Episode 4
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 4
ZAHRA POV
A hankali ta idasa yafa gyalen abayar dake jikinta tana kallon madubi ganin komai yayi ne yasa ta kara sakin murmushin nan nata data saba dashi Akan fuskarta kullum. Sanyi take da Abayar da Baba ya saya masu kwanaki.
Juyowa tayi tana cewa.
“Yawwa Bahijja muje ko?”
Kallon yanayin Bahijjar tayi ganin yadda take b’ata rai tana kallon kayan jikinta tana kuma sake kallon Zahra da kyau, dan gani tayi ita kam batai wani kyau ba, Zahra tafi ta kyau a yau d’in abayar ma sai tayi danasin bawa Zahra tata data sani tata ta d’auka kawai.
“Miya Faru Bahijja?”
Zama tayi saman gado tana cewa.
“Kije kawai ni na fasa zuwa ma”
“Kamar ya naje kawai kuma Bahijja?”
“Eh na ce bazanje ba”
“Amma ai kin san duk ranar Juma’a dole muke zuwa gidan Mama Oto ko”?
“To kije kawai yau ni banda ra’ayin zuwa”
“Wai mi nake ji ne haka hayaniyarku tun waje ana ji?”
“Waifa Umma Bahijja ce wai bazata je gidan Mama Oto ba yau”
“Saboda bak’in hali ko?”
Mama ta fad’i hakan tana duban Bahijja dake k’ara b’ata fuska kamar an mata wani abu.
“Wato ke dai wannan shegen halin naki k’ara gaba yake ko?. Ub*anmi yasa kika ce ke baki zuwa?”
Shiru tayi kamar zata fashe da kuka.
“Bada ke nake magana bane shin?”
Cewar Mama tana wurga mata harara.
“To ni Mama kaina ne ke min ciwo”
“Ba wani ciwon kai wallahi, kuma tashi maza kuje ko kuma ranki idan yayi dubu saiya b’aci wallahi”
Tashi tayi har ruwan hawaye sun fara taruwa a cikin idonta tsabar yadda take jin wani malolan abu ya tsaya mata a wuya.
Haka suka fice zuwa waje suna takawa a k’afa, sunzo bakin titi Zahra ta tsaya tana cewa.
“Bari mu tare abun hawa”
“Ni bazan hau abun hawa ba ai gidan ba nisa ke akwai ba, za’a ce wani mu hau abun hawa”
Sakin baki kawai Zahra tayi tana bin Bahijja da kallon zallar mamaki, sai ka ce ba ita ce kullum duk ranar za zasuje gidan Kakar taso da ita ce ta haifi Babansu take cewa sai an hau abun hawan ba?, duk da Cewar ba wani nisa sosai, to sanin halinta yasa yauma ta rik’o masu kud’in abun hawan gudun mitar ta, sai kuma yanzu take wannan maganar?.
Girgiza kai kawai Zahra tayi tana bin bayanta dan ita kam bazata iya da rigimar Bahijja ba.
Suna tafiya ba mai magana uwar zuciyar kuwa ita ce gaba Zahra na bin bayanta.
Wasu samari ne suka tsaya inda Zahra take suna cewa.
“Please y’an mata bakiji ba?”
D’an tsayawa tayi tana gaidasu dan a girme sun girme mata.
“Dan Allah tabbaya muke?”
“To Allah yasa na sani”
“Gidan Alhaji Baita mai shidda muke nema”
D’an murmushi Zahra ta saki tana cewa.
“Ai ko wajan gidan zamuje, makwafta ne da inda zamuje, kuzo muje saina nuna maku kawai”
Bahijja dake can nesa dasu wani abu taji ya daki ranta ganin ita basu tsaida ita ba dan ita ce farkon wacce suka wuce sai ace sai Zahra zasu tsaida?, gashi ta gansu y’an gayu farare ga saje da gumo daya zagaye fuskarsu hakan ya k’ara masu kyau. Sai taga ma kamar murmushi suke tare kamar sun wani dad’e da sanin juna, har wani ji tayi zuciyarta na bugawa da k’arfin gaske tsabar b’acin rai da take ji yana sake taso mata babu dalili.
“Sai dai amma a Mota muka zo yaya za’ai kenan?”
“To kawai Ku hau motar saiku biyo mu”
“Noo baza’ai haka ba, ki shigo kawai muje tunda kince kusa ne?”
“A’a muna tare da sister ce gata can a gabanmu kuma ma am sorry bazan iya hawan motarku ba gaskiya”
Ta fad’a kawai tana yin gaba.
Murmushi Sa’id ya saki yana cewa.
“Wato Fu’ad yarinyar can ta birgeni akwai class ga sanin darajar mutane”
Fu’ad na bashi amsa suka nufi motar tasu dage gefe d’aya suka shiga suna bin bayansu.
Sun isa daga cikin motar bayan sun tsaya ta nuna masu gidan suna mata godiya ta juya da sauri tabar Wajan zuwa gidan Kakar tasu, dan taga yadda Bahijja ta rigata isa tun d’azu gashi tasan Mama Ota d’in da d’aukar zuga bare ta Bahijja dan duk cikinsu tafi ma nuna son Bahijjar kowa ya sani, duk da har ita Bahijjar ba ragamawa take ba.
Su kuwa Sa’id ya shafa kansa yana sakin huce yana bin inda tabi da kallo da inda suka shiga ya dubi abokinsa ya ce.
“Naso yi mata wata magana ne fa?”
“Da alama yau Abokin nawa ya kyasa dai?. To amma bagaka ganin tayi yarinya da yawa ne ka duba da kyau kuwa?”
“Mtswww to sai aka ce bazata iya aure a shekarun nata ba kenan?”
“Noo ba haka nake nufi bafa, kawai dai sai nake ganin kamar ita kanta Baza’a barta tayi aure a gidansu ba, baka ganin yadda ta amsa mana ne?, kamar ma bata san wata aba soyayya ba?”
“Ni ai nafi son irinsu wa’inda basu san komai ba, ace nine zan fara koya mata nawa darasin a soyayya”
“Hmm yayi to”
“To bazaka ban shawarar yadda zan sake ganinta ba?”
“Ai da alama a nan Unguwar suke”
“Kan hanya fa muka gansu?”
“Ai shine alamar duk inda suke a nan kusa ne. Kai da ko sunan yarinya baka sani ba amma harka kware mata?”
Dariya suka saki a tare suna fitowa daga motar zuwa inda gidan data nuna masu cewar nanne gidan da suke nema d’in…………