Chapter 1
Direban Bus
completed
Littafin
Yusuf Ismail Giwa
***
***
copy right
Yusuf Ismail Giwa
Tunatarwa
Wanan littafi mai suna { Direban Bus} kirkirarren labarine, bai faru da gaske ba. Idan wani yaji abin da yayi kama da shi, ta fuskar dabi'u ko kuma suna, to yayi hakuri bada Sani nufi bane.
Sadaukarwa
Wannan Littafi sadaukarwa ne ga abokan karatuna dake Abdullahi Aminci Collage of Advance Studies Funtua Affiliated to federal University Dutsin-ma Katsina State.
Gabatarwa
Labarine wanda ya shafi rayuwar Direbobi da Fasinja da yadda suke mu'amala ta yau da kullum, akan hanya a cikin mota da irin wahalhalun da ke cikin sana'ar tuki da kalubalen da masu sana'ar Tuki suke fuskanta.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai.
Tashar motar Sabon Gari motor park Zaria Babbar tasha ce da kowane mutum da yake tafiye tafiye a arewacin Nigeria ya santa. Babbar tasha ce da take dauke da manyan Direbobi daga sassan kasar Nigeria. Kusan ko wane gari indai ya shahara a Nigeria idan kashigo tashar zaka samu Direban da zai kaika. Shaharar da Tashar tayi yasa kusan duk wanda yake yin sana'a acikin tashar shima nan danan sai ya zama shahararre. Acikin tashar. Akwai wani shahararren mai dafa shayi, wanda duk wani Direba dake shigowa cikin tashar ya san da zamansa. Zakiru mai shayi.
Dogo fari dan siriri koda yaushe yana rataye da dogon Carbinsa a wuyarsa. Idan ka gansa zaka dauka mayun wacine sabida ramarsa. Amma haka halittarsa take. Yana da wadata sosai rumfar shayinsa tana daga cikin kayatattun shaguna atashar sabongarin Zariya. Asalinsa dan kasar Niger ne. Yayi fice sosai sabida kwarewar sa wajen iya dafa shayi. Idan ya dafa maka shayi ka sha zaka dauka shine yafi kowane mai shayi kwarewa. Saboda Sanin aikinsa. Ya tanadi duk wasu kayan hada shayi wandanda zai gamsar da masu shan shayin sa.
Antaba yin gardama da shi akan ingancin shayinsa har ya sanya gasar cinye kudinsa Naira dubu Goma tsakaninsa da wani Direba. yace wa direban ‘akawai hadin da zanyi maka wanda idan kasha daga nan har Kebbi, kai wallahi har cikin birnin Nijar baza kaji kasala ba, bare kayi gyangyadi’ Direban yace, 'ban yaddaba' nan take aka bashi shayin yasha ya dauki kayan Sokoto a motarsa kirar sharoon Direban nan ya yasha ya tafi Sokoto ya sauke kayan ya juyo ya dawo Sabon gaari Zaria ba tare da yaji kasalaba. Sai ya wuce wajen Zakiru mai shayi ya kame a gabansa. Wato ya sara masahi domin jinjina masa da kuma gasgata shi akan maganarsa. Tun daga ranar dukkan mutanen tashar suka rika girmama Zakiru mai shayi tare da kara jawo masa kostoma.
Ranar Jumu'a misalin karfe bakawi na safe, kamar kullum Direbobi sun cika rumfar shayin Zakiru, kowanne yana rike da kofinsa yana karin kumallo. Wasu shayi da kwai da biredi, wasu kuma indomee da kwai, wasu kuma shayi da biredi da kwai, yayinda wasu kuma iya ruwan shayin suke sha.
Lado direba tsohon Direba ne wanda ya dade yana sa'ar tuki, sabida dadewarsa a sana’ar. Yana da kokarin taba wani fanni na gyaran motar idan ta lalace. Mafi akasari idan motarsa ta lalace shi yake gyara abinsa. In dai ba gyaran yafi karfinsa bane. Gan samemen katone majiyin karfi baki mai barkwanci. Daga cikin dabi’ar Lado idan bashi da kudi, sai yaje wajen Zakiru mai shayi ya nemi yin musu dashi akan ingancin shayinsa. Shikuma Zakiru idan yaji Lado ya fara irin wannnan kananan magan ganun, yasan Lado bashi da kudi. Don haka sai yasanya mashi shayi kyauta domin shi baya da rowa. Koda zuwan Lado abinda ya fara cewa ‘wannan shayin ka ya rage masa karfi sai mun kore ka a tasharnan’ zakiru yace ‘kaga zo ka zauna zanyi maka hadin da sai kaje Gusau ka dawo baka gaji ko kasalaba’ Lado yace ‘karyane ba wani’ zakiru ya hado mashi shayi yabashi.
Lado yana zaune yana shan shayinsa sai wani Direba daga cikin dire bobin Gusau sunansa Bala ya ce dashi, ‘Oga Lado yau zaka leka Gusau kuwa?’ Lado yace ‘kwarai kuwa da yardan Allah’ Direban yace ‘kaje ka hau layina ni yau ina da mara lafiya, kuma ina tunanin haihuwace. Zan saurara tukuna’ Lado yace to Allah Ya raba lafiya’.
Nan take Lado ya kwallawa yaron motarsa kira. Babawo’ koda Babawo yazo, sai Lado ya umarce shi da ya je ya sa masu motarsu a layi domin Bala ne akan layi kuma bazai samu fita yanzun ba, sabida matarsa bata da lafiya zai kaita asibiti’ Babawo yace, ‘Angama Oga’ Babawo shima kato ne amma daya ke yarone yanzu yake tasowa gimansa bai karusa na Ogansaba. Ya nufi inda motarsu take, yana zuwa ya bude kofar motar kirar bus motar tana da fentin launin ruwan ganye. Bata sha wahala sosai ba, kallo daya za kayi ma motar ka tabbatar da lafiyarta. Duba da irin yadda motar take da tayoyi masu kyau. Cikinta kuma, kujerunta basu sha wahala ba. Dukkan su babu wadda ta yage ko tayi wani lahani. Babawo ya shiga cikin motar ya zauna sannan ya yi mata key, motar ta tashi sannan ya figeta, motar taci taya sannan ya kadata ya nufi kan layin Gusau yayi fakin sannan ya fito, ya nufi motar dake gabansa ya leka ciki yayi masu Sallama sannan yace ‘Bayin Allah kuyi hakuri ku fito daga cikin motar nan ku hau waccan Bus din’. Wata mata daga cikin motar kirar sharoon matar tana sanye da wani bakar abaya, takalli Babawo tace da shi cikin nuna fushi, ‘sabida me’. Babawo yace ‘mai wannan motar matarsa bata da lafiya don haka yanzun bazai samu tafiya ba, zai tafi ya kaita asibiti’.Matar wadda kana kallonta zaka tabbatarda ta shirya tsaf zata fara balbala bala’i. Lokaci guda ta ta canza ra'ayi ta canja ra'ayi sannan ta sassauta ra'ayinta. Takalli Babawo tace dashi acikin tausayawa. ‘Allah ya bata lafiya’ Babawo yace, ‘Amin’ wani mutum daga cikin fasinjar yana sanye da koriyar tishet, ya kalli Babawo yace ‘ Gaskiya bazan hau Bus ba’ Babawo yace ‘waccen bus din tafi wannan sharoon din lafiya bakaganin sabuwace kuma kirar zafa?’ Matar nan mai sanye da bakar abaya tace ‘ toh a idodai mota sabuwa ce, amma a haka bazamu ganeba’ wani dan gaye mai sanye da farar tishet da wandon jins tiri kwata ya yamutsa fuskarsa sannan yace ‘shiyasa wallahi nafi so inje gefan titi in hau mota’ Suna cikin hakan sai ga Bala. Koda ya iso wajen sai ya dafa kofar gaba bangaren mai zaman banza. sannan ce ‘ don Allah kuyi hakuri, ga wanda zai kaiku nan ni bazan samu fitaba, matata zan kai asibiti, ku fito kushiga motarsa’ Wani gaye yana sanye da wando 3kwata fari gajere gadukkan alamu daga gidan masu wadata yake duba da yadda fatar jikinsa take lukui-lukui. Ga wata faskekiyar waya kamar karamar computer rungume a hannunsa. Hularsa carboy da ganinta mai tsadace. ya ce a fusace ‘kasan dai matsalar Bus sarai ya zaka juye mu a Bus ai da sai ka sanya mu a mota irin wannan mai gudu’ Babawo yayi dariya sannan ya ce ‘kada ka damu motar tafi wannan gudu,zaface sabuwa inkaga ka samu matsala to saidai halin karfe yauda kullum’
Kasancewar yayi masu magana mai dadi sai suka hakura suka fito suka nufi inda Bus din take Babawo ya bude masu suka shiga. wurin mutum biyu ya rage motar ta cika. Bayan sun zauna sai suka fara santin motar domin laushin soson kujer motar, da kuma fadin kujerun yafi na sharoon. Mutum hudu sunfi sakewa. Bala direba ya shiga cikin motarsa ya kada ta ya fita tashar, da nufin tafiya gida wajen iyalinsa. Babawo ya cigaba da neman fasinjar Gusau. Yana fadin ‘Zamfara Gusau-Zamfara Gusau azo nan’ wata wata baye rabiya sunanta Cinyare dauke da buhun robobinta gadukkan alamu sayarwa takeyi, ta iso wajen.Lokaci zuwa lokaci takan shigo tashan ta hau mota donhaka Lado da Babawo sun saba daukarta. Babawo ya tarbeta yace da ita. ‘Cinyare Gusau zaki?’ Cinyarer tace ‘zanje Sheme’.
Farace gajera mai yawan surutu. Babawo yace ‘ kawo kayanki a daure a but, je ki shiga saura mutum daya ta cika’ Cinyarer ta ce ‘a'a sai an daura kayan a kan ido na sannan zan shiga mota’ Babawo yace ‘to babu laifi’ ya fara loda kayan a but dukkkan fasinjar suka rinka lekowa suna duba kayansu a yayin da Babawo ya ke shirya kayansu a cikin but. Wasu kuma fitowa suke yi sai sunga an loda kayan tukuna. haka dai Babawo yayi ta loda kayan har ya gama.
