Sawun Giwa

09

by @ammimalami99


~~

"Ina bayanki kawata" 

Rafi'a ta fada daga inda take zaune akan mirrorn dakinta tana daura dankwali. 

"iPhone 14 pro fa yake amfani da ita" 

Nana ke fada itama daga inda take zaune kan gadon dakin tana kallon fuskar Rafi'ar ta mirrorn. 

"Kai bata dade da fitowa ba ai gaskiya dole ne ma kiji haushin yarinyar nan dan na rantse da nice ma da tuni na kwace sa kam bala'i" 

Rafi'a ta karasa tana kada kai. Nana ta girgiza kanta maganganun Rafi'a na shiga kanta 

"Ke sai kinma ganshi Rafi'aa, gayen nan ya hadu" 

Nana ke fada kafin ta dago yatsunta tana fara yiwa Rafi'a lissafi. 

"Na farko kinga ga kyau" ta fada tana riko yatsa daya

"Ga iya gaye" ta riko yatsa na biyu

"Ga kamshii na bala'i" ta riko yatsa na uku ta kara da 
"Da na shiga motar sa suma ne kawai banyi ba a wajen" 

Rafi'a ta kece da dariya dan tuni ta saki daurin dankwalin ta juyo ga Nana. 

"Na rantse!! kinji kamshi" Nana ke fada 

"Ga kuma murya mai dadi" ta riko wani yatsan. 

"Sannan ga naira" ta karasa tana riko yatsa na karshe.

"Kekam ai an biyaki wallahi wuff dashi zakiyi saidai kawai taji a salansa" Rafi'a ke fada suna tafawa da Nana. 

"Wuff dashi dinma ai duk wata kissa da kisisina dana iya a kansa zan sauketa dan Aisha tayi kadan tace wai zata taka ni. Sannan ni Rafi'a ba wani abun dake bakanta mun rai kamar aikin nan ai na baki labarin iPad dinnan koh" 

"Kin bani labari" Rafi'a ta amsata tana mikewa daga kan kujerar gaban mirrorn ta nufo gadon dan daukar gyalenta. 

"Toh aikin nan ma in sha Allahu sai ta barsa muna nan dake"

"Allah kawata" Rafi'a ke fada tana bata hannu suka tafa. 

"Sa wasa" Nana ta bata amsa dai dai sanda wani kanin Rafi'a ya daga labulen dakin yana leko kansa. 

"Anty Mama tace wai ki aramata dari biyar" 

Rafi'a taja karamin tsaki kafin ta dauki jakarta dake kan gadon itama ta bude tana fidda dubu daya. 

"Zo karba ka kai mata" Aikwa ya shigo ya karba ya fice. 

"Ace wai iyayen ka ma akanka suka dogara haba" Rafi'ar ke fada tana yafa gyalenta a kafada. 

Nana tayi dariya "Shiyasa yanxu zamuje ki kaini wajen Alhajin nan da kika bani labari in kwashi rabona dan nan da kike ganina banida koh sisi" 

"Ah haba kin saduda kenan" 

Rafi'ar ke fada tana sakin wata dariyar keta dan dama tuntuni take bin Nana da maganar Alhajin nan dan kudi garesa kamar mey har alkawarin daloli ya mata in dai ta kawo masa Nana. Nana ta tabe baki 

"Samarin yanxun ne sai ahankali dazun nan Yusuf ya gaya mun bakaken maganganu dan kawai nace mai ya bani dubu hamsin". 

Rafi'a tayi wata dariya tace "Tun yaushe nake fada miki ki fita harkar sa ki samu wani Alhajin da zaki tatso kudi a wajensa kinga sai ki kama Mu'azzam dinki ki rike gam kina tara abunda kika tara kiyi aurenki" 
Ta karasa bayan ta fesa turare. 

"Maganarki dutse kawata abunda zanyi kenan" Nana ta fada itama tana mikewa suka fice daga dakin. 


