GIDAN YAWA

Episode 5

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 5

“Miye haka ke faruwa ne Babawo?”

Babawo na kuka hannunsa na kare idonsa dake ruwan hawaye ya ce.

“Abba ba Kabir bane wai ni ne nayi fitsarin kwance alhalin an san bana yi”

Abba ya girgiza kai yana duban Kabir dake cin magani ya ce.

“Kabir amma dai kasan Babawo ya wuce fitsarin kwance ko?”

“To dai Yanzu shine yayi a’ato”

“Wallahi Kawu Rabiu bashi ne yayi ba, abunnan ne yayi……

Mangare masa kai Kabir yayi yana huci ya ce.

“To d’an iska tabbayarka akai ne?”

“Kai Kabiru miye haka?, kai wai mi yasa baka da kunya ne?”

“Ni dai da kunya ta yawwa”

“Waye kake fad’a ma haka iyeee?”

Abba ya fad’a yana d’aukesa da mari.

Wani irin sakin baki yayi yana huci, yana duban Abba kamar wadda ke shirin kai masa dukan shima tsabar rashin kunyar da yake ji da ita a lokacin.

“Ko zaka rama ne?”

“Kai kai kai miye haka akeyi ne wajan nan?”

Cewar Kawu Zubairu daya nufo inda suke tsaye.

Wani kuka Kabiru ya saki ganin mahaifinsa a wajan dafe da kumatunsa ya nufi Uban nasa yana wani irin kuka kamar wadda ake yankan naman jikinsa.

“Kai uban waye ya tab’aka?”

“Abba ba Kawu Rabiu bane ya mare ni, harda rufe ni da duka Akan kawai na ce Babawo ne yayi fitsari kuma wallahi shine yayi fa”

“Ohhhoo wato kai Yaya Rabiu abun naka ya zama san kai ko?, haka kawai dan yaro ya fad’i gaskiya shine zaka kamasa da duka tsabar zalunci ko mi?, wato dan ba d’anka bane hala?”

“Yanzu Zubairu ni zaka kallah ka ce wai Kabiru ba D’ana bane?”

“Yo gashi kama nuna tun kan aje ko ina?”

“Wato dai kana nufin ban isa nayi masa hukunci ba idan yayi ba dai-dai ba?”

“Kamar ya idan yayi ba dai-dai ba wai?, ga wannan yaron naka Babawo waye ban san rashin jinsa ba da bak’ar zuciya kamar ta kafuran farko?”

“Ni banma ga abun fad’a ba a nan da har zai d’aga hannu ya ce zai mari Kabiru”

Cewar Inna Asabe. Mahaifiyar Kabirun kenan.

“Kuma ai harda laifinku ya zaku tsaya kuna ji kuna gani ya Kama min d’a da duka haka kawai”

Baki sake kawai Abba ke kallon jama’ar gidan. Wato bamai ganin laifin Zubairu yana k’aninsa zai tsaya akan d’ansa yana fad’a masa magana haka?.

Da kyar Mama ta fito tana cewa.

“Dan Allah Abban Babawo ya isa haka muje kawai”

Wani irin takaici da bakin ciki suka zo masa wuya ba yadda zaiyi dan kawai baida shi a cikinsu Shikenan shine abin wulak’antawa shida iyalansa?.

Babawo yaja hannunsa suka bar wajan suna iya jiyo yadda Inna Dije ke k’ara zuga Zubairu tana cewa.

“Idan banda iskanci da samun waje har Babawo zai ware kwanji wai zai bigi Kabiru Sai ka ce sa’ansa?”

“Au shima da bugun nasa zaiyi wato a nakasta min yaro?”

“Ai ko dai Allah ne ya kawo ka da wuri ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba”

Inna Habi dake fitowa daga d’aki tasa masu baki tana cewa.

“Abun ban haushi ma wai kamar Binta ta fito feee taja miji ita mai miji munafurcin banza”

Dan Allah ya sani sun tsane ta a gidan gaba daya matan gidan bare sunga kowaccensu dana kishiya amma banda ita har yau baida niyyar k’ara aure, har zugashi su Zubairun keyi wani lokacin Akan idan ya k’ara aure Allah zaisa arzik’insa yazo ai k’arin aure bud’i yake kawowa, su bai gansu bane duk sun fisa komai?, ai saboda basu zauna da mace d’aya bane. Shi kam idan suna fad’ar hakan saidai yayi murmushi kawai ta inama zaiyi gigin k’ara wani aure wadda ta gidan ma da D’a d’aya garesu amma abinci na gagarsu wani lokacin?, shi kam gani yake hakan kwata-kwata bafa mafita bace wacce zata b’ille.

“Ai tsabar ta gama dashi ne kawai Habiba ke kam ai ko?”

Cewar Inna Dije.

“Ai ya zama mijinta ce sai abunda ta ce masa. Yanzu da aure ya k’ara ya zauna mace d’aya ta juya sa ne?”

Cewar Zubairu.

“Abba ni dai gaskiya Kar Kawu Rabiu ya sake Mari na dan yanzu haka ji nake kamar bana jinku sosai”

“ah ah ah sha kumurunka yaro Yaya Bature ya dawo kawai ya shiga tsakanina dashi da y’ay’ana dan bazai yuwu ba yawwa”

“Hakanma yafi”

“Dan Allah Abban Babawo Kayi hakuri Ka k’ara hak’uri kaji?”

Mama ta fad’a bayan duk sun gama jin b’ab’atun jama’ar gidan a tsakar gidan yadda kowa a cikinsu yake zaginsa da iyalinsa shine abun yake mugun cin ransa, ya duk’ar da kansa kawai ya dafe kan nasa da yake jin yayi masa wani irin nauyi.

d’agowa yayi a hankali yana sauke idonsa akanta. Tsoro ne ya kamata ganin yadda idon nasa suka kad’a sukai jawur.

“Ke zan bawa hakuri ai Binta, kina matuk’ar hakurin zama da matan gidan a haka ace su duka duk sun had’e miki kai?”

Murmushi mai ciwo kawai ta saki, wai a hakan mafa bai san wasu abubuwan dake faruwa a cikin gidan ba, tunda shi fita yake kullum nemo masu abunda zasu d’anci kuma idan ya fita zai iya kaiwa dare ma bai dawo ba, koda ya dawo d’inma ba gaya masa take ba gudun b’acin ransa da kuma Kar ace tana had’asa da y’an uwansa, amma duk da haka dai ba tsira tayi ba kullum dai cikin zaginta suke………