GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
Ammy ce ta katse mata tunanin da cewa "Gaskiya kin yi min laifi da baki faɗa min ba!" cikin wata marairaicewa ta yi maganar kamar gaske.
Daddy da ke ta zabga murmushi yana kallonta, ya ɗan haɗe rai yana kallon Mamy ya ce "Maza ki ba ta haƙuri" Mamy ta ƙara buɗe idonta akan su duka kafin ta jinjina kai, murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ki yi haƙuri"
Washe baki Ammy ta yi cike da ƙwarewarta ta Kissa ta ce "Ba komai ai, gashi yanzu na sani ai lokaci bai ƙure ba, Abu Hamdan! ni zan ɗauki nauyin komai da kaina, idan ka gama uzurinka sai ka tura min Kuɗin da muka kashe ɗin, ai dole su Ammarah ma su shirya!"
"Kar ki damu Munawwara!, ko me kuke so ku tambayi Magajina ya ba ku" Daddy ya faɗa yana murmushi.
Miƙewa ta yi tana cewa "Mamy! ku yi min list na duk abun da kuke so, ya kamata ma Khadijan ta zo nan ta ɗan shirya ita ma ta ɗan kwana biyu anan" Murmushi me cike da takaici Mamy tayi gami da cewa "Ba komai ba sai ta zo ba ai" "To shikenan Allah yasa alkairi" Ammy ta faɗa tana murmushi, ba ta jira amsa ba ta nufi hanyar fita.
Daddy ya kalli Mamy gami da cewa "To na sallame ku ko?, kin ga ita Madina babu ruwanta kullum burinta ku haɗe kai ku zauna lafiya, ya kamata ki dinga koyi da halayenta, ki cire wannan baƙar hassadar da ƙyashi" "Ai Gaskiya Ummu Hamdan Ba kamar kowace ba ce, za a daɗe ana neman irinta ba a samu ba, mun gode sosai Alhajina" Mamy tayi maganar tana murmushi tamkar ba abun da ya dameta.
Shi ma murmushin yai yana cewa "Ko ke fa, ai kin fi kyau in kina murmushi".
Ammy tana fita tayi karo da Hamdan yana shirin shigowa, ta yi saurin riƙo hannunsa tana cewa "Bikin Khadija ƴar Yayar Mamynku ya kusa, don haka muna buƙatar Kuɗi, Abu Hamdan ya ce in tambayeka" ya ɗan yi turus! yana kallonta kafin ya ce "Wai ɗiyar Yayar Ammy kika ce ko Ɗiyar Yayar Mamy?" "Mamy mana!, meye na wannan tambayar kuma?" "To ai na ga kin fi ta nuna murna ne, kuma in haka ne ai ita zata nemi kuɗin ba ke ba" "Kamar yau na saba ɗaukar hidimarta?, bana son jan magana fa!" tayi maganar cikin sigar faɗa.
"Yi haƙuri Ammyna, amma gani nake ai gwara ki bar su su yi da kansu, komai fa ke kike shigewa gaba ki ce zakiyi musu, kuma haka kike musu da wanda yayi daidai da ra'ayinsu da wanda bai yi ba, yanzu dai sun ɗan jima ba su yi Biki ba a Familynsu, don Allah ki basu dama su yi abunda yafi burge su" "Kawai ka buɗe min bakin Aljihu in zaka iya, in ba zaka iya ba sai ka gaya min, ka san dai ni ba kuɗin ne a gabana ba, magana ake akan Isa da Iko, in ba zaka bani ba zan yi da nawa kuɗin kuma dole ne Daddynka ya biya ni" "Ah dama ba wai na ƙi bane, kawai dai gani nayi ita ma Mamy fa tana da ikon da zata...." katse shi tayi da cewa "Wai kana nufin zaka faɗa min abun da ya kamata in yi ne?"
