GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar Giwa

by @auntyindo

Sai gaf da Magriba ya samu ya zille ya koma ɗakinsa, yana shiga ya rufe ƙofar ya ƙara lulawa can ƙarshe sannan ya zauna a bakin gado, Lambar Hibba ya fara laluba sai lokacin ya ga tarin kiranta har uku, zuciyarsa ta ƙara bugawa, ya yi saurin tura kira jikinsa na karkarwa.  Ba wani ɓata lokaci ta ɗauka tare da sallama cikin  murya me ɗauke da damuwa.   

 "Hibbah!"       "Na'am!, ashe dai ka san ni ce, na zata Ɓatan kai ka yi ai"      cikin raunin murya ya ce "Kiyi haƙuri don Allah, wallahi ban kyauta ba!"  

tayi murmushi me ciwo gami da cewa "Uhm!, da ka san ba zuwan zakayi ba da baka wahalar da ni ba, duk da ban san dalilinka ba"      shiru yayi tare da sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, kamar ba zai magantu ba sai kuma Ya ce "Na so nayi miki ƙarya, amma ban iya ƙarya sosai ba, gashi gaskiyar tana da ɗaci!"     yadda yayi maganar kamar zai fashe da kuka yasa jikinta yayi sanyi,  amsa ta bashi da cewa "Rayuwar da aka gina ta Bisa gaskiya da gaskiya tafi kyau da ƙarko, fiye da Rayuwar da aka Gina da Soyayyar da ba a yi mata Ado da Gaskiya ba!" 

Ya ja dogon numfashi ya sauke, kafin ya ce  "Ammyna ce ta hana ni fitowa,   wata Yarinyar Ƙawarta me kama da Figaggiyar Kaza ta zo, shine fa aka tsareni  wai ba zan fita ba har sai ta tafi, yanzu ma da ƙyar na samu na bar wurinsu,      don Allah kiyi haƙuri Kinji Hamdana!, tsautsayi ne, wallahi da na san zata zo da tun safe zan bar gidan nan sai dai a neme ni a rasa!"

  Sadda kai ƙasa tayi tare da sa dogayen yatsuntsa ta goge ƙwallar da ta fara gangarowa kan kumatunta,  sai da ta sauke wani gwauron numfashi ta saki ajiyar zuciya sannan ta samu damar yin magana cike da son kwantar masa da hankali   "Kuma da gaske sai ka gudu?, ai kuwa in ka zo ni ma zaka tarar bana  nan,  haka shine mafi daidai ai, don uzurin Ammy dole yana gaba da naka,   kar ma nan gaba ka ce zaka ƙi saurarar uzurinta, in kayi haka kuwa nima zan tayata ƙwanƙwasar kanka!"    murmushi me tafe da hawaye ne ya suɓuce masa, cikin rawar murya ya ce "Haka kika ce ko?"     "Eh mana, ai gaskiya na faɗa,  wai ba dai kuka zaka yi min ba?"      "Eh ba kuka zanyi ba,  kawai dai don Allah ki yafe min Hibba!"   yanzu kam kukan nasa yaƙi ɓoyuwa sai da ya samu nasarar fitowa.

 "Laaa!  kai kuwa Allah ya yi ka da Shagwaɓa!, da gaske kukan fa kakeyi,  ko dan dama an ce Ƴaƴan Fari  akwai son yin kuka"    Ƙoƙarin danne kukan ya fara yi yana goge ƙwallar tare da sakin murmushi,    "To ai ina da Yayye Har uku! amma ɗaya ta rasu, sai Aunty Fauzah, da Yaya Marwan"          "Tofa ashe haka akai,  ai baka taɓa gaya min ba, kuma fa kamar nasan Yaya Marwan ɗin,    to ni ai gani nayi ma Ƴan Gidanku duk Maza sun fi Yawa ni kuma duk tsoronsu nake ji"      "Hibba nifa ba su ne damuwata ba yanzu, ki ƙyaleni da zancen su, muradina kawai Ammy ta fahimci bana son abunda take min ɗin nan"      "To na barka, amma don Allah ka dena kukan nan,   kana karya zuciyata, kar ka sa tsoro da fargaba su ɗarsu a raina, don ni abun nan ban ɗauke shi wani babba ba, hasali ma  ni dariya kake bani da wannan shagwaɓar, naso ina gurin da na tari ruwan hawaye  in kaiwa su Raihana su gani!"    "Dama nasan ba zaki taɓa kimanta irin zafin da nake ji ba, na tabbatar da zaki kintato da baki ɗauki abun wasa ba,   ni kaɗai na san abinda nakeji, babu wanda ze iya fahimta ta"   

