Muradin zuci
by @bintuuu
Tun ana sauran kwana biyar su koma Nigeria Papa yasa Habiba hada kayan Fadwa tsaf acikin jibga jibgan akwatunan da ya siyo mata guda biyu. Dan kayan da ya siya mata zuwa wannan lokacin bazasu dauku cikin madauki daya ba saboda tarin yawansu, wuni biyu Habiba tayi tana hade kayan guri daya sannan ta hau killace na uwar dakin nata dana Baby Khadijah, su Imam kuwa sun riga da sun hada komai daman tun kafin zuwan wannan lokacin. Da Papa yaga yanda Mamma ta hada komai nata kamar wanda bazata dawo qasar ba saida yayi mata magana "Fatima bazaki bar wasu ba? I want us to return during fall (Autumn season), saboda akwai sauran ayyukan da ban gama kammalawa ba anan" batareda ta juyo ba tace "Ni dai na gama zaman qasar nan babu abunda zai dawo dani zuwa nan da September kuma, babu alkhairi ko na misqala zarratan acikinta, zaman cikinta bai qareni da komai ba sai guzirin baqin ciki" ta qarasa magana tana sake tula wasu sauran kayan cikin qaton box dinta, yana kallonta yace "Wane irin maganane wannan kuma, kinaji fa maganan aikina nake miki wanda dole zan buqaci iyalina a kusa dani saboda dogon zaman da zan dawo yi" sai sannan ta kallesa tace "Wallahi bazan sake takowa cikin qasar nan kwana kusa ba. Nasani gaba kuma ko 'yan biyu za'a ajiye mana a kofar gida" tsayawa kallon juna sukayi sai can ya girgiza kai sannan ya nufi crib din da Baby Khadija ke kwance aciki ya fara kokarin daukanta. Tana tsayen take kallonsa amma ganin bai kulata ba yasa tayi kwafa ta cigaba da jera kayanta tana ayyana yanda zata bullowa alamarin in sun koma.
Ana gobe zasu tafi su Ladan sukazo yi musu sallama tareda 'ya'yansu biyu wadda babbar suke kiranta da Kamila sai ma biyinta da shima ake kiransa Kareem wanda shekarunsa sukazo daidai danasu Imam. A wannan lokacin ma saida Mamin ta san yanda tayi ta dora Momman akan wasu maganganun da suka kebe a dakinta. Ladan kuwa da ya karbi Fadwan sai tausayinta shima ya kamasa na ganin za'a tafi da ita inda ko a mafarki batada wani hadi da mutanen dake rayuwa a qasar, can ya miqata ga Papan yace "Allah ya baku ladan riqonta ya kuma albarkaci rayuwarta da na 'yan'uwanta gaba daya" Papa ya amsa da Amin yana kallonta, dan a badini shima in aka tona zuciyarsa tausayin yarinyar yake ji a kullum, saboda har sannan bai cire rai da dawowar mahaifiyar ta ba, a kullum yana fatan suji sallamanta akan ta dawo karban yarta amma ya sani wannan mafarki ne da bai san ranar farkawansa ba.
Ranan da zasu tafi tunda sassafe Ladan din yazo sannan Papa ya kira musu Uber guda biyu, daya Ladan ya shiga dasu Imam harda Habiba dake goye da Fadwan, dayan kuma shi ya shiga tare da mai dakin tasa yana riqe da Khadijah suka tafi Airport. Isarsu basu dau wani lokaci ba yayi sallama na aminci da aminin nasa sannan jirginsu ya tashi. Wuni guda sukayi cur kafin suyi layover a Heathrow Airport -London na wasu qalilan din awanni sannan suka sake bin wani flight din da zai kaisu Lagos. Nan ma sai da suka kwana biyu a Lagos suna hutawa a Babban family house din su Papan sannan suka sake bin wani flight din zuwa Kanon Dabo, inda anan ne kuma zasu kai ga Masarautar Kumi dake garin Kano, babbar daula da karfin iko da dukiya yasa tayi qaurin suna a kaf fadin Nigeria a wannan lokacin. Sunan Masarautar Kumi babu lungu da sakon da bai zagaya ba tun a 18-hundreds har zuwa wannan qarnin da ake ciki, wanda sarki Abdulfatah yake jagorancin ta a wannan shekarun tareda 'ya'yansa maza guda hudu wanda uku suka fito daga dakin uwar gidansa mai suna Amina (wadda ake kira da Uwah) sannan guda daya kuma ya fito daga dakin Amaryarsa mai suna Aisha (wadda Allah yayiwa rasuwa shekaru biyu kenan) .