~~

"Zafin jikin ya sauka ma" 

Nurse Hadiza ke fada daga inda take zaune kan gadon Inna gefen Khausar da tayi lamo saboda rashin lafiyar da takeyi. 

"Tasha maganin ai shiyasa" 

Inna ke fada tana bare taurar da Nurse Hadiza ta kawo mata dan Inna na son taura kuma akwai wata gwaggon Nurse Hadiza dake aiko musu mai kyau daga can garinsu shiyasa duk idan ta aiko mata sai ta shigo ta kawo wa Inna. 

"Alhamdulillah, in sha Allah zata warware sanyin nan ne da ya fara shigowa yake taba ta" 

"Shi dinne dama kinsan ana fara sanyi toh yau lafiya gobe ciwo" Inna ta amsata tana kai taurar data bare bakinta. 

"Inna amma dan Allah wannan karon da jikin ya tashi sosai a kaita asibiti" Nurse Hadiza ke fada. 

"In sha Allahu ai wancan karon ma lalura ce ta saka ba'a je asibitin ba yanxu kuma ai kinga sauki yazo" 

"Gaskiya kam Alhamdulillah dama abu duk idan aka samu jinkiri a cikinsa alkhairi ne ke zuwa" 

Nurse Hadiza ke fada sanda Juwaira data dawo daga bandaki kenan ta shigo dakin. 

"Maman Emann" Juwaira ta fada tana baiwa Nurse Hadiza hannu dan dama suna shiri sosai. Nurse Hadiza tayi dariya kafin su fara hira Hadizan na mitar cewa rabon Juwaira da gidanta tun sallah babba daga ita har Aisha. Daga wannan maganar ne da Aisha ta shigo zancen Nurse Hadiza ke tambayar toh ina Aishar ma. 

"Tunda aka kira wayarta ta fice ai" 

Inna ke fada kafin ta fara mitar wayar daren nan da ba so take ba koh kadan. 
Aisha kuwa tana dakinsu. Tana tsaye bakin dayar windown dakinsu dake kallon bayan gidansu inda ragunan Baffa suke kuma wata kila sanyin ruwan nan da akayi ne ya saka su sukayi shiru ba kajin duriyarsu. Windown a rufe take tana tsaye a gabanta ta jingina da bangon wajen kuma da yake wutar dakin a kashe take hasken wutar corridorn waje ne kadai yake shigowa cikin dakin. 

Tana zaune ne a dakin Inna sanda Nurse Hadiza ta shigo dubiyar Khausar kuma suna hira taga ana kiranta wa kuma zata gan yana kiranta idan ba El Yakoub ba. Taji kafafuwanta na yin sanyi sanda take karasawa dakinsu dab da wayar zata tsinke ta dauka tana dorata akan kunnenta. Tausashiyar muryarsa ta mata sallama ta amsa sa tana karasawa gaban windown nan ta tsaya. 

El Yakoub dake tsaye shima wajen sabuwar windown parlonsa da aka saka mai kwanaki ya fito da hannunsa daga cikin aljihun sa yana shafa sumar kansa ahankali sanda muryarta ta shiga kunnensa. Dama tun bayan sallahr isha'i yake tunanin kiranta ya tambayeta ya jikin Khausar amma ya kasa dan basu taba wata wayar ba idan ba akan abunda ya shafi aiki ba. Sai bayan sun gama waya da Hajiya tukunna yayi shahadar danna numberta ya nufi windown nan ya tsaya bayan ya zuge labulen yana kallon yadda wajen yake a jike saboda ruwan da akayi ranar.

Yaji sanda ta dauka motsintsa na shiga kunnensa kafin ya furta mata sallamar data amsa mai a natse. 

"Barka da dare sir" ta sake furtawa sanda ya gama shafa sumar kan nasa yana maida hannun cikin aljihun wandonsa na flannel launin fari mai layyuka shudaye. 

"Barka dai" El Yakoub ya fada. 

