Chapter 1
ABS CHARITY HOSPITAL
A hankali aka fito da shi daga cikin asibitin, cikin yanayi na rashin jin ƙarfin jiki yake ɗaga ƙafarsa, hannunsa dafe da cikinsa sai lumshe ido yake saboda azabar ciwon da cikinsa ke yi. "Wai Yaya a haka kake cewa muka koma gida ka ji sauƙi? Dubi halin da kake ciki fa, tafiya ma da ƙyar kake yin ta". Cikin ƙarfin hali ya ce "Kada ka damu Nasir, ai na ji sauƙi Alhamdillah".
"Yaya ban ga alamar sauƙi a tattare da kai ba, ka yi haƙuri mu koma a sake duba lafiy..." "Nasir!" Ya kira sunansa da ƙarfi ba tare daya bari ya ƙarasa maganar ba, kafin ya ce "Bana buƙatar komawa cikin asibitin nan, ku mayar dani gida, idan ma mutuwar ce nafi so ta ɗauke ni ina cikin iyalina". Ƙaramin yaron dake kusa da shi Sudais ya ɗaga kansa ya kalli mahaifin nasa, sannan ya mayar da dubansa ga asibitin da suka fito, girgiza kai ya yi, tare da duƙar da kansa ƙasa, ji ya yi mahaifinsa ya riƙe hannunsa suka ƙarasa inda motarsu take ajiye, shiga suka yi ya jingina kansa da kujera yana jin yadda cikinsa ke yi masa azababben ciwo. A hankali ya furta "Ya Allah!".
Nasir ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka bar gurin. Koda suka isa gida yamma ta yi. A madaidaiciyar harabar gidan aka yi masa shinfiɗa ya kwanta, jikinsa ko ina zafi yake jin yana yi masa. Sudais ya zauna a kusa da shi yana kallonsa, idonsa sun kaɗa sun yi jawur, cike da tsantsar ƙaunar yaron ya kalle sa ya ce "Sorry Sudais. Don't worry, ka yi mini addu'a, in sha Allah zan samu lafiya". Mammy dake zaune a ɗayan gefensa ta ce "Ai kasan halin Sudais kwata-kwata baya ƙaunar ya ganka a cikin halin na rashin lafiya, yanzu sai ya ɗaga hankalinsa fiye da kowa a gidan nan". Abba ya yi murmushi mai ciwo, ya dubi Sudais, sannan ya mayar da kallonsa ga Faruk wanda ke bin Sudais ɗin, hannunsa ya kai ya shafa kan Zahra dake saman cinyar Mammy ya ce "My Zahran Abba, idan kuka rasa ni za ki yi kewar Abbanki ko? Kada ki damu ga Ya Sudais nan zai ci gaba da kular mini daku, kuma ga Uncle nan zai maye muku gurbina". Da sauri Sudais ya kalle shi, yana tsare shi da ido tamkar yaga baƙuwar fuska, Nasir ya ce "Yaya wannan wace iriyar magana ce kake yi haka? Don Allah ka daina kana tayar mana da hankali, in sha Allah za ka warke, ai ba yau ka fara yin ciwon cikin nan ba kuma ka tashi, wannan ma za ka warke da izinin Allah".
"Kayya Nasir, wannan ciwon ba kamar wanda na saba yi ba ne, kai dai ga amanar yaran nan na bari a hannunka. Duk da bani da shakku a kanka, nasan za ka kula da su tamkar yaran da za ka haifa, Allah ya raya su, ya baka ikon kula da su, Sudais ga Uncle nan, ina son ku kasance masu biyayya a gare shi kai da ƴan uwanka, ku ɗauke shi tamkar ni. A'isha ki ƙara kula da tarbiyyar yaran nan, na san kina iya bakin ƙoƙarin ki amma ki dage, ki ƙara kula, ka da ku saki jiki da kowa, ku yi haƙuri da rayuwa a duk yadda ta zo muku" . Ya kai ƙarshen maganar yana dafe cikinsa saboda wani irin ƙulle masa da ya yi, ya ji kamar ana yankan hanjinsa da almakashi. Da ƙyar ya buɗe bakinsa ya riƙe hannun Sudais cikin tsananin ciwo ya ce "Sudais, ka ja ƴan uwanka a jiki, bayan Uncle ka da ku yarda da kowa, mutane ba abin yarda ba ne, duk yadda kake da mutum zai iya cutar da kai ta inda baka yi zato ba, ƙalilan ne masu gaskiya da amanar da ba za su iya cutar da wanda suke tare da shi ba". Sake dafe cikinsa ya yi yana ambatar sunan Allah. Cikin azabar ciwo ya sake cewa "Sudais ana cutar da al'umma ta inda ba a yi tunani ba, wannan ƙasar tamu tana buƙatar gyara. Ina fatan Allah ya cika maka burinka domin ka yi maganin azzaluman ƙasar nan masu fuska biyu, sannan ka ɗauki fansar cutar da aka yi muku, Sudais an cutar daku, Allah ya baka iko da nasarar gano ta in da aka yi muku wannan cutar, ina matuƙar son gurin da nake aiki, da AS...." Bai ƙarasa maganar ba cikinsa ya yi wani irin ƙugi tare da ƙulle wa guri ɗaya, murƙususu ya fara yi, da ƙyar ya kai hannunsa ya riƙe na Sudais yana girgiza kansa, hankalin su Mammy ba ƙara min tashi ya yi ba. Sake murɗawa ya yi, ƙara riƙe hannun Sudais ya yi, nan take ya fara salati yana kalmar shahada, yana kai wa ƙarshe daga nan ya yi shiru bai sake motsi ba.