Bayan ya gama sai yace ‘ko wannen ku ya shiga mota zamu hada kudin mota mu tafi’ Bayan duk sun gama shiga, sai Babawo ya kira wani dan union sunansa Adamu, dunkulallen bakin katone duk da shekarunsa sun tura amma yana karfi ajikinsa. Tsohon direba ne wanda yayi gwagwarmayar tuki tun shekara ashirin da suka gabata. Duk afadin garin Zaria an sanshi a wancan lokaci. Daga baya sai ya samu matsala, da yake kuma bai yi wa kansa tanadi mai kyau ba duk abin da ya samu a wajen karuwai da kuma caca su ka kare. Don haka a haka ya gama sana'ar a tsiyace don haka sai ya dawo tasha ya shiga cikin union don shima yaci arzuki. Yanzu baya raga ma dire bobi ko kadan. Koda ya iso sai ya fara fada ‘gaskiya Babawo ka raina mana wayo yanzu lodinne ma har kayi kacika motar ban Saniba don wulakanci’ Babawo yace, acikin bacin rai ‘kai dalla kada ka raina mana wayo inda bansan da zamanka ba zan kira ka ne ‘Adamu yace kai dan uwarka ni kake ma tsawa’ Babawo ya ce ‘nayi maka tsawan ko zaka bige ni ne’ Adamu ya kai ma Babawo mari. Babawo ya kauce. Shi kuma yayi kukan kura da nufin daga Adamu ya buga da kasa. Amma sai aka yi sa'a Lado direba ya iso da wuri.Ya sanya hannunsa ya ingije Babawo, Babawo ya tafi baya taga-taga sannan Lado yasanya hannunsa ya tsinke shi da mari. Jama'an da ke kallon rigimar sun kasa rabawa, sukayi maddalla da hukuncin da Lado direba ya dauka. Ganin irin tantagaryar rashin kunyar da Babawo yanuna wa Ado. Babawo yace ‘oga kasan abinda ya faru ne?’ Lado direba yace ‘rufe mana baki bana son jin komai, babban mutum kamar oga Ado kayi rigama dashi, komu girmama shi mukeyi bare kai yaron mota, wanann da kake gani tun kafin kazo duniyar nan yayi tuki, don haka idan kana so muyi tafiyar nan tare ka bashi hakuri’ Babawo yace ‘oga ado kayi hakuri don Allah’ oga Ado yayi dariya sannan yace ‘kace kai shegene, Babawo ni abinda nake so dakai shine wannan tasha tamu ce gaba daya amma kowa da barayinsa kana da naka hakkin nima ina da nawa don haka ba laifi bane kowa ya tsare nashi. Ni alhaki nane in san waye zaiyi lodi sanan kuma nine zan bashi damar yin lodin, tare da tabbatarda cewa ya cike ka’idojin wannan tasha. kayi lodi ban Sani ba, don natambayeka nayi laifi?’ Lado yace ‘oga kayi hakuri shi Babawo nayi zaton waye warsa takai tayadda idan nasa shi aiki zai yi shi a wayance, Bala ne akan layin sai aka kirawoshi aka ce da shi matar sa bata da lafiya don haka yace in hau layisa. ni kuma sai na kirawo Babawo nace yaje ya haulayin, amma ni nayi zaton amatsayinsa na wanda ya san harkarnan da zuwansa zaiyi maka bayani amma don Allah kayi hakuri’ Ado yace ‘babu kome ya wuce, aje ahada kudin fasinja’
Ado ya leka kofar fasinja yace ‘ku hada kudin mota kuyi ku tafi’ wanda ke zaune a kujerar gaba yace ‘ mai gida nawane kudin’ Babawo yace dubu biyar ne’ fasinjar ya dakko 5000 ya mika mashi sai wanda ya ke a tsakiya tsakani Direba da mai zaman banza. Shi kuma ya ce ni ‘Kotorkoshi zan sauka’ Babawo yace ‘Dubu biyar zaka bayar’ fasinjar yace ‘ aiko wallahi ba haka ake biya ba, don me za'a daidaitani da mai zuwa Gusau’ dakyar tare da sa bakin Lado dire ban motar aka rage ma fasinjar naira dari uku. Hakanan ya biya, sabida yana gudun kada ya fita motar samun wata yayi mashi wahala, Babawo yaleka kujerar baya yace ‘ Bayin Allah ku miko naku kudin’ Dukkansu su hudu dake a kujerar baya manyan mutanene dukkansu Gusau zasu. Mutum uku tare suke zasu tafi daurin auren wani dan uwansu ne. Babban cikinsu ana kiransa mai farin gemu domin kuwa yana da farin gemu. Da kuma alamun dattijantaka a fuskarsa. Sai na kusa dashi wato Malam Sani yayi sani sosai, shiya ake kiransa da Malam. Sai kuma Malam Sale shi malam Sale malami ne ayanzun haka yana ruke da carbinsa a hannu yana tasbihi.
Don haka suna tare da goro rike a hannu, suka hado kudinsu suka mika. Daya kuma tafiyarsa daban wani mai shiru- shiru baya Magana. Shima ya mika nasa kudin. Sai kujerar ta biyu Cinyare ce a farko tace ‘Sheme zanje’ Ado yace, ‘kawo dubu ukku’ baye rabiya tace, ‘Ina bazan biya dubu ukku ba’ Ado yace ‘ga kayanki masu yawa sannan kice bazaki biya 3000 ba, to sakko mu nema wani’ Cinyare ta yunkura zata sauka sai matar da ke kusa da ita mai bakar abaya tace ‘ baiwar Allah kiyi hakuri mana kinga irin zaman da mukayi sannan kuma shi kanshi lodin kayan sai an kara sauke shi, in dai kina da hali don Allah ki biya su’. Cinyare tace ‘to zan bayar da Dubu ukun, amma wallahi ba ayi mani adalci ba’ Lado yace ‘Kawo dai, duk kin dame mu da gwaranci,’ Mai bakar abaya tace ‘ni yan kara zani’ Ado yace ‘dubu uku da dari biyar’ Matar tace ‘Daidai da kudin mai tsafe harda kaya kenan’ Babawo yace, ‘eh’ Matar tace, ‘Toh, na amince amma ka gayawa Direba, yayi mani afuwa mijina yana nan agefen hanya damun isa, shi zai bada kudin motar’. Babawo yace ‘ Baiwar Allah, idan fa mukaje kika bamu matsala bazanji kunyar yi maki jahilci ba, kin ganni nan nima shegen kainane’ matar tace ‘Ai baza ayi hakaba’ Gaye mai 3kwata ya ciro wayarsa yace ‘taransfer zamma’ Babawo yace ‘to kai Oga kaji kana da asusun banki ko?’ Lado na gefe yace ‘Babu kome, bari mu tashi zan karanto maka lambar’ Mutum na karshe wani mai koriyar shirt shima Gusau zaije ya mika masu 5000 kujera ta karshe itama suka hado kudinsu suka miko wa Babawo. Sannan suka koma gefe. Ado da Lado da Babawo suka yi lissafin kudin akacirema union nasu aka fitar da kudin lamba sannan aka sallami Ado. Mai 3kwata ya leko yace ‘muna jiranku nefa, ina direbanne? yazo mu tafi dukkanmunan muna da uzurin da ke gabanmu’ Lado yace ‘ina tafe, bakaga abinda muke yiba’ Ado yace ‘To shikenan, ku rufe but ku tafi Allah Ya tsare’ Babawo ya ya ciro igiya ya daure but ta yadda komin gudu kayan fasinja ba zasu fadoba. Sannan yacema Lado ‘Oga mutafi komai yayi’
Lado ya bude kofar direba ya shiga ya zauna, sannan ya mayarda kofa ya rufe. ya sanya kafarsa ta hagu ya take kuloci, sannan yayi wa motar key ta tashi. Sannan ya sanya kafarsa ta dama ya taka totur ya bata wuta so sai sannan ya tafi ahankali. Babawo da ke waje yana ta yiwa sauran direbobi shegan taka yayi sauri yabi motar da gudu ya rike saman kofar motar tana tafiya. yace fasinja ‘kudan gyara zamanku in zauna. Suka gara zamansu shima ya samu wuri ya zauna. Ko da suka iso get sai mai tsaron get ya miko masu takardar receipt. Lado ya karba ya ce ‘Haba Baballe, yau bazanci albarkacin mai duka ba?’ Baballe yace ‘Ai sabida albakacinSa ne har ka iya fitowa aiki. Dalla bamu hakkin mu ka kara gaba’ Lado ya ciro 200 ya mika masa sannan ya mika masa takardarsa yace karbi abinka banso dan wahala’ Ya taka motarsa ya fita tashar, ya haukan titi ya tunkari GRA Babawo yace ‘Oga bazamu zagaya ta cikajiba sabida yayan banza’ Lado yayi dariyar mugunta sannan yace ‘yau bazamu boye wa kowa ba tanan zamubi yau duk duk dan shegiyar da ya tsayamin agaban mota sai na bi takan shege’ Babawo yayi dariya yace ‘sai da kai oga’
Cikin sa’a basu ga kasteliya ba a PZ haka kuma road safety duk basu fitoba haka Lado yaci gaba da tafiya akan titi yana shankan ababen hawa.
Koda suka iso MTD sai Lado ya hango Jami'an Kasteliya, su Biyar sun tsaya akan hanya. Suna jiran isowar mai tsautsayi su cika hannayensu dashi. Lado yace ‘Babawo kaga wadancan mutanen banzan sun fito, yau kuma anan suke bukatar tsayawa’ Babawo yace ‘Oga yaza'ayi kenan?’ Lado yace ‘Toh ‘Ni dan uwarsu zasu hana ni wucewane?’ Babawo yace ‘Na Sani Oga babu wani rukuki da zai firgita ka wallahi’ Lado yaci gaba da cewa ‘Tunda babu shegen da ya siya mani mota akwai wani dan iskan me dammara da zan sau rara mashi ne, ai wallahi sai in take dan Kasteliya ba wani abu bane’. Koda suka isa daidai inda yan Kasteliya suke sai Lado ya sauke wuta kamar zai tsaya yana isowa kusa da su sai ya bude wuta. Motar tayi wani irin gunji dama salansar motar ta fashe tayi wani irin kururuwa mara dadin ji. Jami'an suka watse gefe daya shi kuma Lado ya fita a tsiyace. Babawo yace ‘Allah Ya bar mani Oga na’. Yaci gaba da cewa ‘An buga dakai anbarka kowa ya ja dakai shi ne a kasa. Dakalin majina ahauka azame ka hau mutum ka zauna daidai kutu-kutu mugum icce, bakaci ba ka turnike tsohuwa da hayaki’ Lado ya dakko wani lemo mai sanyi, na kamfani Popcoala ya mika wa Babawo. yace ‘wannan kirari ai dole na biyaka’ Babawo ya karba yayi godiya. fasinja kuwa suka yi tayin dariya ganin irin diramar Lado da yaronsa Babawo.