Sarki Abdulfatah dattijon mutum ne da ya kasance mai sanyi da dattako ta kowanne fanni, a inda wannan kyawawan dabi'un nasa suka sauqa har zuwa kan 'ya'yansa guda hudu da Allah ya basa, Abdulaziz (wato Papa) shi ya kasance na fari kuma Yarima mai jiran gado a wannan lokacin, sai na biyunsu Abdulrazaq da na ukunsu Abdulmalik sannan Abdulrahman da suke uba daya dashi kuma qaraminsu. Sanin hali da kuma irin tarbiyar da mahaifinsu ya tasosu dashi yasa Papa baiji shakku ko kadan akan daukan Fadwa ba. Hasalima yasani wannan shine hukunci mafi daidai da mahaifinsa zaiso ya yanke a wannan lokacin, shiyasa baya dana sani ko kadan akan daukanta kuma cike yake da yaqinin iyayensa zasu karbeta kamar yanda ya karbeta shima.
Auren Papa da Momma hadi ne na Allah a sanadin iyayensu a inda masarautu biyu suka hade ta fannin aure. Momma ta fito daga daular Kubaya da ke garin Bauchi, 'yar sarkin dake reigning a wannan lokacin shima, su uku mata suka fito a dakinsu, babbarsu Aina'u sai Binta da Khadija wadda suke kira Madina sai kuma babban yayansu daya kabiru . Kasancewarsu 'ya'yan mace ta biyu a gidan sai hakan yasa mahaifiyarsu ta zamo mace mai babban buri a rayuwa, dan daga Binta har Aina'u da ta kasance yayarta saida kowaccensu ta shiga gidan gani na fada, a inda Aina'u take auren hamshaqin mai kudi a Abuja wanda kuma ake juya qasar dashi a siyasance, sai ita Binta (wato Momma) dake auren dan sarkin Kumi mai jiran gado. Daula da tarin dukiya ta sarki Abdulfatah da 'ya'yansa yasa mahaifiyarta ta san yanda tayi ta tusawa mahaifin nasu aqidar auren har ta isa kunnen sarki Abdulfatah, wanda shima yayi farinciki da kuma amanna da kasantuwar hakan har auren ya qullu tsakanin 'ya'yan nasu. A farkon tarayyar aurensu Binta ta kasance mace mai duqar dakai ga mijinta kuma tayi kokari sosai wajen boye halayenta na badini amma akace hali zanen dutse, da tafiya ta fara nisa nan kuma Abdulaziz ya fara gane wace irin mace iyayen nasa suka aura masa ta fuskar halayya.
Haihuwarta na farko mai martaba ya sa aka musu cuku cukun visa suka tafi United States ta haihu acikin garin Houston, inda ta haifo 'ya'yanta biyu maza masu haiba, na farin daya fito a mintuna ashirin na farko aka saka masa suna Imam sai na biyunsa Imran. Ya'yan da suka fito cikin gata ta kowanne fanni na rayuwarsu, ta inda Imran ya dauko kamannin Papa gaba da baya harda duhun fatarsa sai kuma Imam ya dauko mahaifiyarsu ta fannin hasken fatarsa. Papa bai taba jin yana alfahari da Momma irin na wannan lokacin ba, dan wannan kyauta da Allah ya basa ta silar ta ba qaramin farin ciki hakan ya saka masa ba, ya kuma dauki damarar zama da jure kowanne hali da mai dakin tasa zata bijiro dasu ko agaba ne. Dan Adam da samun waje..sai ya kasance Momma batayi duba da hakuri da sanyi irin na mijinta ba gurin wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu, sai tayi amfani da kyawawan mu'amalarsa a gareta gurin baje kolin duk wani fitinarta akansa, amma a dukkan mafari dole ya kasance da qarshensa, dan karo na farko tayi gamo da wani bangaren halayya daga mijin nata akan jinjira Fadwa, kuma a karo na farko ya fara taka mata burki akan halin da ta sabarwa kanta dasu. Amma kunaga wannan soyayyar da yake nunawa Fadwan a gurin matarsa ba wata wutar yake sake cinnawa a zuciyarta ba? Shin hakan zai fidda da mai ido kuwa?...
