GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
GADAR GIWA
by @auntyindo
"WAYE WANCAN??" ta ji ya furta cikin wata dakakkiyar murya.
Ɗan kallonsa tayi ta kawar da kai kafin ta ce "Sunansa Junaid, shine mai Ɗansahun da yake kaini aiki wasu lokutan!"
"Amma shi ne kike tsaya Hira dashi akan Layi?, kin yi daidai kenan?, wai ma ba kin iya Driving ba?"
ta gyaɗa kai, "Oh kuma kin san da hakan kike bin gari wai don zaki fita?, to ki sallame shi zan siya miki Motar sai ki dinga driving da kanki"
"Kai?" ta faɗa tana kallonsa, suna haɗa ido ta kawar da kai tance "Ni bana so, Ɗansahun shine iya ƙarfina, ba zan iya wani jigila da Mota ba"
"Amma kin san ba...." da sauri ta katse shi cikin murya irin ta me shirin fashewa da kuka "Ya Hamdan!, don Allah kayi shiru!" Ido ya cigaba da zuba mata cikin wani irin salo mai ɗauke da launi daban-daban, wani gefen tausayinta ne ke mamayarsa, wani sashin kuwa tsananin kishinta ke ƙara zuga shi, ga wutar so da ƙaunarta na ƙara ƙona zuciyarsa.
Ya ɗan numfasa kafin ya ce "Ina matuƙar Kishinki Hibba!, ba na so in ga kowane Ɗa ya raɓe ki!" "Don Allah ka dinga kishin idonka a buɗe ba wai ido rufe ba, ni banida wata alaƙa da shi ko ta kusa ko ta nesa, ko wa zaka Tambaya ma ni bana saurarar kowa ko a Da bare yanzu da nasan akwai Alƙawarinka akaina" ta ƙarasa maganar tana goge hawaye.
"Am!... Kiyi haƙuri, amma dai yanzu ki sallame shi, yau da kaina zan kai Matata" "Ka je ka faɗa masa da kanka" "Okay!" ya faɗa a taƙaice, tunanin ta yadda zai je ɗin ya fara yi sai ga Khalil ya shigo, ya ce "Yawwa ƙanina zo, maza je ka gayawa Wancan me Napep ɗin ya tafi kawai ba yanzu zata je ba" Khalil ya amsa tare da juyawa don isarwa.
Mayar da kallonsa ya yi kanta gami da cewa "Hamdana! ashe inada tsohon laifi ko?" girgiza kai kawai tayi alamar A'a.
Ya ɗan murmusa kafin yace "Haka dai kika ce, ni nasan na yi shi yasa ma na zo da wuri don bada haƙuri " "To ai na haƙura tun tuni, kawai dama ka san jira bashida daɗi ne" "Oh baki damu akan rashin zuwana ba sai akan jirana da kika yi?" yayi maganar yana kafeta da miyagun idanun nasa, ta ɗan murmusa gami da cewa "Ji neman magana, to ai duk abu ɗaya ne ka faɗa a suffa biyu" shima murmushin yayi yace "Gashi na sa kinyi murmushi duk da baki shiryawa hakan ba?, don Allan ki dena hira da kowa please!" Murmushi me sauti kawai tayi ba tare da bashi amsa ba.
Shiru ne ya ratsa tsakani kafin ya ce "Hibbana, rayuwarki sam bata dace da damuwa ba, kin fi kyau da farinciki da kwanciyar hankali a koda yaushe, gashi ni kuma na shigo rayuwarki na rikita ta da Damuwa harda Ƙunci" "Uhm! haka dai kake gani amma ba haka bane, kowa fa da irin tasa ƙaddarar, sai dai ta wani tana da alaƙa da ta wani, kamar dai yadda tamu take da alaƙa da juna"
Ya ɗan murmusa cike da kulawa ya ce "Duk da gaskiya kika faɗa amma kin faɗa ne don kawai in ji daɗi"
"Tunda kuwa gaskiya na faɗa ai kaga abun a yarda ne"
ya jinjina kai ba tare da ya magantu ba.
follow my channel
***
Sun ɗan jima cikin yanayin shiru ba tare da kowa yayi wani yunƙuri ba, sannan Hamdan ya katse shirun cikin matuƙar raunin Zuciya,,, "Hibbah!, a Koda yaushe nakanji ina da ƙwarin gwiwar yiwa kowa Alƙawarin zan fara rayuwa dake kuma ina me sa ki farinciki,,, amma bana samun ƙwarin gwiwar cewa zan Ƙare rayuwata a tare da ke kuma cikin wannan farincikin, a duk lokacin da na binciki zuciyata hakan kawai nake samu a matsayin Amsa!"
