40
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----40
kinga muje ciki ki huta kici Abinci
Da kyar Iman ta lallaba Hafsat zuwa ɗakin ta
koda suka shiga dakin hafsat ta zauna kan kujera sai kare ma iman kallo take tambayoyi ne fal kan bakin ta wanda take jira Iman ta amsa mata su
abinci ta kawo mata hafsat ta ce"iman nasan kema baki ci ba ko?"
murmushi tayi ta ce"anjima zanci hafsat"
haka kawai taci abincin badan ranta yaso ba sai dai tana idan taci Hakan zai sa iman ta amsa mata tambayoyin ta
kadan taci ta ajiye plate ta koma kusa da iman ta ce"iman tunda na shigo cikin gidan na san kina cikin damuwar ki daure ki fadamin Abinda ke damunki"
murmushi yaƙe tayi "hafsat na fada maki ba abinda ke damuna"
hafsat ta miƙe tana gyara zaman mayafin ta ta ce"iman kar ki manta duk duniya baki da yar Uwar data fini mun taso tare tun muna yara tare muke zuwa makaranta muyi wasa tare bacci kadai ke raba mu shima watarana gida daya muke kwana,baki da abokiyar shawara sai ni kamar yadda nima duk matsalar data taso min tare muke warware hawaye ya soma saukowa daga Idanun Hafsat ta ce"yaushe ƙika fara boyeman damuwarki ashe dan kinyi aure zaki manta da shaƙuwar mu bazan iya jurar ganin ki a wannan halin ba dan haka Iman ni zan tafi"
bedroom ta shiga ta dauko jakar ta iman tasha gaban ta wani irin kuka ta fashe dashi ta kifa fuskar akan kirjin Hafsat kuka take kamar ranta zai fita
sun jima a haka hafsat ta zauna da ita kan kujera ta kamo hannunta ta ce"iman ki daure ki fadamin abinda ke faruwa cikin gidan nan"
iman bata boƴe mata komai ba cikin halin da ta tsinci kanta tun bayar auren Suhail da zeenah komai sai da ta fada mata
hafsat ta hade rai ta ce"irin rayuwar da kike kenan shine baki fadawa kowa ba iman so kike ki kamu da ciwon zuciya iman duba kiga You in depreesed taya za'a ce kullum mutun na zaune a daki shi kadai"
cikin kuka iman ta ce"hafsat yaya Suhail bashi da laifi,he is not like that before kawai Akwai ke damunsa nasan in sha Allah everthing will be fine"
murmushi takaici hafsat tayi ta ce"ai nasan bazaki taba ganin laifin saba sai kici gaba da zama har ranar da bakin ciki zai kashe ki"
hafsat tana tausayawa iman halin da take ciki "a kananun shekarun ta bai ci ace ta fara fuskar tar matsalolin miji da kishiya ba duka ma yaushe akayi auren
har la'asar sunan a zaune
zeenah na dakin ta tare taji dawowar suhail da sauri ta miƙe ta gyara zaman dankwalin tun dazu ta shirya take zaman jiransa koda ya shigo haka kawai yaji yana son yaga iman
hakan yasa ya nufi part din ta tana bedroom sai Hafsat a falo tana kallo
da namakin ya kanta zama yayi kan kujerar cikin fara'a baƙuwa mukayi a gidan namu
murmushi hafsat tayi ta ce"yaya Suhail ina wuni"
"lafiya qlau hafsat ya hanya, irin wannan unexpected visit haka"
"murmushi tayi ta ce ai tun jiya Iman tasan da zuwana"
"aiko kinga bata fadamin ba"
murmushi tayi a fili a ranta kuma tana tunanin yadda Suhail yayi pretending kamar komai na tafiya lafiya
Zeenah taji suhail shiru bai shigo ba ta fito daga daki jennifer ce tsaye a dakin tana mopping zeenah ta fito
"jennifer Suhail bai shigo bane"
"mah yana ɗakin iman"
lokaci guda fuskar zeenah ta chanza
"mi yake yi a chan kuma"
"i don't know mah"
tsaki taja bata san lokacin da tayi wa jennifer tambayar ba dan tunda ta shigo gidan tayi mata kashe akan koda wasa kar ta sake ta shiga part din iman
Ba tare da ta sake magana ba ta nufi part ɗin Iman
Tun kafin ta ƙarasa ta hango Suhail