sautin Bubbuga ƙofar  ɗakin ne ya katse masa hanzari, da sauri ya ce "Shi ke nan ga Ammy nan,  sai anjima zan kira ki"  bai jira amsa ba ya katse kiran yayi wurgi da wayar  ya nufi toilet cikin sauri don ɗaura Alwala.

  Khalil da ke zaune gefe yana kallon Hibba taɓe baki yayi yace "Gaskiya son da kike wa Yaya Hamdan ɗin nan yayi yawa, yanzu  duk wannan  ƙuntata mikin da yayi  ke ce kika zauna kina rarrashinsa, ai ko kaɗan ya kamata ki nuna masa kuskurensa,  wuni fa kikai kina haƙilo akansa amma wai yaƙi zuwa, kin kashe aikinki, kin kashe lokacinki, kin....."  katse masa maganar tayi da cewa "Ya isa haka Khalil!,    nufinka in ce masa ya bujirewa Mahaifiyarsa ko me?"   "Ni ban ce ba amma ya kamata ki nuna masa  kin wuce  ya yi miki hakan, kuma ko kunya harda buɗe baki yana baki labari, ke kuma wai kika hau kai"  

 "Saboda ya gaya min gaskiya sai in hau shi da faɗa in ce zan yi fushi?,   so kake na koya masa Ƙarya ma kenan!,   to ni ba haka nake ba,  idan yana faɗa min gaskiya ina ƙin karɓa dole wataran Ƙarya zai fara yi min"       "To ai shikenan, ya yiwa kansa, mu dai bara mu je     mu dakawa liyafar da aka haɗa masa wa-wa!"     "In ka tashi ka cinye har kwanon!"  ta faɗa tana zabga masa harara cike da ɓacin rai.

 Dariya yayi kafin ya gyara zamansa ya ce "Ni wallahi Yaya Hibba yardar nan da kika ɗora akansa har tsoro take bani,  yanzun ma fa baki da tabbacin Gaskiya ya faɗa miki, sannan kuma ni tsorona ɗaya ma kar ya Aureki ya Mayar da ke Bazawara   Daga baya cin Mutunci ya biyo bay....."  wani kofi da ke kusa da ita ta raruma ta jefa masa tana faɗin ''Yi min shiru Dan Ubanka tunda baka faɗen Alkairi"  hakan bai wadace ta ba don haka ta miƙe ta kai masa wawura tana cewa "Munafiki! sai na ragargaza maka baki!"   Miƙewa yayi da gudu ya fice yana dariya, ai kuwa ta rufa masa baya suka fara aiki zagaye a gidan.

 Rasa inda ze yi yayi sai tsintar kansa yayi a Kitchen ai kuwa ta biyo shi Salin-alin ba hanyar guduwa, ta kama  ta fara jibgarsa ,  tana  yi tana huci.

Maama ce ta leƙo Kitchen ɗin  tana cewa "Meye hakan ne  wai?!, lafiyarki kuwa?"      dena dukan nasa tayi  tare da bawa Maama amsa "Shine bashida  Mutunci sai tsokanata yake wai dan Yaya Hamdan bai zo ba, kuma fa... kuma...."  Kuka me tsanani ne ya kufce Mata dole ta haƙura da yin maganar ta bawa Kukan damar fitowa.