Ba miqaqqiyar tafiya bace a wannan labarin. Sai mun hau tudu da kwari dangane da labarin Fadwa acikin wannan babban gida na sarauta a inda zamu gani shin da gasken zata kasance daya daga cikinsu, ko kuma zata rayu ne a qarqashin kaddarar da ta barota da qasar haihuwarta?
-------
Ranan da jirginsu ya sauqa garin Kano da yammaci suka samu motoci har guda biyu suna jirar isowarsu dan kaisu gida kuma duk a qarqashin umarnin Mai martaba dan mutum ne da yake daukaka lamarin 'ya'yansa ta fuska me kyau wanda kowa ya shaida hakan, kar ma azo batun 'yan biyun jikokinsa da yake matuqar so. Duk wanda yake kwana ya kuma tashi acikin Masarautar nan yasan soyayyar dake tsakanin Mai martaba da jikokinsa biyun nan wanda hakan har ya taba mahaifiyar su, shiyasa duk fitinar Binta a gidan kusan tarin lokuta mai martaba yana kauda kansa ne dalilin wannan 'ya'yan nata guda biyu, duk yanda Uwah take kwana da abun a ranta haka take hakurin zama da matar dan nata mai shafaffen ido.
Sai yamma lis motarsu ta isa shimfideden gate din da zai shigar da mutum cikin tanqamemen gidan, a inda gidan Papa yake nesa da sashen mahaifan nasa, dan tafiya ce mai dan nisa da aqalla zata dauki mutum 15 minutes in yana tafe bisa kafa ba abun hawa ba. Gefe da babban building din su Papan kuma wani building ne da bai kai nasun ba amma ya tsaru shima iya tsaruwa sannan bana kowa bane face 'ya'yansu guda biyun nan, gini ne tsararre da Mai martaba yasa aka yisa musamman dansu ya kuma zuba hadimai masu kulawa da sashen, sai ya zamto Twins suna da nasu kebabben gidan wanda ko basu wuni acikinsa ba suna zuwa kwana acikinsa. A yammacin nan sun san sun dawo gida dan tun kafin aje ko'ina jama'a suka fara cincirindon zuwa sashensu, sanin za'a shigo dinne yasa tun wuri Papa ya ware daki daya dake cikin falo na farko na sashen Momman yasa Habiba kintsa kayan Fadwan anan, dayake suna da hadimai masu tarin yawa sai ya zamto ko Ina tsaf yake a gyare. Momma kuwa gaba tayi zuwa falonta na biyu kafin a dangana da makeken dakinta, sai ya kasance duk wa'inda suka shigo can falon nata suke isa dan Papa ficewa yayi zuwa nasa sashen daganan kuma ya wuce gurin Uwah.
A babban falonta ya sameta zaune da wasu qannenta da suke cousin suna magana, shigansa ya samu guri ya bisa kujera ya gaisa da mahaifiyar tasa, ta amsa da "Ma sha Allah, ya gajiyan hanya" yace "Alhamdulillah" sai ya juya ya gaishe da iyayen nasa dake zaune ta dayan sashen falon, daya da suke kira Baba Ladi tace "Sannunku da dawawo, kunsha zaman turai ba laifi" yayi murmushi kawai, sai ta sake cewa "Naji labarin har da wata 'yar ka dauko riqo daga can" yace "Eh Babah, Allah yayi ikonsa" kafin ta sake cewa komai Uwah ta katseta da fadin "Wato anan dai zakuyi gaisuwan barkan, ai kwa qarasa kuga 'ya'yan nasa" sukayi murmushi sai Baba Ladin tace "Zamuje Dada" ta kalli Papan tace "Allah ya taya riqo, ya bada ladan niyya, gaskiya kayi qoqari sosai" dayar ma tace "Sosai gaskiya, Allah yayi jagora" ya amsa da "Amin Amin". Sai da ya jira suka gama sauran maganganunsu da Uwah suka tafi sannan ya gyara zama sukayi sabuwar gaisuwa, nan da nan Hadimarta mai suna Laraba ta cika masa gabansa da kayan ciye ciye, yakai hannu ya dauki yankan kankana guda daya Uwahn tana kallonsa tace "Ya iyalin naka?" ya amsa da "Alhamdulillah, suna kintsawa ne" ta gyada kai sannan tace "Sai anjima zaka qarasa gurin Dattijon?" Yace "Eh yanada baqi yanzu" tace "Toh ba damuwa, anjima sai mu hadu acan din".
