Chapter 9
by @reza12
MATAR MAZA 9
(Life Story)
Karfe sha ɗaya na safe jirginta zai tashi zuwa Dubai, hakan yasa take kiran Namra domin ta faɗa mata yadda sukayi. Tana ɗagawa tace "Dan Allah kizo officer ɗin mu ki same ni, bani da damar fita". Ta faɗa da sigar roƙo domin kusan sau biyar kenan tana cewa tazo ko sau ɗaya ne taga gurin aikin nasu amma ba taƙi. Kuma ba wai ki tayi ba, bata da lokaci ne yanzu kwata-kwata, amma yanzu da yake filin jirgin a hanyar ne yasa tace gata nan zuwa. Ƙaton kamapani ne mai girman gaske, wanda mutane ne daga sassan kasashen duniya iri-iri suke aiki a gurin harda ƴan chana indiya da dai sauransu. Sanye take da doguwar riga yar Dubai ja, hannunta riƙe da karamar jaka ta fito kamar wata budurwa. Idan baka santa ba ba zaka ce tayi Aure ko sau ɗaya ba bare kace tana da ƴa ba. Tana fitowa ta kira ta tace gata a cikin gurin tazo ta shiga da ita. Ba'a fi minti biyu ba sai gata itama da shigar doguwar riga baka. Da gudu ta ƙaraso ta rungume ta. Ta ce "Yau dai Allah yayi gaki gurin aikin mu". "Karfe sha ɗaya zan shiga Dubai so bani da lokaci muje". Ta faɗa suna tafiya. Bayan sun hau linta ta danna musu hawa na bakwai kenan zai rufe suka ga an riƙe ƙofar an shigo. Da sauri Namra ta gaida shi tana murmushi. Ya amsa yana kallon Azima, itama shi take kallo. Ta ce "Amma oganmu ne, shine mai wannan gurin". Namra ta faɗa tana kallon Azima da bata gaida shi ba. Fari ne mai dogon hanci wanda sarƙar kuros ɗin da ta gani a wuyansa ya tabbatar mata shi ɗin waye. A kallon farko da tayi masa bata bashi ƙasa ko yare ba domin gaba ɗaya ta kasa gane ko ba'indiye ne, ko Balarabe ko Bature ba. "Hi" ya faɗa yana ta kallonta. Itama ta yi yadda yayi tana kawar da kai. Har lintr ta kawo su suka buɗe suka fita. Da mamaki taga yana binsu a baya har cikin ofishin Namra ɗin. Ya ce "Ina takardun suke?" Ya faɗa yana zama a ɗaya daga kujerun officer ɗin. Da makami Namra take kallonsa shi da baya ko zuwa gurin da ma'aikaci yake ko waye kuwa. Ai da sauri ta fito da su ta miƙa masa. Ya amsa yana ta bin Azima da kallon gefen ido. Sai kuma ya zauna a ciki ya fara dubawa. Azima ta ce "Amma jirgina zai tashi, zamuyi magana idan na sauƙa ko na dawo naga kina kan aiki ko?" Kafin tayi magana ya ce "No kuyi maganar Ku yanzu zan fita". Yana faɗa ya tashi ya nufi hanya yana ta kallonta. Bayan ya fita ta ce "Mun tsayar da magana da Alhaji Sule zamuyi aure". Ta faɗa tana sake jin ta gamsu da auran nasa. "Wai mai yasa baki da tunani ne, kin san mai ta taka da tace miki haka?" "Ko mai ta taka ina daidai da ubanta, Allah sai na shiga gidan ayi Uwar da za'ayi ko ni ko ita, bare ma nasan ita ce da wahala domin ita take kallon namiji a wata ƙaniyar, bata san ni a gurina tamkar ledar biskit suke ba". Namra ta kwashe da dariya tana faɗin "Laidar biskit dai Azima, Allah dai ya raba ki do soyayyar wani da zaki ji kamar ki mutu idan ba shi ba". "Wallahi babu wannan namijin a duniya, ke nifa zuciyar nan tawa haka Allah yayi min ita babu son kowa a ciki sai na uwata da kannena". "Haha yarinya kenan, ajuri zuwa rafi, ina raba ki da kamuwa da wanda bai kai wanda kike yaudara