 Maama ta bi ta da kallo me cike da Tausayawa kafin ta ce "Ki ce dai haushim Kaza huce Kan dami akai,  to kiyi shiru ai wataran na nan in sha Allahu, tayuwu wani babban uzurin ne ya hana shi zuwa"        "Kai kuma Khalil ka dena kar na ƙara ji, bana son shiririta"     ya ce "To na dena, amma fa gaskiya na faɗa, ni tsoron Yaya Hamdan ɗinnan nake" duka Maama ta kai masa tana cewa "Jakar Ubanka! fita daga nan,  wannan ita ce gaskiyar?"     ficewar yayi tare da cewa "A'a zolayarta nake"  
 Hibba dai Kukan da takeyi bai bata damar yin magana,  duk yadda ta so sassauta shi ta kasa har saida Maama ta ja hannunta  suka dawo ɗaki ta fara yi mata Nasiha sannan ta samu nutsuwa, har ta gabatar da Sallar Magrib.

  Washegari....

Misalin Ƙarfe goma na safe.
 Ta shirya tsaf cikin tsaleliyar  Atamfa, ɗinkin  Doguwar riga ta buga Mayafinta  wanda ya ƙara fito da tsantsar kyaunta, idanunta  na sanye da wani haɗaɗɗen Tabarau,    (glass)   tayi matuƙar kyau  kamar a sace a gudu, komai yayi lif yayi daidai da ita.

 Sallama ta yiwa Maama sannan ta fice   ta nufi wajen Junaid mai adaidaita sahu,   sanar masa tayi  ta aiki Khalil  zai karɓo mata saƙo sai ya dawo sannan zasu tafi,  ya amsa  tare da kawo tashi hirar  don kuwa akwai shi da lafiyar Surutu.  

Duk da irin damuwar da take ciki hakan bai hanata saurarensa ba, don surutun nasa ko baka fiya magana ba wani lokacin zaka so tankawa. 
Tuni  suka fara hira cikin raha da dariya   yana yi tana  taya shi tare da tunzura surutun nasa.
****************************

   Cikin yanayinsa na Nutsuwa  ya soka parking a ɗan gefensu   tare da zuba musu na Mujiya  yayin da zuciyarsa tayi wata muguwar harbawa.
Ji yayi kamar ya koma inda ya fito, sai dai sanin muhimmancin zuwan nasa yasa shi danne zuciyarsa,  ya zabari Tabarau ɗinsa baƙi ya ɗora akan haɗaɗɗiyar fuskarsa.

Cikin nutsuwa ya fito daga Motar cikin wani mugun haɗe rai tamkar bai taɓa murmushi ba.
Sanye yake da ƙananun kaya Jeans baƙi  da T-shirt fara wadda aka yiwa ado da launin Baƙi,  hannunsa na riƙe da manyan wayoyinsa guda uku.

Kamar bai san dasu a gurin ba ya sa kai hanyar  gidan Maama cikin wani ƙasaitaccen taku tamkar Bujimin Zaki.

  Hibba kuwa ta ji motsin Mota amma kasancewar ba me shiga shara ba shanu ba ce ko juyawa bata yi ba.
Sai da taji  Junaid yayi shiru  ta kalleshi taga wani gurin yake kalla sannan ta juya ita ma don ganin  abunda  yasa shi yin shiru don tasan ba ƙaramin abu bane.

  Zata iya cewa Mugun Katari idonta yayi, don kuwa Mummunar faɗuwa da gabanta  yayi ba ƙaramin yamutsa hazo yayi a ƙwaƙwalwa da zuciyarta ba.

  Sai da ya wuce Junaid ya ce "Ikon Allah, amma wannan Mutumi anyi ɗan Gadara, wato Kuɗi Duniya ne Hajjaju!"   Har lokacin idanunta na kan bayan Hamdan wanda  Take hango Wani Ruhi daban a Tare dashi!,  ga wani Mugun kama da yayi mata  da wani Matashin Yaro wanda tafi tsoronsa fiye da Kowa a Ƴaƴan Familyn su Maama.

