Sawun Giwa

10

by @ammimalami99

Last free chapter!!


~~


Shekaru ashirin baya


"Wai kin dauka wasa nakeyi miki koh" 


Hanif yake fada daga inda yake zaune sanda Muneera ke mika masa kofin ruwan da ta zuba mai. 


"Toh Ya Hanif wannan maganar taka batada kai bare kafa, ya za'ayi El Yakoub ya ciri kudi naira akan naira har naira miliyan arba'in me zaiyi dasu toh?" Ta gama fada bayan ta zauna. 


Hanif ya kada kai dan ruwan data basa ma kasa sha yayi ya mayar dasu kan center table inda ta kawo mai juice mai sanyi na inibi da ruwa a cikin jug sai dambun nama. 

Muneera tabi kofin da ya ajiye da kallo dan ita ta basa ruwan ne koh zaiji sanyi a zuciyarsa, sanyin da zai wanke mai abunda ya lullube mai zuciya har yake zuwar mata da wani zancen da bata gama fahimtarsa ba. 


"Ni nake aiki da El Yakoub a office ni nasan me yake faruwa. Shekaran jiya Abba yayi signing contract din wasu kayan da za'a shigo dasu daga China Naira miliyan goma. El Yakoub ya ciri naira miliyan ashirin"


"Saboda meyasa toh" Muneeran ta tambayesa idanuwanta na haskawa da wani abu mai kama da mamaki. Abunda tun dazu Hanif yake jira ya gani kenan dan fara saqa mata gadar zaren da zata kaisa ga tasa nasarar tunda har El Yakoub ya san yanda yayi ya auri Muneerar alhali shi yakeda wannan kudirin tuntuni saboda shima ya rab'i dukiyarta kasancewarsa d'an uwanta na gefen uba. Ya daga kafadunsa alamar bai sani ba. 


"Ina fada miki koh dole El Yakoub yana tsara wani abu ne" 


"Ki kalla" ya cigaba yana yana ware mata yatsun hannunsa na dama


"Kuna shekara nawa aka matsa sai anyi aurenku?" ya tambaya yana hade babban yatsan hannun da karamin gabaki daya alamar lissafi zai mata kenan kuma yayi shiru yana jira Muneera tayi lissafin tambayar da ya mata a kanta 


"Watanki nawa a gidan kika haihu?" Ya sakeyin shiru dan ya bata damar yin lissafin 


"Sannan yana gama makaranta Abba ya basa babban matsayi a babban kamfaninsa" 


"Sannan kiga yanda Abba yake ji dashi dan a yanda Abba yake jin shawaran El Yakoub akan aikin nan koh wallahi koh ke kika ce masa kar ayi abunda El Yakoub yace ayin bazai fasa ba kinji na rantse miki" 


Wannan maganar ta daki Muneera dan dai tasan yanda mahifinta yake tsananin ji da ita kuma koh me tace tanaso ayi toh shi kuwa za'ayin idan tace bataso kuma baza'ayi ba. Wa'ensu irin maganganu ne Ya Hanif d'an uwanta yake fada mata yanxu?


"Allah kadai yasan wani irin aiki sukayi suka rike bakin Abba dan nidai nasan wallahi ba haka kawai suka barsa ba" 


Hanif ya cigaba da fada zuciyarsa na washewa da ganin yadda kalamansa ke tasiri akan Muneera kafin kuma ya budi bakinsa ya fadi layin maganar da Muneera tajisu tamkar saukar bam a kanta dan sune asali kuma tubalin duk wani abu da ya biyo baya a cikin rayuwarsu har izuwa yanxu saboda sune kalaman da suka saka shakku da zargin El Yakoub din a ranta har suka kaita shiga ramin da Hanif ya haka musu suka aikata abinda ya rushe komai da komai. Abinda yayi sanadin rugurgujewar y'ar rayuwar da El Yakoub ya fara kokarin gina musu a tare. 


"Kawai so yake ya tsufar dake shi yasa ya ajiye ki a gida kina kular masa da yaronsa kinga yana gama kwasar rabonsa zaije yayi aurensa ke kuma kina nan"



~~


Present....


YK Ventures, Bauchi


Hayowarta saman kenan kuma maimakon ta iske Ayo kadai a wajenta da ta saba zama gaban counter dinnan sai ta hango Habeeb da Ameer zaune a kan kujerun nan dake tsakiyar wajen sun baza takardunsu a kan center table dinda ke wajen tareda Kabir da wata mata Mrs.Onukusi. Ameer yana dagowa yaganta ya sakin mata murmushi da mata alamar ta karaso dan ana tattaunawa ne akan meeting dinnan na gobe. 


