GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 20

by @nusybee143

Page 20



"Sannu da zuwa Ummeey"ta faɗa tana rarraba idanu 

"Yau kuma me kika je kika jangwalo?

Dama ina ganin fitarki ta ɗazu na san ba banza ba,ina kika je Shaheeda?"

"Ummeey lambu kawai na je,ce miki aka yi na yi wani abin ko?"

"Ban sani ba,tashi ki tafi ubanki yana son ganinki"babu musu ta saka hijabi ta fice daga ɗakin, Ummeey ta bi ta a baya 

Da sallama ta shiga parlourn abban nasu,shi kaɗai ne ya amsa, Ummeenta ta yi sallama itama, Shaheeda ta samu waje ta zauna tana kallon Hajiya Atika da Safwan ta gefen ido,saura ƙiris ta fashe da dariya ganin yadda Hajiya Atika take ta cika tana batsewa 

Sai da ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya, sannan Abba ya ce "Shaheeda wato iya shegenki ƙaruwa yake yi ko?"

"To fa!su Fatima iyayen laifi!Abba me aka ce maka na yi yanzu ?"

"Ƙaniyarki na ce!

Wato dai ba za ki fasa halinki ba ko?

Ɗazu me ya haɗa ki da Safwan har kika zagi mahaifiyarshi?"

Kallon Safwan ta yi tana ƙwalalo idanu ta ce"innalillahi!

Abba zagi kuma?

Ka san dai bana zagin manya abba,zuwa ya yi fa yana gaya min magana akan zan fita ƙasar waje,kawai sai na ce masa ai ba'a kai daƙiƙai,ya ce ai shi ba daƙiƙi bane,na ce mu gani a ƙasa,shikenan fa!

Oh Allah!Abba ka gani ko?dama fa na ce akwai mutanen da suke baƙin ciki da tafiyar nan tawa a gidan nan,ga alamu nan dai muna gani"

Ummeey ta dubi Shaheeda cikin takaici,don ta tabbatar ba haka aka yi ba, saboda ba sabon abu bane a wajen Shaheeda cin zalin yara a gidan musamman Safwan,shi kuma kamar dole in dai ya ganta sai ya yi mata magana,amma kafin ta yi magana Abba ya yi abin da ya saba duk sanda aka yi case da Shaheeda a gidan 

"Shaheeda ni nake so ta tafi karatu ƙasar waje,da kuɗina na biya mata, babu wanda ya isa ya sa na janye sai Allah, don haka bana son sake jin an taɓo ta da maganar tafiyar nan

Babyn abbanta!"ya faɗa yana mayar da hankalinsa ga Shaheeda,yana sakin fuska, Shaheeda ta yi murmushi tana faɗin"na'am abbana na kaina "

"Allah ya yi miki albarka, Allah ya taimaka ya bayar da abin da aka je nema,na san ba ki da wasa a karatu, to ina son ki ƙara dagewa,banda kula abokan banza,banda shiririta duk da dai na san ba halayenki bane, Allah ya yi miki albarka "Shaheeda tana murmushi ta ce"Ameen Abbana "

"Amma abban yara wannan ba yi bane!ya yarinya zata yi min rashin kunya kuma ka goya mata baya?"

Kallonta ya yi fuska a ɗaure ya ce"Atika!

Ba Shaheeda ba,duk ɗan da babba ya kasa jan girmansa a gabansa na ba shi umarni ya take,idan har kina son girmanki ki girmama kanki,sai Shaheeda ta girmama ki,ku tashi ku tafi,na sallame ku"kasancewar yau girkin Hajiya Zainab ya sa bata tashi ba,ta bi su da idanu kawai, Shaheeda tana murmushi ta rissina tana faɗin"sai da safe "sannan ta miƙe ta fice daga parlourn 

Ta san Hajiya Atika ba ƙyale ta ta yi ba, don haka ta tsaya kamar wadda take danna waya kawai, Hajiya Atika ta zo kusa da ita, cikin ɓacin rai ta ce"yarinya ƙanƙanuwa kamarki,wai kin iya haddasa husuma,wata ƴar tamilo da ke,Ni za ki haɗa da mijina?to......"

