta bi ta da kallo tana auna mata zagi,amma ita ko a jikinta, tunda dai ta samu inda ta juye nata ɓacin ran ai shikenan 

Yau ma dai tana zaune bayan isha'i tana game a laptop ɗinta da Muyassar ya siya mata sai ga Ummeey fuskarta a haɗe,ta ɗaga kai tana kallon Ummeey gabanta yana faɗuwa,a duniya babu mutumin da take tsoro,take shakkar ta ga sauyin fuska a tare da shi kamar Ummeenta,ko mahaifinta da ya kasance mafaɗaci bata damu da sauyawarsa ba kamar ta Ummeenta,don haka ta cigaba da bin ta da kallo gabanta yana faɗuwa 





#Nusy_bee