RAYUWAR SAMHAD

.. ..

by @maryamstar248



BOOK TWO PAGE 3⃣2⃣

Su na ahaka ne doctor ya ƙaraso, bayan shigowar doctor ne police ɗin da Alhaji Basgir ya kira auka ƙaraso, alfarmar mintuna ashirin Alhaji Bashir ya nema akan yana so ya karashe kashe wani case ɗin idan ya gama za'a tafi da me laifi, basu musa ba suka zauna jiran agama abinda za'ayi a basu me laifi su tafi da ita, tunda anriga da an sanar musu.


Bayan taimakon da Doctor ya bawa Daddy ne aka samu ya dawo hayyacinsa, amma hawaye sun gaza daina zuba daga idanuwansa, tsantsar tsanar Mamy ce damɓare a cikin rinannun idanuwansa, a hankali ya tashi zaune dafe da zuciyarshi da ke masa tsananin zafi da ƙuna, cikin dishewar murya ya ce.


"Beela Allah ya isa tsakanina da ke, kin cutar da rayuwata, kin tarwatsamin ahali, kin sabauta zuciyata ta hanyar rabata da abinda take matuƙar ƙauna, bazan yafe maki ba kije ke da Allah, insha Allahu sai rayuwarki ta ɗaiɗaita, sai kin zama abar tausayi, muguwa kawai me baƙin hali, bansan mi nagani awajenki ba da nar na nace akan saina aure ki, ina kaico da san zuciyar da na gwadawa matata akan ki, kije na sake ki saki uku, na ƙarasa datse ɗayar igiyar da ke tsakanina da ke, police ku ficemin da wannan muguwar azzalumar matar me tarwatsa farin cikin ahali, bana son sake ganinta a gabana na tsaneta."


Fizge-fizge Daddy ya fara tare da maganganu masu ban taudayi, Alhaji Bashir ganin halin da ɗanshi ke ciki ya saka shi bawa police damar tafiya sa Mamy.

Zumbur Maman Nabila ta tashi tare da kare ƴarta ta na kumfar baki akan babu ubanda ya isa ya tafi da ita, ganin zata ɓatawa mutane lokaci ya saka a hurzuƙe Malam Umar ya ce.
"Idan ta tsaya ɓata muku lokaci ku haɗa harda ita ku tafi kawai."
Maman Nabila ganin wa ta jibgegiyar mace ƴar sanda ta tunkarota ta na huci ya saka ta saki Mamy da ke ta rizgar uban kuka.

Bayan an tafi da Mamy Maman Nabila ta saka kuka gami da kururuwa taje gaban Alhaji Bashir ta ɗuka ta na ma shi magiya akan ya saka baki a dawo ma ta ƴarta, bata san sanda Malam Umar ya taso ba sai jin saukar wani wawan bahagon mari daya ɗauke ta da shi tare da zazzafan gargaɗi akan idan ta saki ta sake magana zai datse igiyar auren da ke tsakaninsu.
Gum tai ta koma ta zauna dan ko da wasa ba zatai gangancin barin Malam Umar ya sake ta ba, tasan shine da Mamy sune gatanta kuma masu rufa ma ta asiri.

Murmushi Alhaji Bashir yai tare da kiran sunan Samha wacce ta lafe jikin mijinta ta na ta faman kuka, shi kuma duk ya rikice sai rarrashinta ya ke.

Cikin sheshshekar kuka ta amsa tare da rarrafowa ta dawo gabanshi ta zauna dan yanzu ko tashi bata iyawa.


Shafa kanta yai tare da shi ma ta albarka sannan ya ce.
"Zan gabatar muku da Aishatu Samha matar jikana Mubeen wacce ta kasance ɗiya ga Abdullahi, ita ɗin ɗiyace ga marigayiya Nabila ƙawar marigayiya Aisha kuma ƙanwa ga Sarhabila."

Tsit kowa yai a wajen su na mamakin wannan lamari, Maman Aisha ce ta rarrafo zuwa gaban Alhaji Bashir ta damki Samha tare da fashewa da sabon kuka ta na shafa fuskarta, daga yanayin yanda ta ke kukan zaka tabbatar da kukan farin ciki ne, yayinda Malam Ahman ya goge kwallarshi ya na ta faman sakin murmushi, Maman Nabila kuwa sakin baki tai kamar sakara ta na kalon Abbu sannan ta dawo ta kalli Samha, da ƙyar cikin in ina ta samu ta furta.
"Wa....wa....wann...wannance jikata ɗiyar na...na...nab..."

Sai kuma wani sabon kukan ya sake kwace ma ta, yayinda Hajiya Adama ke zaune kurum ba ta fahimtar komi sai bin kowa take da kallo kurum dan sam ta kasa gane inda aka dosa.

Basu dawo daga wannan mamakinba aka kira wayar Alhaji Bashir inda ya ɗaga tare da bada izinin shigowa.


Buɗe ƙofar akai wani matashin saurayi wankan tarwaɗa ya fara bayyana kamin daga bisani Baban Saniga da Mama suma suka shigo a tare.

Zabura Mubeen Samha Abbu da Hajiya Adama sukai a tare, bakin kowanen su na karkawa amma sun kasa cewa komi, ita kuwa Maman Nabila suman zaune tai ganin kamanni irin na marigayiya ɗiyarta zayyane akan fuskar matashin saurayin.

DAGA ALƘALAMIN 

MARYAM STAR ⭐⭐⭐




🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

DAGA ALƘALAMIN 
MARYAM STAR ⭐⭐