Ahaka dai akai ta tafiya cikin nishadi har suka isa playover ya shige karkashin play over suka mike hanyar sokoto.
Cunkoson ababen hawa dake a karkashin playover Zaria ne ya baiwa masu tallan Ruwan sanyi da Biredi da Lemo na ruwa dana bawo damar tallata hajarsu ga fasinjar motar. Wani mai tallan Ruwa ya kango ma Babawo ruwan sanyi ta kofar barayinsa Babawo bai ankara ba sai da yaji sanyi afuskarsa an manna mashi sassanyar ruwan leda afuskarsa. Babawo ya auna ma mai tallan ruwan zaki’ kutumar ubanka, dan iskan yaro, matsa ka bamu wuri’ Cinyare tace ‘ ansa Naira Ashirin ka bani ruwan’ Babawo yace ‘kawo kudin nan ba zamu siya a wajensa ba. Ga wani can gaba, ya kwalla mashi kira, kai mai ruwa mai ruwan ya taho da gudu ya ce mai gida ruwanne?’ Babawo ya bashi Naira Ashirin ya miko masa ruwa shi kuma ya mika ma Cinyare.
Mai 3kwata yace ‘Aboki na, na ga alamar hanyarzu fushin dazu bai sake kaba’ Babawo yayi dariya yace ai komai ya wuce’
Lado direba yayi dariya sannan yace ‘ Babawo da yanzu kana can an sakayaka’ Babawo yace ‘Oga ai nasan baza ka barni a hannunsu ba’ Lado yace ‘Iya wuya sai na karbo ka wallahi, Amma kasan sai ka rika kulawa, domin idan ka dakko wata rigimar wadda tafi karfina wallahi ubanka zakaci, domin kasan suna da daurin gida a gwamnati, ni da kai kuma ubanwa garemu’ Babawo yace ‘ Allah da manzo su ke garemu oga. Lado yace to ai duk musulmi suna alfahari da Allah da manzo kaidai ka kiyaye kawai’ fasinja suka ce lallai kam arika kiyewa yafi’
Ahankali gosulo yana raguwa har suka iso imanto anan ne Babawo ya hangi wata fasinja ya daga mata hannu itama ta daga masa alamar tafiya tayi. Babawo yace Oga tsaya ga fasinja.’ mai 3kwata yace ‘A'ina zaka sanya ta? Babawo yace katsaya kayi kallo mota na cika ne’Lado ya yi fakin tare da yin hon. Babawo ya bude kofa ya fito ya tambayi fasinjar ina zaki fasinjar kyakyawar mace budurwa fara tas mai matsakaicin tsayi kallo daya zakayi mat aka tabbatar da matukar kyawunta. Babawo ya kare mata kallo. Tana sanye farin leshi mai tsadan gaske. Sannan ga wata faskekiyar waya ahannunta kai da gani ansaba sayen data. Tana rike da wata jakar fos ahannu sai kuma wani takalmi mai tsini ta sanya a kafarta. Ta amsa cikin yanga ‘Funtua zanje’ Babawo yace ki zauna a ataciment kafin muje Samaru’ fasinjar tace ‘ok nawa? Babawo yace ‘Yi sauri kihau kada a kama mu’, Tayi sauri tashiga. Cinyare da mai 3kwata suka matsa mata ta shiga. Babawo yace ‘muje Oga. Yayi sauri ya hau motar ya jawo kofa ya rufe. Lado ya tuka motar suka tafi.
Bayan Lado ya gama warware motarsa sai fasinjar Funtua tacewa Babawo ‘Malam nawane kudin motana’ Babawo yace ‘kibayarda 2000’ Fasinjar tace ‘1500 zanbayar Babawo yace ‘A'a, ai ba fitsari muke sanya wa motarba’ fasinjar tace ‘Amma kai mahaucine ko?’ Babawo yace ‘Me kuma ya kawo wannan maganar?’ fasinjar tace ‘Nasan dai mahautane suka kware wajen bakar magana’ Babawo yace ‘To ni Bafulatanine, kuma dan asalin zazzau’ fasinjar tace ‘kace kune masu kasa dole ka ruka fadin abin da kaga dama’ Babawo yace kamar yaya kuma’ fasinjar tace ‘Ku fulani waye ya kai ku yin abinda yaga dama akasar nan?’ Babawo yace ‘Tanan kika bullo’ mai 3kwata yace ‘wannan maganar haka take, yan zun waye akasar nan ya isa yayi abinda fulani suke yi?’ Babawo yaji abin ya fara yin yawa sai yace ‘kunga agaskiya wasa nake yi ni ba Bafullatani bane’ Gaba dayan fasinjar motar suka balle da dariya. Lado direba ya yi dariya ta isheshi sannan yace ‘Shegen yaro,sai dakai Babawo, shi yasa nake son fita aiki dakai’ Babawo dandali uban shagalallu kowa wa biye maka zai yi asara, ko baiyi ta kudi ba zaiyi ta Sallah’ Babawo yace ‘Allah ya biya Oga’ fasinjar baya duk dasu dattawane amma ba'abarsu a baya ba wajen shekewa da dariya. Mai nikafi tace ‘kowa ya tuba don wuya ba lada’ Babawo yace wa fasinjar Funtuwa ‘kawo dubu daya da da dari Biyar a rage maki’ fasinjar tace ‘toh zan baka yan naji na matse kadan kara hakuri’
Gidan mai na Total dake Zango a Zaria yau anyi sa'a babu layin motoci da sauran ababen hawa sosai. Lado yace ‘Babawo kaga gidan man nan babu layi, bari mu shi ga inyi ful tank sabida tsaro’ Babawo yace wannan hakane cikita cif oga. Kaifa dama baka barin mota da yunwa’ Lado yace ‘kwarai kuwa ai ni da mace da mota duk dayane awaje na yadda bazan matata da yunwaba hakama motata bana barinta da yunwa’ Babawo yace ‘Amana ce Allah Yaba mu, kaga kuwa ai bama ci amanaba’ Lado ya sanya danja sannan ya karya kwana ya sulala a hankali ya shiga cikin gidan mai. Yayi fakin a bayan wani mai kekenape. Yayi masa hon tare da cewa’ matsamana danuwarka’. Mai keke nafe ya fito ya fara tsiya. Yace ‘Bazan matsa ba, ba anan ka ganni ba’ Babawo ya fito ya ce da mai kekenafe ‘Dan uwarka zaka matsa ko kuma sai mun dauke wannan kahirar agwagwan munyi jifa da ita’ Mai kekenafe yace ‘Bazan matsaba’. Jama'a suka taru suna bada baki. Cikin masu taya su Lado har da mai 3kwata.Lado ya kalli Babawo da mai 3kwata yace ‘Ku kama man shegiyar agwagwannna mu yanka ta’. Nan take kowannensu ya kama bankarenda yayi masa dadi, suka dauke keke nafe din suka matsar da ita gefe. Wasu yan mata su biyu suna cikin keken, yayi da sukaji an daga su tare da kekenafe suka kwalla kara don firgici. Mai kekenafe din fadi yake ‘wallahi idan aka bata mani keke sai an biyani’ Lado kuwa fadi yake ‘uwarka zamu biya ka’. Lado yace ‘kai Babawo shiga motar nan ka matsa mani da ita wajen mai bada mai’ Babawo yai sauri ya shiga motar yayi mata key, ya matsa da ita kusa da masu zuba mai. Lado ya ce ma mai zuba man ‘ Cika mani tankin’ Mai badamai yace ‘Allah dai ya biya’ Mutumin ka ya ji zaiyi ciniki mai tsoka yayi ta washe baki har yana fadin ‘Mai gida ammafa kana da karfi fa, kaga yadda kuka dage kekenape kuwa harda wasu yan mata su biyu a ciki amma kuka dageta’ Lado yace ‘toh Allah na tuba, ni zai yima iskancin banza, ni sai inci uwarshi wallahi’. Man da aka zuba bai wuce lita hudu da rabi ba sai tankin ya cika. Mai zuba man yace ‘Oga ashe kai dama kari ne za kayi’ Lado yace eh, mana’ suka yi lissafin kudi ya dauki kudinsa ya bashi, shi kuma ya shiga mota yayi key Babawo ya rufe kofa suka tafi suka hau titi. Suka kara gaba.
Duk da azababben gudun da Lado yake yi amma bai hanashi fira da fasinjar motar ba. Mai 3kwata yace ‘Direba yau ka nuna mana kai kakkarfane sosai’ Lado yace ‘shi wannan mai agwagwan bai san dama haushin irinsu nakeji ba, har ya tsaya yana mayar mani da magana. Da abin yayi nisa, da sai na dauke shi da mari’. Wani fa sinja dake gaba barayin mai zaman banza,baki dogo yana da zubin wayayyun mutane,yana sanye da kayan Hausawa, doguwar riga da wando yadin shadda ya sanya hula ga wani bakin kwaba, sannan yasanya bakin tabarau. Ya kalli Lado yace, ‘Wai mai yaron nan yayi maka ne nifa ban san dalilin daya sa ka yi mashi haka ba’. Lado yace ‘kanaji, ta inda zamubi mu wuce mu sha mai, shi kuma sai yayi fakin a wajen yana gyara. kaga ko gefe ya kamata ya koma yayi gyaransa. Sannan kuma kasan dama, mu direbobin bus bama shiri da masu kekenafe, abu kadan za suyi mana mu ci uwarsu domin ba sa'an yin mu bane su’ Mutumin mai zama a barayin mai zaman banza yayi dariya sannan yace ‘Nafi yarda da wannan maganar ta karshe, baku shiri da masu kekenape shi yasa ba wuya ku sauke fushinku akansu’.