Aisha tayi shiru tana sauraren wani aiki zai bata kuma dan koh dazu ta duba tagan bai tura mata komai ba ta email. 

"Ya sanyi?" Ya aiko mata tambayar data dasa mamaki a ranta. 

"Alhamdulillah" Ta amsa sa tana kamo gefen rigarta ta tsakanin yatsun ta. 

"Uhm... ya jikin Khausar" 

Ya tambayeta abunda dama ya kira ya tambaya din. Aisha ta sunkuyar da kanta kamar yana gabanta cikin jin dadin wannan tambayar da yayi mata 

"Jiki da sauki bacci ma takeyi yanxun" 

"Masha Allah" ya fada sanda ya kai dubansa kasa yana kallon fararen kafafuwansa da ya manta bai sakawa socks ba sanyin tiles dinda yake tsaye yana shigar mai kafa. 

Shiru ya biyo baya na d'an wucewar sakanni. 

"Aisha"  Ya kira sunanta. 

Wannan sunan da ya shiga bakinsa kamar me dan ita kanta Aishar tasan ba wanda yake fadan sunanta haka kamar shi.

"Sir" ta amsa sa. 

Ya lumshe idanuwansa ahankali ya sake budewa. 

"Zan iya zuwa dubiya" ya tambayeta. 

Ba yau ya saba fadan maganganun dake bata mamaki ba dama. 

"Na'am, yanxu?" 

Ta fada tana raba jikinta daga jinginar datayi ga bangon nan wadda sanyinta ke ratsa y'ar doguwar rigar baccinta data saka. Rigar da Inna ta ringa fadar yanxu ita ana sanyi zata dauki wannan rigar ta saka. Rigar gado, dan kusan shekarar rigar nan uku kuma Aisha na bala'in son rigar ta kasa sadaka da ita kuma duk randa ta sakata sai Inna ta ringa fadan duk sanda ta riko rigar nan yageta zatayi tunda Aishar bazata bari a sakata sadaka ba. 

El Yakoub yayi d'an murmushi kafin yace "Uhm yanxu" 

Aisha ta girgiza kanta kamar yana gabanta "Sir yanxu ai dare yayi" 

"Nasani Aisha gobe nake nufi dama" ya bata amsa yana kallon waje. 

Sai kawai ta hade labbanta waje daya tana danne murmushin da yazo mata wato magana ya gaya mata kenan. Lallai ma mutumin nan. 

"Uhm amma sai na tambaya" ta fada tana komawa baya ta sake jingina bayanta da bangon. 

"Wa zaki tambaya? Inna?" ya fada. 

Ta gyada kanta tana sake danne wani murmushin tana tuna wannan ranar da yayi mata interview dinnan. 

"Eh" ta fada. 

"Fatan dai kin fadawa Inna ni ba tsoho bane kuma banida tsauri" 

Aisha bata san sanda ta saki wata siririyar dariya ba. Wata y'ar dariyar data bi speaker wayar zuwa cikin zuciyar El Yakoub. Sai kawai ya sake lumshe idanuwansa. 

"Eh na fada mata" Ta basa amsa bayan ta gama dariyar yatsun hannunta guda hudu akan bakinta yayinda mamakin inda tambayar ta fito ke dabaibayeta.

"Dagaske?" ya fada mamakin na fitowa ta cikin muryarsa dan har girarsa biyu ya daga sama alamar mamakin. 

"Eh na fada mata kai ba tsoho bane ba" 

"Amma kuma baki fada mata banida tsauri ba" ya karasa mata maganar. 

"A'a fa" Aisha ta fada tana sunkuyar da kanta dan wannan yanayin kawai jinsa take kamar ba gaske ba. 

"Kin fada kenan?" ya sake tambaya. 

"Sir ai kanada tsaurin wani sa'in" 

Aisha ta furta maganar da bata san yaushe ta fito daga bakinta ba tayi saurin hade labbanta waje daya kawai kuma batareda tayi tsammani ba taji wani daddadan sauti na dariyarsa yana shigowa cikin wayar zuwa kunnenta. 