Sai kawai ta zauna itama aka fara aikin da ita Habeeb yana briefing dinta akan sabbin abubuwan da aka kara saboda dama yakamata ace meeting din ranar Wednesday ne amma sai mutanen suka daga shi zuwa gobe akan wani uzuri wanda hakan ya saka dole su kammala komai da zasu gabatar musu yau dinnan. Suka cigaba da aikin har sanda taje office dinta tayi printing wasu takardu ta sake fitowa kuma a cikin ranta kawai tambayar kanta takeyi ina El Yakoub? 


El Yakoub dinda tun dazu magana daya biyu sai Habeeb yace idan yazo kaza. Idan yazo kaza. Kuma da kowani ambaton sunansa zuciyarta tana sake tunano mata abunda ya faru tsakaninsu ne jiya da daddare. Yanda komai ya faru cikin wucewar sakanni amma ita a wajenta ganin su tayi kamar wani zamani daya. Allah ya gani har taje kwanciyar bacci abunne a ranta duk kuwa da ba wani abunne ya faru ba amma yanda yakai jajayen yatsun sa ya kamo gefen gyalen nan da yanda zuciyarta ta ringa harbawa kamar zata fasa allon kirjinta ta fito wani abu ne da bazata taba iya mantasa ba da kuma wannan layin maganar da ya fada da har yanxu bata gama rarrabe kalaman ba dan gano ma'anarsu 


 "You don't have to distract yourself when you're talking to me Aisha"


Ya akayi yasan cewa rike gyalen wani nau'i ne na kokarin dauke hankalinta daga yanda idanuwansa ke kokarin narkar da ita a wajen da ma kowani lokaci idan ya zuba mata su. Ta kasa fahimtar yanda idanuwansa keda irin wannan kaifi da tasirin wani abu da bata gama sanin meye shi ba. His eyes are just so full of something she can't seem to name. Bata sani ba idan ita kadai ce but a duk lokacinda ta kallesa tana ganin wannan abun, wani abu da har yanxu haruffan duniya basu kai tayi amfani dasu ba wajen fassara sa. 

Ta tuna sanda bayan ya fadi maganar ta juyo ta kallesa kafin ta daga kai ta kalli motar da koh daga bacci aka tasheta aka nuna mata ita zata shaida ta. Motar Mu'azzam. 


Taga sanda El Yakoub ya juya ganinsa zuwa ga motar bayan ya saki gyalen nata kafin ya juyo ya sake kallonta. Kuma wata kila ya karanci sanayyar motar da wanda ke ciki a idanuwanta sai kawai yayi mata sallama tana mai godiya ya shiga motarsa ya bar wajen yayinda ita kuma ta nufi motar Mu'azzam da yake fitowa daga cikinta, ya zagayo inda take suka gaisa. 

Kuma koh daga ganin yanda gabaki daya wannan rahar da ya saba zuwa da ita bata ganta a fuskarsa ba tasan cewa ganinta tareda wani ne ya haddasa hakan sai kawai ta fadi wata karyar da bata san sanda ta hada ta ba dan Allah yagani har zuwa sanda ta taka daga inda El Yakoub ya janye motarsa zuwa inda ta Mu'azzam din take tunanin kalaman El Yakoub din takeyi da yanda ya riko gyalenta shiyasa tayi mamakin abunda tace masa din. 


"Yaron oga na ne yazo karbar wasu takardu a hannuna" 


Ganin yanda Mu'azzam din ya sake bayan ta fadi kalaman ya sakata fahimtar ya yarda da ita kenan. Bata jima wajensa ba dan dama yace mata yazo kallon kwallo ne yace wa abokanansa zai karaso ya ganta kafin ya koma ya daukesu su wuce. Tana komawa cikin gida kuwa sai dakin Inna inda ta tarar da kayan dake baje a tsakiyar dakin Khausar ta fiddo komai da komai dake ciki tunda dama wajenta aka zo in ji ita Khausar din. Bayan Inna, Juwaira da kuma Khausar ita kanta mamakin yawan kayan tayi dan bayan ma kayan ciye ciye da adadin su ke da yawa hadda wasu color pencils masu kyau da wasu littafai na rubutu na makaranta wanda kana gani kasan na mata ne. 