"Tooooo!

Ƴar tamilo kuma?"Shaheeda ta faɗa tana kama haɓa tana zare idanu"

"Eh na faɗa! ƴar tamilo, ƴar tamilo ma da haka take da an shiga uku"

Shaheeda ta gyara tsayuwarta ta ce"idan ni ƴar tamilo ce ke kuma sai yaya kenan?

Tsaka ko?"

"Shaheeda nice tsaka?

Har fitsara da rashin mutuncin naki ya kai ki kira ni da sunan dabbar da Allah ya tsinewa?"

"A'a to menene marabarki da ita? tunda dai Allah ya tsinewa mai hassada,kuma ga ki nan a cikinta dumu-dumu,kin ga kuwa babu laifi don na kira ki haka

Kin ga ni mu bar wannan zancen, gobe zan tafi karatu Belgium,a saka mu a addu'a "tana kai wa nan ta sa kai da nufin wucewa 

A fusace Hajiya Atika ta ce"Allah ya tsare ni da yi miki addu'a,sai dai na roki Allah ya tsine miki albarka "

Shaheeda ta ce"ko da yake bar shi ma, addu'a yawanci za ki ga ana neman malamai su taya mu da ita da manyan bayin Allah,don ta karɓu,amma ke kika yi addu'a da wannan bakin baki ai sai ki sa ma ta ƙi karɓuwa,sai anjuma "ta wuce tana ƴar dariya ranta fes, Hajiya Atika ta gama masifarta ta ja hannun Safwan da ya yi shiru yana kallon ikon Allah ta wuce sashenta ranta a ɓace 

Washe gari aka tashi da shirin tafiyar Shaheeda zuwa Belgium,tun safe Muyassar ya zo gidan, don shine zai kai su airport 

Suna zaune a ɗakinta suna haɗa kaya ya dube ta da kulawa ya ce"Shaheeda!ni dai roƙona a gare ki don Allah kar ki ce komai aka yi miki za ki rama,ki zama mai haƙuri mana,babu wanda ya kai mai haƙuri riba,amma rashin haƙurin nan babu abin da yake haifarwa sai dana sani "

A kaikaice ta kalle shi ta ce"tunda na zo duniya nake ganin yadda ake ƙuntata ran Ummeey,mace mai haƙuri,sai dai ta ƙunshe baƙin ciki ta yi kuka,ka san da haka kai ma,ko da baka san wani ba ka san wani, tunda wani lokacin a gabanka ake ci mata mutunci,amma ni ko yaya aka taɓa ni ina tabbatar da cewa na sauke bashin wannan tsokanar da aka yi min,da na sauke sai na ji ni wasai, lafiya lau,to kuma sai ka ce min wani haƙuri yana bayar da abin da rashin shi bai bayar ba?

Ka ga abar maganar,raina zai iya ɓaci"Muyassar ya girgiza kai cikin jinjina halin Shaheeda ya ce"an bar ta babyn Daddy "ta yi murmushi tana wani blushing 

Da kanshi ya kai su airport ita da Ummeey,don kaf cikin matan gidan babu wadda ta bi su,hakan bai dame ta ba,ta cigaba da sabgoginta har ta bar gidan 

Uncle Habib ne zai kai ta har Belgium,don haka suka same shi a airport,ta ɗagawa Alhaji Yusuf hannu,suka shiga cikin airport ɗin zuciyar Shaheeda cike da matsanancin farin ciki da ɗoki 