"Duk iya nazarina ba na iya samun tabbacin ba zan sa ki Kuka ba!...." "Ina jin kamar in jaraba rungumar Ƙaddarata ni kaɗai, na barki ki Auri Ismail, saboda yanzu karon farko na kasa bawa kaina yaƙini akan rayuwata bare har in gasgatawa wani!... amma na rasa ta inda zan fara, fatan dai hakan da nace ban miki laifi ba Hamdah!"
"Kafin ka shigo rayuwata ya kamata ka zo da wannan Shawarar!, amma yanzu ba zatayi tasiri ba, saboda an zo lokacin da na riga na kamu da Sonka kuma Ƙaddara ta kaika matsayin wanda nake son na rayu a ɓangarensa!, idan kuka ne kawai, ba baƙona bane, ina sonka koda kuwa son ne silar zubar Hawayena a kullum!, Ƙaddarata ta riga ta zaɓa min kai Hibban! kuma zan yi bakin Ƙoƙarina wajen kasancewa a tsaginka duk wuya duk runtsi!" ta ƙarasa maganar tana zuba masa wani raunataccen kallo da idanunta da suka cika taf da ruwan hawaye.
Ɗago hannu yayi tare da kaiwa wajen fuskarta yana shirin goge mata ƙwallar, cike da tsananin tausayi da karyewar zuciya tare da faɗin.. "Hibba! kin...." katsewa maganar tayi, yayi saurin janye hannunsa tare da jingina a jikin bango yana lumshe idanunsa gami da haɗiye wani ƙullutun yawu da ya cake a maƙoshinsa...
Da sauri ta goge hawayen nata tare da ƙaƙalo murmushi ta ce "Kayi karin kumallo kuwa ka fito?, da alamunka fa Yunwa kake ji don na san ka akwai ci"
Buɗe idanunsa yayi a hankali gami da juye su akanta, "Tabbas Hibba ke kyautace daga Allah!, ban so na gurɓata rayuwarki da damuwa ba, sai dai b ani da mafita!" abunda zuciyarsa take saƙawa kenan yayin da narkakkun idanunsa ke ɗafe akan fuskarta.
Ƙasa tayi da nata idon, don gudun karyewar zuciya, domin kuwa kallon da yake mata yana ɗauke da wasu sinadarai wanda ke matuƙar taɓa zuciyarta.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki ƙara yiwa Maama sallama mu wuce yanzu, kuma yau za ki bani labarin Abun da Gidauniyar nan taku ta Ƙunsa"
ta ɗan zaro ido gami da cewa "Wai a yau?" "Eh yanzu ma kuwa" "To amma dai ba zaka hana ni fita ba bayan Mun yi Aure ko?, na saba sosai...." katse ta yayi da cewa "Idan kin same ni a Mota sai ki cigaba da surutun, maybe ki samu amsa" ta ɗan turo baki gaba gami da juyawa ta nufi cikin gida.
Ba wani daɗewa ta yi ba ta dawo, lokacin har ya kunna Motar yana jiran fitowarta.
Inda yake ta zagaya tana ɗan murmushi ta ce "A ina zan zauna?" murmushin da bai wuce kan laɓɓa ba yayi kafin yace "Zauna inda nake, ko kusa dani" "Innalillahi, ni fa ba baƙar magana na nema ba" "To na ce dai zamuyi magana, sai ki zaɓi inda ya fi miki daɗin zama" Zagayawa tayi Kujerar gaba ta zauna tana cewa "Yau dai kamar ba kai ba, rigima iri-iri"
Ya ɗan murmusa gami da fara driving sannan ya ce "Dama haka nake, wani lokacin inada rigima, yanzu dai fara bani labari akan Gidauniyar, sannan shi Ismail waye a cikinta?"
Ta ɗan gyara zama kafin ta fara jero bayani "Gidauniyar tamu dai wani sashin na Taimako ne, wani sashin kuma Masana'anta, Gidauniya tana Koyar da Sana'o'i ga Mata da Matasa sannan tana bada Jari da duk wani tallafi da zai temakawa Kasuwancinsu, na gefe guda kuma wanda suke da ƙarfinsu suna Biyan kuɗi su Koyi abubuwa da dama a cikin Makarantarmu, irin su ɗinke-ɗinke kala daban-daban su make'up girki da sauransu, Gidauniyar tana bada tallafi sosai amma ta fannin sana'a ne yawanci, a cikin wanda muka koyar kyauta da kuma wanda suka biya suka koya duk me ra'ayi akwai damar yin aiki tare da mu, Muna da sashi da yake kamar kamfani ko me aka sarrafa muna da hanyar da muke bayarwa ga Ƴan Kasuwa, kaga idan mutum ya koya kuma yayi aiki a Masana'antarmu babu ruwansa da matsalar abokan cinikayya ko rashin ciniki, kawai Albashi zaka dinga karɓa, to wannan shine a taƙaice"
ya ɗan nisa kafin ya ce "To duk naji wannan, ke a wane sashi kika ƙware kenan? kuma wane irin matsayi gareki da suke nemanki ido rufe haka?"