ba, kuma wallahi irin wannan soyayyar har mutuwa ake yi" "Eh za'a mutum tunda ita mutuwar wasa ce ba, sai kawai na mutu akan Namiji, kai Allah dai ya raba bawa da wahala, mata kuna ganin ta kanku, ai ba'a son Namiji Kamar haka". "To lokacin da zaki so ɗin ai ba sani kike ba yarinya". "Hahah wallahi baki san so ba shi yasa kike faɗin haka, baya shawara baya tambaya baya..." "Kinga dan Allah ya isa haka, haba, baya baya baya, to nima bana". Ta faɗa tana yatsine fuska. Daga haka hirar ta ƙare saboda lokacin da bata da shi. Har gurin mota ta rakata sannan ta dawo ofishin nata. Tana zama sai ga ogan nasu ya shigo officer ɗin yana tambayr wacece Azima, kuma yar waye a garin nan domin irin shigar da tayi da motar da ta hau ga kuma batun tashi a jirgi da yaji.
Da mamaki Namra ke kwallonsa. A ranta tace "Wai ko dai Azima tana bin malamai ne, tunda ta fara aiki anan ko magana bai taɓa haɗa ta da shi ba, duk da kuwa ta ƙyasa, amma gashi daga zuwan Azima ya shigo har ofishin ta. Ta ce "Ita ɗin matar aure ce". Ta faɗa a ɗan rikice". Abraham ya danyi murmushi ya samu guri ya zauna. Ya ce "Naji hirar da kukeyi akan tana son ta auri wani". Ta zaro ido ta ce "Eh ai mu musulmai idan aka saka maka ranar aure to kin zama amarya ne". Ya ce "Mukuma Kirista sai an daura, dan haka bani number ta". Ya faɗa har lokacin yana murmushi. Ta miƙa masa ya amsa yasa ya bar ofis ɗin. Azima na fita sai ga kiran Bilal. Ta ɗaga da fara'a. Bayan sun gaisa ya ce mata yana so zasu haɗu suyi magana. Ta ce masa yanzu haka zata shiga jirgi nan da minti goma ne, ya bari ta dawo. Ya ce "Mai zaki je yi?" "Kaya zan sayo". Ta faɗa duk da kuwa tsana yasan mai take zuwa yi. Ya ce "To a fasa tafiyar a faɗa min kuɗin ticket ɗin jirgin zuwa da dawowa da kuma kuɗin kayan da ribar duk zan biya yanzu ki faɗa min inda zamu haɗu magana ce mai muhimmanci". Azima ta cire wayar a kunne tana dubawa da kyau, tayi murmushi a ranta tana jin Lallai wannan kasuwancin nata yayi riba. Ta ce "Anya zaka iya kuwa?" Yayi dariya mai sauti ya ce "Gaba ɗaya nawa ne jarin naki?" Ta sake yin murmushi ta ce "Ba sai an kai nan ba, a fara gama wannan". Ai kuwa take tafiya ta fasa, tayi masa lissafi ta tura masa, ko minti biyar ba'ayi ba sai ga kuɗin ta, ita kuma ta sauya ranar tafiya zuwa jibi ba tare da ta yi a sarar kuɗin ta ba. Sosai wannan karan ma Bilal ɗin ya jijigata, kuma har ga Allah bata ma jin koda wasa zata iya auransa saboda tana tsoron gidan sarauta. Gara dai ta tsaya a mutane kamar ita. Bayan sun zauna ya ce "Magana nazo muyi dake serious". "Ina jinka mai martaba". Ta faɗa da wasa. Yayi murmushi ya ce "Amm aure nake so muyi Azima, zan saya miki gida naki ke ɗaya ba tare da kin zauna da sauran mata na ba, ko gidan naki ma ba zasu sani ba, ina sonki ina so na mallake ki domin na gaji da dakon soyayyar da mukiyi, dan Allah ki bani dama pls?" Ya ƙarasa yana riƙe haninta dake kan tebul ɗin gabansu. Ta zame hannunta ta ce "Ranka ya dade aure fa kace, kana jinin sarauta ina kai ina auran yar talakawa iri na, kuma ba ai ko a gida ba za'a bar ka ba, koda an barka idan ma anyi auran dan ginka ba zasu mutuntani