Episode 6
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 6
BAHIJJA POV
“Abunda kike fad’a min Bahijja gaskiya ne?”
“Na rantse da Allah Oto ai kin san bazan miki k’arya ba ai ko?”
“Ai ko indai hakane ya zama dole na zauna da mahaifinku aure shine kawai ya dace daku gaba d’ayanku, bazaku ja mana abun kunya ba”
Turo baki Bahijja tayi ta ce.
“Haba Oto kuma harda ni ciki?, wadda na ce miki ni ba ruwana”
“Ai wallahi harda ke y’ar nema gara a aurar daku bazaku ja mana abun magana ba”
Bahijja dake shirin magana Zahra tayo sallama ta shigo gidan.
Wani kallo da Oto ta jefa mata yasa Zahra Shan jinin jikinta a hankali ta kai ta zauna kusa da Bahijja data baze itama Bahijjar na y’ar harararta.
“Mama Oto ina wuni?”
“Da ban wuni ba zaki ganni ne?. Wato ke yanzu har kinyi girman tsayawa da wani k’aton a waje ko?, wato baki tafasa zaki k’une ko”?
“Wallahi Mama Oto bafa tsayawa nayi dasu ba tabbaya ce kawai suka min shine ni kuma…..
Dakatar da ita Bahijja tayi wajan cewa.
“Wallahi Oto har ganinsu nayi suna dariya a tare kamar wasu Miji fa da mata”
Ido waje baki bud’e kawai Zahra ke kallon Bahijja data tak’ark’are tana mata wannan zugar.
“Ai ki barni da ita nasan matakin da zan d’auka”
“Wallahi Allah ba haka bane”
“Rufe min baki k’arya zata miki ne ko yaya?”
“A’a Mama Oto amma itama bata fahimci abun bane wallahi”
Zahra ta k’are maganar zuciyarta na bugawa tasan Oto da mitar bala’i yanzu wannan d’an abun saita maida shi babba cikin dangi kowa yaji har a k’ara ma abun gishiri da magi.
Tunaninta ne ya katse jin abunda Oton ke fad’a.
“Ai gara azo a aurar daku haka nan dama ni bana son karatun nan da shi Rabiu yake so kuyi bana so”
Hankali a tashe Zahra ta ce.
“Haba Mama Oto ai karatu yanzu shine a gaba, to duka ma nawa muke Oto?, nifa banfi shekara 18 bafa Bahijjar ce da 15”
“Au a hakan ne zaki ce Baku isa aure ba?, to idan an maku karku zauna”
“Mama Oto a dai barmu muyi karatun dai”
“Baza’a barin ba na ce, ni kake fad’a haka ko?, ai dai kunyi sakandare ko to ta isa ita?”
Dariya Bahijja ta saki yadda Oto ta kira Secondary.
“Ke kuma y’ar nema mi kike ma dariya?”
“Hhhhhh Oto bafa haka ake kiran Secondary ba”
“Ke dallah tafi can ni ina ruwana tunda ba karatun bokayen nan naku nayi ba”
“Bokaye kuma Oto”?
“Ahh yo to miye marabarsu da bokayen to?”
“Hmmmm”
“Kyace hmmm mana, su kuma y’an iskan da kikaje kika tsaya dasu su waye saiki ce su turo gidanku ayi maganar aure”
K’asa da kanta kawai Zahra tayi idan Oto na wani abun kamar wacce ta zare fa. Bamai babban laifi sai Bahijjar da bata da man kai itama.
“Bahijja tashi mu tafi kinga dare ya fara”
“Au yau bazaku kai mangaruba d’in ba?, saboda kawai nayi magana keda baki san gaskiya ko?”
“A’a kin san ai Baba ya ce mu daina kaiwa daren nan?”
“To ai Shikenan yayi kuje d’in zan daiyi magana da Mahaifin naku”
Sosai hakan da Zahra taji sai taji gabanta ya fad’i daurewa kawai tayi ta saki murmushi kad’an bata ce komai ba.
“Bari na d’akko maku abu a d’aki Ku kaima Ummar taku”
Shigewa d’aki Mama Oto tayi ta fito da wata leda tana mik’a masu, godiya Zahra tayi mata jawo hannun Bahijja da sauri suka fice daga gidan.
Suna fita Bahijja ta wani warce hannunta tana turo baki.
“Ke yanzu Bahijja abunda kikai ya dace kenan?”
“Mi kuma nayi?”
Bahijjar ta fad’a tana duban Zahra da wani irin kallo.
“Amma kin san dai bai kamata kije ki fad’ama Mama Oto wannan maganar ba ko?, saboda kin San dama da kyar ta bari zamu ci gaba da karatun nan, danmi yanzu zaki zo ki fad’a mata hakan?, kin san hakan miye zaije ya jawo ne?”
Tab’e baki Bahijja tayi ko a jikinta dama ita bafa wani son karatun take ba dan haka ta ce.
“Ni wannan ba damuwa ta ba ce yawwa”
“Mi kike nufi ne?”
“Ohho”
“Wai mi yasa Bahijja baki da kunya ne da tunani idan kikai wani abun ne?”
Juyowa tayi da harta fara tayi tana kallon Zahra kallo irin rainin nan ta ce.
“Karki sake ce min banda kunya.
Kuma bari kiji sai nayi sanadiyar rusa karatun nan, danni dama baya gabana”
“Idan har baya gabanki ni miye zaisa kije kimin wannan sharrin?”
“Au sharrin na miki ma?”
“Kware kuwa ai kin san bazan tab’a tsayawa da wani saurayi dan so ba”
“Wannan kuma keta shafa”
Da k’arfi Zahra ta d’aga hannu zata sauke ma Bahijja mari, mita tuna kuma ta sauke tana cije baki.
Bahijja dake dubanta da mamaki ta saki wata kwafa had’e da juyawa ta ci gaba da tafiya.
Bin bayanta kawai Zahra tayi bak’in cikin hali irin na Bahijja na cika mata zuciya. Ta rasa wanne irin abu ne ke damun y’ar uwar tata da tunda suka tasa ba wata jituwa a tsakaninsu, saima banbancin ra’ayi da halayya yadda kasan ba gida d’aya suke ba, sai ka ce irin y’an uban d’in nan suke da Bahijjar bawai Uwa d’aya Uba d’aya ba………..