MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

A wannan daren babu wanda bacci ya yiwa dadi shida itan, and for the first time tunda suka zo qasar kimanin wata na biyu kenan a wannan daren suka raba makwancinsu, wanda hakan ba komai ya qara jawowa ba illa tsanar Fadwa da duk abunda ya shafeta a zuciyar Momma. Tayi kuka kuma tayi tsinuwa mara adadi ga wanda ma ya ajiye musu yarinyar a gidansu in the first place, dan a nata tunaninta gani take babu abunda riqon yarinyar zai jawo musu banda rushewar duk wani farin cikinsu a rayuwa. Da aka wayi gari twins sukazo gaishe ta tun daga bakin kofa Imam ya sha jinin jikinsa ganin yanayin mahaifiyar tasu, sai ya qarasa gareta a sanyaye tana zaune a bakin gado ta sunkuyar da kanta. Ahankali ya zauna kusa da ita sannan Imran ya zauna ta dayan barinta shima duk sukayi shiru, sai ta dago kanta tana kallonsu tace "Meye kun wani sani a tsakiya?" ahankali Imran yace "Kiyi hakuri" ta kalleshi sannan tace "Me kuka min? ba kun samu qanwa har kuna qin zuwa gurina ba, kuna gani banida lafiya amma rainon ta ya fi muku zuwa gurina ko?" nan ma Imran yace "A'a Momma" sai kawai sukaji Imam yace "Momma please let her stay with us" batasan lokacin da tureshi da dan qarfinta ba har saida ya kusa faduwa, a zazafe tace "Ficemin daga dakinnan kafin in saba maka, wanda baisan kishin nasa ba" sai kuma ya sake dawowa gefenta ya zauna bai fitan ba, kamo hannunta yayi ahankali yace "I'm sorry Momma" ta kwace hanun nata "Ka rufemin baki" yayi murmushi tareda sake kamo hannun nata, sai kuma tace "Kunyi breakfast?" ya gyada kai sannan Imran yace "Momma yaushe zamu koma gida? an koma hutun fa kuma Papa baice komai ba" sai ta shafa kansa da dayan hannunta tace "Soon. We'll go back soon".
 Papa ne ya leqo dakin ganin yanda suka sa uwar tasu a tsakiya yasa shi yin murmushi, yace "Sirri kuke yi ne?" suka murmusa amma banda Momma data kauda kanta bata kallesa ba, sai ya qaraso ya zauna shima a gefen Imam yana kallonta yace "Ya jikin naki?" ta juyo kadan ta amsa da "Lafiya" Imran yace "Papa yaushe zamu koma gida?" yace "Ka gaji da qasar nan kaima ko?" ya gyada kai sai Papan yace "Zamu koma in Momma ta haihu in sha Allah" nan kuma Imran din ya sake cewa "Allah yasa namiji za'a haifa mana" sai Papa yayi murmushi yana kallonsa kawai, anutse shima Imam yace "Amin" nan kuma Momma tace "Meyasa kuke son namiji?" kafin su amsa Papa yace "Ai haka debate din yake daman, namiji na son a haifa musu namiji, mace na son a haifa musu mace" Imran yace "Munason namiji tunda munada Fadwa yanzu ai" kawai iyayen suka tsaya kallonsa, ganin haka sai ya miqe adan hanzarce zai fice daga dakin sai Imam ya miqe shima, Papa bai bar kallonsu ba yace "Ina zakuje kuma?" Imran ya amsa da "Banyi breakfast ba" da haka ya nufi kofa Imam na biye dashi suka fice,  sai sannan Papa ya juyo yana kallonta da kyau, ganin yanda ta dinke fuska yasashi nausar da murya yace "Fatima, abun da ya faru jiya.." bai qarasa ba tace "Banason jin komai daga gareka indai ba akan bayar da yarinyar nan bane Baban jidda, sabanin da muke samu akanta ya nunamin zaman ta a gurinmu ba wani alkhairin da hakan zai haifar" sai ya miqe anutse yace "Bazan bayar da ita ba, you should learn to live with that...abunda na fada miki jiyan shi zan sake fadi, Fadwa 'yata ce yanzu and nothing changes that" da haka ya juya zai fice kawai ta duqar da kanta tareda dafa goshinta tana jin wani zafi na taso mata tun daga qasan zuciyar ta. Atake kuma cikinta yayi wani irin juyawa da qarfi,  ta buga wani uban qara tana salatin da yasa Papan juyowa daga bakin kofan da sauri ya sake nufota yana tambayan lafiyanta a rikice, durqushewa tayi bata bar yin salatin ba tana dafa cikin, dakyar ta iya fadin "I think my water broke" ya zare ido tareda juyawa ya kwala kiran Habiba da qarfinsa, aikuwa da gudunta ta qaraso dakin su Imam na biye da ita dalilin jiyo qarar da mahaifiyar tasu tayi, da sauri Habiban ta rufe kofa sanin zasu iya shigowa sannan ta qarasa da saurinta tafara riqe Momman dake fitar da numfashi, ga wani gumi da ya fara jiqata tun ba'a je ko Ina ba, atake Papa ya hau tambayanta in zata iya tashi, ta gyada kai dakyar alaman Eh sannan suka hau dagata shida Habiban dan ficewa da ita zuwa mota, dan a bayyane yake haihuwar ce tazo gadan gadan.