ba, zan sha wahala sosai a gurinsu, dan haka please abar wannan maganar". "Ai na faɗa miki a gida daban zan ajiye ki, babu wanda zai san da maganar, dan Allah ki bani dama, ina mutuwar sanki sosai, na kasa iya riƙe kaina a kanki?" Ta ce "To ai nima a gida ba za'a yarda ba, domin Hajiya ba zata bari ba, gidan sarauta ai sai yan sarauta mai martaba". "Muddin kin amince to ki barni da Hajiya ɗin zanje har gidan na nusar da ita har ta yarda". Azima fa ta tabbatar da gaskiya yake, ita kuma wallahi ba zata iya ba. Sai kawai tace masa "Tom bani nan da sati ɗaya zanyi tunani, kuma zanyi magana da Hajiya". "Sati ɗaya fa, ai yayi yawa, ni da nake so a ɗaura aurn a sati ɗaya". Tayi murmushin nan nata mai tafiya da hankalin mai martaba. "Ta ce "Kar ka damu, ka bar shi a hakan muddin ta yarda to an gama mai wahalar".
Daga haka ta nufo gida ta samu Mansur a ƙofar gidan ta tsaye da motarsa. Yana ganinta ya buɗe ya fito itama haka. Ya ce "Waye wanda kuka haɗu shine mijin naki ko bazawari?" Ya faɗa yana dariyar rainin hankali. Ta ce "Wai meye matsalar ka dani, mai yasa kake bibiyata ne, kai baka da aiki ne sai da ido da gulma kamar wani mace"? Ya ce "Ina so ne na tabbatar da gaskiya akan kina da aure ko babu, kuma na tabbatar, dan haka ki sani baki da miji sai ni, ko kuma Hajiya ta san da wannan maganar wallahi". Yana faɗa ya shiga Mota ya bar gurin. Ta kai minti uku a gurin tana mamakin wai ita akewa barazana. Har ta shige gida tana mamaki. Washegari sai ga Namra tazo har gida a rikice tana tambayar ta wai Abraham ya kirata. Ta ce "Waye kuma haka"? Nan ta faɗa mata yadda sukayi. Tayi dariya ta ce "Ni kuma ina ni ina haɗa hanya da Kirista ana zaune lafiya". Namra ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Wallahi kam, ai dama ba kyau, mutanen da basa Sallah". "Rashin hankalina bai kai nan ba gaskiya". Suna cikin hirar Mansur yadda zata rabu da shi sai ga Bilal ya kirata yace gashi a ƙofar gidan ta, ta kalli narma ta ce "Kai yau dai na shiga goma da wannan ɗan sarautar". Hakan yasa suka fita ita da Namra tana bata labarin sa, ita dai Namra lamarin Azima yafi karfinta. Wannan karan harda dogarai uku, kuma tare da wasu jif guda huɗu sabbi masu numfashi. Namra sai kallon motar take tana satar kallon Bilal ɗin, tabbas ta tabbata Azima tana bin bokaye, idan ba haka ba ina ita ina ɗan sarauta. Nan ta gabatar masa da Namra a matsayin ƙawarta, yayi murmushi suka gaisa. Yace mata ya dawo jin abun da ta yanke ne. Ta ce "sati ɗaya fa na ce ba kwana ɗaya ba". "Ai ina ce kwana ɗaya kika ce Madam". Suka yi dariya sannan ta sake bashi hakuri akan ya bari sati ɗaya. Bayan sun yi sallama ya zaro rafa biyu na dubu ɗaya ya bawa Namra ya ce tasa kati. Take ta rikice ta fara godiya. Bayan ya tafi ta dinga yiwa Azima tambayoyi akan wani irin mai take shafawa da turare. Ta ce "Kamfanin baby and me zaki je, nima ranar naga Siyam Olosha Model ta musu talla shine na saya, kuma tun lokacin ma cen ne gurin sayayya ta saboda ita". Narma ta ce "Dan Allah bani address ko ki faɗa min sunan shafinsu a online na garzaya yanzu". Nan take ta faɗa mata suna cigaba da hira akan sa.