Khausar dadi har bata san inda zata saka kanta ba. Har dasu highlighters da wasu kyawawan sets din pen da pencils da pencil case mai kyau. Kuma sai a lokacin Inna tayi maganar da Aisha tayi tsammaninta tun sanda aka fada mata El Yakoub din zaizo


"Ke Aisha meye tsakaninki da mutumin nan?" 


Daga inda take zaune tana jujjuya littafin da Khausar ta miko mata da kuma color pencils dinda ke ajiye a kafarta tayi saurin dagowa ta kalli Inna. 


"Wallahi babu komai Inna" 


"Toh nidai nasan ba bi yake duk ma'aikatansa ba yana kyautatawa y'an gidansu dan haka nasan akwai wani abun sai dai idan fadamun ne bazakiyi ba" 


Inna ta sake fada daga inda take zaune akan 1 sitter dinta inda ta saba zama. 

Aisha ta sake girgiza kanta cikin son nunawa Inna gaskiyarta.


"Inna babu komai dagaske, inba wannan ba babu wani abu da ya taba shiga tsakanina dashi idan ba aiki ba" 


Inna ta jinjina kanta bayan tayi shiru na d'an sakanni tana kallon Aishar dakin yayi tsit dan daga Khausar dake hayaniyar kallon kayan nan har ma da Juwaira dake zaune a kasan carpet din ana kallon kayan da itama shiru sukayi suna sauraren Innar da Aisha. 


"Shikenan, amma dai ki tsaida hankalinki waje daya Aisha kuma ki tsare mutuncinki irin wa'ennan mutanen da dukiya ta zauna musu ba abun yarda bane. Sannan ki rike addu'a kullum nasihata gareku kenan" 


Aisha ta amsata da toh tana sunkuyar da kanta dan haka kawai itama sai ta samu kanta da tambayar meye ainahin abunda ke tsakaninta da El Yakoub din. Koh dai dagaske akwai wani abun kamar yadda Juwaira da Inna sukayi tunani saidai wannan tunanin da ma tushen tunani sun wargaje ne tareda bushewa suna bin iska kamar an watsar da toka sanda El Yakoub ya tako kafarsa cikin kamfanin yana iske su inda suke zaune wajajen karfe goma na safe. Kuma tun bayan kallo dayan nan da yayi mata bayan ta gaishe sa bai sake kallon gefenta ba. Koh wata tambaya ya watso mata da zata basa amsar ta bazai kalleta ba har ta gama masa bayanin da zatayi kuwa sabanin daa da yakan dago ya zuba mata idanuwansa koh ya jinjina kansa ahankali alamar gamsuwa.


Koh sanda sha daya tayi taje ta hado masa matcha da kuma yankan apple mango dinsa da ya kwana a fridge yayi sanyi dan koh ita da take yankansa sai da taji kwadayinsa bai kalleta ba. Itama kawai sai ta tattara sa ta ajiye gefe tana sake jaddada ma kanta kamar yanda ta fadawa Inna jiya cewa ba komai tsakaninsu sai aiki kyautatawa ce kawai irin tasa. Wani abu da taji yana cizon kasan zuciyarta kadan kadan batareda ita kanta tasan dalili ba.


"Amma yau bakida wani aikin da zakiyi koh and zaki barni na saukeki gida" 


Ameer yake fada mata sanda suka gama aikinsu karfe shida na yamma kuma Allah yagani yanda take jin gajiya a jikinta a wannan lokacin ji take dama tana rufe idanuwanta zata ganta a kan katifarta. 


"Ranar ma ai saboda za'ayi ruwa ne shiyasa na yarda" 


Ta bashi amsa tana kashe ipad dinta da tazo da ita yau dan samun saukin wasu ayyukan ta saka ta a cikin jakar ratayar ta. Taji dariyar da Ameer yayi yana cewa 


"Ah haba"


Daidai sanda Habeeb ya fito daga office dinta El Yakoub a bayansa yana sanye da jacket din suit da ya mayar kuma sabanin Habeeb dake rike da jakar da yake zuwa aiki da ita shi yana rikeda jakar laptop dinsa ne kawai sai wasu files guda biyu da wayarsa. Kuma sai alokacin ta samu yi mai kallon kwarai, a sanda ya mata kallo daya yana dauke idanuwansa bayan sun fito din. Sai taga kamar idanuwansa sun fada dan idan ba idanuwanta bane ba ma sai tace kamar bashida lafiya kuma hakanne kuwa dan jiya bayan El Yakoub ya bar kofar gidansu wani ciwon kirji ne ya farmake sa wanda ya saka ba shiri ya paka motarsa gefen hanya yana kwantar da kansa jikin headrest din kujerarsa bayan ya sanya maganinshi karkashin harshensa. 