A wannan yanayin suka isa asibitin a inda tun kafin su qarasa da ita ciki nurses suka taho da gadon daukanta akayi ciki da ita Papan da Habiba na biye dasu, sai da aka shiga da ita labor room sannan Papa yace da Habiban ta koma gida dan kula da sauran yaran tunda an barsu su kadai. Ranan wuni Momma tayi tana labor, ta azabtu iya azabtuwa kafin ta haifo 'yarta kyakkyawa me kama da ita. Bayan an shiryata aka miqo wa Papa ita ya rungumeta a jikinsa kamar ya maida ita ciki dan murna. Sai bayan Momma ta huta sosai zuwa 9 na dare sannan ya kira can gida Nigeria, sunyi murna iya murna barin ma Anti Aina'u data fara tunanin zuwa, amma sanin itama tana dauke da nata cikin yasa Papa yace mata A'a ba sai ta zo ba, a inda ya tabbatar mata da kuma sauran 'yan'uwansa akan sunanan dawowa cikin sati uku dan zuwa America a wannan lokacin ba abu bane me sauqi. A washegarin ranan Papa ya koma gida ya taho da yaran nasa har da Habiban zuwa asibitin, ganin Momma da Baby ba qaramin farin ciki ya sanya 'ya'yan nasu ba, suka dauki jinjirar fuskokinsu cike da yalwan murmushi kamar basu suka ce sunason namiji ba. Hankalin Papa na kan Fadwa har Habiba ta sauqe ta daga goyen da take a bayanta, nan ya dauketa sannan ya hau tambayan ko ta bata madaranta, ta amsa da Eh a ladabce duk Momma na kallonsu.

Bayan shudewan wasu mintuna masu tsayi Ladan yayi sallama a dakin shida matarsa Zulaiha wadda yara ke kiranta da Mami, 'yar asalin Nigeria ce a inda ta kasance 'yar'uwa ga Ladan din ta fannin iyayensu har auren hadi ya shiga tsakninsu. Da fara'a suka qaraso sai Ladan ya dubi Momman yana mata sannu da jikin nata, sai Mami ta karbi jinjirar daga hannun Habiban sannan ta zauna a gefen gadon itama tana mata sannu sannan suka gaisa. Ladan kuma sai ya miqa hannu gurin Papa dake zaune a resting chair ya karbi Fadwa yana fadin "Kaga yarinya tayi wayo kamar ba ita ba" Papa na murmushi yace "Gaskiya, kullum qara wayo take" zama Ladan din yayi a gefensa sannan ya dan dunguri hancinta yana mata murmushi, kallonsa take qur da ido kamar ba jinjira ba sai kace mai haddace kamanninsa, bai bar murmushin ba yake kallonta sannan yace "An miki qanwa kema" Mami na kallonsu tace "Uhm, gaskiya ne" ta qarasa maganan tana juya kanta gurin Momma dake kallonsu Ladan din kawai. Sai da suka gama gaisawa bayan Ladan ya bada Fadwan ya karbi jinjirar shima yayi nasa addu'an sannan duk suka fice tare dasu Imam din kuma har sannan Fadwa na riqe a hannun Papa ya fitan, sai lokacin Mami tace da Momman "Ban taba ganin inda Iyaye suka fifita son dan wani akan nasu ba, kina ma da hakuri Maman Jidda" sai Habiba ta nufi toilet yin wani uzurin dan tasan kwanan zancen kuma, Momma ta dan gyara zamanta jin an sosa mata inda yake mata qaiqayi, tace "Hmm, kema kin ga abunda nake gani kullum ko" tace "Ai iya abunda na gani kadai ya isheni shaida Maman Jidda" ahankali Momma tace "Ashe dai bani kadai bace nake ganin rashin daidai a lamarin nan, Kinsan har hadani yayi da Anti Aina'u akan lamarin yarinyar nan, dan nace bazan riqeta ba" Mami tace "Haka Baban Kareem ya fadamin. A Ina aka taba yin hakan?. Tunda baki aminta da riqonta ba ai ba'a dole, bare ma D'an wani ai ba abun riqo bane sam, kar ma azo ga dan farin mutum da basu gaji da'a ba ko kadan" ran Momma na suya tace "Ina yin magana sai yace min tausayinta yake ji, akan ta babu irin maganan da baya ganin daman fada min, Idona fa ya kalla yace min ta zama 'yarsa da zatayi amfani da sunansa na matsayin ubanta sai inyi abunda zanyi, ki fadamin dan Allah ko dutse ne a qirjina bazan ji dacin hakan ba? A yanda Baban Jidda ya juya hali akan yarinyar nan shi yafi komai baqanta min rai, ba haka nasan mijina a baya ba Maman kareem, Yarima mutum ne da Idan nace banason abu to komin son da yake wa abunnan sai ya hakura dashi koda Uwah zata nuna baqin cikinta akai, ban taba tunanin akwai ranar da zatazo wai ni zai kalli Idona yace min 'Yayi abunda banaso din sai inyi abunda zanyi in na isa' Ni faaaa!" ta qarasa maganan hawayen na zuba mata tana sharesu, sai Mami ta kamo hannunta daya tace "Kiyi hakuri Maman Jidda, a gaskiya nuna miki cewan baki kai din ba shine mistake  na farko da yayi, yarinya kuma dan kince bakyason riqeta babu mai miki dole ai" sai da ta gama share hawayen sannan tace "Maman Kareem ki bani shawaran yanda zanyi, wallahi Allah ne shaida banason yarinyar nan har raina kuma bazan taba sonta ba, da nayi tunanin harda hadin bakin mijinki aka daukota amma yanda Yarima ya juye gaba daya na tabbatar da ba sa hannun shi" sai Mami ta sauqe numfashi sannan ta girgiza kai "Ko daya wallahi Maman jidda, hasalima Baban Kareem ba yadda beyi dashi akan ya hakura da daukanta ba amma ya dage akan qudirinsa. Mijinki mutum ne mai addini sosai da sanyin hali ga kuma tausayi , kuma kiyi duba da irin gidan da ya fito, shiyasa hakan yayi tasiri sosai akan yarinyar. Amma kuma shi dan wani ba'a nuna masa so irin haka, duk inda akaje aka dawo nakan nan dai shine mai tausayinka" Jinjirar ce ta katsesu da kukanta sai Mamin ta miqa mata ita ta karba, sai da Momman ta dage riganta ta saka mata abincinta a baki ta karba sannan ta dago kai tace "Kinsan sau uku kawai ya dauki yarinyar nan, amma hankalinsa na kan waccan din ana kawota ya dauketa kina gani da ita ma ya fice riqe a hannu" sai Mamin ta dan tabe baki tace "Abunnan fa ke zakiyi tufka a lamarin tun wuri, ko sama da qasa za'a hada karki karbi yarinyar ko da kun koma can gida, zaki gani shida kansa zai bayar da ita riqo a wani gurin, ai saida kwanciyar hankalin matar gida ake samun nutsuwar tafiyar da kowanne lamura" Habiba da fitowanta daga toilet kenan sai ta dan tabe baki tana girgiza kai ganin yanda Mamin ke qara kunna wani wutar a zuciyar uwar dakin nata, amma babu halin ta kwabesu.