Washegari kafin ta tafi Dubai saida suka sake yin magana da Alhaji Sule akan batun auran da ya rage kwana biyar, tuni tayi blocking number matarsa. Tana filin jirgi tana waya da Bilal domin yanzu kusan bayan awa goma sai ya kira domin dai ta samu ta yarda da shi. Taji an ce "Were are you going?" Ta ɗan kalli gefen da taji maganar, sai taci gaba da wayar tana mamakin tambayr rainin hankali kamar wata karamar yarinya. Ya sake cewa "katse wayar nan muyi magana?" Ya faɗa da Confidence, Hakan yasa ta sake kwallonsa da kyau lokaci ɗaya ta gane shi amma ta sake yin banza da shi. Ya ce "Baki ji abun da nace bane"? Ta sake yin banza da shi. Bata ankara ba, taji an zare wayar daga kumatunta an kashe. Ta juyo azafafe kaman zata mare shi ta ce "What is mentality of this, are you stupid?" Ta faɗa tana kai hannu zata amshi wayar amma ya saka a aljihu. Yayi gaba ya ce "Biyo ni muddin kina son wayar ki" yana faɗa ya tafi ya barta tsaye da mamaki da kuma ruɗani da tunani iri-iri. A fili tace "Kutumar ubancen, wannan yasan ni kuwa. Har minti uku bata bishi ba, shi kuma bai dawo ba, har minti bakwai zuwa goma gashi kuma an fara kiran masu shiga jirgi. Haka ta ji an kira sunanta, ta nufi jirgi ta shiga tana mamaki. Har jirgin ya daga bata daina mamakin wannan gya ɗin ba.
Kwananta biyu batayi waya da kowa ba, kuma bata sayi wata wayar ba har ta dawo. A lokacin auransu saura kwana uku. Kamar almara tana sauka a jirgi ta ganshi a gurin da suka rabu wancen lokacin. Ta kawar da kai. Ya ce "Ji mana, I'm sorry please". Ya faɗa yana bin bayanta. Taki yin magana har sai da ya sha gabanta. Ta ce "Bani wayata?" Ya zaro da sauri ya bata. Kasancewar bata kira kowa ba, kuma ba wanda yasan da ta dawo yasa dole ta shiga motarsa ya kaita gida. A hanya yake ta mata surutu wai yana sonta, harda mata alkawarin duk abun da take so zai mata, shi dai kawai ta yarda da shi, ya faɗa mata sunansa Abraham shi ɗan Ingila ne, wannan kamfanin na babansa ne. Labarai dai kala-kala da abubuwan da bata tambaye shi ba. Tun daga ranar shima ya shiga layi ya dinga kiranta babu jinkirtawa. Har kwana biyu lokacin ana gobe za'a ɗaura auran ta. Izuwa lokacin suna waya shi sosai har ɗan sakewa da shi. Bilal kuwa so take kawai sai tayi aure ya sani shi da Mansur yadda da kansu zasu gudu. A ranar da daddare suka shirya komai da kuma gurin da za'a je a ɗaura auran. Hakan yasa ta kwanta da nufin aure washegari. Ai kuwa tun karfe huɗu na yamma suna gurin ita da Namra da wakilan ta da ya haɗa ta dashi. Sai dai har kusan biyar ba ango, har biyar da rabi, a takaice dai har shida. Haka kuma number sa bata shiga, dole suka dawo gida ransu a bace da abun da yayi musu. A daren kuma sai ga kiransa, tana ɗagawa da nufin fara zaginsa taji