GIDAN YAWA

Episode 7

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 7

“Yaya Bature ance kana son gani na?”

“Eh to sai yanzu kaga damar zuwan amsa kiran nawa?”

“Ba haka bane naje sarar itace ne shi yasa saida na gama nazo”

Gyara zama Yaya Bature yayi yana duban Zubairu ya ce.

“Zubairu ya kawo min k’arar cewa ka samar masa yaro kana duka alhalin Babawo ne mai laifin”

Shiru ya ratsa wajan yayi kasak’e yana jin wannan abun mamaki.

“Kenan ni ban isa na yanke hukunci akanshi Kabirun ba?, kuna nuna min fa kamar cewar ba d’ana bane?”

“Kaga kaji ance maka wani abu wai shin Rabiu?”

Cewar Yaya Basiru dake zaune gefensa.

Girgiza kai yayi yana jin Yaya Bature na sake cewa.

“Kaima kasan dai Babawo da bak’ar zuciya kai kasan da wahala a kwashe dashi ta dad’i, amma kawai daga zuwa yaro ya fad’a maka k’arya da gaskiya saika hau Ka zauna ka kuma kama Kabiru da duka?, idan ma adalci zakai a gane duka Ka d’auke su y’ay’an naka da kake ta fad’a basai ka had’e su duka ba kayi masu hukunci tare?”

“Yawwa ai kaga hakan idan yayi shine zan yarda ya d’aukesu da Babawon duk d’aya a wajansa, amma haka kawai nazo naga ya kwashe Kabiru da marin dahar yanzu yana cewa baya ma ji sosai tsabar zafin marin daya d’aukesa dashi”

Zubairun ya idasa maganar yana hararar Abba dake zaune tsakiyarsu kansa k’asa yadda kasan shine k’arami duk wajan a cikinsu, a ciki Sama’ila ne kawai babu danshi yafi tafiye-tafiye zuwa Lagos su Ibadan haka, neman kud’i. A girme yabawa Zubairu shekaru sama da biyar, amma shine aka kirasa a gabansa harda shi ake mai wannan wulakancin kenan?.

“Ana magana kayi shiru Rabiu?”

“A’a Yaya Basiru ni mi zance?, kawai kuyi abunda ya ce maku badai cewa yayi na fita a harkar y’ay’ansa ba?, to insha Allah zanyi hakan”

“Au haka ka ce?, kai ana shirin dai-daita komai kai kuma kana cewa haka nan?”

“A’a Yaya Basiru ai an riga an yarda da abinda ya kawo ya ce nayi, dan haka inaga abunda na ce shine kawai zanyi na fita harkarsa da iyalinsa tunda ya riga da ya nuna min cewar nasa ba nawa bane”

“Wato Rabiu baka dai kunya ko?”

Tashi tsaye yayi dan gaya idan ya zauna wajan nasu za’a cigaba da b’acin rai ne, dan daya san ma hakane bazai zo ba akan wannan maganar banzar da bata kai ta kawo ba akan yara kawai?.

“Au tashi kake yi ma ana maka magana?”

Wani kallo daya jefama Zubairu da yayi maganar saida yasha jinin jikinsa ya nuna sa da yatsa ya ce.

“Wai ko ka manta ne ni ba sa’anka bane?, ko kana d’auka dan kana da arzik’i zan zauna ka takani kamar yadda kake ma wasu?”

Zabura Yaya Bature yayi sai yaji kamar dashi yake wannan maganar ma, domin yadda Zubairu ke basu kud’i har tsoron masa magana suke idan yayi ko ba dai-dai bane. Shima kuma Zubairu tunda suka taso yaga Rabiun yafisa kwarjini da komai gashi duk cikinsu shine kad’ai yayi karatun boko harya wuce yayi digress d’insa tun lokacin Zubairu ya tsani Rabiu kamar ba uwa d’aya Uba d’aya suke da juna ba.