A daren kowa ya hallara a Babban Falon Mai martaba dake sashensa, wanda anan ne yake gudanar da duk wani taron da ya qunshi iyalinsa da 'yan'uwa. Momma na riqe da Khadija ta shigo Habiba na biye da ita a baya riqe da Fadwa a nannade cikin towel. Imam da Imran daman suna gefen Mai martaba an cika musu gabansu da kayan marmari shi kuma yana kishingide da hannunsa daya kan tum tum pillow irin na gidajen sarauta. Sanye Dattijon yake cikin alkyabba amma madadin rawani akansa sai ya zamto hulace da ta zanu da adon irin na alkyabban. Papa dake sanye cikin nashi kayan sarautar shima yana zaune tare da Abdulrazaq sannan Abdulrahman dan Abdulmalik baya qasar shima a lokacin yana matakin karatunsa na Phd a Manchester (England). Samun waje Momma tayi a gefen matar Abdulrazaq din mai suna Maimuna ta zauna. Cike da nutsuwa Mai martaba ya fara gudanar da taron da addu'a, sannan aka gaggaisa, Momma kanta a qasa ta gaishe da surukan nata sannan Mai martaba ya dan miqe zaune, ganin haka sai Abdulrahman ya miqe tsaye tareda nufan Momman ya karbi Khadijah sannan ya kaita ga mahaifin nasu, karbanta yayi yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi yace "Ma sha Allah, Sannu Khadija" Uwah tayi murmushi tana kallon jikar tata itama, sai da ya mata addu'o'i sannan ya miqata ga Uwah itama ta sanya wa yarinyar albarka sannan ta miqata ga Uncles dinta suma, sai kuma yace "Ina baquwar tamu?" duk mutan falon sai da sukayi murmushi harda Papan, Uwah tace "Ai da ita ake tafe daman" nan da nan Habiba ta miqe tareda kai Fadwan gurin Uwah, ta karbeta tana kallonta sosai, kasancewan ko'ina da hasken wuta a falon sai ya zamto idonta tar yake a bude tana kallon kowa, nan da nan idon kowa ya koma kanta suna kallonta, Uwah na murmushi tace "Ma sha Allah, kaga yarinya kamar ita tayi kanta" Abdulrahman dake kallonta shima yace "Ma sha Allah" sai Momma ta dago kai tana kallonsu, da aka miqa Fadwan gurin Mai martaba ya karbeta sai yace "Tubarakallah wannan Idanu kamar daman da shirinta na aurena tazo" sai duk mutan falon suka dara banda Momma, Maimuna da kuma Habiba. Uwah tace "Ai kuwa bazan iya kishi da wannan ba, inaa" sai Momma ta juya tana kallon yarta dake riqe a hannun Abdulrahman din amma idonsa na kan Fadwa, ji tayi kamar ta miqe ta karbeta ta bar falon amma tasan ko giyar wake tasha bazata fara kwatanta yin hakan ba ko da wasa, sai ta gyara zama tana duqar dakai cikin qunar rai, wato dagasken dai 'yan'uwansa zasu goyi bayansa akan daukan yarinyar, lallai bataga ta zama ba, lallai ne tasan ta yanda zata bullowa al'amarin tun kafin dare ya mata.
Ta bangaren Papa kuwa fuskarsa cike take da fara'a a wannan lokacin, dadin ganin yanda ahalinsa suka karbi Fadwan ya sanya masa farin ciki matuqa arai. Da Mai martaba ya mata addu'a har dashi aka amsa a falon shima yana kallon diyar tasa da har sannan idonta ke bude. Sai da aka miqata ga su Abdulrazaq sannan Mai martaba ya fara nusar dasu gaba dayansu game da ita, ya musu nuni da yadda da kaddara da kuma taimako a rayuwa, cikin girmamawa mutan falon suke amsa nasihar tasa, a tausase ya sake cewa "Wannan yarinya ita irin tata kaddarar kenan a rayuwa. Mafi kyawun riqon da za'a mata shine a alaqanceta ta fuska me kyau. Fada mata abunda ya faru da ita ba daidai bane, Inason dukkaninku ku zamo masu rufe wannan al'amari. Ban yadda wani ya tona mata wannan sirri in ba dolen hakan ce ta faru ba" duk suka amsa har Momma da Papa.
Free pages
Bintu Musa ✍️