yana faɗa mata cewar ba zai iya auranta ba tayi haƙuri ta samu wani, shi dai kam yana son matarsa, batayi masa komai da zai ƙara aure ba". Sosai ta kasa magana ta rasa mai zata ce, ita dai ba sonsa take ba amma abun ya tsaya mata. Har ta buɗe baki zata tambaye shi taji ya kashe wayar, tabi wayar da kallo kamr dai mamakin ne ya ishe ta. Tana cikin wannan tunanin taji an kirata da sabuwar number ta daga, sai ga muryar matarsa. Ta ce "Amaryar ɓoye, fatan dai an yi aure lafiya ko, to Allah ya bada zaman lafiya tare da kwaratanki da kika saba tarawa, yar iska yar balaja'u mai bin mazan mutane karuwa kawai, ke a tunaninki wasa nake miki da nace ba zaki iya auran mijina ba ko, to bari kiji ba wai ke kaiwa ba, mijina ko matan waje irinki wallahi yafi karfin su, dan ni ɗaya aka yi shi, shegiya kawai wawiya karuwa mai halin yan iska tsinanniya kwartuwa ƙazama ballagaza". Haka ta gama mata zagin tsamar nama bata iya ko motsi ba, wasu kalaman ma ba'a taɓa faɗa mata su ba. Tana kashe wayar ta zauna daɓas ta riƙe kanta dake juyawa mata, gaba ɗaya ta shiga tashin hankali. Dama ita saboda matar sa tayi niyyar auran kuma gashi ta ci galabarta. Abun da ya fara zuwa kanta shine wannan matar tana yin asiri ba haka ta bar Alhaji Sule ba. A lokacin taso ta sake jarraba Sa'a amma da yake tana tsoron asiri take tayi blocking number sa da nata, a ranta tana jin ta kuma gama da sahafinsa, suje chen suci uwarsu shi da ita, amma wannan zagin ba zata yafe shi ba, wallahi sai ta biya bashi da babarta. Bangaren Namra kuwa tuni ta sha dariya harda riƙe ciki jin abun da ya faru.
Ta ce "Wai da gaske shi da kansa ya kira yace miki ya fasa?" Ta faɗa har lokacin tana dariya. Azima ta ce "Bana son iskanci fa, koma dai menene nice dai da riba, domin dama wallahi bana ko jin sonsa gaba ɗaya, ni haushi ma yake bani, ya cika sanyi, bana son namiji mai sanyi da yawa, abu kamar mace a gurin". Namra ta sake fashewa da dariya tana faɗin "Da makaho ya rasa ido sai cewa yayi wari gare shi". Azima ta shaka ta ɓata rai ta ce "Mai kike nufi, wai ina sonsa kuma naji haushi ko? To Bari kiji nifa dama auran sati ɗaya na shirya yi da shi, kuma bawan allannann ko a kafa..." Bata ƙarasa ba ta ce "Ba wannan ba, wani labari na samo nace Bari nai saurin sanar dake". "Ina jinki" ta ce "Wannan dan Sarkin da yake zuwa gurin ki wai yana da cutar HIV, yanzu wata kawata take faɗa min". Azima ta dafe kirji tana kallon Namra kamar idanunta zasu fado. Sosai ta shiga tashin hankali bata wani tsaya wata-wata ba ta kira shi. A lokacin baya ƙasar tace zata yi magana da shi, yace mata sai ya dawo. Gaba ɗaya ta kasa sakuni domin ba ƙaramin tsoron wannan cutar take ba...📝
Please like and share, comments dinku na ƙara min ƙwarin guiwa.