"A'a kawai dai..." sakin hannunsa tayi tare da yin gaba tana cewa "Kawai na gama magana, bari ma in je in faɗawa su Ammarah"
Ya bi bayanta da kallo cike da takaicin shishshigin da take yiwa Mamy, kowacce fa mata ce a gidan amma ba dama Mamy ta zo da wani uzuri ko buƙatarta sai Ammy ta shiga tayi kane-kane sai abunda ta gama damar yi musu, ya ma rasa ta ya akai Daddy yake yarda da zaƙin bakin Ammyn har haka.
A kwana a tashi asarar me rai...
Kwanaki ƙara shuɗewa suke yayin da wasu kwanakin suke ƙara gabatowa.
Dama akan ce abun da ba a sakawa rana ba shine baya zuwa, wanda aka saka ranarsa kuwa dole ne sai ya zo.
Auren Hamdan da Hibba ma kullum tawowa yake yi yayin da zukata da yawa ke cikin ruɗani, damuwa, da tunani.
Hibba da Raihana suna zaune a wajen da suka saba zaman hutawa in suna aiki, Raihana ce ke ƙoƙarin jan Hibba da hira, ita kuwa duk hankalinta baya gurin yana kan tunanin rayuwarta.
Cikin ɗan takaici Raihana ta ce "Ni fa na gaji da wannan abun naki, sai na gama maganata sai ki wani tambaya me na ce" "Allah ya baki haƙuri, kawai tunani nake ne shiyasa"
"Ai dama nasan kina cikin damuwa wallahi, kalli fa yadda kika rame kullum ƙarewa kike kamar kuɗin guzuri, amma in na tambayi damuwarki sai ki ce ba damuwa, kuma ni bana iya ɓoye miki damuwar tawa musamman in akan Soyayya ne, ni ce ma da shishshigi, zuwa yanzu ya kamata in gane matsayina in ja jikina"
Hibba ta ɗan murmusa kafin ta ce "Rigimarki dai kawai, na gaya miki tuntuni in lokacin sani yayi zan gaya miki, kuma daman kin san dai in lokacin Aure ya tawo Mace tana ramewa ko?" "Haka dai ake cewa, amma ai ba dole bane don wasu ma yanzu ƙiba suke yi in auren ya tawo, ke dai ban ga abun damuwa ba, don a ganina kin gama yin sa'a da zaki Auri wannan Hamdan ɗin wallahi" "Aikin banza, na gaya miki fa Auren mai kuɗi ko wani me ji da kansa ba wai burgewa ba ce bare ma a ce sa'a, yin soyayyar zata iya zama burgewa amma in aka zo batun Aure a nan matsalar take, za a iya samun wasu halaye ko ɗabi'u da basu zama na burgewa ba a rayuwar Aure, hallau za a iya samun wasu manyan matsaltsalu ta gefe, kin ga wannan ba za a kira shi sa'a ba, zaɓin Allah dai shine mafi girman sa'a don haka gwara mu dinga neman zaɓinsa" "Eh to kuma fa kin fini gaskiya Hibban Hamdan!, amma yanzu ma kina nufin ba zaki gaya min ba?"
"Eh gaskiya sai nan gaba, amma karki ɗauka wata damuwa ce, kawai fargabar Aure ce" Hibba ta faɗa tana murmushi,
"To naji, yanzu dai kin san mene ne?, Za mu je irin Ɗan yawon nan na Masoya nida Saurayina Sadik, irin su shan Ice cream ɗinnan da coffee, to kuma kin ga ni ban saba ba, gaskiya bana son fita daga ni sai shi, don haka ki shirya mu je tare da ke "
"Ni?!" Hibba ta faɗa tana zaro ido da alamun mamaki, "Eh ke ɗin, Ranar Lahadi zamu je wannan me zuwan, sai ki shirya" "A'a gaskiya, wannan sabga ce ta masoya biyu, kuma nima fa ba sabawar nayi da fitar nan tare da Saurayi ba gwara ke ƙila ma kin taɓa zuwa ni kuwa ban taɓa ba, don haka ki je ke kaɗai zaku fi sakewa" "Ai kuwa wallahi ƙaryarki, wai don Allah me yasa bakya son yin ƙawance dani ne?, haba don Allah!, sai in ta shishshige miki ina kutso kai ke kuma ba ki ɗaukeni matsayin wata ƙawarki ba bare kuma shaƙiƙiyarki, yanzu Fisabilillahi ko ba daɗi tunda na cire tsananin kishina nace mu je tare ai se ki yarda, kuma har gaya masa nayi fa tare da ke zamu je"
Ido Hibba ta zubawa Raihana yayin da kalamanta suke ƙara tasiri a ƙwaƙwalwarta, kuma hakane, ita Raihana ta ɗauketa matsayin ƙawarta Aminiya, ita kuwa tafi barinta a matsayin wanda za a dinga gaisawa ana ɗan taɓa hira.