"Ɗinki mana, kuma ƙoƙarina da jajircewa shiyasa basa so na ɗan yi nesa da Gidauniyar, a ɗan lokacin da nake ɗauka in naje, ina koyar da Mutane da yawa, sannan ina kula da Ma'aikatanmu , sannan ina matuƙar kawo haske a Meeting wajen kawo abubuwan da za a ƙara samun cigaba" "Oh ashe haka ne!, kenan dai yanzu na huta da kaiwa Tela ɗinkina ko?" "Kayyasa!" ta faɗa tana dariya, ya ɗan kalleta kaɗan, ya maida idonsa ga titi yana cewa "Abun dariya ne kenan?" "To ai ba ɗinkin Maza nake yi ba, Hasali ma ni ban wani maida hankali kan ɗinkin tufafi irin su atamfa ba" "To ai sai ki faɗa min da yaren da zan gane, sai cewa kike Ɗinki, kuma kin ce ba haka ba" "Oo ya Allah!" ta faɗa tare da dafe goshinta, cigaba tayi da cewa "Su Zanin Gado, Filo, da Filo na kan kujera da na adon ɗaki, da Kayan Yara Ƴan kanti na maza da na Mata, su Huluna, beads work, night dressing na Matan Aure, su Abaya, da suwaye, wani abun ma dai sai na tuna kawai, to irinsu nake nufi ba Ɗinkin Maza ba" Ya ɗan yi dariya gami da cewa "Ai na zata harda kayan Ƙarti kike Ɗinkawa" "Laa! ni ƴar nan!" ta faɗa cikin sigar shagwaɓa.
"To yanzu sauran Ismail" "Wayyo ni Ƴar Mutanen kirki!, ka sa inata zuba"
"Amsa tambaya ai ba zuba ce kawai ba, don haka ina saurare"
"To shi dai Ismail Mamansa Hajja Halima su ne Manyan Ƙusoshin Gidauniya, su ne masu asalinta, kuma masu temakawa, yanzu dai ita bata fiya shiga cikin komai ba, sai dai Wakilinta wato Ismail, shi ne yake sanya ido akan Motsin komai kamar yadda su asalin manyan suke yi, to shine dalilin da yasa zaka dinga ganinsa a ciki amma a zahiri ba a cikin yake ba, don sai ya ga dama yake zuwa kokuma in wani babban dalili, to wannan shine" "Oh! to yanzu na gane" kafin ya ƙarasa maganar ta ce "Barka da ka gane, in kuma da wata tambayar jefo sai in cigaba da surutun, tunda ta kama ni"
Ya ɗan murmusa ya ce "Ai ba iya tambaya ba, da so samu ne har gani da ido sai in yi, amma dai yanzu ki cigaba da bani labari yadda kuke aikin, amma ina fatan banda maza kuke koyarwa"
"In kaji an ce Maza to sashin Tallafi ne, sana'a ake nema musu wadda ta dace da Maza ba irin tamu ta Mata ba, ka ga banida alaƙa dasu, aikina shine tofa albarkacin bakina in ana Tattaunawa, in ce ayi kaza zai fi a ƙyale kaza zai fi"......
Cigaba tayi da bashi labarin kamar yadda ya nema har suka isa.
**************************
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, a kowane ɓangare babu wani kyakkyawan canji, don wani sashin ma sai abunda yayi gaba.
****************************
Daddy, Mamy.
Suna zaune kan Sofa a ƙawataccen Falon Daddyn, Mamy ce ke ɗan yin magana shi kuwa hankalinsa a kan takardunsa, sai tayi sa'ar gaske yake bata amsa, ɗagowa ya kalleta kuwa zata iya cewa tunda ta zauna bata ga yayi hakan ba.
Ɗan gyaran murya ta yi kafin ta fara magana cikin inda-inda "Am.. dama... dama Bikin Ƴar Yayata nake son yi maka tuni, don lokacin ya zo, kuma muna buƙatar Kuɗi sosai ni da Yara don yin shirin da ya dace"
"Allah sarki ashe abun ya zo!, amma baki kyauta min ba Mamy da baki gaya min ba, wannan wane irin rashin Kara ne?, Bikin Ƴar Yayan guda ai ni ya shafa ba ke ba!"
Mamy ta zubawa Ammy dake maganar cikin raha da murna ido, tana jinjina irin girma Kissar Abokiyar zaman tata.
A gefe guda kuwa haushin zuwanta ya isheta, wannan shi ake kira Abunda ake gudu ya afku, sai da ta gama zagaye-zagaye da fakar ido sannan tazo ga Daddy duk dan tasan haka zata faru, amma da yake Shu'umar Mata ce sai da ta biyo, da alama dai wani Munafikin ɗan nata ne ya gaya mata.
Waɗannan Tunanikan ne suke zagaye a cikin Ƙwaƙwalwar Mamy........
*Aunty INDO*