Ya lumshe idanuwansa yana sauraren bugun zuciyarsa a cikin bangon kirjinsa da yanda zafin ciwo ke zarce kirjin nasa zuwa duk wata jijiya dake jikinsa. Ya dafe saitin zuciyar yana sauke numfashi ta baki cikin son sama wa kansa sauki tareda kiran sunayen Allah a ransa. Mafi yawancin lokuta ciwon nasa yana tashi ne idan ya tuna wani abu dake taba zuciyarsa koh yayi wani aiki na gajiyarwa da zai daga rate din bugun zuciyar. Wannan karon lumshe idanuwansa kawai yayi yana kokarin fahimtar ainahin abunda ya tada ciwon nasa. Kuma duk cikin tunanin nasa abu daya kwakwalwarsa ke tariyo masa shine sanda Aisha ta waiga ta kalli motar nan da yanda yanayinta ya chanja lokaci daya attention dinta gabaki daya yana kau daga kansa zuwa ga na cikin motar. Kuma zai rantse a yanda yake tuno komai din dai dai wannan lokacin ne bugun zuciyarsa ya kara karfi kuma bai san ainahin meye yaji a wannan lokacin ba dan ba ya ma iya tuna kalaman da yayi amfani dasu wajen yi mata sallama ya shige motarsa. 

Abunda kawai ke daure masa kai shine menene hadin Aisha, da na cikin motan da kuma ciwon kirjinsa?? 


Da kyar ya iya kai kansa gida dan maganin nasa kaso talatin kawai ya iya cire masa na ciwon. Kuma y'ar jinyar da yayi da daddaren nan kafin ya samu bacci ya daukesa ne ya saka sa yin lattin zuwa aiki. Koh sanda zaizo da safen nan Magaji ne ya tuko sa shima kuma dan zuwan nasa ya zama dole ne saboda mutanen da zasu zo gobe sunada matukar mahimmanci ga kamfaninsa shiyasa ya daure yazo office dinnan yau su kamalla komai tunda mutanen sun daga tafiyar tasu zuwa gobe. A hanyar tasu ta zuwa office dinne ya sake maimaitawa kansa karatun cewa Aisha secretaryn sa ce kawai babu kari bare ragi duk wani abu da ya hada sa yanada dalilin sa banda abu daya kwara daya tal wanda yayi na hana Ameer kai ta gida shekaran jiya. Shi kadai ne bai samu damar samo masa dalili ba kuma bai bawa kansa damar dulmiyawa a tunaninsa ba. Shiyasa koh yanxu da yaga sun sakko kasa tana nufar motar Ameer din bai ce komai ba. Ya juya yayi taku daya, biyu, uku kafin ya kasa rikewa ya juyo din. 


"Aisha" ya kira sunanta, ya rabb. Ya lumshe idanuwansa sanda ta juyo yana sake budesu. 


"Sir" 


Aisha ta amsa sa tana juyowa dan itama tsakani da Allah bata san meyasa ba tana taka kafarta ne tareda bugun zuciyarta da fatan ya kira sunan nata din. 


"Zo" ya fada. 


Sai ta taka kafar tata kuwa ta nufesan kamar yanda ya bukata tana jin idanuwan Ameer a kanta daga inda yake tsaye yana bude kofar motarsa. 


"Sir" ta sake fada bayan ta karaso gabansa. Ta kalli sanda ya daga jajayen yatsunsa ya shafa goshinsa harma da sanda ya cije lebensa na kasa kafin yace 


"Karki manta edits dinda zakiyi a document dinnan, it's very important bana son kuskure" 


Ta gyada kanta ahankali tana jin zuciyarta na fadawa can can can cikin cikinta. 


"In sha Allah, idan nagama zan turo maka" 


Kuma a wannan lokacin gajiyar dake cikin jikinsa da ma sauran ciwon nan da bai gama barinsa ba ya saka ya buda baki kawai yace 


"No, ki barsa idan nazo gobe sai nayi reviewing komai kafin meeting din" 


Sai ta gyada kanta "Okay sir" 


Yayi shiru na wucewar sakanni biyu kafin ya juya kawai yana nufar motarsa. Aisha ta bi bayansa da kallo. Shikenan dama???


~~


Nana ta sake jan wani dogon tsaki daga inda take zaune kan dakalin wajen wanke wanken su tana kwashe ragowar miyar kubewar data rage cikin plate dinda su Juwaira suka ci abinci tana juyewa cikin bokitin sharar dake gefenta tana yatsine fuska. 