Numfasawa tayi cikin sanyin jiki ta ce "Kiyi haƙuri, kawai dai na taso ne ba tare da shaƙuwa da kowa ba face Maama, Abba sai Ƙanina, bana shiga hurumin kowa kawai nafi yin rayuwata haka nan, shi yasa, amma yanzu inada Babbar Aminiya, don haka ranar lahadin sai ma na riga ki shiryawa"
Raihana ta saki murmushi har ranta tayi farinciki da jin hakan, cikin fara'a ta ce "Amma fa ranar saura kwana bakwai kenan Aurenki, zaki gayawa Hamdan dai ko?" cc "A'a! gaskiya, ba zan miki ƙarya ba in na gaya masa ba zai bari ba, don haka sai dai kawai ya ji na dawo, ai dai da rana ne zamu je ko?" "Eh mana da rana ne, bayan Azahar haka zuwa la'asar kin ga kafin magriba mun dawo" Hibba ta sauke wani gwauron numfashi saboda zuciyarta da ke bugawa da sauri-sauri ba tare da tasan dalili ba, cikin ƙarfin hali ta ce "Saura ki ɗauki Abaya ki zabga ranar, mun gaji da ganinki da ita, na fi so in ga kina buga Ɗauri irin na Manyan Mata" Raihana ta ƙyaƙyace da dariya gami da cewa "Kuma wallahi da ita zan saka, amma fa sabuwa ce ban taɓa sakawa ba" "Ai ka ji!, ko Larabawa basu kai ki saka Abaya ba, to gaskiya ba zaki saka ba, shi ma Sadik ɗin ai sai ya gaji" da sauri Raihana ta ce "Yawwa !, me zai hana mu saka kaya iri ɗaya kawai?, sai mu yi sabon ɗinki Atamfa ko Shadda?" tunowa tayi ashe fa cikin shirin Bikin Hibban ake don haka tayi saurin cewa "Au ashe fa ke a cikin satin Biki ake, wai ma ya akai baki dena zuwa aiki ba ya kamata ki ɗauki hutu fa, duk da naga sai wani kyau kike ƙarawa da alama dai Maama ta zage tana gyara Ɗiyarta, wallahi kinyi suɓul kamar a sace a gudu!" ta ƙarasa maganar tana dariya.
Ita ma Hibba dariyar tayi tace "Wallahi kuwa, ni har gajiya nake da gyare-gyaren nan, Ƙanwar Babana ce ma tafi zaƙewa ita da Ƴarta Aunty Habiba, ga son su ɗirka min magani wani lokacin ma bana sha, gyaran fatar nan ma na gaji, ko Gas na girki yanzu bana son kunnawa duk sun ɗaɗe min fata"
Raihana harda tuntsurawa saboda dariya don har ta fara hango yadda ake kama Hibba a murjeta, ta taɓa ganin yadda aka yiwa Antin ta tun anan ta fara tsoron abun.
Hibba ce ta katse ta da cewa "Ke fa daɗina da ke akwai dariyar ƙeta, yanzu dai yadda za a yi kawai muyi kayan iri ɗaya, tunda kina so ai ba ze gagara ba, amma fa kawai kuɗin zan baki ki bayar a ɗinka mana, sai ki zaɓo atamfar da kanki"
"Yawwa an gama tawan, Allah ya barki da Hamdan" Hibba ta turo baki gaba irin ko a jikina ɗinnan.
Ranar Lahadi...