da hafsat suna hira cike da fara'a wanda duk cikin kwanakin bata gansa cikin walwala hakan ba ti wacece wannan din a iya sanin sa bashi da wata kanwa ko yar uwa mai shekarun
tanaso ta sami Amsar tambayar ta haka yasa ta shiga dakin sai taunar cingum take wanda ya zame mata jiki kullum cikin cinsa take
tana shiga sukayi ido biyu da Hafsat hararar ta tayi Hafsat kuma ta kasa sauke idanun akan zeenah tundaga kalar kayan da ke jikin ta da Kuma yadda ta shigo tana taunar cingum ta gama gane ko wacece zeenah dole iman ta fuskanci ƙalubale kala- kala a wajen zeenah domin ta lura idanunta a sanke suke tass
zeenah ta kalli suhail ta ce"babe Wannan kuma daga ina"
"sistern iman ce"
"ohhh no wonder shiyasa na ganta ita ma gatan kamar gudar to ku duk haka dangin ku suke a tsiyace yar uwarki ta baki labarin jar miyar da ake cin shine kema kika zo kici ko thank god mijina yana da kudin da zai cika duka dangin ku idan kuna bukatar Hakan"
Suhail ya kalli zeenah ya ce"leave zeenah"
kallon sa tayi "babe daga na faɗi gaskiya kuma sai kace na fita"
a tsawace ya ce"zeenah idan baki fita ranki zai baci"
fita tayi Suhail ya juya wajen hafsat ya ce"hafsat kiyi haƙuri"
murmushi tayi ta ce"ya wuce ya Suhail"
sun jima suna hira Sallar la'asar ce ta fitar da shi zuwa masallaci
hafsat ta shiga Bedroom din iman zaune ta same tana game
waje ta samu ta zauna ta kalli iman "dama wannan ce kishiyar taki"
iman ta daga kai
hafsat tayi folding hannun ta ta kalli iman
Seriously Iman, dama wannan ce kishiyar taki let me tell You the truth da ke kanki baki santa ba iman
taya kike tunanin zaki sami hankalin Suhail alhali kina boye kanki kullum? ki daina mantawa da cewa ke ma mace ce mai kyau banga da abinda ta Fiki ba a iya classiq din sa yayi haƙuri dake tunda ya samu matar da zata masa ado da Kwalliya ai dole ya tattare ya koma wajenta ya barki da malamantar
da ciwon zuciya a daki"
hafsat faɗa take wa iman kamar zata bige ta tare da nuna mata dabarun rayuwa da kuma yadda zata dawo da soyayya da kulawar mijinta
har dare suka kai suna hira imann ta dafo masu indomie ta kawo masu
hafsat ta ce"iman Suhail din na indomie kika kai masa"
iman ta manta rabon da ta dafa abinci da Suhail shi kansa har ya haƙura amman har cikin ransa yayi kewar daddadan girki ta wanda Zeenah bata masa kullum yana fama da Abincin yar aiki tun yana ƙin ci har ya dawo yana ci dan bazai yi yu kullum yana Hanyar resturant ba
iman ta ce"Hafsat i can't remember time din da Suhail yaci abincina "
zaro ido tayi batayi tunanin abin ya kai haka ba "kin bashi baici bane ko kuma kece baki girka masa ba"
shiru tayi dan bama tasan mi zata ce mata ba
hafsat ta ce"muje Kitchen"
tare sukayi girkin dare jallof rice da grilled chicken suka girka sai fruit salad da hafsat ta hada masa bayan sun gama gama Hafsat ta jera komai a tray ta kalli iman ta ce"sai kije ki shirya ki kaima sa"
wanka tayi ta fito cikin wata doguwar riga colour sky blue mai sauƙin ado amma ta amshe ta sosai
ta shafa light perfume sannan ta gyara rolling ɗin kanta
Hafsat dake kallon ta ce"wow ko kefa"
wata kunya taji ta kamata
hafsat ta ce"yadda kike boƴe kyawun ki ba ƙaramin kwarar kanki ki ke ba iman You Are beautifull that You don't even know You have it"
murmushi tayi ta kama hanyar master room din suhail tana yana zaune bakin gado sanye da boxer yana dan na laptop din sa
yaki karar knocking "come in" ya faɗa
a hankali iman ta tura kofar dakin ta shiga
Tana shiga ya ɗago kai daga laptop ɗinsa.