"Aisha" ya kiraye sunanta bayan yayi y'ar dariyar. 

Ta sauke numfashin da bata sanma ta rikesa ba alokacin da yake dariyar nan. Dariyar da taji ta ratsa ranta da wani abu mai sanyi. 

"I'm your boss fa koh kin manta" 

Ta girgiza kanta da sauri "Kayi hakuri" ta fada tana cigaba da murza rigarta dake cikin yatsunta. 

"Idan kin tambayeta toh ki fadamun kinji" 

"Toh in sha Allah" Ta fada tana kallon kasa inda ta kamo rigarta tana kallon launin rigar. 

"Sai da safe" ya furta itama tace 

"Unhm sai da safe sir" kafin suka sauke wayar. 

Aisha ta tsaya tana kallon fuskar karamar Nokiarta bayan call din ya katse tana biya dukkan wayar da sukayi yanxun nan a kanta. Kamar idan bata sake maimaitawa ba zai bace daga kanta ne batareda ta iya tuna sa ba.


~~

"Kuma kince masa eh yazo din?" 

Juwaira ta tambayeta daga inda take zaune gaban murhu a cikin kitchen da sassafe tana zuba kullun wainar da take toyawa a cikin tanda. Aisha dake kwashe miyar taushen data gama hadawa tana zubawa cikin kular Mallam tace 

"A'a cewa nayi dai zan tambayi Inna" 

Juwaira ta jinjina kanta kawai kuma sai da jira ta gama zubin tukunna ta mayarda ludayin cikin bokitin da kullun nan yake ciki sannan ta juyo ga Aisha. 

"Toh yanxu ita Innar me zaki ce mata" 

Aisha ta rufe kular Mallam tana girgiza kanta "Wallahi bansani ba, shiyasa nake neman shawararki ai". 

Juwaira ta murmusa "Lallai kin kirawo ruwa yarinya" 

Aisha ta ajiye kular Mallam gefe tana dakko ta Maman Nana zuciyarta na sake tunkushewa da tunanin datayi bacci ta kuma tashi dashi yau na yanda zata tambayi Inna zuwan El Yakoub. 

"Kinsan Allah kina fada mata zancen zuwansa ganin zatayi kamar akwai wani abu a tsakaninku dan chaa zatayi ki tsayarda hankalinki waje daya kisan me kikeyi"

Aisha ta gyada kanta cikin yarda da zancen Juwairar. 

"Amma ke kin tabbatar ba sonki yakeyi ba" Juwairar ta tambayeta.

Aisha bata san sanda ta dago daga zuba miyar nan ba bakinta na bude kansa tareda bugawar zuciyarta cikin mamakin furucinta. So? Wa? Ita? El Yakoub din?? Sai kawai Juwaira tayi wata y'ar dariya kafin ta fara jujuya wainar ta. 

"Haba Ya Juwaira ya kike sako wata maganar, nace miki fa tare mukaje pharmacy dinnan ya biya kudin maganinta da inhler. A sannan ne yasan batada lafiya har ya kirani yaji ya jikinta yace kuma zaizo yau" 

"Toh in tambayeki mana" Juwairar ta fada 

"Uhm" Aisha ta amsata tana cigaba da zuba miyarta bayan ta gama girgije maganar da Juwaira fa fada yanxu daga kwakwalwarta. 

"Tsakanin ke da khausar wa yasani?" 

"Ni" Aisha ta amsa ta

"Toh, kinga kenan wajenki zaizo ya fake da zuwa dubiya" 

"Inna lillahi dan Allah ki daina wannan maganar mana, oga na ne fa" 

Aisha ke fada tana dora kular Maman Nana kan kafarta, ta dakko murfin tana rufeta zuciyarta na ture duk wata magana da Juwairar ke fada daga cikinta dan bata ma son suyi dadewar da zasu samu wajen zama a ciki.