💫

Roxy ta ɗago da idanunta da suka juye saboda damuwa da rashin samun kayan mayen da bata yi ba ta zuba su akan Haisam da ya yi shiru tun ɗazu yana kallonta,a sanyaye ta ce"Shaheeda ta bar Nigeria cike da farin cikin zuwa Belgium, ba tare da ta san cewa ta je ne don ta haɗu da hanyar tarwatsewar rayuwarta da farin cikinta ba na har abada, wannan tafiyar ta Shaheeda ita ce silar komai a yau, har zuwa samuwar Roxy, wadda a tsawon wanzuwarta babu wani abu mai suna farin ciki ko walwala,babu wani abu mai suna jin daɗin rayuwa,sai tarin ƙalubale,guje-gujen neman matsera daga nan zuwa can,kuka a ɓoye, saboda a wannan ƙadamin Roxy ta san babu mai lallashinta,sai dai rauninta ya zama makami ga mai harinta"Haisam da ya zuba mata idanu ya ce"ta yaya?kuma meyasa?"

Roxy ta ɗan girgiza kai ta ce"ba na ce ba dai,amma bari na cigaba "ta cigaba ba tare da ta sake kallonsa ba





💫


Kwanan uncle Habib biyu a Ghent yana kammalawa Shaheeda komai,ya samar mata lafiyayyen ɗaki a hostel ɗin su,ya ba ta dukkan abin da take buƙata sannan ya yi mata sallama ya bar Belgium zuwa Nigeria 

Kwata kwata rayuwa bata ba wa Shaheeda wahala a sabon wajen da ta tsinci kanta ba,ta cigaba da rayuwarta cikin farin ciki, tana zama cikakkiyar yar gari sai gashi har ƙawaye gare ta

Bata yi cikakken watanni huɗu ba a Belgium ta iya Yaren dutch na ƙasar Belgium, sannan ta yi manyan ƙawaye Alice da Olivia 

A ɓangaren karatu kuwa Masha Allah za'a ce,don a first semester ɗin su ita ce ta yi musu overall,dama fa Shaheeda ba baya ba ta fannin kai, kaf gidansu babu wanda ya kai ta kwanya,tun tana ƴar ƙaramarta bata taɓa faɗuwa a jarrabawa ba,gata da sauƙin kai,ita matsalarta a rayuwa rashin haƙuri,amma duk da hakan Abba ya fi sonta fiye da kowa a gidan,kuma a bayyane yake nunawa,hakan ne ma ya ƙara rura wutar ƙiyayyar da mutanen gidan suke yi mata 

Ummeey da ta san hakan zai iya faruwa kullum kokarinta ko da ace Abba ba zai iya daidaita soyayyar da yake yiwa yaran nashi baki ɗaya ba amma aƙalla ya ɓoye irin son da yake yi mata,sai dai inaaa!ko saurarenta ma baya yi,akan Shaheeda ba ya sauraren kowa 

Yau kwanansu biyu kenan da komawa Second semester, karatu ka'in da na'in ya ɗauki zafi ga Shaheeda, musamman da ya kasance wannan semester ɗin ita ce ta biyu,ko na ce ta ƙarshe a level one 

Yau ta tashi da menstrual cramps ɗin ta,kuma ya matsa mata sosai,gashi har jiri yake saka ta,ta samu da ƙyar ta sha magani sannan ta koma ta kwanta

Ta juma tana bacci sannan ta farka,ganin har yanzu akwai sauran lecture ɗaya da lokacinta bai fita ba ya sa ta miƙe ta yi wanka,ta sauya kaya zuwa doguwar rigarta,ta ɗauki jakarta ta fita

Sai dai ba ta yi nisa ba ta fara jin jiri, da alamu har yanzu jikin nata sai a hankali,amma haka ta dake ta cigaba da tafiya,don burinta ta samu ta yi attending lecture ɗin nan,don ta tsani fashin lecture 

Ba ta ankara ba ta ji jiri ya kwashe ta ya yi ƙasa da ita,har ta saddaƙar da ta faɗi ma,amma sai ta ji an riƙe ta,ta ɗago da sauri tana kallonsa