Ta sake jan wani tsakin tana ji kamar ta saka ihu dan kawai Mama taga yau bata fita ba wato shine ta dauki wanke wanke ta dora mata akai a cikin daren nan haba dan Allah gashi Allah yagani ita bason harkar tuwon nan takeyi ba. Ta sake jan tsaki sanda taji wayar Maman ta nokia data ara mata fitilarta tayi wanke wanken na kokarin zamowa daga cikin hular kanta dan sakala ta tayi gaban hular tunda Nepa sunki kawo wuta daren ranar gabaki daya dan wulakanci. Gashi itama wayarta ba wani charge gareta ba shiyasa ta ajiyeta karta kunna flashlight charge ya karasa cinyewa shiyasa taji haushin kudin nan da Yusuf ya hana mata dan so tayi ta ta ciri koh dubu goma ne a ciki ta siya power bank. Gashi shi kuma wannan dan ** Mu'azzam din data saci numbersa daga wayar Aisha ta turawa sako koh amsa sakon nata baiyi ba bare ta samu damar yin wayar dashi kamar yanda ta bukata. 


Ga tulin uban haushin rashin samun Alhajin nan da taso a hadata dashi dan cewa yai wai yayi tafiya Lagos kuma da Rafi'a ta tambayesa kudi cewa yayi bazai tura ba sai ya dawo ya tabbatar cewa Nanar ce dagaske dan bazai yadda Rafi'a tamai wayo ba. Duk wa'ennan abubuwan ne suka sake taruwa suka haddasa mata bakin cikin da take ciki a ranar. Barinma idan ta waiga tsakiyar gidan inda su Inna suka shimfida katuwar tabarma sun baje suna hira yayinda Aisha ke zaune a wajen itama ta jingina da bango ipad dinnan a cinyar ta tana dannen dannen iyayi. Ita sai taga ma kamar kuri Aishar keyi da wayar, so take ta nuna mata ta kai inda bata kai ba shiyasa. 


Sai bayan hayaniyar kanta ta sauka sanda ta gama wanke kwannan nan tana dauraye su ta jiyo maganar data haddasa mata faduwar gaba tareda haska mata hanyar mabullin samun nasararta na yin sanadin barin aikin Aisha. Ta jiyo sanda Inna ke tambayar Aisha wai dannen dannen nan har yanxu bai kare ba ita fa damunta take da karar nan da sanda Aisha ke baiwa Inna sharhin mahimmancin aikin da takeyi da manyan bakin da zasuyi gobe. 


"Yanxu wannan file din da nake hadawa fa Inna duk abubuwan da za'a gabatar ne a meeting din" ta kara da 


"In ban gama hada file din ba ai da matsala" 


Taji sanda Inna ke cewa toh ta dai kiyaye bakinta ta fadi alkhairi koh tayi shiru. Nana ta murmusa ahankali daga inda take saka wani kwano a cikin katon kwandon da uwarta ke saka kwannan ta. Lallai kuwa Aisha tayi kuskuren fadan wannan maganar sanda take nan, ashe da Maman Nana tace mata tazo tayi wanke wanken nan wani abunne Allah ya tanadar mata ashe wata kofa ce ubangiji zai bude mata da zata taka cikinta da nasarar rugurguje rayuwar Aisha a tunaninta kenan ba. Kuma ita kanta Nanar tasan cewa bata taba rokar Allah abu da duka zuciyarta ba a rayuwarta kap kamar ranar ba. Yanda ta ringa rokon Allah ubangiji ya saka Aisha ta kwana da wayar nan a dakinsu. Kuma hakan ce ta kasance din kuwa dan bayan Nepa sun kawo wuta chan wajajen karfe goma Inna da Khausar suka shige daki itama Aisha tattaro kayakkinta tayi hadda wannan wayar tayo dakinsu inda Nana ta kunna Tv tana kallon sabon film dinda ta karbo aronsa shekaran jiya wanda sam hankalinta sam ba akai yake ba. Allah Allah take Aisha ta shigo dakin nan da wayar. 


Mintina kusan ashirin kuwa da shigowarta Juwaira itama ta shigo dakin sai kawai Nanar ta tashi tana rufo kofar gabaki daya da cewar 


"Sai ku shigo ku ringa barin kofa a bude mutum yana bacci sauro na cin ubansa, mtcheeww" 


Wannan rufe kofar datayi ne ya saka Aisha fasa komawa dakin Inna kamar yanda tayi niyya ta mike ahankali daga inda take zaune ta nufi windown dakinsu ta bude sanda taji Khausar na kokarin komawa dakin Inna bayan taje bandaki ta dawo. 