Wayar Lado tayi ringi, Lado ya dauka sai yaga abokin aikin sa ne wanda ya bashi lodinsa wato Bala direba, Dukda gudun da Lado yake yi bai hana shi dauka ba yace ‘Hello, Bala yamai jikin?’ Bala yace ‘an gode wa Allah kuma ta sauka lafiya, an samu saurayi’ Lado ya yanka wata iriyar dariya mai kama da ihu. yace ‘mutumina shike nan gida ya samu yanzu yaranka hudu kenan ko?’ Bala yace ‘wallahi kuwa’ Lado yace to Allah Ya raya mana su’ Bala yace Amin, ai yanzun kun tashi ko? Lado yace ‘gamunan a Samaru’ Bala yace to asauka lafiya’ Babawo ya karba wayar yace ‘Oga Bala Allah Ya raya abinda aka samu’ Bala yace ‘Amin Babawo nagode, sai kun dawo’ Babawo ya mika ma Lado wayarsa.
Lado yace ‘haka nake son haihuwa mai saukin wahala’ Mai nikafi tace ‘Ai abin na Allah ne, baka tsara ma kanka’ Lado yace haka ne’ wanda yake zaune atsakiya tsakanin direba da mai zaman banza ya fara gyangyadi zaiyi bacci sai rangaji yakeyi. Lado yace ‘Kai dan tsakiya ka daina baccin nan. Tafiyar nan ba muyi kome ba, amma tun yanzu zaka fara mana bacci’ Dan tsakiya ya karkade kansa sannan yace ‘Wallahi jiya banyi isasshen bacci bane’
Ahaka dai Lado yaci gaba da sheka gudu kamar wanda aka biyo. Duk motar da yasa ma kai, shi kenan ya bace mata. Baya saurarawa duk wata mota. Fasinja basu san lokacinda aka wuce Samaru ba, saidai suka gansu a bakin asabitin koyarwa na Ahmadu Bello University. mai 3kwata yace, ‘kai Direba lallai yau muna ganin gudun Zapa’ Lado yace ‘mai 3kwata mai kagani ne?’ mai 3kwata yace ‘kafin yau nayi matukar raina duk wata motar haya idan ba taxi bace amma akaron farko naji na gamsu da tafiyar Bus, ta hanyar yin interview da kai’ Lado yace ‘kaga shike nan gani ya kori ji’ Mai nikafi tace ‘yaushe muka wuce Samaru ban Sani ba’ Cinyare tace tun dazu aka wuce’ Fasinjar Funtuwa tace ‘sannu yaron mota kace da anje samaru zan koma kan kujera’ Babawo yace ‘ yi hakuri na manta bamu da fasinjar Samaru, amma kada ki damu muna da fasinjar kan hanya, zaki hau kujera.’
Suna cikin wannan hirar suka iso garin Shika dake karamar hukaumar Giwa nan danan sai Lado ya faka mota agefen titi. yace wa fasinja ‘kuyi hakuri naji injin yayi zafi, ina tunanin ruwa ne zan kara mata’. Nan danan ya fito, Babawo ya bude kofar fasinja. Sannan duk wadan da suke zaune akan inji shima ya sauka. Sai kuma mutum biyu da ke zaune akan kujera kusa da direba suka sauka suma. Sannan Lado ya bude injin sannan ya sanya hannunsa ya bude lagireton. Tariri mai karfi ya taso, kai kaje motar konewa za tayi. Babawo ya dakko ruwa a galan ya mikawa Lado. shi kuma ya rika zuba ruwan a hankali har lagireton ya cika. Alokacin da Lado da Babawo suke kokarin gyara mota. Shi kuma mai 3kwata hankalinsa ya karkata wajen fasinjar Funtua. Tun lokacin da ta hau motar nan ya ke ta satan kallon ta. Yana son yayi mata magana amma kuma yana jinkunyar sauran fasinja. Don haka yanzu da akayi fakin a gefen hanya sai ya fara tunanin yanzun ya samu cikakkiyar dama da zai yi mata magana. mai 3kwata ya matsa kusa da fasinjar Funtua yayi mata Sallama. ‘Assalamu alaiki’. Itama ta'amsa cikin natsuwa ‘wa'alaikassalam’ Ta kalleshi sama da kasa taga yana yinsa da alama babban yaro ne. Wata tangarda aka samu, shi yasa ya zo ya hau motar fasinja kamar dai ita. A kallon da tayi masa, nan danan ta lissafa kudin kayan da yake sanye dasu.Yana sanye da wata riga shet da'alama zatayi tsada sosai, domin ta raka kaninta ya siyo wata akasuwa naira dubu goma. Kuma bata kai kyan ta mai 3kwata ba. ga kuma wando Mai 3kwata wanda kwanaki Yayan ta ya siya irinsa a kasuwar funtua naira dubu goma da dari bakwai. Sai wani katon takalmi kwaba da ya sanya. Iri daya da na wani abokin karatunsu, ya fada mata naira dubu goma sha biyar ya siye shi. Ga wata waya a hannunsa iphone17 tasan kudin wayar sunkai naira dubu dari da hamsin. Agogon hannunsa kuwa zai kai naira dubu ashirin. Kai tsaye tayi lissafin suturar sa zata kai dubu dari biyu da goma sha biyar. mai 3kwata yace ‘fasinjar Funtua ya kike? kai tsaye ta amsa masa da cewa, ‘Sunana Ihsan ba fasinjar Funtua ba’ mai 3kwata yace’ Ai kuwa naji dadi da nasan sunanki cikin sauki haka’ Ihsan tace ‘Jin dadi kuma’ mai 3kwata yace ‘kwarai, maganar gaskiya tun lokacin da kika shigo motar nan naji kin shige cikin raina. Sai dai bansan wane irin kallo za kiyi mani ba’ Ihsan tace ‘Babu kome’ Ita mace ai baza tayi mamaki ba don namiji yace yana sonta.’ Lado ya rufe injin bayan ya gama gyaran yace ma Babawo ‘kirawo wadanda suka fita suzo su shiga mota mu tafi’ Babawo yace ‘ Kai mai 3kwata ku zo mutafi’ Ihsan tare da mai 3kwata suna ganiyar fira amma hakanan suka yanke suka shiga mota. Lado ya tuka mota suka tafi.To amma da yake kusa da kusa suke zaune, sai mai 3kwata ya rubuta lambar wayarsa sannan ya juya mata fuskar wuyar yana nuna ma Ihsan a boye, ta yadda sauran fasinja ba zasu gane ba. da yake ita kuma yar hannuce tana ankare da shi. Lokacinda ya juwo mata da fuskar wayar sai ta karanta lambar ta kwafe a wayan ta. Sannan ta seba lambar da suna mai 3kwata. Sannan ta shiga whatsapp dinta ta bude data sannan ta tura mashi sako kamar haka;
‘Hello, Ihsan ce.’
Koda mai 3kwata yaji shigowar sako sai ya duba ya gani, don kaka shi ma sai ya mayar da amsa;
‘Hi, Ihsan aiki
Kin sha kyau’.
Ihsan tace,
‘ko’
mai 3kwata yace,
‘Kwarai kuwa, fada mani
address dinki’
Ihsan tace,
da sauri haka?’
Mai trkwata yace
‘kin san ance da
zafi-zafi
akan duki karfe.
Abari ya huce kuma
Shi ke kawo rabon wani’
Ihsan tace,
‘tunda ina do lambarka
kada ka damu’.
mai 3kwata yace,
‘ok’
Ihsan tace,
‘ba kayi fushi ba’
mai 3kwata yace,
‘no ba kome’
Ihsan tace,
‘to ina son kayi mani
wani abu wanda
zan gane bakayi fushiba’
mai 3kwata yace,
‘ok bani accaunt
lambarki’
Ihsan tace,
‘lambata itace opay na’
‘mai 3kwata yace,
ok ga 20000k
ki sha ruwa’
Ihsan tace,
‘thanks ilove you’
Ta dago kanta suka hada ido, tayi mashi murmushi. Adaidai lokacin suka iso tashar Marabar Guga. Cinyare tace ‘Direba atsaya zan bada sako’
Lado Direba yayi tsaki,ya take burki ya tsaya sanan yace ‘kinsauka?’ Cinyare tayi dariya tace ‘sai kace tsuntsuwa’ Lado Direba yace ‘toh yi sauri kada ki bata mana lokaci domin ba karamin aiki na babe in tafi in barki’ Cinyare tace ‘ayi hankuri Direba yanzun zan dawo’ Babawo ya bude mata kofa. Ta fita ta nufi wajen wani mai saida kayan robobi, wanda gadukkan alamu dan uwantane. mai 3kwata ya kalli Direba yace ‘ Da gaske kana nufin zaka iya tafiya ka barta? Lado yace ‘Kwarai kuwa saunawa ina yin haka, ai indai fasinja ya bata mana lokaci tafiya muke yi mu barshi’ mai 3kwata yayi dariya sannan yace ‘gaskiya Direba kai din na dabanne’ Babawo yace ‘oga idan mai 3kwata yana ganin hakan bazai yiwu ba ya sa mana kudi ya gani idan bamu tafi mun bartaba’ Lado yace ‘ka kaleshi kawai naga alamar mai 3kwata bai san muba’ Mai trikwta yace ‘Badon kada in dauki alhakin baiwar Allah ba da na sa maku kudi wallahi’ Mai zaman banza yace a'a kuyi hakuri kada ai haka’ Suna cikin surutan su sai ga Cinyare ta dawo. Ta shiga motar aka mayar da kofa aka rufe. Lado ya tuka mota suka kara gaba.