Na ɗan lokaci idanunsu suka haɗu.
Suhail ya rasa dalilin da yasa zuciyarsa ta buga da ƙarfi
Blue ɗin rigar jikin ta da kamshin turaren da ya shiga ɗakin gaba ɗaya sun sa ya kasa ɗauke idonsa daga kanta
a gaban ta ajiye tray din mamaki ya kasa boƴuwa a fuskar yau iman ce tayi masa girki
ta juya zata fita ya ce"come and serve"
juyawa tayyi kamar yaddda ya bukata ta zuba ta miƙa masa
kamshin girki ya cika dakin gaba daya
fuskar nan ba yabo ba fallasa duk sanda ta tuna Abinda Suhail yayi mata takan ji zuciyar na mata zabi banda ya zama dole ko ganin fuskar sa bata kaunar yi
tana gama zuba masa ta fita zuwa part din ta
suhail na cin abincin amman gaba ɗaya tunaninsa na kan ta yana lura da yadda kullin ƙara nisan kanta ko take dashi ya tabbatar da Abincin data kawo masa arzikin zuwan hafsat gidan ne yasa ta kawo
tabbas zuwan Hafsat ya bude masa ido ya fahimci irin nisan da ya bari ya shiga tsakaninsu da Iman.
washe gari da wuri ya fita court sakamakon wani cases da yake dashi hakan yasa bai samu damar shiga bangaren kowa ba ya wuce
daren jiya zeenah kasa bacci tayi wasu sabin habit take gani a wajen suhail kwana biyun duk ya fara chanza ma ta tunda ranar data gansa tare da hafsat suna fara'a ko breakfast din da jennifer ta kawo mata ƙasa ci tayi
hafsat ce ta fita Kitchen dan dora masu girkin rana sakamakon iman ce tayi masu na safe
tana tsaye jikin cabinet zeenah ta shigo tana taunar cingum fridge taje ta dauko ruwa Hafsat ta cigaba da uzurin ta ba tare da ta kalle taba
Hafsat ta cigaba da haɗa kayan girki kamar bata ma lura da shigowar Zeenah ba.
Zeenah ta kurɓi ruwa sannan ta jingina da fridge tana kallon Hafsat daga sama har ƙasa kallo da babu komai a cikin sa fa ce raini
“Miya kawo ki kitchen Nan”
A fusace hafsat ta ce”Abinda ya kawo ki shiya kawo ni”
Zeenah ta yi dariyar rainin hankali “Ashe hasashe na ya zama Gaskiya na cewar abincin ya koro ki daga Chan”
“Abincin?Kinga yunwa a jikin ko an fada maki shi Suhail da yunwa yaga iman ya aura ya aure ta saboda tarbiyyar Wanda da dukkan alamu babu ita a tattare dake”
Zeenah ta ce, “Ke kina ganin tarbiyya ce zata sa mace ta rike miji?”
Hafsat ta ce“A’a amma rashin tarbiyya na iya sa ta rasa shi”
Zeenah ta daga hannu zata mari hafsat ta janye hannun ta da karfi
Dai dai lokacin iman na shigo wa
Kuyi hakuri da Wannan Sai Gobe kuma