Kyakkyawan guy ne sosai, waɗanda alamu suka nuna shi ba cikakken ɗan Belgium bane,amma ya fi kama da halfcast

Da sauri ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa,ƙatuwar sarƙar Cross ɗin da take wuyansa,da da tattoo ɗin da yake gefen wuyansa ta ɓangaren hagu ne ya alamtawa Shaheeda cewa shi ɗin ba musulmi bane,ta yi ɗan murmushin yaƙe tana faɗin "na gode"da Yaren dutch sannan ta wuce ta bar wajen 

Sai dai har aka yi lectures aka gama Shaheeda bata fahimci komai ba,asalima hankalinta yana wani wajen dabam,tunaninta ya tafi  

Da aka gama lecture suka fito ita da ƙawayenta Alice da Olivia, kasancewar su ma suna da rawar kai da surutu irin nata sai labarin yadda lecture ɗin ta kasance suke yi,amma shugabarsu a surutu da kauɗi ta yi shiru 

Olivia ce ta fara kula cewa kamar ƙawar ta su tana cikin damuwa,ta taɓo ta tana tambayarta,amma sai ta girgiza kai tana murmushi ta ce cikin Yaren dutch "babu komai,ko kin manta bana jin daɗi ne"

Alice ta kalle ta ta ce"ai sai da na ce ki zauna kika ƙi,gashi nan duk kin yi wani iri"ita dai bata yi magana ba,suka cigaba da tafiya har suka isa hostel 

Kwana biyu da faruwar hakan Muyassar ya sauka a Belgium,kamar a mafarki su Shaheeda sun fito daga lecture suka ganshi,ai kuwa Shaheeda bata yi wata wata ba ta tafi da gudu ta ɗane shi tana murna, shine ya yi saurin riƙe ta don kar ta faɗa jikinsa yana faɗin "oh Shaheeda!

Ke fa ba kya girma ko?"tana murmushi ta ce"na yi kewarku yaya,ina Ummeey?ina abbana?ya kowa da kowa?"

Muyassar ya ce"babu tarba mai kyau,babu abinci, ballantana drinks,amma an fara yi min tambayoyi,sannu shugabar masu hankali"

Zumɓura baki ta yi,ya yi murmushi,su Alice suka ƙarasa suka gaisa,sannan suka wuce wajen zaman ɗalibai a makarantar 

Gaban Shaheeda ya buga da ƙarfi sakamakon hango guy ɗin nan da ya riƙe ta sanda ta yanke jiki zata faɗi,ya yi kyau sosai,yana sanye cikin kayan da suka amshi jikinsa kalar blue black,ya mayar da hankali sosai akan littafin da yake gabansa,za alamu karatu yake yi

Cikin ƙanƙanin lokaci Shaheeda ta nemi dirircewa,har sai da su Muyassar suka fara ganewa,amma sai ta wayance ta canja magana

Sun juma a wajen suna hira cikin farin ciki ita da Muyassar,har sai da Guy ɗin nan ya tashi ya bar wajen sannan ta cewa Muyassar zata koma saboda ta duba darasinta na yau, Muyassar bai wani ja ba,ya ce "Allah ya yi jagora baby sister,ki dage da karatu,nima in sha Allah very soon zan koma na je na haɗa Masters ɗina"

Waro idanu ta yi tana murmushi ta ce"like serious?

Na bar Nigeria kai ma shine za ka bari?

To amma da ba cewa ka yi tare za mu tafi ba?"

Sosa kyakykyawar sumarsa ya yi ya ce"aure wai Mummy na ta ce zata yi min,ni kuma I'm not ready gaskiya, shiyasa zan koma, beside ina da wadda nake so,ita kuma zata ba ni wata"

Murmushi Shaheeda ta yi ta ce"alright!

All the best! Allah ya taimaka,ni zan shiga ciki to"suka yi sallama,ta nufi hostel shi kuma ya nufi komawa hotel ɗin da ya sauka 





#Nusy_bee