******
ADAM A ADAM GLOBAL HOLDINGS.
Babban katafaren kaffani ne na alfarma. AAA GLOBAL HOLDINGS na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da suka yi fice a duniya, wanda ke da rassa a ƙasashe daban-daban. Kamfanin ya shahara a fannonin kasuwanci, zuba hannun jari, da fasahar zamani, kuma ya zama abin koyi a nahiyar Afirka da ma Duniya baki ɗaya. Kamfanin ya zama tamkar ginshiƙin tattalin arziƙi ga mutane da dama, kuma sunansa yana daga cikin manyan sunayen da ake girmamawa a fannin kasuwanci. A cikin babban ginin hedikwatar kamfanin da ke birnin tarayya Abuja, a bene na sama. Zaune yake a cikin ofis ɗin yana duba wasu takardu, a jikin table ɗinsa an rubuta CEO office. Adam Aliyu Adam kenan, matashin saurayi mai kimanin shekaru talatin, kuma babban ɗankasuwa, wanda Duniya ta san da zamansa, mutum ne mai haƙuri da kamun kai, wanda ya kasance dukiyarsa ba ta dame shi ba, kuma ko kaɗan mata ba sa gabansa.
Adam A Adam hamshaƙin ɗan kasuwa ne mai natsuwa da hangen nesa, wanda ke gudanar da manyan kasuwancinsa cikin kamala da kamun kai, sai dai a bayan fage, yana aiki a wani ɓangare daban wanda ya kasance shi yake jagorantar ayyukan sirri da bincike na manyan laifuka da babu wanda ya san yana wannan aikin sai makusantan shi.
Wayarsa ce ta fara ringin, sunan ogansa ne na gurin aikinsu ya bayyana akan screen ɗin wayar, cikin nutsuwa ya ɗauki wayar tare da yin sallama ya kara a kunnensa. "Ka zo yanzu ina son ganinka. Akwai muhimmin aiki da za ka yi a kan wasu" "Ok sir gani nan zuwa". Daga haka ya ajiye wayar, tattara takardun ya yi ya ajiye su guri ɗaya, tashi ya yi tare da ɗaukar wayoyinsa ya bar ofis ɗin, cikin girmamawa ma'aikatan kamfanin ke gaishe shi har ya fito harabar gurin. Motarsa ya buɗe ya shiga. A hankali ya jata tare da barin kamfanin, kai tsaye gurin ogansa ya nufa domin ya ji kiran da yake yi masa.
******
Matashiyar budurwa ce da ba za ta wuce shekaru goma sha bakwai ba, tafiya take yi a cikin uwar ranar da ake ƙwalawa kamar wata korarriya, uniform ɗin makarantar secondary school ne sanye a jikinta, kayan fes da su, sun sha karin guga, sai dai yanayin yadda take tafiyar ne zai tabbatar maka da ba a nutse take ba, gabaɗaya gumi ne yake keto mata a jiki tsabar ranar da ake yi, fat, fat, fat, haka take tafiya tana dukan ƙasa da takalminta. Duk inda ta ɗaga ƙafarta ta dire sai ƙura ta tashi a gurin, ta zo za ta wuce ta majalisar wasu samari a zaune a gefen hanya, ɗayan ya ce "Ah Sani ga mutuniyar nan ta yi halin na guduwa daga makaranta, ka duba yanzu fa sha biyu da rabi ta yi, amma gata nan ta dawo, anya yarinyar nan ba asarar kuɗin tara ake yi ba?". Sarai ta ji abin da suka faɗa, amma da yake yau a mugun gajiye take ga yunwa tana ji ya sa ba ta tsaya kula su ba ta yi gaba abin ta, sai dai a ranta ta ce "Zan yi maganinku, wannan maganar da kuka yi kun jawowa kanku da kuma ƙannen ku, idan na kama Sa'a ƙanwarka sai na naɗa mata na Jaki". Ganin da suka yi ba ta kula su ba ya sa suka kwashe mata da dariya, tana jinsu ta ci gaba da tafiyarta.