Wani daga cikin dattawan dake kujerara baya, yana sanye da bakin rawani . yace wa abokin tafiyarsa ‘kaji labarin gwamnati zata fara gino man fetur a arewacin Nigeria ko? abokin sa mai farin gemu yace ‘wannan labarin ai ya dade domin ita gwamnati sai tayi shekara goma tana cewa za tayi wani abu amma kaga abin yaki ci yaki cinyerwa’. Mai rawani yace ‘wannan hakane ko kasan Shehu Shagari shi ya fara cewa zai dawo da birnin tarayya Abuja daga Legas amma abin bai yiwu ba sa a kusa da karshen mulkin Babangida?’ Mai farin gemu yace kwarai kuwa, kaga ko tsakanin wannan maganar da shagari yayi zuwa dawo da head kwata Abuja shekara kusan sha biyar ne’. Babawo yace ‘Baba mai rawani yanzu Abuja zata shekara nawa’ Mai rawani yayi dariya sannan yace ‘yaro ai yanzu Abuja shekaran ta arbain kenan’ Babawo yace ‘lokacin muna samari kenan’ mai farin gemo yace ‘kai yaro shekara arba'in kana inda zamu koma’ mai 3kwata ya fashe da dariya sannan yace ‘ Baba mai farin gemo ai Babawo da wuya ya wuce shekara ashirin da biyar, domin nasan da wuya idan an haifeshi lokacin da 2000 ta cika’ Mai farin gemu da Mai rawani suka fashe dadariya.
lokacin da suka iso tashar zomo. sai wayar daya daga cikin makwaftan mai farin gemu wato Malam Sale, tayi ringin nanan da nan yayi sauri ya dauka daga gidanr aka kirashi matarshi yaronshi yayi hadarin mashin ana bukatar shi a gida. Malam Sale ya rude ya rasa mai ke yi mashi dadi nan danan ya sanar da mai farin gemu da mai rawani abin da yake faruwa. Basu yi kasa a guiwa ba suka bakaci Lado direba ya tsaya ya sauke Malam Sale. Nan danan Lado ya tsaya cikin tausayawa da girmama wa Lado ya ciro kudin motar Malam Sale naira dubu biyar ya bashi. dukkan fasinjar suka nuna alhininsu ga Malam Sale tareda addu'ar Allah Ya ba ma yaron lafiya Lado da Babawo suka tarban ma Malam Sale wata motar da zata kai shi gida mai farin gemu ya ciro kudin mota naira dubu daya ya bama Malam Sale yace ‘ wannan ka biya kudin mota’ Malam Sale yayi godiya sannan direban ya ja motar ya tafi.mai farin gemu yace ‘ikon Allah kamar yaji abinda zai faru ajikinsa domin shi kadaine bai ce komai ba tun da muka hau motarnan’
Dukkansu suka koma suka hau mota. Anan suka kara samun wani fasinjar wani gaye ne sanye yake kokarin tsalako titi. Yana sanye da katon takalmi koba ga wata rigar sanyi kai kace sanyi yake ji, ga wata katuwar jaka goye a bayansa. Babawo ya dagamasa hannu sannan ya tambaye shi inda zaije, gayen yace ‘Funtua’ suka dauke shi suka tafi.
Ihsan kuwa tana tayin chatin da kawayenta. Kuma tuni ta baiwa wata kawarta mai suna Jamila labarin mai 3kwata wanda daga haduwarsu acikin mota har ya tura mata naira dubu ashirin. Jamila ta kara kitsa mata yadda za tayi ta kara tatsarsa kafin su sauka, domin bai zama dole su kara haduwa ba.
Ihsan tace,
‘kinga ya nuna
yana sona don
haka idan na kira
zai zo’
Jamila tace,
‘ke kinji
kina son sa a cikin
ranki kenan?’
Ihsan tace
‘a'a,sam
bana sonsa’.
Jamila tace,
‘To ki kara tatsar sa
daga nan kinga sai
ki karya layin’
Ihsan tace,
‘Shegiya Jamila
na gode sai kinji ni’
Mai hular sanyi ya na kokarin gyara zamansa sai ya taka mai Mai 3kwata’ mai Mai 3kwata ‘kai baka ganine kake takani’ mai hular sanyi yayi tsaki sannan yace ban lurabane’ mai Mai 3kwata yaji wani irin fushi a ransa an taka shi kuma anki abashi hakuri.bai san lokacin da yace amma kai banzane wallahi kayi ma mutum laifi amma ka kasa bashi hakuri’ mai hular sanyi y ace ‘allah ya kyauta in baka hakuri don kawai na takaka ban Sani ba’ Jama’a suka sanya baki suna basu hakuri amma ina abin sai kara ruruwa yakeyi. Mai Mai 3kwata yace wallahi sai hadaka da yansandan Giwa’ mai hular sanyi yayi dariya sannan yace ‘katambaya kaji mu yan sandan Giwa mune muka ladabtar dasu wallahi’ mai zaman banza yace kamar ya dakai aka ladabtardasu’ mai farar hula yace lokacin da muka kamasu da laifi dumu-dumu haka muka yi zanga-zanga muka shiga station din muka yi masu duka sannan muka kona station din ai dalilin dawo dasu nan gefen hanya kenan’ abinda fasinja basu Sani ba shine mai zaman banza asp ne na yansanda don haka ana zuwa bakin police station Giwa sai yace ma Lado direba yi fakin anan Lado ya tsaya mai zaman banza ya daga waya yakira wasu yansanda daga cikin station din nan suka fito ya sa suka tasa keyar mai rigar sanyi zuwa cikin station mai zaman banza yace wa Lado ku tafi kawai kada in bata maku lokaci wannan zamu koya masa hankali’ Lado ya taki mota suka kara gaba. Suna tafiya suna jimamin abinda ya faru.
Lado direba ya cigaba da rusa wa motar wuta, iska tana shigowa ta kowanne bangare daga gilashin motar. Iska tayi ta shiga ma fasinja idanu. Cinyare tace ‘Direba, iska yayi yawa a rafe mana gilasannan mana’ Lado yace Babawo’ Babawo yace ‘sai dakai Oga fadi ai ma’ Lado yace ‘waye ke managwaranci bamu gane abinda yake fada’ Babawo yace ‘Oga Cinyarece kasan a garin Ogomasho ta girma’ Lado yace ko dai a Apapa ne babu ruwanmu ta Sani nan arewa ne kuma kasar Zazzau. Munan yaren hausa muke yi sai kuma Arabiya da turanci duk wani Bayerabe ko Inyamuri dole ma ya dage yayi mana yarenmu. Don haka in zakiyi Hausa kiyi Hausa’ Bayebiya tace ‘ Hausa nayi ba
Yoroba nayi ba, nace iska tayi yawa arage. Mai farin gemu yace ‘ Kai Babawo ku dubi Allah ku rage gilasannan asamu saukin iskannan kunji’ Babawo yace ‘Angama Baba mai farin gemu. Ke kuma Cinyare kinci albarkajin sa wallahi amma badon halinkiba’. Ya sanya hannu ya rage gilasan. Kowanne daga cikin motar yaji dadin rage gilasan domin an samu saukin iskar da ke shiga ma fasinja idanu.
Lokacin da aka iso tashar motar Giwa sai wasu fasinja suka sanya hannu nan dana Babawo yace ‘Oga tsaya ga wasu kaya nan mu kwashe’ Lado yayi sauri yayi fakin. Babawo ya tarbesu, sannan yace ina za kuje’ fasinjar namiji ne da matansa su biyu da yaransa kana su Biyu. suka ce ‘Gusau’
Mai shiru-shuri ya sakko yace ‘Gaskiya na gaji da wannan tsaye-tsayen abani kudina in hau wata motar bazan iyaba’. Aka bashi hakuri amma yaki ya hakura. Lado ya ciro dubu uku da dari biyar ya bashi. Da yaki ansa amma dayaga baza’a kara mashiba sai ya ansa’.
Lado yace wa sababbin fasinja ‘namijin ya shigo gaba ya zauna. Matan su shiga baya, yaran su haukan inji’.
Dan tsakiya ya sauka sabon fasinja ya shiga ciki kusa da direba sannan shi kuma ya zauna a barayin mai zaman banza. Babawo ya sanya su acikin motar,shi kuma ya makale akofa Lado ya
figi motar suka tafi a guje.
Ahaka aka wuce kofar tasha. Fasinja suka leko suna kallon tarin buhunan hatsi da ke zankare acikin tashar. Mai rawani yace wannan gari akwai albarkar hatsi.’ Mai farin gemu yace ‘kwarai kuwa’
Hassan wanda ke zaune kusa da mai faringemu da kuma sabuwar fasinja da aka sanya, yace ai duk ranar Alhamis nan muke shigowa mu nemi arzuki. Garin akwai manoma da yan kasuwa har ma da yan boko. Shiyasa nan da nan garin ya bun kasa, amma ba wani tsohon gari bane’ Babawo yace wa Baba Hassan ‘Baba yanzu kana ganin wannan garin zai kai shekara nawa da kafuwarsa?’ Baba Hassan yace, ‘Kasan da yake garin sashi biyu ne, Giwa da kuma Anguwan Shehu. Anguwan Shehu ne tsohon gari zata iya kaiwa shekara dari da hamsin. Sai kuma Giwa ita ba zata wuce shekara cassa'inba. Domin mutanen Giwa sun taso ne daga sassan karamar hukumar kamar tsohuwar Giwa, Kago da Badagasa. Yawancin mutanen garin Giwa daga wadannan wuraren suka taso. Amma kafin zuwan Giwa dama akwai anguwar Shehu, wanda su kuma sun dade da al umma. Sai da anguwar Shehu ta shekara hamsin da wani abu sannan Giwa tazo suka hade, ayan zun ba kowa bane yake iya bamabance ina ne Giwa kuma ina ne unguwar Shehu ba. Gonakai na mutanen anguwar Shehu da yawa su suka sadaukarwa jama'an Giwa domin suna son baki. Ko a yanzun Anguwan Shehu tafi ko wacce anguwa tara baki wadanda suka taso daka nesan duniya. Ainihin shi mai anguwa Shehu daku ke jin labarisa. An hafeshi a birnin Zariya ne. Gidan sune suke da sarauta ma'aji babban Zazzau. Bayan ya girma sai ya bukaci ya fita yayi yawo a sassan kasar. Amma ya kirkiri wannan yawon ne sabida baya son sarauta, idan yana zaune agarinsu dole sai ya amshi gadon sarautar ma’aji babban zazzau. Don haka yabar garin yayi tafiye-tafiye ’Garin hakan nema har ya zauna a Nijar daga baya ya dawo ya yanki wuri a inda ake kira Anguwan Shehu Giwa anyazun. Lokacin har bayinsa ya yanta domin su zauna tare garin ya bunkasa. Baki daga makoftansa suka yi ta zuwa suna rabarsa. Sabida dadin zamansa. Akwai kauyakun da suka tashi musammnan suka dawo Anguwar Shehu da zama. Kamar; yalwa, kauyen kofa, hayin bawa dama sauran wasu kauyakun da ba duka suka tasoba. Zuri’ar Malam Shehu sune zuriar gidan Safa a yanzun’.