Hibba da Ƙawarta sun sha kyau iya kyau, Atamfar tayi masifar amsar jikinsu ta bi tayi ladabi, gashi ta ɗinku, an sha ɗauri Ture ka ga Tsiya sai baza ƙamshi suke.
Sai da suka yi sallar la'asar sannan suka bar gida aka shiga gari, Raihana da ɗan Saurayinta da ke a sit ɗin gaba, su kaɗai ke hirarsu don wani abun Hibba ma ba jin su take ba, tunaninta ɗaya abunda ya dameta, sai sun haɗa ido da Raihana ta jefo mata harara sannan take ɗan washe baki.
Daga ƙarshe ma tun da tayi lif a jikin Kujera ta lumshe ido sai da taji Raihana na cewa "Ki fito mana ko baccin zaki cigaba da yi?" sannan ta buɗe idonta da sukai mata nauyi ta fito tana ɗan lullumshe su saboda alamun wani wahaltaccen bacci da ke shirin surarta.
Bin bayan su Raihana kawai take yi ba tare da ta damu kan ɗago idanunta ta ƙarewa gurin kallo ba, sai dai koda bata yi kallon ƙwaƙwaf ba ta tabbatar sai ka isa zaka halacci wajen, Babu wata hayaniya, ga tsafta komai fes, ga kyawun tsari da ƙyale-ƙyale duk da kuwa da rana ne babu ƙarin wasu lantarki hakan bai hana wajen haskakawa ba, yana da girma sosai sannan ya ji Table da Chairs masu bala'in kyau, gasu nan rukuni-rukuni sai wanda ka zaɓa.
Bayan sun zauna aka fara cika su da kayan maƙulashe kamar yadda suka umarta.
Raihana sai murmushi take yi shauki ya cika mata zuciya, sai dai abu ɗaya zuwa biyu da yake shirin yiwa farincikin nata lahani, damuwar da Hibba ke ciki da kuma wani abu da take hange daga gefe.
Hira suka cigaba da yi ita da Sadik Hibba kam har yanzu aikinta ɗan murmushi ne in taga an sako ta a zancen.
Cikin zolaya Sadik ya ce "Ƙawarmu lafiya kuwa? Amaryata ta gaya min kina da surutu kina da fara'a sosai, amma naga har yanzu baki saki jiki ba, kodai kunyata kike ji?" Hibba tayi dariya tana kallon Raihana ta ce "Haka kika faɗa?" Ta yi far! da ido gami da cewa "Eh ɗin!, ai da gaske nake, kawai dai don...." ganin Hibba ta zaro mata ido yasa tayi shiru da zancen.
Hibba ta ce "Kawai bacci nake ɗan ji shiyasa, da sai na dame ku da surutu"
Cigaba sukayi da ɗan hira jefi-jefi Hibba takan ɗan saka baki, Raihana kuwa lokacin hankalinta ya fara barin jikinta ya tsallaka can wani sashi don fayyacewa kanta wace irin barazana ce wannan take kallonsu?....
Lokaci guda Zuciyarta ta fara harbawa da sauri-sauri, ta fara ƙoƙarin yafito Hibba tana yi mata inkiya.
Hibba ta fahimci kamar Raihana na da magana kokuma wani abu da take son nuna mata, sai dai sanin halinta na barkwanci har da shiririta yasa Hibba taƙi saurarenta don bata so su yi abunda Kimarsu zata zuba a idon Sadik.
A kowane Harbawar second Tsoro da firgicin Raihana ƙaruwa yakeyi, ko hirar ma ta dena ta zubawa sarautar Allah ido.
Cikin nutsuwa Sadik ya tambayeta abunda ya sa ta sauya lokaci ɗaya sai dai ta kasa bashi amsa, sai ta fara ƙoƙarin daidaita kanta.
Gani tayi abun yaƙi ci yaƙi cinyewa don haka ta kamo hannun Hibba tana faɗin "Wai Hibba sai nusar da ke nake yi amma kin ƙi ganewa" "Me fa?" Hibba ta tambaya cikin nutsuwa.
