BARRISTER SUHAIL

39

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----39 

Duk wani ɗaga murya da Iman keyi wa suhail bai kulata taba kuma bai buɗe kofar ba bakin gadon ta koma ta zauna ta dafe kan ta ji ya soma juya mata. 

a hankali ya koma kusa da ita 

shiru ya ratsa dakin 

iman ta tsaya tana kallon sa cike da bacin rai 

"ko kazo ka fadamin cewa kana so ka koma dakin matar ka har abada?"

dukar da kansa yayi yama rasa wani uzuri zai bata wanda zai sa ya shafe laiifin a wajenta na kusan watan daya kwashe a dakin zeenah

"iman ki fahimceni nasan nayi kuskure Please accept my apology hakan bazai kara faruwa ba in sha Allah"

"Suhail idan ka ga dama ka kare Rayuwar ka gaba daya dakin zeenah,Amman ka sani Allah baya goyon bayan zalinci matukar bani na yafe maku ba haƙƙina zai tsaya tsakanin ku ranar gobe kiyama"

tabbas sun kure haƙurin iman tunda har zata iya rufe ido ta bata masa irin Wannan maganganun

ya rasa miyake masa dad'i

kwanciya yayi akan gadon zuciyar chunkushe da abubuwa marassa dad'i 

iman ta dauki pillow ta koma ƙasa 
 ta kwanta 

kiran da zeenah ke mashi ya farkar da shi daga dogon baccin daya sauke sa ya manta rabon da yayi bacci mai dadi irin haka kullum yana fama da jarabar zeenah har mamaki yake ita wata irin macece da bata gajiya da Abu daya kullin cikin nemansa take abinda iman bata yi matukar bashi ya neme taba bazata taba naiman saba,koda shi ya nemeta kullin cikin nuna masa gajiyar ta ke duk halin da yake ciki sai dai ya haƙura dan baison abinda zai takura mata 

ganin kiran yaƙin
 karewa ya daga ransa a bace"zeenah what again"

"babe na kasa bacci tsoro nake ji"

"wani kalar tsoro please ki gyaleni na lura a dole sai kin kaini wuta"


kuka ta fashe dashin"please babe wallahi da gaske nake na kasa Bacci"

abinda bazai iya jura ba kukan mace kuma baisan Dalilin tsoron nata ba haka ya tashi a hankali ya buɗe kofar ya fita a hankali gudun kar iman taji sa 

ba tare da yasan duk wayar da sukayi da zeenah akan kunnen 
iman babu abinda bata ji ba 

kofar tabi da kallo idan har suhail yana tare da zeenah bazai taɓa samun natsuwa a rayuwar sa ba ta tashi tayi Alwala ta fara sallar har sai ta ji ta fara jin alamun bacci ta kwanta 

hasken ranar da ya shigo dakin ya farkar da ita daga dogon bacci da takeyi da mamakin ta kalli agogo karfe bakwai da sauri na nufi bathroom tayi alwala tayi sallah

tana idarwa ta fara gyaran daki kamar  electric burner ta kunna ta saka turaren wuta a hankali kamshin ya cika ko ina har part din Suhail kamar anan aka kunna shi 

koda ta gama ta shiga wanka ta shirya cikin wani farin laces dinkin doguwar riga tayi light make up tana daura dankwali Suhail 
ya shigo cikin shirin fita unguwa 

yi tayi kamar bata san da zuwan saba ta cigaba da daurin ta 

suhail ya ce"Iman zamu fita da zeenah ko kina bukatar wani abu"

kai ta girgiza alamun babu 

tana jin fitowar su da zeenah dake ta faman zaba masa surutu har suka fita 

iman dake tsaye taji an chaki kamar an zuciyatar da mashi 

 "ya salam"

Ta furta a hankali tana ƙoƙarin kawar da tunanin Suhail daga cikin zuciyarta 

A gefe guda kuwa, Suhail yana zaune cikin mota amma hankalinsa gaba ɗaya yana wajen iman 

Tun daga yadda ya same ta cikin farin lace, da yadda ta ƙi kallon sa ko sau ɗaya 

zeenah dake front seat sanye da riga da siket na Atamfa duk ya kamata ga sani karamin chantily veil ta yafa sai taunar cingum take 

tana lura da suhail tun sanda suka fito ya chanza babu wata walwala a tare dashi 

"babe lafiya kuwa"

"Zeenah i'm feeling headache ko zamu bar fitar nan zuwa sani lokaci"

hade rai tayi

"ban yarda ba idan ma bazaka iya driving din ba i can Help"

mukulli motar ya miƙa mata sukayi exchange  zeenah taja motar suka yi gaba zeenah bata tsaya ko ina ba sai bakin wani babban store da ake siyar da atamfo da laces wanda kaf Abuja babu inda ake kawo kayan ƴan gayu daya wuce nan Suhail ya kalleta dan bata faɗa masu nan zasu zo ba 
"zeenah mi kuma zamuyi anan"

"babe akwai kayan da zan duba"

fita tayi suka karasa ciki shagon wajen da yafi ko ina kaya masu tsada ta nufa laces da atamfa da material ta kwasa sai da ta cika chart dasu tamkar nai shirin hada lefe 

suhail da ya gaji waje ya samu ya zauna bayan ta gama hada wa akayi masu lissafin kudin sama da miliyan biyar Suhail ya ce"zeenah kudin kayan nan sunyi yawa"