Mai farin gemu yace ‘kai yau naga wanda ya san Giwa ciki da bai’ Mai rawani yace ‘Malam Hasan da tarihi, ai ba dama. Wannan tarihi yadda kaji labarin haka nima mahaifina ya gaya mani kafin Allah yayi masa rasuwa. Domin da ya rika mu'amala da mutanen Anguwar Shehu’ Adaidai lokacin da aka haura gadar Giwa an karya kwana sai Lado Direba yace, ‘Baba Hassan ai nan bangaren hagunmu nanan ne Anguwar Shehun ko’ Hassan yace ‘kwarai kuwa gatanan gari guda’
Lado yace ‘Ai mu Direbobi muna Sanin Garuruwa kuma akwai abokina Lado niga anan anguwan Shehu yake.Tare mukayi makarantar allo a Dan mai gauta’
A dai-dai lokacin Lado ya take burki. Fasinja duk suka fara salati. Cikinsu ya duri ruwa suna sallallami. Wata katuwar akuya ce ta gilma. Ta fito daga Hayin Mahauta ta tsallaka zata gangara rafi. Lado ya tura wa akuyar wani irin zagi cikin fushi. Sannan ya fizgi motarsa yaci gaba da gudu. Bayan fasinja sun dan sarara sai matar da ke zaune akan inji tace da Ihsan dake kusa da ita ‘Baiwar Allah karfe nawa yanzun?’ Ihsan ta kalli wayarta sannan tace ‘kafe Goma da rabi’ matar tace ‘ na gode’ Ihsan tace ‘haladai sauri kike yi ko?’ Matar tace ‘wallahi kuwa buki garemu gobe shiya sa muka fito da wuri saboda muje muyi aikace-aikacen gida’ Ihsan tace ‘hala dai kanwarki ce shiya sa zaki tafi tun yau’ matar tace’A'a kanin mijin mune zai yi aure kuma shine auta a dakinsu kin ga ai mune kirjin biki’ Ihsan tace ‘Lallai kam, naga kun taho kwanku da kwarkwata da a'lamun zaku kwana biyu ko?’ matar tace ‘Gaskiya ko dai ana ganin dawowarmu sai nan da kwana biyu’ Mai 3kwata ya kalli Ihsan yace ‘Sannu yar jarida wannan irin tambayoyi haka? Haladai ke wakiliyace daga BBC’ Ihsan tayi dariya.
Lado ya daga murya yace ‘kai Mai 3kwata banji alat ba, ya aka yine?’ Mai 3kwata yace ‘Ok na manta bari intura maka’. Babawo yace ‘Maye ke mantuwa ba uban daba’ Mai 3kwata yace ‘Kai ne maye ni kam bani da maita’ Babawo yace ‘Mai 3kwata wanan fa Hausace kawai, ba fada bace’ Mai 3kwata yace ‘Na Sani ba fada bace, amma wa ke son a dan ganta shi da maita?’ Cinyare tace ‘Mai 3kwata kodai ni da ba yaranku ba, nasan wannan irin maganar’ Mai 3kwata yace ‘ Oh! harda su kaza a cin danko’ Cinyare tace ‘Mai 3kwata me kake nufi kenan?’ Mai 3kwata ya fashe da dariya. Duka motar ta kaure da dariya. Mai 3kwata yace wa Cinyare ‘Ki daina shiga hurimin da ba naki ba’ Cinyare tace ‘Kai Mai 3kwata, meye kuma hurumi?’ Fasinja suka kara kaurewa da dariya. Lado yace wa fasinja, ‘ku daina biye wa wannan bagwariyar, shekaranta ashirin birnin Zariya amma har yanzun bata iya hausa ba.Yadda nake jin Yarbanci wallahi bata jin Hausar mu haka. Kuma daidai da kwana daya bantaba yi da baye rabe ba kawai haduwar titi ne na tsinci Yaren’. Mai 3kwata yace ‘Kufa dama direbibi akwai ku akwai gane-gane’ Lado yace ‘Kai Mai 3kwata ban manta ba, tura min kudina’. Mai 3kwata yace ‘Karanto lambar muji’ Lado ya karanto lambar.Mai 3kwata ya fara turawa, sai ya dago kai suka hada ido da Ihsan. Ihsan tayi masa wani lallausan murmushi. Nan da nan Mai 3kwata ya tuna da cewa itama bata biya kudin motar taba. Ya tuna lokacin da aka ce ta biya naira dubu daya da dari shida. Dan haka sai ya hada da nata ya tura. Lado yaji kara karan wayarsa da alama kudin sun shigo. Nan danan ya karkace ya ciro wayarsa, ya duba sai ya ga harda karin dubu daya da dari shida. yace ‘Mai 3kwata na ga harda kari ne, ya akayi’ Mai 3kwata yace’Nabiya ma fasinjar Funtuwa nata. Lado ya fashe da dariya sannan yace ‘Mai 3kwata zakaci ubanka daga shigo wanka har ka lega ka hango. Wa yagaya maka anayi mana so yayya acikin mota’ Mai 3kwata yace ‘Kaga nayi mata magana?’ Babawo yace ‘Ai babuwanda bai fahimci halin da kuke ciki ba, tun dazun kuke soyewarku’ Mai 3kwata yace kai jama'a duk abinda ka keyi ko ka boye, ana nan ana kallonka’ Itako Ihsan tunda ta dukar da kai har yanzun ta kasa dagowa.
Wani mai babur ya manno da gudun tsiya, ya sha gaban motar Lado sannan ya tsaya ahankali har Lado ya matso Kusa dashi. Sai da ya kura ce shi sannan yayi masa hon. Dama kuma hon din motar Lado na babbar mota ne. Idan ya kunna shi kai kace tirela ce, sabida masifar kararsa. Mai babur ya firgice ya sauka kasa aguje kadan da ya fadi. Dan tsakiya yace ‘Kai direba kana baza kafasiti akan hanyarnan’ Lado yayi dariya sanan yace ‘Kana gani fa don sharri, ya shiga gabana sannan ya tsaya. Tunda ni kuma ina da maganinsa shi yasa na dauki mataki akansa’.
A haka dai suka ci gaba da tafiya cikin fira da raha irin ta matafiya wadanda suka hadu a hanya babu dangin iya babu na baba. Har sukayi tafiya mai nisa sun kusa marabar Yakawada.
Wayar na zaune a barayin mai zaman banza. Tayi ringi. Koda ya duba yaga wanda ya kirashi. Sai yafara waige-waige. Daga nan sai ya fara magana cikin harshen Fillanci. Atunaninsa babuwanda yake jin Fillanci acikin Motar. Sai dai, bai Sani ba, Lado direba ya yi yawon duniya. Ya shiga lungu da sako na kasar Nigeria don haka yana jin fillanci sosai. Lado yayi shiru kamar shima baiji abinda mai zaman banza yake fadi ba. Bayan ya gama wayar tashi adai dai lokacin sun shigo marabar ya Yakawada. Sai Lado ya sauke wuta. Yace wa fasinja ‘ku gafarceni zan karbi sako akan wannan layin’. Fasinja suka amince. Lado ya karya kwana ya shiga babban layin dake cikin marabar Yakawada. Bai tsaya a ko in aba sai a daidai karamin Ofishin Yansanda dake a garin. Musamman hukumar Yan sanda suke bude kananan Ofisoshinsu a Garu ruwanda suke da mutane da yawa. Sabida tsaron rayuka da sulhunta masu husuma da kuma ladabtarda masu laifuka sai dai idan rigimar tafi karfinsu sai su tura babban ofishin su dake garin Giwa.
Koda Lado ya fakin. Sai yayi sauri ya zagaya kofar mai zaman banza ya ya bude kofar, ya cakumi wuyar mai zaman banza ya falla mashi mari sau biyu. Fasinja suka fara Sallallami tare da neman Sanin abin da ya faru. Mai 3kwata yace ‘ya akayi haka? Dattawan dake baya suka yi sauri suka fito domin jin ba’asi. Lado yace ‘ku kwantar da hankalinku shi yasan abinda yayi don haka shi yasa na nufo damu ofishin yan sanda kaitsaye’. Cinyare tayi Sallati tayi Yarensu sannan tace ‘wannan wace iriyar kaddarace ta kawoni cikin motar nan?’ Yan sanda da ke zaune akan kujerun su suka taso suka daka masu tsawa tare da tambayarsu abinda yake faruwa Lado yace ‘ranka ya dade wannan da kaka gani infomane’ ankira shi a waya azatonsa ba wanda yake jin fillanci sai ya fara Magana da yaren fillanci al hali tun da ya shigo motar nan da hausa yake Magana. A cikn Maganar tasa sai yake cewa’ a wannan karo duk mutum daya sai kun biyani naira dubu dari biyu’ acan bangaren kuma sai aka ce dashi ‘mun yarda amma ka kawo mana masu kudi ba matsiyataba’ shi kuma ya amince ahakan. Sannan kuma sai ya kara cewa wannan Alhajin da kuka dauka satin da ya wuce iyalansa sun sayar da gonarsa zasu kawo kudin. Acan bangaren kuma sai akace aikin ka yana kyau sai kaji mu’ sannan ya kashe wayarsa. Domin in kafa sheda shi yasa na ciro waya ta na danna rokodin.’ Lado ya ciro wayarsa ya kunna, yan sanda suka ji abinda mai zaman banza ya fadi. Da yake akwai wani kurtu wanda shima yana jin yaren. Nan da nan ya fassara wa ogan nasu abinda mai maganar ya fada. Koda mai zaman banza yaji abinda ya fadi ya fito acikin wayar Lado direba. Sai hankalinsa ya tashi ya fashe da kuka yana cewa ‘na shiga ukku!, don Allah ku rufa mani asiri wallahi na tuba bazan karaba’. Yan sanda suka ce ‘eh dama ai bazaka karaba’ fasinja suka cika da mamakin abinda ya faru. Yan sanda suka jinjina wa Lado direba bisa namijin kokarinsa da irin jajircewarsa wajen kawar da bata gari. Nan take shugaban yan sandan ASP Sadau ya bukaci Lado da ya tura masa recoding din. Lado ya tura masa kamar yadda ya bukata. Sannan kuma ASP ya dakko wata sitika ta girmamawa ya bama Lado yace ‘ka manna wa motar ka ta na da mahimmanci musanmman idan jami’an tsaro suka kama motarka zaka samu sassauci’; lodo ya ansa sannan yayi godiya. ASP ya anshi lambar Lado sannan ya sallame su suka hau motarsu. Shi kuma Babawo dake makale a kofa ya dawo ya zauna akan kujer mai zaman banza. Suka tafi shi kuma imfoma aka tura shi a sell kafin anjima a tafi da shi babban ofishin Yan sanda dake Giwa.