“Kai kuji min yaro dan Allah?”

Cewar Yaya Bature.

Bin bayansa sukai da kallo dan bai tsaya ba yana fad’ama Zubairu haka yayi gaba ransa a matuk’ar b’ace.

“Ai ya rigada ya raina mutane ne kawai Yaya Bature”

Cewar Zubairu yana mik’ewa sai yaji Yaya Basiru na cewa.

“Duk da haka dai Zubairu kasan dai Rabiu Yaya ne a wajanka ko?, to ya kamata Ka rink’a kiyaye harshenka gaskiya”

Kud’i ya fito yana mik’ama Yaya Bature dubu biyar. Washe baki Yaya Bature yayi idonsa kamar zai fad’o baki washe ya ce.

“Ah ah anyi haka Zubairu kai baka gajiya ne da hidima haka?”

Murmushi yayi ransa fas ya mik’ama Yaya Basiru da yayi gum da baki ganin an fiddo kud’i kar yaje yayi wata magana yajama kansa.

“Au harda ni Zubairu?”

“Ai ba wani abu Yaya Basiru”

“Kai Kai kai ai ko mun gode ai kawai ka rabu da wancan zuciya ke ja masa yana ma arzik’i k’ulli daya zauna da yanzu bai samu wannan ba don Allah?”

Cewar Yaya Basiru baki washe.

“Ai bak’in ciki yake damu bare ni da yake ganin nayi masa nisa, girman kaine dashi shine ke hanasa biyayya ya ci arzik’i yabar kuma arzik’i inda yake”

“Wannan haka yake. Kawai ka rabu dashi da tsiyar da yake fama da ita”.

********** “Wai ance a kawo wanki?”

Kallon yaron da yayo sallama Inna Habi tayi tana tab’e baki dan tasan ba wacce ke wanki da Surfen Masara ko wake sai Binta dan haka ta dubi yaron da kyau jin Bintar bata lek’o ba ta ce.

“Kai kaje Ka ce bata nan”

Yaro ya juya ya fice.

Ita ko Mama sallah take tana ta so ta idar domin zuwa ga yaron amma kawai taji abunda Inna Habin ke fad’a.

A tsanake ta gama sallar ta shafa addu’a tana jin ba dad’i a ranta dan samun wankin a yanzu zasu samu na cin abinci zuwa ko gobe ne dan yau ba laifi mai gidan nata yayi Faskaran icce an biya sa yayo masu cefane dan harta d’ora abincin ma.

Fitowa tayi tana duba murhun data d’ora ruwan shinkafa ganin yadda tukwanyar ta jirkice ruwan ciki ya zube ya kashe wutar, yasa ta saurin zuwa ta sauke tukwanyar ta gyara wutar da kyar ta kama tana maida tukwanyar akan wutar ta jawo kujera ta zauna kawai dan tasan zaman harta gama saifi mata.

“Amma yanzu fisbilillahi Habi kina ganin tukwanyar ta jirkice a murhun nan mai mak’on ki gyara min?, sana kuma kin san fa ina d’aki yaron nan ya shigo masu kawo wankin nan ai saiki tsaida shi ko sallah fa nayi kawai shi yasa kika ji shiru ban amsa ba”

A yadda ta fad’i maganar cikin sanyi bada wata manufa ba ko fad’a duk hakan baisa Inna Habi yi mata magana mai dad’i kamar yadda tayi mata ba, saima wata uwar harara data jefa mata da wani kallo tana fad’in.

“To ko zaki dake ni ne dan kawai nak’i gyara miki tukwanya da tsaida yaro?, ko kuwa dama gadi kika aje ni na miki ne shine ban sani ba?”

Girgiza kawai Mama d’in tayi tana yin shiru kawai. Ai ko Inna Habi da haushi da takaicin shirun data mata ya cikata ta fara fad’ar maganganu akan Mama d’in son ranta…………