"Saboda yana oganki sai akayi yaya, shi ba namiji bane?" 

"Hm baki san mutumin nan bane, ya za'ayi ma.." Ta kasa karasa maganar dan kalaman a cikin kwakwalwarta kadai suka tsaya koh zuciyarta basu kai ba bare su samu nasarar fitowa daga bakinta sai kawai ta girgiza kanta tana tattare girarta waje daya 

"Kai gaskiya ni kima daina wannan maganar daga gani ma kinsan cewa fa yanada iyali" 

Juwaira ta fara dariya tana kwashe wainarta kafin ta dakko wani kwano mai murfi da suke zuba mai ta dauki cokali tana debo man tana zubawa. 

"Naji dai, in tayi tsami ai zamuji" Juwaira ke fada bayan ta gama dariyarta. 

"Ki barni da Inna kawai zansan me zance mata in yaso idan yazo sai ku fita ke da Khausar su gaisa tunda jikin nata da sauki kuma kinga bazai yiwu ya shigo cikin gida ba tunda ba parlon baki garemu ba" 

Aisha ta gyada kanta cikin na'am da maganarta.  

"In yaso idan sun gaisa ta dawo kinga sai ki tsaya ku sha zancenku tunda abunda zai kawo shi kenan dama" 

Juwaira ta karasa tana y'ar dariya. 

"Dan Allah ki bari, wani zance kuma ana zaune kalau" 

Aishar ke fada cikin son Juwairar ta daina maganar dan idan tana fada zuciyarta dakko mata hoton El Yakoub takeyi kuma hakan yana haddasa mata rawar gaba. Allah na tuba wannan mutumin me ma ya iya a rayuwarsa idan ba aiki ba. Ita bata ma hangosa yana wata hira koh zance bare ma na soyayya. Da gani matarsa tana fama. Ta ayyana a ranta tana ture maganar Juwairar na cewa wai zance zaizo wajenta. Ita asuwa? 

Saidai sam maganar bata bar ranta ba duk kuwa da yanda ta ringa kokarin ture ta har sanda Juwaira ta sanar da Inna zancen zuwan nan wanda ita Aishar bata san mey ta fada mata ba. Ta shigo daki daga wanken wanken da tayi sanda Innar ke ce mata tace mai yazo din toh Allah bada lada. Wani abu da ya bala'in daure mata kai dan batayi tsammanin haka ba daga Inna kuma tayi tayi Juwaira ta fada mata me tace mata tace bazata fada ba. 
Kuma minti talatin da gama sallahr Isha'inta chipp taga sakonsa ya shigo wayarta 

Ina waje’ 

Kuma idan za'a tsaida ta a tambayeta mey da mey ya faru bayan taga wannan message din bazatace gashi ba dan yanda zuciyarta ta ringa bugu a kirjinta da ma yanda taji kafafuwanta sunyi sanyi lakwai kai bazakace ma tasan El Yakoub din ba kuma tana ganinsa kullum sau biyar a sati. Gabaki daya hankalinta ba a jikinta yake ba har sanda tacewa Inna ya zo. Da sanda ta fito wajen dakin rikeda hannun Khausar da taji sauki dan bata jima ba da gama cin indomien da Aisha ta dafa mata. Game ma take bugawa a ipad din Aishar sanda yazo. Da sanda Juwaira ta biyo bayanta da gyale tana ce mata bazata fita da hijabi ba wallahi. Har zuwa sanda Maman Nana ta dago labulen dakinta ta lekosu tana tambayarsu mey ta gansu cirko cirko a tsakar gida Juwaira tace mata ai Mu'azzam ne yazo dubiyar Khausar. Da ma sanda suka fito waje iskar wajen na banbanta da ta cikin gida sanda suka karaso wajensa inda yake tsaye bakin motarsa hannayensa biyu harde a kirjinsa sanadiyar tsadadden kamshin turarensa mai dadin kamshi da ya gauraye iskar wajen. Kuma sai alokacin nan, a lokacinda ya dago yahada idanuwa da ita tukunna wannan abun da ya kulle kansa a cikin cikinta ya warware. 