Da irin wa'ennan maganganun Mami ta rinqa qara ingiza zuciyar Momma akan lamarin, ta rinqa dorata a hanyar da kwata kwata babu mabulla acikinta sai tarin kurakurai, kasancewan daman Momman tana neman abokin kuka  yasa taji dadin yanda Mami ta kalli lamarin a fuskar da take kallo itama, har saida likita tazo duba Momman sannan zancen nasu ya tsaidu wanda hakan ba qaramin dadi yayiwa Habiba ba, dan abune dake bayyane akwai rashin tausayi a lamarin nasu barin ma Momman saboda tun ranar farko da tace a maida yarinyar waje cikin sanyin ta bata tsoro matuqa. Sannan bata tashi yarda da rashin imanin uwar dakin nata ba sai da ta fara hanata kula da yarinyar qarfi da yaji, wanda ita batasan dame zata fasalta zuciyar Momman ba saboda duk wanda zeyiwa jinjiri dan kimanin satikai horon yunwa toh lallai rashin imanin yakai maqura.

Cikin kwanaki biyu da suka biyo baya aka sallamesu suka koma gida Habiba ta cigaba da kula da Momma sosai, sai ta tsiri goyon Fadwan akai akai ta yanda ko kitchen taje yin aiki zata kunceta ta bata madaranta, ko kuma inta shiga gyaran bandakin Momman nan ma ta sauqota ta wanke mata sayin da tayi, kuma taga nutsuwar hakan a idon Papan sosai dan burinsa shine yarinyar ta samu kulawan da ya dace daman. A kwanaki uku da suka sake biyo baya kuma yayi waya da Mai martaba a inda ya sanar dashi sunan da yake son a sakawa jinjirar, sanin cewa mahaifin nasa zai sa ayi yanka a 'yar tasa yasa yayi shiru bai kashe wayan ba bayan sun gama magana, jin haka sai dattijon nasa yace "Kana da wani abun fadi ne?" a ladabce yace "Ina neman alfarman a hada musu yankan ranka shi dade" dan shiru Mai martaba yayi da fari kafin yace "Ba damuwa". Da wannan Mahaifin nasa yasa akayi yankan raguna da shanukai akayi sadaka, a inda Yarinyar  taci suna Khadijah, Fadwa kuma aka bar mata sunanta. Cikin sati uku da 'yan kwanakin da suka biyo baya wanda ya kama new year suka hau fara shirin komawa gida.



Free page 

Bintu Musa ✍️