BARRISTER SUHAIL

41

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----41 

Dai-dai lokacin Iman ta shigo kitchen ɗin.

Da sauri ta ƙaraso ta kama hannun Hafsat 

“Mike faru”

Zare hannunta tayı Daga riƙon da tayi mata "iman ki barni na koya na kishiyar nan taki hankali ko tayi tunani kowa irin ƙi ne da zata fadi magana ya kyaleta"

zeenah ta fara tsoron hafsat ganin yadda take ta masifa tuni tabi ta gefe ta fita 

hafsat cike da baccin rai ta koma. Dakin iman ta soma hada kayan ta a trolley iman ta kalle ta "hafsat ina kuma zaki je"

"zan tafi gidan nawa uban, matuƙar na cigaba da zama a gidan wata rana sai na ba kishiyar mugun bugu tayi tunanin kowa irin kine who does she think she is "

iman ta ce"dan Allah kiyi haƙuri hafsat kar ki tafi"

"iman i have made my decision,ya rage naki ki dauki shawarar dana baki  idan ba haka ba ki fara kirga sauran kwanakin a cikin gidan nan"

taja akwatin ta tafi iman kasa raka ta tayi ko bakin kofa ta zauna bakin gado tana hawaye wannan wata irin masifa ce haka Hannu ta daga tayi addu'a Allah ya kawo mata mafita cikin rayuwar ta amman yau duk santa da gidan taji ya fita a kanta har ta fara tunanin ta samu Suhail ya sake tace chan ta auri wanda matsayin yazo ɗaya

kuka tayi mai isarta kafin ta tashi ta wanko fuskar ta ta zauna bakin gado tana jiran dawowar suhail

bashi ya dawo ba sai karfe biyar na yamma falon babu kowa ya nufi Dakin iman ganin babu kowa a falon ya nufi bedroom iman na kan Prayer mat tana azkhar da sallama ya shiga cikin takin 

dago kai tayi tare da amsa masa sallamar sa 

ya fara duba inda zai Hafsat ganin bai ganta ba yasa ya tambayi iman "ina Hafsat"

shiru tayi ta kafe sa da ido a iya zaman da sukayi jiya wata shaƙuwar ce sukayi da Hafsat tana da saukin kaii sosai 

sai da yayi mata magana a karo na biyu ta ce"ta tafi"

"ta tafi kuma,but ta ce zata dade hope lafiya dai"

"this question should be answer by zeenah"

"zeenah kuma?"

"ehh"

a fusace ya fita zuwa Dakin zeeenah tana zaune tana scrolling a wayar tana ganin sa ta miƙe 

"babe sannu da zuwa"

"miya hadaki da Hafsat kika koreta"

"ido ta zaro babe,ni ban koreta hasalima ita ce tamin rashin kunya infact ban ma san ta tafi ba sai jennifer ta fadamin"

zeenah "You are lying haka kawai baza ta tafi ba na san abinda zakiyi sarai nasan wacece ke ki bar ganin ina daga kauda ido daga dukkanin abinda kike a gidan nan"

Wata irin faɗuwar gaba Zeenah ta ji yau ita Suhail yake fadawa baƙaƙƙen maganganun nan 

"Suhail Wannan rashin adalci ne a gidan nan"

Rashin adalci shine abinda aka yi wa Iman tsawon watanni 

shiru tayi bata kara cewa komai ba Suhail ya fice daga dakin zama tayi bakin gado ta shiga neman lambar Yusrah unfortuanetly taji wayan a kashe wurga da waya gefe ba mamaki aikin da aike mata kan Suhail ne ya soma karyewa 

a gefe guda hafsat tana barin estate din gidan suhail ta nufi park ganin idan tace zata koma Katsina dare zaiyi hakan yasa ta nufi kaduna

karfe biyar ta isa kofar gidan malan hannun ta rike da trolley Ammi na fito daga daki idanunta ya sauka kan hafsat 

da namaki ta ce"Hafsat kece da yamma haka"

murmushi tayi ta ajiye jakar ta ce"Ammi daga gida nake"

"Amman shine zaki bi hanyar nan kisan gari ba lafiya ita zaituna ce ta barki"

"Ammi tun dai nazo lafiya ai shikenan"

jakar ta dauka ta kai daki  kafin 
ta fito waje ta samu gefen Ammi ta rafka tagumi gaba daya hankalin baya wajen babu komai a zuciyar face tausayin iman bata san wani hali ta shiga bayan tafiyar ta ba tana tsoron kada wani abu ya same ta 

Tunawa da tayi cewa ko ba komai Suhail ba zai bari a zalunci Iman ba yasa ta ɗan sami kwanciyar hankali

Ammi sai kalllon ta take lallai Hafsat akwai abinda take boyewa a ranta sai da ta gama Ayyukan tsakar gida ta dawo wajen ta ta zauna 

"Hafsat lafiya?mike damunki gaba daya baki da walwala ba haka kika saba zuwa gidan nan ba"

Murmushin yaƙe tayi bata son ta fadawa Ammi daga Abuja take gidan iman tasan matukar ta fada mata halin da Iman ke ciki Ammi zata shiga damuwa sosai,tasan wacece Ammi macece da Allah ya dora mata san yara ba iya nata ba hatta ita da take diyar kanwar duk sanda wani abu ya same Ammi na shiga tashin hankali sosai bata taɓa samun natsuwa har sai taga komai ya daidaita hakan yasa ta boƴe mata dan mamanta ce kadai da yaya Mubarak suka san da zuwanta Abuja banda Ammi kuma tun tana hanya ta faɗa masu kar wanda ya gayawa Ammi taje Abuja don zata tambaye ta lafiyar iman ita kuma bazata iya boƴe mata halin data sami iman a ciki ba hakan yasa maganar ta tsaya a tsakanin su

son ƙawar da tuhumar da Ammi ke yi mata tayi ta hanyar cewa "ammi mi kika girka"