"Khausar dakko min charger ipad dina cikin jaka ta" 


"Toh" 


Khausar ta fada tana shigewa dakin. Aisha ta jirata har sanda taje ta dakko charger ta miko mata. Ta rufo net din windown kafin ta dawo cikin dakin ta tsugunna gefen T.V inda extension yake ta saka kafin ta dakko wayar ta laka tana killace ta can gefen inda ba wanda zai taka ta tana komawa saman katifarta. Juwaira dama littafinta take saurare ta saka wayar a kunnenta ita ma kuwa kawai sai ta danna kiran Mu'azzam dan a irin wannan lokutan mafi yawanci yana kiranta kafin tayi bacci. Bai dauka ba har wayar ta gama ringing dinta ta gama itama kuma bata sake kira ba ta shiga cikin files dinta na wayar tana bude wani littafi da Juwaira ta addabeta sai ta karanta wai shi IZAYA na pherty. Da farko ma kin kulata tayi sai bayan ta fada mata ai itace marubuciyar Mulki koh Sarauta da Farar Taska tukunna ta yadda zata karanta din dan littafin shima ba karaman dadi ya mata ba. 


Tana cikin karatunsa sanda Nana ta kashe kallon itama ta samu gefen katifarsu ta kwanta. Mintina ashirin da haka bacci ya dauki Aisha. Mintina goma da baccin Aisha itama Juwaira tayi bacci kuma sai da Nana ta jira awa daya cip. Awa daya cip cip da tabbacin cewa baccin Aisha da Juwaira yayi nisa tukunna ta mike zaune. 


( Oh what wickedness can make us do Allah karka bamu ikon yin hassada da kowa. Allah ka kare mu da aikata sharri ga kowa ya rabbi. )


Tayi sadaf sadaf ta nufi wajen da Aisha ta killace wayar nan kuma hannu na rawa ta damko wayar ta cire murfinta tana taba screen din. Yadda haskenta ya dallare mata fuska yasaka taji fitsari na taruwa a mararta tayi sauri ta rage hasken tana kai dubanta ga Aisha dake kwance tana baccinta hankali kwance. 


Ta janyo kasan wayar inda recent apps dinda Aishar ta shiga suka bayyana cikin wata iriyar sa'a da saida ta saka Nana sauke wata ajiyar zuciya duk kuwa da yanda zuciyar ke kadawa kamar ana buga ganga. Ta danna app din power point kamar yanda tagani. File dinnan na sama, abunda ya nuna cewa shine na karshen da Aisha tayi amfani dashi. Saida ta tabbatar da cewa shi dinne tukunna ta saka yatsanta ta danne sa options din yanda takeso tayi da document din na bayyana kansu kuma chan kasa idanuwanta suka dakko mata kalmar delete. 


Babu wani bata lokaci koh sake shawara akan abunda take kokarin yi kuma cikin rufewar ido dama zuciya gabaki daya Nana ta saka yatsa ta danna delete dinnan, document din ya bace daga wajen yanda kuka san ba'a taba yinsa ba. 



~~


Awa daya da rabi baya. 


"Ah Ah MZ ga babynka fa na kira bazaka dauka bane" 


Mada yake fada daga inda yake zaune a front seat yana mikowa Mu'azzam wayarsa dake kara dukda yaga sanda Mu'azzam din ya taso daga kwanciyar da yayi a bayan motar ya kalli wayar dake cikin console din motar ya sake komawa ya kwanta. 


"Mtcheew" Mu'azzam yaja tsaki ya karbe wayar yana sakata cikin aljihun wandonsa kuma cikin muryarsa wadda kanaji kasan ba qalau yake ba yace 


"Banason iskanci Mada an gaya maka ina daukar wayarta idan kaina ya dau chaji ne" 


Wanda ya kira Mada ya kwashe da dariya Kwala dake jan motar shima yana tayasa. 


"Okay bata san kana ay yane ba koh, kasan ni mantawa nakeyi" Madan ya fada yana juyowa ya kalli Mu'azzam din. 


"Shege MZ sonta kake dama wai dagaske" Madan ya sake fada ganin Mu'azzam din ya sharesa. 


"Sonta yake dan wahala" Kwala ya baiwa Mada amsa.