SAUTIN KARSHEFree

ArewaPen original

General fictionFreeCompleted

SAUTIN KARSHE

  • 1views
  • 31chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

ABS CHARITY HOSPITALA hankali aka fito da shi daga cikin asibitin, cikin yanayi na rashin jin ƙarfin jiki yake ɗaga ƙafarsa, hannunsa dafe da cikinsa sai lumshe ido yake saboda azabar ciwon da cikinsa ke yi. "Wai Yaya a haka kake cewa muka koma gida ka ji sauƙi? Dubi halin da kake ciki fa, tafiya ma da ƙyar kake yin ta". Cikin ƙarfin hali ya ce "Kada ka damu Nasir, ai na ji sauƙi Alhamdillah". "Yaya ban ga alamar sauƙi a tattare da kai ba, ka yi haƙuri mu koma a sake duba lafiy..." "Nasir!" Ya kira sunansa da ƙarfi ba tare daya bari ya ƙarasa maganar ba, kafin ya ce "Bana buƙatar komawa cikin asibitin nan, ku mayar dani gida, idan ma mutuwar ce nafi so ta ɗauke ni ina cikin iyalina". Ƙaramin yaron dake kusa da shi Sudais ya ɗaga kansa ya kalli mahaifin nasa, sannan ya mayar da dubansa ga asibitin da suka fito, girgiza kai ya yi, tare da duƙar da kansa ƙasa, ji ya yi mahaifinsa ya riƙe hannunsa suka ƙarasa inda motarsu take ajiye, shiga suka yi ya jingina kansa da kujera yana jin yadda cikinsa ke yi masa azababben ciwo. A hankali ya furta "Ya Allah!". Nasir ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka bar gurin. Koda suka isa gida yamma ta yi. A madaidaiciyar harabar gidan aka yi masa shinfiɗa ya kwanta, jikinsa ko ina zafi yake jin yana yi masa. Sudais ya zauna a kusa da shi yana kallonsa, idonsa sun kaɗa sun yi jawur, cike da tsantsar ƙaunar yaron ya kalle sa ya ce "Sorry Sudais. Don't worry, ka yi mini addu'a, in sha Allah zan samu lafiya". Mammy dake zaune a ɗayan gefensa ta ce "Ai kasan halin Sudais kwata-kwata baya ƙaunar ya ganka a cikin halin na rashin lafiya, yanzu sai ya ɗaga hankalinsa fiye da kowa a gidan nan". Abba ya yi murmushi mai ciwo, ya dubi Sudais, sannan ya mayar da kallonsa ga Faruk wanda ke bin Sudais ɗin, hannunsa ya kai ya shafa kan Zahra dake saman cinyar Mammy ya ce "My Zahran Abba, idan kuka rasa ni za ki yi kewar Abbanki ko? Kada ki damu ga Ya Sudais nan zai ci gaba da kular mini daku, kuma ga Uncle nan zai maye muku gurbina". Da sauri Sudais ya kalle shi, yana tsare shi da ido tamkar yaga baƙuwar fuska, Nasir ya ce "Yaya wannan wace iriyar magana ce kake yi haka? Don Allah ka daina kana tayar mana da hankali, in sha Allah za ka warke, ai ba yau ka fara yin ciwon cikin nan ba kuma ka tashi, wannan ma za ka warke da izinin Allah". "Kayya Nasir, wannan ciwon ba kamar wanda na saba yi ba ne, kai dai ga amanar yaran nan na bari a hannunka. Duk da bani da shakku a kanka, nasan za ka kula da su tamkar yaran da za ka haifa, Allah ya raya su, ya baka ikon kula da su, Sudais ga Uncle nan, ina son ku kasance masu biyayya a gare shi kai da ƴan uwanka, ku ɗauke shi tamkar ni. A'isha ki ƙara kula da tarbiyyar yaran nan, na san kina iya bakin ƙoƙarin ki amma ki dage, ki ƙara kula, ka da ku saki jiki da kowa, ku yi haƙuri da ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters31
premium2
30

Chapter 29

Premium
Updated 13 days agoAvailable now
31

Chapter 30

Premium
Updated 7 days agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play