"Wani Ɗan Saurayi ne yake ta Bibiyarki wallahi, kuma kin ganshi can sai kallonki yake kamar tsohon Maye, ba ma wannan ne ya tsorata ni ba Matuƙar kama da yake yi da Hamdan shine tashin hankalin"
Wani wawan tsalle zuciyar Hibba tayi, ta zazzaro ido cikin tashin hankali tana faɗin "Hamdan?" "Kar ki tsaya jayayya, kin ganshi can tun be gudu ba"
Da sauri Hibba ta maida idanunta inda Raihana ta nuna mata, sai dai tana juyawa yana miƙewa gami da juyawa ya nufi hanyar Fita...
Jiki na kyarma ta tashi tana shirin rufa masa baya, Sadik ya dakatar da ita da cewa "Gaskiya nima na ga Yaron yana ta kallonki, amma kar ki bi bayansa kai tsaye haka, bari ni in je in duba, don daga gani Yaron ba irin masu Martaba Al'umma ba ne"
Gyaɗa kai kawai Hibba tayi tana lumshe idanunta da suka fara gane mata duhu-duhu saboda wata hatsaniya da ƙwaƙwalwarta ke yi.
Raihana ta ja hannunta ta zaunar da ita, ita ma ta zauna sannan ta ce "Kin gane shi kuwa?" girgiza kai tayi alamar A'a.
Raihana ta ce "Wani dogo haka me ƙananun kaya riga ash color haka?" "Ni fa ban gan shi ba, na dai ga bayansa a fizge, amma ta ya zan yarda yana kama da Hamdan?, siriri ne ko ?" "Ba fa Siriri za a kira shi ba don yana da faɗi, sannan da tsayi sai kuma yana da ɗan haske ba kamar Hamdan ba, kuma shi wannan Yaro ne fa don bana jin zai kai 25 years, amma ina me tabbatar miki yayi kama dashi koda kuwa ba su da alaƙa ta jini, na fa san Hamdan ɗin nima, wallahi har idanunsa ma suna matuƙar kama, kuma kallon da yake miki ba na tunanin iya burge shi kika yi ne, kallon yafi kama da na Manufofi masu kyau da marasa kyau, naji tsoro sosai da irin kallon nan ban taɓa gani ba wallahi!"
Dafe Goshinta tayi tare da faɗin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" "Baki yarda dani ba har yanzu ko?" girgiza kai Hibba tayi kafin ta ce "Na yarda da ke sosai ma, kawai ina cikin firgici ne, duk da ban tabbatar ba amma sai naga kamar na taɓa ganinsa, ni dai yanzu gida zan tafi"
Daidai lokacin Sadik ya dawo wajen tare da sallama, bayan ya zauna ya ce "Ai kuwa ban samu na haɗu da shi ba, kafin na ƙarasa tuni har ya shiga mota ya bar wajen"
Hibba ta rausayar da kai cike da tausayin kanta ta ce "To shikenan!" tashi tayi ta ɗau ƴar jakarta tana cewa "Zan tafi gida yanzu Raihana" "Don Allah ki zauna mu tafi tare, nima yanzu zan tafi" Raihana ta faɗa cikin sanyin jiki.
"A'a kiyi zamanki kawai, gwara in tafi ni kaɗai kinga zaku ɗan tattauna" Sadik ya ce "To ai abunda ya shafeki ya shafemu ki temaka ki tsaya anjima kaɗan sai mu tafi, na ga yanzu ma kamar tafiyar zata yi miki wahala ke kaɗai"
Raihana tace "Eh mana!, don Allah ki tsaya, ni bana so ma ki fita ki ƙara cin karo dashi"
Ba don ranta ya so ba ta koma ta zauna gami da buga tagumi.
"Wai kun san shi ne?" Sadik yayi tambayar yana kallon Raihana, ɗan gyaɗa kai tayi ta ce "Ni ban taɓa ganinsa ba gaskiya, amma ina ganin kamar ƙanin Saurayinta ne, kamarsu ɗaya, kuma ta ce ma kamar ta taɓa ganinsa"
*Aunty INDO*