"haba babe its just five million shine kake cewa sunyi yawa idan bana kwalliyar ina kyau ai kaima bazan birge ka ba"

bashi da zabin da ya wuce ya siya kayan ,zeenah duk wani kyalekyelen duniya count her in tanason rayuwar karya dan mutunta kai komai nata very expensive and classiq take yin sa indai maganar ado da gayu zeenah can take first 

zata iya kashe ko nawa ne ta siya kayan gayu ita kanta batasan adadadlin suturar  ta ba idan Yanzu taga kaya ya birge sai ta siya ban da da Mummy dakw taka nata birgi ki sa abinda yafi haka

 baka taɓa ganin  ta da karamar sutura kullum cikin saka sababbin kaya kake duk yadda ka kai da sanin ta bata ka taɓa ganin ta maimaita kaya ba duk min tsadar da tayi sawa daya ta wuce da wurin ta 

duk tsadar kaya indai yayi mata kyau bata shakar sayan sa 

haka Suhail ya biya kudin kayan gaba daya aka masu packaging suka saka a mota suka bar wajen 

wani haɗaɗɗen resturant ta kaisa tayi masu ordern abincin da snacks pizza Shawara bugers da duk wani kayan kwalam haka aka jibe masu akan table 

duk cin da sukayi basu ci rabin abinda aka kawo masu ba bayan sun gama zeenah ta dauko dollars ta biya su ko ta kan change ma bata bi ba 

haka suka wuni yawo a garin Abuja har Magariba kafin suka dawo gida 

Iman na zaune kan Prayer mat gama sallar ta kenan tana azkhar taji shigowar motar su bakin window ta koma taga zeenah na fito da kaya niƙi-niƙi mai aikin ta jennifer ta kira ta shigar mata dasu ciki 

sakin labulen tayi ta cigaba da Azkhar din ta har aka gama sallar isha'i ta tashi Kitchen ta shiga ta dafo indomie da tea ta koma ciki 

tana zaune wayar ta dake kan side bed ta soma Ringing kiran Hafsat ne ya shigo bayan sun gaisa hafsat ke shaidawa Iman cewar gobe zato zo Abuja

wani irin faduwar gaba taji bawai bataso Hafsat tazo gidan ta bane bataso tazo taga halin da take ciki gata dai a gidan miji amman bata da maraba da wacce ke gaban iyayen ta ita ba sakakka ba ita ba matar aure ba,gaba daya miji baya ta ta ta 

shirun da tayi yasa jikin Hafsat yin sanyi 
"iman kinyi shiru"

murmushi tayi ta ce"ba shiru nayi kawai i'm just wondering kece zaki zo gidana bayan koda ina kaduna baki zo ba"

Hafsat ta ce"kinsan komai sai Allah yayi yanzu ba gashi nace zanzo ba"

iman ta ce"Allah ya kaimu lafiya hafsat"

Ajiye wayar tayi karon Hafsat da Zeenah kawai take tunani matukar zeenah tayi wa Hafsat koda kallon banza ne baza ta jura ba sai tayi magana hafsat bata da haƙuri ko kadan ko da suna primary kullin sai sunyi faɗa ko sun ce gidan su daya da iman mutane  mamaki suke kwata-kwata halin su ba iri daya bane an sha fada da iman sai dai Hafsat ta shigar mata bata da aiki sai kuka hakan yasa kowa ya rainata a makarantar duk abinda akayi sai ace iman 

washe gari tun da safe Iman ta fara shirin tarbar Hafsat tun safe ta shiga Kitchen sai wajen Azahar ta kammala 

duk fitowar da Zeenah zatayi sai taga iman a Kitchen bata taɓa ganin ta ta jima haka a wajen ba tunani ta ke a ranta ko dai suhail ya saka ta 

ganin bata amsar tambayar ta koma ciki tana jiran dawowar sa 

Bayan iman ta gama ta koma daki tayi wanka ta saka wata Black abaya tayi rooling karewa kanta kallo tayi a mirror ganin yadda ta rame 

wayar ta dauko ta kira hafsat jin ko ta ƙaraso Hafsat ta ce Yanzu suka sauka a motar tana park Iman ta tura mata da address din gidan 

ba'a fi mintuna talatin ba hafsat ta faɗa tana kofar gate din 

Palorn ta koma ta dauki telephone ta kira dakin mai gadi tana da bakuwa bakin gate 

hafsat na tsaye mai gadi ya buɗe mata shi ya ɗaukar mata jakar har zuwa main palorn na gidan 

da sauri iman ke saukowa daga kan step ta ƙaraso wajen ta wani tsalle tayi ta rungume ta cike da so da kauna 

sun jima a tsaye a haka kafin suka rabu 

iman ta dauki jakar ta suka shiga ciki 

a falon iman ta sauke ta 

Hafsat ta bude baki "Iman kinga yadda kika rame kamar bakya cin abinci babu abinda ake gani a jikin sai katon kai"

murmushi Iman tayi "Hafsat ni ce ma mai katon kan"

Hafsat ta ce"ke baki gani bane ko shi Suhail bai taba fada maki bane"

iman ta tashi ta ce"kinga muje ciki ki huta kici Abinci"