"wake da shinkafa ne yana Kitchen ki duba yadda zai ishe ki"

Hafsat ta mike zuwa kitchen amma ko kadan ba ta jin yunwa

Ta ɗauko plate ta zuba kaɗan sannan ta koma falo

Suhail na barin zeenah ya koma dakin sa zuciyarsa cike da ƙiyyaryar ta ya rasa zeenah wata irin macece da bata san zaman lafiya bai sake fitowa ba sai da aka kira sallar magariba sai ya gama har isha'i ya dawo gidan 

dakin sa ya koma yana kwance akan gado ya lumshe idanunsa 

tunanin iman kawai yake Murmushinta, kulawarta da kuma yadda take kokarin faranta masa rai duk suka dawo masa a zuciya 

kamar wanda tsikara ya tashi ya nufi part dinta 

babu kowa palorn sai saukin karatun Alkur'ani dake fita daga bedroom cikin wata kalar murya mai narkar da zuciya ya jima yana. sauraren cool voice din wanda sautin ke amsa kuwa cikin kwanyar kansa 

cike da natsuwa ya shiga dakin jin an  turo kofar dakin yasa dagowa bayan ta kammala ayar da take karanta wa 

dago kai tayi Idanunsu suka haɗu.

Na wasu dakiku babu wanda ya yi magana

Suhail ya gyara tsayuwarsa yana kallon ta "iman please i need cup of coffee"

a yadda yayi Maganar taso tayi murmushi amman ta dake ta maida Alqur'ani kan side bed ta fita Kitchen

da sauri ya dauko wayar dake kan mirror ya aike ta ta hada masa tea da kawai ya samu access da wayar ta 

yayi Sa'a wayar babu Password,iman bata taba sakawa wayar password ba pictures ya fara shiga yaga

Wani hoto ya tsaya kallo na tsawon lokaci Hoto ne da aka ɗauka ranar walima,Iman na tsaye tsakanin Malam da Ammi tana dariya 

jingina kai yayi da alon gadon yana tunanin girman hakkin iman daya dauka na rabata da farin cikin ta da yayi bai sani ba ko Allah zai iya yafe masa ya rabo ta da farin ciki Sannan ya gaza kyautata a matsayin sa na mijinta 

ya jima cikin wannan yanayin ya tuna ba abinda ya kawo sa kenan ba Contact ya shiga ya dauki lambar da tayi saving da soul sister♥️ wanda ba makawa yasan ta hafsat 

bayan ya gama ya dauki wata lamba ya maida wayar ya ajiye kenan iman ta dawo hannun ta riƙe da coffee ta miƙa masa 

amsa yayi tare da sakar nata wani soft smile thank You Ammi's Daugther a yanayin da ya kirata sai da taji wani iri a zuciyatar ta sunan ya yi mata dad'i wanda har ya kasa boƴe reaction din ta sai da tayi murmushi duk da na gefen baki ne Suhail yaji dad'i sannan kuma ya samu sunan da zai rinƙa kiranta dashi ganin taji dad'in suna 

ya fita ya koma dakin tass ya shanye coffee dinnya ajiye cup din lambar hafsat ya fara dialing kusan kira biyu ba a daga ba 

dayar lambar daya dauka ya tura recharge card 

iman na kwace taji karar shigowar text tana dubawa taga katin dubu Biyar mamaki take ko wani ya yi mistake ya saka mata yaya Mubarak kadai ke saka mata kati shima baya wuce na dubu daya 

tana wannan tunanin waki sakon ya kara shigowa ganin ɓakuwar lamba yasa tayi saurin dagawa massage bda aka tura mata ya tabbatar mata da katin daga ga suhail ne 

"Ammi's Daugther thank You for the tead" shine Abinda aka turo 

lambar Hafsat ta shiga kira dan rashin kati ya hanata kiranta taji ko ta isa gida lafiya 

ji tayi kamar waya take ta jira har kusan minti Talatin still bata gama Wayar ba

hakan yasa ta haƙura ta kwanta

Hafsat na shigowa daƙi ta tatar da misscall din Number dailing tayi Suhail ya katse ya sake kiran ta

"hello Hafsat ykk"

"Lafiya qlau Amman ban gane mai magana ba"

murmushi yayi ya ce"Suhail ne"

ido ta zaro "yaya Suhail i'm sorry kasan banda Number ka"

"don't mind,i just call to thanks soo for the visit duk da ma baki jira munyi sallama ba"


murmushi tayi a karo na biyu"tafiyar ce tazo kai tsaye shiyasa"

"yanzu sai yaushe kuma"

"a yanzu dai ba rana gaskiya kam"

"kodai kina fushi akan abinda zeenah tayi maki"

"halin dana iske Iman a ci yafi batamin rai fiye da abinda tayi min,amman duk da haka iman is still backing You up bana cewar ba laifin ka bane kasan miyasa haka saboda ta dora rayuwar ta akan kane "

yaya Suhail yayi ƙasa da murya"i know amman basan ta yadda abubuwa suka lalace haka ba but trust me zan gyara kuskure na"

daga karshe Hafsat ta ce"Iman tana bukatar mijinta bawai tausaya kawai ba"