SIRRIN ZUCIYA

Chapter two

by @aysharano22

🤍SIRRIN ZUCIYA🤍

By Aysha Rano✨

02

Wani ihu da Esther ta saki shaff ta manta cewa cikin class suke tsabar farin ciki.

Nan take hankalin kowa dake cikin class ya dawo kanta, including lecturer.

Ba shiri tayi gum da baki ta shiga rarraba ido don ba ta san yaushe ihun ya fito ba. Tsabar farin ciki ne.

Nunata lecturer ɗin ya shiga yi da hannunsa yace:

“You, stand up. What’s that your name again?”

Ba musu ta mike tsaye tana kallonsa.

Yace:

“Your name?”

Tace:

“Esther… Edward.”

Yace:

“Esther Edward, why are you shouting in my class?”

Duk ta daburce tace:

“Ss… sorry sir.”

Yace:

“That’s not the answer to my question. I asked why are you shouting in my class?”

Tace:

“Nothing sir… sorry sir.”

Tsaki ya saki before ya nuna mata ƙofa yace:

“Get out.”

Ba musu ta ɗauki wayarta ta fita daga class ɗin sum-sum, don da waɗannan tambayoyin da ya tsareta da su, ita gara ya koreta ta san korarta yayi.

Lilly da Suhana dai gum kake ji kamar ba tare suke surutun da ita ba.


Suhana Abraham Montana shine cikakken sunanta. Yoruba name dinta kuma Moremi wanda paternal grandfather dinta ya sa mata tun tana jaririya.

Mahaifinta Mr Abraham Montana shahararren business tycoon ne kuma sananne a kudancin Nigeria. Ɗan asalin jihar Ogun ne amma hatta iyayensa, kakanin Suhana kenan, a Lagos suka yi rayuwarsu, likewise shi ma mahaifin nata.

Ita ma kuma a Lagos aka haifeta, anan ta taso, anan kuma take duk wani karatunta. So technically su cikakkun yarbawan Lagos ne kuma kafatanin danginta Christians ne.

Mahaifiyarta mai suna Matilda ita ma Christian ce amma ta Arewa. Asalinta Jos dake jihar Plateau.

Kowa ya san northern Christians suna jin Hausa sosai, wasu ma baza’a taɓa gane they are not Muslims ba in terms of dressing ɗinsu da kuma yadda suka iya Hausa.

So mahaifiyar Suhana na ɗaya daga cikin irinsu domin kuwa an haifeta a Jos, tayi har secondary school dinta a Jos. Sai da zata shiga jami’a ne ta tafi University of Lagos inda anan suka haɗu da mahaifin Suhana har suka yi aure.

Duk da ita ma Christian ce kamar su, amma ita daga baya ta musulunta ta hanyar wata aunt dinta data kasance musulma, wanda kuma shine dalilin da yayi sanadin rabuwarsu.

Kasancewar ‘ya’yansu biyu ne, sai ta tafi da first born ɗinsu mai suna Melisa. A lokacin tana da shekara 14.

Shi kuma daddy ya ɗauki Suhana mai shekaru 10.

Don sai da aka kai ruwa rana ma kafin ya yadda ta tafi da Melisa, don a cewarsa bazata je ta cutar mishi da ’ya ba ta jefata cikin addinin musulmai.

Amma sanin da yayi ko ina za a je baza a taɓa bashi damar riƙe duk su biyun ba, dole ya haƙura ta tafi da ita.

Tun daga nan kuma ya sama ransa ’ya ɗaya gareshi a duniya kuma ita ce Suhana.

Bayan ita bazai taɓa karɓan Melisa a matsayin ’ya ba, musamman data zaɓi tabi mahaifiyarta ta je tayi addinin da bai taɓa tsanar wani addini a duniya ba kamar shi.

Wannan dalilin yasa tun da suka tafi basu sake ji daga gare su ba kamar yadda suma basu ji daga gare shi ba.

Har zuwa yanzu da Suhana zata cika shekara 22, wanda yayi daidai da shekara 12 kenan da rabuwar iyayensu.

Tun daga lokacin kula da Suhana ya koma hannun nanny, wacce ita ma ta kasance Christian ɗin Arewa, shi yasa ta iya Hausa sosai.

Dama tun Mom ɗinsu na nan ita ce ke kula da su, amma bayan tafiyarta sai nannyn ta zama tamkar mahaifiya a gareta, don tana tausayinta sosai tana kuma sonta saboda bata taɓa yin wani abu na cutarwa ba a gareta.

Shi yasa daddy ke kyautata mata, domin farin cikinsa a duniya shine ya ga Suhana cikin farin ciki.

Wannan dalilin yasa Suhana ta taso cikin gata da soyayya, don ko da ta rasa uwa, mahaifinta bai taɓa bari ta nemi wani abu ta rasa ba.

Yana mata duk abin da take buƙata saboda money is not his problem.

The only matsala da suke samu always shine rashin zaman da baya yi a gida.

He’s a very busy person. Da ƙyar yake iya squeezing yayi one or two weeks a gida tare da ita saboda tight schedule ɗinsa.

Shi yasa tun da suka rabu da Mom dinta ko tunanin aure bai sake yi ba saboda ya san ba time ne da shi ba.

Koda yaushe gidansu daga ita sai nanny da domestic staff ɗinsu guda biyu sai mai gadi.

Don ma Allah ya taimaketa ta haɗu da Esther da Lilly tun Primary School, gashi kuma har yanzu da suke jami’a basu rabu ba.

Friendship ɗinsu ma sai sake ƙarfi yake, da bata san ya rayuwa zai kasance mata ba tsabar loneliness saboda they are like sisters to her.

  ✨✨✨

My Dear Habibties❤️

Alhamdulillah, Allah Ya sake dawo da ni gare ku. Allah Ya sa yadda na fara lafiya, haka na kammala lafiya. Na yi kewarku sosai, kuma ina fatan za ku ji daɗin wannan sabon tafiya da za mu fara tare.

Littafin SIRRIN ZUCIYA littafi ne na kuɗi.

Za ki biya ₦500 zuwa

0013569116
Aisha Ahmad Tijjani
Ja’iz Bank.

Bayan kin biya, sai ki turo min da receipt ta lambar da ke sama.

Littafin ya kasu kashi biyu:
📖Book 1 da
📖Book 2

Nagode da goyon bayan da kuke bani a ko da yaushe. Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya bar zumunci.
Love you all❤️


Rano✨