Sun dade suna tafiya babu wanda yace wa wani uffan sabida mamakin abinda ya faru.
Fasinja dayawa sun tarbe motar amma da Direban da yaron motar duk sun shiga cikin zurfin tunani wanda ya hanasu kula da fasinjar kan hanya bare su tsaya su dauke su.
lokacinda aka iso garin Gangara, sai mai faringemu yayi ajiyar zuciya sannan yace ‘kai jama'a wanan rayuwa haka, ina duniyar nan zata kaimu. Mutane babu tsoron allah azuciyarsu’ Mai rawani yace ‘al lamarin sai dai Allah Ya gyara mana’. Mai farin gemu yace ‘Direba kai kuma Allah Ya saka maka da al khairi. Badon Allah yasa ka iya wannan yaren ba, da shi kenan Allah kadai Ya san irin barnar da wannan azzalumin mutum zai cigaba da yi a doron kasa’ Babawo yace ‘Oga a ina ka koyi fillanci?’ Lado yace ‘a duniya mana’ Babawo yace ‘wannan abin da ya faru, yasa naji ina son in iya fillanci wallahi’ Lado yace ‘sai ka dage kuma ka bada himma. lokacin da na fara koyon fillanci kamar in bari, domin abin da wahala amma sai na jure ina daukarsa ahankali. Watarana wani direban J5 muka kwana tare awajen wani taro mun kai fasinja. Sai yaji ina yima wata bafullatana fillanci ita kuma tana yi mani dariya taji ban iyaba ina yin kuskure. Sai direban j5 yace mani kada kada mu ka dage kayi ta jarabawa watarana zaka iya ina mai tabba tar maka wadannan filanin idan baka jin yarensu sun dunka wulakan ta ka kenan. Agabanka zasu fadi miyagun magan ganu akanka. Amma ko kadan idan suka fahimci kanaji kafi karfin wulakancinsu. Duk idan na tuna shi ina jin dadin shawarar da ya bani. gashi yau tayi mani amfani irin amfanin da ban taba zatoba’. Mai 3kwata yace ‘ Gashi mai zaman banza zai yi zaman banza a sell’ Fasinja suka kwashe da dariya.Sautin dariyar ne yayi sanadiyyar farkawar Ihsan, wacce ta dade tana yin gyangyadi a motar, ko da ta farika sai ta tambayi Mai 3kwata mi ake ma dariya’? Mai 3kwata yace ‘lallai anyi babuke,yanzun duk abinda ya faru ke baki Sani ba’ Ihsan tace ‘ina bacci mana’ Babawo yace ‘gaskiyane Mai 3kwata, tunda ta farka sai adora a inda aka tsaya kunayi mujna jin dadi’ Mai 3kwata yace ‘kai dan sa ido bai yiba’ Sannan yaci gaba da cewa infoma aka kama acikin motar nan’ Ihsan tayi ajiyar zuciya. Mai 3kwata ya kwashe labari ya fada mata bai rage mata komaiba. Ihsan ta cika da mamakin abinda ya faru. Sannan tace’lallai duniya makaranta’ Mai 3kwata yace ‘kwarai, ko baki je makaranta ba duniya zata koya maki karatu’
Cinyare kuwa tun da aka shiga mota daga marabar Yakawada ta fito da carbinta tana jansa tana istigfari har yanzun bata daina ba, kuma bata yiwa kowa maganaba sabida tsoro ya kamata.
Babawo yacewa Lado ‘oga kasan mamakin da kabani’ Lado yace ‘a'a sai ka fadi’ Babawo yace ‘koda kaji yana maganar sai kayi shiru abinka ka sulala damu ofishin Yansanda kai tsaye’. Lado yace ‘toh ya zanyi dashi kai kasan da tun lokacinda naji yana maganar, na nuna masa na fahimci abinda yake fada, da zai iya sauka ya gudu’ mai 3kwata yace ‘kwarai kuwa, hakan da kayi yayi dadai’. Allah Ya kare mana gabanmu da bayanmu. Lado yace ‘amin’ Lado ya kara da cewa, ‘kuma sai da na tabbatarda waya ta tayi sebin muryarsa da na dauka sannnan na nufi damu chaji ofis’. Dan tsakiya yace ‘kaji aikin hankali’Baba Hassan yace ‘. Toh jama’a Allah Ya karemu Ya kuma yi mana maganin irin wadannan mugayen mutanen’ fasinja suka amsa ‘amin Baba Hassan’
Koda suka iso Marabar Maska, sai wani fasinja ya daga masu hannu yana nuna alamar Gusau Lado yayi sauri yayi fakin sannan Babawo ya sauka ya nufi wajen fasinja ‘ fasinja sukace ‘kai direba ina zaka sanya su? Lado yace ‘mota tana cika ne?’ Babawo yace, ‘ina zaku? Fasinjan su biyu ne duk Gusau zasu. Suka ce ‘Gusau’ Babawo yace ‘ daya yahau gaba daya kuma yaje direba ya goya shi’fasinjar yace ‘a’a na hakura Allah Ya sauke ku lafiya’ Lado yace ‘ka shiga muje mana’ fasinjar yace ‘A’a ni bana son matsatsi, ku tafi kawai’ Babawo ya ce wa fasinjar ‘kawai ka siya taka motar kaga sai ka hau kai kadai babu matsatsi’ Lado yace ‘kai Babawo dalla hau mu tafi. Irin wadannan fasinjar ko ka sanyasu a motarka sai sun baka haushi’ Babawo ya hau suka kara gaba’ Lado yace ‘ko nawa zai biya na fasa daukarshi, dan uwarshi mu zai gaya ma matsatsi’ Babawo yace ‘wannan gaskiyace ogah’ mai 3kwata yace ‘Tunda bashi a wajen sai ku hakura hakanan. Ni kaina da kuka gani, larurace ta sa nahawo wannan motar taku. Ina da tawa motar kuma lafiyar ta kalau wani sabgar aka tafi da ita. Mai gidanmu yace lallai da wannan motar za’a don haka na kama hanya naje tasha nah au motar haya.’ Shima din baku Sani ba yana da motar ko kuma bashi da ita’. Mai rawani yace ‘wannan gaskiya ne Mai 3kwata’
Ahaka dai sukayi ta tafiya acikin motar mai dauke da mutane goma sha Shida. Lokaci bayan lokaci sai kaji wani ya soko wata maganar wacce za’a dade ana tattaunawa.
Suna cikin haka sai Mai 3kwata yaji karar shigowar sako cikin wayarsa. Koda ya duba sai yaga mutumiyarsace Ihsan tayi masa test ta massage a cikin sakon tace,
‘salam masoyi kada ka gaji, ina bukatar wasu kudin wallahi ina da problems da yawa a gida’
Mai 3kwata yayi farinciki da Ihsan takirashi masoyi don haka baiyi kasa a guiwaba wajen kara ingiza mata wasu dubu ashirin din kai tsye. Ihsan taji kudi sun kara shigowa kai tsaye, ta daga kanta tayi ma Mai 3kwata wani irin lalausan murmushi wanda hakan yana nuna godiya.
Babawo yace ‘gaskiya ina ganin har aurennan acikin motarnan za’a daura shi’ Mai 3kwata yace amma kaiko Allah wadan halinka, Wallahi kacika sa idon tsiya.’
Cinyare tace kai Babawo a motar nan kowa yasan halin da Mai 3kwata da yar Funtua suke ciki don haka ka kyalesu suyi soyayyarsu’
Lado direba yace ‘Babawo kaiko ka samu matsala tun da acikin masu fada maka gaskiya harda bagwariya’
Cinyare bata so Lado yana ce mata bagwariya. Don haka tayi tayin fada, shi kuma yana yi mata dariya. Ahaka dai aka ci gaba da tafiya ana raha wani lokacin kuma ayi fada har dai aka isa garin Dan kawo. Bayan an bar garin kadan sai daya daga cikin matan da zasu je Gusau tace ‘direba yarinya ta zatayi bahaya adan tsaya’ Lado yace ‘inna lillahi wa’inna ilaihi raji’una, yanzun dole sai kin sanya mun tsaya acikin wannan dajin’ mijin matar yace ‘direba wannan dajin ai bashida matsala kuma in kayi la’akari da yanzun kakane ba lokacin duhun amfanin gona bane’ Babawo yace ‘kurinka sanya wa yara fanfas mana sai anshiga mota ku sa mutane su tsaya a daji, haka akeyi’ mutumin yace ‘to baza a sanya ba zakayi mani rashin kunya ni zaka gayawa fanfas yarana sunkai goma. Ko banza kuwa na saba da hidimar yara. Cikin fushi yace ‘Da’alla kutsaya yarinya zata yi kashi in ba so kuke tayi awandonta ba wari kuma ya buwayi kowa’ Lado direba yayi banza dashi kamar bai san yana yin Magana ba. Yarinyar ta fara kuka ‘’mama zanyi kashi!’ matar tafara magiya ‘direba don Allah ka tai make ni ka tsaya yarinyar nan a matse take wallahi’ Lado yace ‘ baiwar Allah zan tsaya amma mujinki wawane bai iya maganaba’ mutumin ya fusata ranshi ya baci yafara balbala bala’I. Lado yayi fakin. Matar ta sauka ta gangara da yarinyar kasan titi domin tayi kashin. Lado ya bude kofa ya zagayo ya kalli mutumin sa wanda ya dade yana ta bala’i yace da shi. ‘Matarka tafika hankali wallahi,Magana wannan ace kai baka iya sarrafa harshe kayi Magana mai dadi ba’. Abu kamar wasa rigima ta kaure dattawan da ke kujerar baya suka sauko domin kai dauki. A yayin da ake ta kafsa rigima fasinja na kokarin su raba fada Ihsan tare da Mai 3kwata wuri suka samu suka zauna a gefen titi suna ta shan soyayyarsu basu san meke faruwa ba. Dakyar aka raba Lado da mutumin. Daga karshe sai mutumin ya yanke hukuncin cewa shi ya fasa yin tafiya akan motar abasu kudin iya inda suka zo, za su hau wata motar. Akayi iya lallashin sa amma ya ki yadda don haka Lado yace ‘ ku kyaleshi ya sanya kudi a hannu ya dakko kudi ya bashi yace ma fasinja ‘kushiga mota mu tafi’ suka shiga mota suka tafi suka bar mutumin da matansa da kuma yayansu biyu akasa suka tafi. Tafiyarsu keda wuya wata motar zamfara state taransport ta tsaya ta daukesu akan farashi mai sauki Lado direba ya hangesu ta mirror alokacin da motar zamfaran ta daukesu. Yayi tsaki sannan yace ‘ya bani haushi wallahi ai badon darajar su mai rawani ba wallahi da sai na bubbuge bakinshi wallahi’ Babawo yace ‘oga agaban matansa nefa’ Lado yace ko a gaban uwarsa nefa’ Malam Sani yace ‘ayi tayin hakuri dai dirteba’
Mai 3kwata yace ‘Babawo ina sauran fasinjarne injidai ba tafiya kayi ka barsuba’ Babawo ya balle da dariya sannan yace’Mai 3kwata kai baka san abinda ya faruba ka fada cikin koginso kayi ninkaya kaga kuwa bazaka san abinda ake yi a wajeba’ fasinja suka yi dariya sannan Lado yace ‘Mai 3kwata tsakaninka da Allah bakasan abinda ya faruba?’ Mai 3kwata yayi murmushi sannan yace ‘Don Allah mu bar wannan maganar’ fasinja suka kwashe da dariya’
Motar da ta dauki fasinjar da Lado ya ajiye ta wuce motar Lado a tsiyace kamar wadda aka biyo. Lado yayi tsaki yace Allah Ya tsare’ Babawo yace ‘oga motar nan fa tsoho ne yake tuka ta, amma kaga yadda yake cin ubanta kamar wani yaro’ Lado yace ‘ai kasan Zamfarawa haka suke, mayin motane idan suka hau mota ji suke kamar sun kure dadi a duniya’ Malam Sani yace ‘kai direba ni ma Bazamfare ne, naji kana nema ka takalemune, to kul!’ Lado yayi dariya sannan yace ‘Baba Malam Sani ku dinne kun fiye son mota. Sabida tsabar son mota duk Gwamnan da yahau mulkin Zafara sai ya yi zubin motocin sufuri. Sannanan kuma idan motocin sun fara tsufa sai kaji jama’a sun fara Allah wadai da gwamnatinsa wai don ya bar motocin sufuri sun fara tsufa. Sannan su kansu shuwagabanninku basu da aikinyi sai sayen manyan motoci. Su bukatarsu kawai shine ya kasance akasar babu wanda yafi su hawa mota mai tsada. Muna gani fa, idan gwamnan ku zai wuce sai mungaji da kidaya motocinsa.’ Fasinja suka kaure da dariya. Malam Sani yace ‘gaskiyar ka direba. Indai maganar hawa mota ake to bazamfare iyakane.’