"Ina wuni sir" ta furta mai.

"Ina wuni" ya jiyo muryar Khausar itama. 

Sai kawai El Yakoub ya lumshe idanuwansa yana sake budesu. Allah yagani tun jiya da ya kirata a waya tun daga lokacin nan gabaki daya ba kwakwalwarsa ce take tafiyar dashi ba zuciyarsa ce. Dan duk wasu abubuwan da ya fada jiya a wayar nan bai san ma yaushe ya fade su ba sai bayan sun sauke wayar tukunna. Kuma gabaki daya ranar ya tafiyar da ita ne da jiran jin amsar da zata basa akan zuwan nasa ilai kuwa yana zaune a parlor yana wani business call a laptop dinsa da ma'aikatan kamfaninsa dake Abuja sanda wayarsa tayi haske da alamar shigowar sako kuma yana kai idanuwansa ba tareda ya bude wayar ba kasancewar batada key yaga layyukan rubutun da ta turo mai

'Assalamu alaikum, Ina wuni'
'Barka da rana'
'Na tambayi Inna tace zaka iya zuwa'

Kuma shi kanshi bai san mey yaji a wannan lokacin ba dan Daniel na gabatar da nasa jawabi ya dauki wayarsa ya tura mata reply yana tambayarta karfe nawa zai iya zuwa kuma sai bayan mintina kusan biyar tukunna ta amsa sa. Ya shirya yazo din kuwa kaman yanda tace. Sai bayan ya bude motarsa ya fito tukunna ya tura sakon nan dan haka kawai yaji yana son shakar iskar dake kadawa a waje mai sanyi dake ratsa jikinsa. Kuma yana tsaye a wajen ne sanda ta fito itada Khausar. Idanuwansa suka tsaya a kanta na d'an sakanni bayan ta iso gabansa. Atamfa ce a jikinta doguwar riga A shape dinnan launin shudi da orange. Gyalen data yafa akanta ma orange dinne mai kananan duwatsu ya zagaye fuskarta. Da kyar ya iya kawad da tunanin da yazo kansa a lokacin yana juyo dubansa ga Khausar ya amsa gaisuwarta. 

Aisha ta tsaya a wajen tana kallonsu a ranta tana yaba shigarsa sanda yake tambayar Khausar ya jikinta fatan dai tana shan magani. Yau wani yadi ne a jikinsa launin cream da ya bala'in karbarsa ya masa kyau kamar koh yaushe idan ya saka manyan kaya. Hular kansa brown ce mai kananan designs hasken fitilar gaban gidan Hajiya Zulai yana hasko mata jar fatarsa. Da sanda murmushi ya hau bakinsa lokacinda Khausar ta amsa wata tambayar da ya mata wadda bata ji ba. 

Hira sukeyi da Khausar dan idan ba kunnenta bane har ji tayi yana bata labarin sanda yana karami idan bashida lafiya kuma bakinsa ba dadi akwai wani yoghurt da mamansa ke basa. Shi kadai yake iya sha yaji dandanon bakinsa ya dawo. Tana kallo sanda ya bude gaban motarsa yana fito da wata katuwar ledar da sai da tayi tantamar idan Khausar zata iya daukarta. Ilai kuwa sai ga Ja'afar karamin yaron kishiyar Hajiya Zulai da ya girmi Khausar din da wajen shekaru hudu yazo shiga gidansu dan kamar abu zai siyo wajen Inna. 
El Yakoub ya kira sa har ma ya basa hannu suka gaisa kafin ya mika mai ledar yace mai ya kai wa Khausar ita ciki har ya hada mai da dubu daya. Kuma sai bayan sun shige ta kofar gidansu tukunna ya juyo gareta dai dai sanda taji zuciyarta na fadawa can can can can kasa cikin cikinta. Ba karamin kyau yayi yau dinnan ba ya rabbi. 