 Ganin ya kutsa kai cikin gidan kai tsaye yasa Junaid saurin miƙewa daga zaman da yayi a gefen Adaidaitarsa, cikin kaɗuwa ya ce "Hajjaju Makkatu Antin Manya,   wancan  Wane ne? ko Yayanki ne?!"    Wani gwauron numfashi ta sauke gami da lumshe ido cike da son nemawa kanta nutsuwa,     girgiza kai tayi tana shirin cewa "A'a"  sai kuma ta yi saurin gyaɗa kai saboda wani abu da ya faɗo Mata.

  "Haba! ni fa na ga kuna kama, amma ya akai yake hawa wannan Arniyar Motar ke kuma kike hawa Ɗansahu?"  sai da ta ɗan  yi jim! kafin ta iya ba shi amsa "Uhm! alaƙar ba ta kusa ba ce, kawai dai akwai Dangantaka,  ni kuma Ɗansahun shine iya ƙarfina, baka ga Abbana ƙaramin ƙarfi gareshi ba?"      "E... kuma fa haka ne... ai ban yi wannan tunanin ba, ashe ba alaƙar kusa ba ce ai wallahi na ɗauka ma shima ɗan Gidan ne,  Ɗan Duniya Hayaƙin Wiwi,    kin ga wata Shegiyar Fita?!! ai shiyasa bana wasa da neman Halal Hajjaju" 

 Ɗan murmushi tayi don hankalinta na kan Wanda ya motsa zuciyarta,    Junaid ya ce "Ai Hajjaju shiyasa nake kiranki da haka fa!, don wallahi da an ganki an san ba Raini, gabakiɗaya kin fi kama da Ƴaƴan Sarakuna, ga Zarra, ga Izza, Ga shigar Alfarma, ga uwa Uba Kyau!,  ni dama nasan in kaji Gangami Akwai Labari Wallahi Allah ya muku komai   Gimbiya Sarautar Mata!"    Yanzu kam an kai matakin da bazata iya jurar surutun nasa ba, don haka ta murmusa ta ce "Wannan ai ikon Allah ne Junaid, ba wai kuɗi ko iko muke dashi ba, talakawa ne mu  masu nemen rufin Asiri a gurin Allah, shine kawai, kar ganin wancan yasa ka kaimu inda Allah bai kai mu ba"

   "Kuma haka ne, amma ai Allah ya amsa, ya rufa muku.."     katse shi tayi da cewa "Zan shiga ciki  mu gaisa"  bata jira cewarsa ba tayi gaba.

  Cikin sanɗa ta shiga Gidan tare da danne duk wani hautsini da zuciyarta ke yi.
Yana zaune a Tsakar gida kan Tabarma a gefen Maama suna ƴar hira,  ta yi sallama, Maama ce ta amsa shi kuwa sai ya sauke rumfar ido.

Tana ƙarasowa ciki ya miƙe ya  yiwa Maama sallama ya fice,  cikin takaici gami da sanyin jiki ta ƙarasa kusa da Maama ta zauna tare da zubawa guri ɗaya ido.

Maama ta ce "Kun gaisa ne?" girgiza kai kawai tayi,  "To kuma kika zo kika sakani gaba anan?"      "To ai tafiya zai yi ma"      ta faɗa cikin ko in kula,  "Haka ya gaya miki?,  ai sai kinga ya tafin zaki ɗorar"      "To bari in duba"  
Tashi tayi ta fice jiki a sanyaye,   bata yi tunanin ma duba rila ba  kawai ta sa kai zuwa waje.

 "Ina kuma za ki je?"  muryarsa ce ta ratsa kunnuwanta  ta ɗan jinkirta sannan ta juyo tana zuba masa idanunta da rauni ya fara bayyana a cikinsu...

  Cikin nutsuwa ya tako zuwa daf! da ita yana zuba mata wani arnen kallo tamkar zai haɗiyeta,  kawar da kai tayi gefe  tana jin kamar ta fashe da kuka.......