Ko da ta ƙarasa gida harshenta kamar zai zazzago tsabar yadda take mazurai da ido tana fitar da harshen waje. Tun daga soron gidan take kiran "Innarmu, Innarmu, Innarmu na dawo, ina abincina yake? Don Allah ki ajiye mini shi a tsakar ɗaki kafin na iso, wallahi yunwa nake ji kamar zan mutu, hanjina ban da kiran Ciroma babu abin da yake yi". Ta kai ƙarshen maganar tana shiga cikin gidan, Halima da take tsaye tsakar gida tana shanya kaya da sauri ta ce wa ƴarta Abida "Ke ɗaga ba ta guri ta wuce, ko so kike yi ta hankaɗe ki ta wuce ne?" Babu shiri Abida ta ɗaga daga kusa da ƙofar ɗakin Inna. "Eh lallai Halima, wato ta ɗaga ga annoba nan ta dawo ko? Halima ni kike kira da annoba? Bari na ci abinci, kin ci bashin wannan maganar da kika yi" ta mayar da dubanta ga Abida da ta rakuɓe gefe ta ce "Ke kuma munafukar yarinya, uwarki ta fara koya miki saƙa da mugun zare ko? Zan yi maganinki ne". Daga haka ta afka cikin ɗakin tana sake rangaɗawa Inna kira. Halima ta ja hannun Abida suka koma ɗaki.
Inna na kwance ta fara bacci ta ji hayaniyar da Ma'u ke yi a waje, buɗe idonta ta yi, tana kallon ƙofar ɗakin, shigowa Ma'u ta yi, tana faɗin "Inna ina abincina? Na dawo yunwa nake ji".
Cikin takaici Inna ta ce "Wai ke Ma'u ba za ki taɓa yin hankali ba ne? Kullum baki da aiki sai rigima da yi wa mutane shirme? Ke shikenan ba za ki san kin girma ba ne? Allah ya sa na ji kin taɓa yarinyar nan sai na sanar da Yayanki, kin san dai halinsa sarai". Tunzuro baki ta fara yi waje, tana hura hanci, ta ce "Ni dai ina abincina? A bani na ci kar ulcerta ta tashi". Inna ta ce "Ta daɗe ba ta tashi ba, yau ba'a yi girki a gidan nan ba, kinga sauran gari nan ki kwaɗa ki ci, ni da Halima duk shi muka ci" wani uban ihu Ma'u ta yi, ta dira saman kujerar dake ɗakin ta fashe da kuka tana faɗin "Haba Inna, wane irin gari kuma ana zaune ƙalau? Ni wallahi ba zanci garin kwaki ba tunda ni ba akuya ba ce, bayan kin san ɓata mini ciki zai yi ya riƙa saka ni gudawa". "Au ba za ki ci ba? Wato muda muka ci mune awakin kenan? To tunda baki so sai ki zauna da yunwar, duk lokacin da aka gama girkin dare sai ki ci". Inna ta yi maganar tare da komawa ta yi kwanciyarta. Ma'u ta ɗora hannu aka ta ce "Wayyo Allahna yunwa za ta kashe ni, na je makaranta na dawo an hana ni abinci. Yau na bani, na lalace, wayyo cikina, jama'a ku riƙe ni na yi sama, na zazzage, ƴaƴan cikina za su fito" . Da sauri Inna ta tashi tare da ɗakko abin duka ta nufe ta da shi, ai Ma'u na ganin haka a ɗari uku da ashirin ta arce ta bar ɗakin.
*****
Yana isa gurin aikinsu ofishin ogansa ya wuce, cikin girmamawa suka gaisa kafin Oga ya tura masa file ɗin da ke kan tebur ɗin gabansa ya ce "Duba wannan ka gani, wani sabon lamari ne da nake son ka yi bincike a kansa, ina son ka kwantar da hankalinka ka yi bincike cikin ƙwarewar aiki kamar yadda ka saba, ba na son a samu kuskure ko kaɗan. Shi ya sa na zaɓe ka da wannan aikin, saboda na san kai ne kaɗai za ka iya yinsa yadda ya kamata".
Adam ya buɗe file ɗin a hankali, yana karanta bayanan cikin natsuwa, sannan ya ɗago da kansa ya ce "Naga komai, yanzu me kake so na yi a kai?" Ya tambaya cikin girmamawa. Oga ya jingina da kujerarsa ya ce "Ina son mutane nan da ake zargin suna ɓoye wa a bayan kasuwanci suna cutar al'umma, ka shiga cikin su ba tare da sun gane kai waye ba ka yi bincike a kansu domin tabbatar da gaskiyar lamarin".
Jinjina kai ya yi, ya ce "Ok sir, in sha Allah zan gudanar da wannan aikin kamar yadda ka buƙata". Ɗaga masa hannu ya yi alamar jinjina, sannan suka yi sallama ya bar ofis ɗin, yana fita kai tsaye gida ya nufa domin a mugun gajiye yake.
Amanarcool
***