"Aisha" ya fadi sunanta yana sake jingina bayansa jikin motarsa. 

Ta dauke idanuwanta daga kan fuskarsa sanda tace "Ina wuni sir"

"Mun gaisa ai" ya bata amsa. 

"A'a baka amsa ba da na gaisheka" 

El Yakoub ya daga girarsa biyu a tare dan karamin murmushi na kokarin hawa labbansa maganganunta burgesa sukeyi bai san meyasa ba.

"Na amsa mana bakiji bane kawai" 

Sai kawai ta gyada kanta batace komai ba ta kamo gefen gyalenta tsakanin yatsun ta akan idonsa. 

"Ina jinki" ya fada yana kallon yadda yatsunta suke rike da gyalen. 

Ta dago "Na'am"

"Ina saurarenki"

"Akan me fa" ta tambayesa

"Kince inada tsauri wani sa'in, soo ki fadamun duka lokutan dana miki tsaurin ina jinki" Ya fada. 

Koh kad'an El Yakoub bai yi tsammanin abunda ya biyo baya ba dan siririyar dariyar nan da yaji tayi cikin waya jiya da daddare da ta mai tsaye a kai yagani yanxu akan fuskarta tareda sautinta me dadi dake fitowa ta bakinta. 

"Kayi hakuri ni fa ba abunda nake nufi ba kenan" ta fada bayan tayi dariyar. 

El Yakoub ya furzar da karamin iska daga bakinsa saboda tasirin da wannan dariyar ta masa kafin yace 

"Sai dai idan kalmar tsaurin tanada wata ma'anar da ban sani ba"

Ta girgiza kanta "A'a danace tsauri, ba wai ina nufin tsauri tsauri ba" 

Ya tattare girarsa yana sauraren wannan bayanin nata 

"Ina nufin kamar yanda baka wasa da aiki da dai sauransu kuma kaga ai wannan abu ne mai kyau koh" Ta karasa tana kaucewa kallonsa saboda yanda ya zuba mata idanuwa yana sauraren bayanin nata. 

"Wayo kenan wannan" ya bata amsa jin kwane kwanen da take kokarin yi masa. 

Aisha ta girgiza kanta tana kallon gefen gyalen nan data kamo "A'a sir ba wayo bane ba" 

"Hm" ya fada kawai yana jinjina kansa. 

"Me kika cewa Inna akan zuwa na?" 

Ya tambayeta abunda bai san cewa ita kanta bata sanshi ba. Bata san me Juwaira ta fadawa Inna ba har tace yazo din batareda ta mata wata maganar ba. 

"Cewa nayi zakazo duba Khausar" 

"Ni wa kenan?"  ya tambaya. 

Yaga sanda ta dago daga kallon gyalen nan ta kallesa "Kai oga na mana"

"Oganki mai tsaurin nan koh" 

Sai kawai ta sakeyin wannan dariyar kamar yanda yaso din dan dama ya fadi kalmar tsaurin ne dan ta sakeyin wata dariyar yagani. 

Ta girgiza kanta "A'a sir bance haka ba" 

Yayi murmushi, murmushin da ya saka zuciyar Aisha dagowa daga fadawar nan datayi tana kara girma a cikin kirjinta. 

"Aisha" ya kira sunanta 

"Na'am sir" 

Ta amsa sa bayan ta dago kuma abunda ya biyo baya sanda ta amsa san wani abu ne da bata taba lissafa shi ba. Ya miko hannunsa daga inda yake tsaye yasaka yatsunsa biyu jajaye yana kamo karshen gyalenta ya janyeshi daga rikon data masa dai dai sanda kuma motar Mu'azzam ta karyo kwanar da zata shigo dakai layinsu.

~~

Gan gan gan🤣

Wai meke shirin faruwa ne???

Gafa Mu'azzam ga El Yakoub 

Wo ho ho!!! Akace wai Ali yaga Ali😂😂