Lado yace ‘Nimafa wannan motar a Zamfara na sayeta lokacin gwamna ya raba ma mutanensa motar, sar wani dan majalisa da yake sirikin mu ne, mun bashi mata. Sai ya kira woni ya ce ‘in bada wani abu in dauki wannan’ nan nadanyi mashi wani abu nima na ci arzuki.
Babawo yace ‘arzukifa muna kancinsa Oga’ Lado yace ‘kai da kasan kome’
Malam Sani yace ‘ashe ma mota tamuce’ Lado yace ‘’ ba taku bace amma yar garin ku ce’
Mai 3kwata yace ‘Gaskiya wannan dan majalisa anyi dan kwal uba, hakkin al’umma ya dauka ya karya farashi ya kai wa dangin matarsa’ Lado yace ‘mai 3kwata hassada kirikiri’ mai 3kwata yace ‘sorry oga wallahi na dan tabaka ne kawai ba wani abu nake nufi ba’
Koda suka iso garin Yar tafki sai wani mai mota ya tsayar da Lado zai bashi juye. Lado yayi fakin sannan yafita tareda Babawo. Wancan direban yace mutum uku ne daya zaije Gusau biyu zasu tsafe’ Lado yace ‘bamu sunan’ suka shirya direban ya biya, sannan suka shiga mota suka tafi. Daga nan basu kara tsayawa ako in ba sai a jabiri sannan Babawo ya kalli Ihsan yace ‘Budurwar Mai 3kwata ina zaki sauka?’ Mai 3kwata yaji dadin wannan Kalmar da babbawo ya fada. Ihsan tayi murmushi sannan tace ‘Randa zan sauka’ Lado yace ‘Allah sarki ,Mai 3kwata za’ayi bankjwana da masoyiya, saidai zan baku shawara, dan Allah kuyi kokari wannan soyayyar taku taci gaba, ku rike juna da amana banda yaudara kunji ko’. Mai 3kwata yace ‘kada ka damu zamu gaya maka daurin aure’ mai Rawani yace ‘Aiko da ka kyauta kuma Allah ya ida nufi’ fasinja suka ‘amin’
Cinyare tace ‘komin saurin unguwan zoma ai ta bari a haihu. daga haduwar mota shikenan har an fara maganar aure’Lado yace ‘kunji wannan bagwariyar ko, tana bakinciki da wannan soyayyar taku Ihsan kada kiji haushinta dama shi aure dole sai an tara makiya da masu kushe da hassada’ Ihsan ta dago kai ta kalli Mai 3kwata sannan tayi dariya.
Adai dai lokacin suka iso wajen da jami’an kasrota suke tsayuwa. Lado yace ‘Babawo ga mutanenmu tsaya kaga yanda zanyi dasu’. Babawo yace ‘aiki sai maishi wani kaya sai amale babban goro sai magogin karfe oga a gida oga adawa.ko wa ya ja dakai zai fadi, Gusau kuwa ko basa so sai kaje. Allah ya kiyaye mana kai oga Lado direban Bus’
Lado yaji wannan kirari ya ratsa shi bai san lokacin da kutsa cikin jami’an nan ba. Kusan gaba dayansu suka nemi su daka mashi wawa koda Lado ya ankare sai yayi wani irin tuki irin nasu na gwanayen tuki gaba dayansu ya tarwatsasu wani mai tsautsayi acikin su sai da goshin motar ya banki kwan kwasonsa yayi tsalle ya yi alfura ya yi mirgine akasa sannan ya tashi duk ya kuje a fuska da hannuwansa. Lokacinda ya tashi Lado direba yasha rawul sun daina hangensa. Jami’an suka yi barazanar bin Lado amma inaa ashe motarsu hotoce kawai ko mai babu acikinta direban yace ‘oga tun lokacin da muka iso tayi kukan rashin mai ta mutu shiyasa bangyara fakinba na barta anan inda take’. Wani daga cikin jami’an yace’ oga na rike lambar motar’ ogan yace ‘very good ‘ karanto lambar muji’ koda ya karanto lambar sai ogan yace ‘stupid, lambar motar motatace ka karanto’ sauran jami’an suka balle da dariya ogan ya daka masu tsawa sannan ya umarci wani daga cikinsu ya tafi da wanda akajima ciwo asibiti.
Bayan Lado ya sha rawul ya hau kan titin bypass hanyar Gusau, sai ihsan tace ‘akwai nan’ Lado yace da ita ‘haba budur wan Mai 3kwata bakiga siradin da muka tsallako bane?, ai kyayi hakuri mudan kara gaba, kada yan garinku su biyomu. Bayan yadan kara gaba dai dai wani gareji sai ya tsa yace ‘yifaka-faka ki sauka mu samu mu gudu’. Ihsan ta sauka Mai 3kwata ya daga mata hannu ita ma ta daga masa sukayi bankwana tana murmushi. Mai 3kwata ji yake kamar ya sauka yabi Ihsan gidansu. Ahaduwarsu wanda bai wuce awa da rabi ba amma har yaji yana matukar kaunarta kamar wadda suka share kwanaki koma watanni. Yana ji yana gani suka rabu. Lado ya taki motarsa suka kara gaba Mai 3kwata yana ta lekenta ta hau keke nafe ta nufi anguwarsu. Shi kuma Lado ya nufi hanyar Gusau.
Bayan sun isa anguwar Dahiru sai Lado ya hangi wata mata fasinjar sheme dama ya saba daukarta matar ba taji ga rashin kunya tallan magani takeyi amma rashin kunya kai kace namiji ce irin yan barkinnan. Lado yacewa Babawo ‘Ga mutumiyarka nan Megari’ Babawo yace ‘dakyau ai ko ba wajenta sai wani ya sauka na dauketa’ fasinja suka kyakyace da dariya. Sabida jin wannan maganar ta Babawo. Megari ta sanya hannu ta tarbesu. Lado ya tsaya yayi fakin. Babawo ya sauka ya tarbeta sannan yace da ita ‘naga har kina sanya hannu kina tarbemu, kema kinsan iya wuya sai mun tsaya mun dau keki’ Megari tayi dariyar shakiyanci sannan tace ‘ai naSani ni daku amanace babba a tsakaninmu’ Lado yace ‘sai dake wallahi’ Megari tace ‘nagode Lado direban Bus’ Babawo yace da ita ‘hau mota Megari, ‘yi faka-faka, gari naruwa’.
Megari tana sanye da gyale mai ruwan kasa doguwa, bakace mai girman jiki ga shegen surutun tsiya tana dauke da wani karamin kwandon roba da alamun magunguna take sayarwa. ta zauna agefen kofa sannan Babawo ya zauna a inji ya rufe kofa suka tafi. Megari ta kalli fasinja tace ‘jama’a Salamu alaikum’ fasinja suka ansa ‘wa’alaiki salamu’ me gari tace al’ummar Annabi muna dauke da magani kala-kala wadanda ke magance larurori dabandaban. Kamar basir sanyi kasala rashinkuzari. Sannan kuma muna da maganin gyaranjiki na mata sannnan kuma abangaren maza muna da maganin gyaran gida’
Babawo yace ‘Megari ni maganin gyaran gida zaki bani’ Lado yayi sauri yace ‘Megari kada ki bashi wannnan bashi da mata’ megari tace ‘dama ai maganin gyaran gida ba’abama yara’ mai farin gemu yace ‘Megari ina so abani maganin kuzari kin san mu tsofaffi sai da shan magani’ Megari tace ‘Baba kana da gaskiya kusha maganin nan kusamu ku fita kunyar iyali’’ Lado yayi dariyar shakiyanci. Sannan yace ‘Megari bakida mutunci’’ Megari ta mika ma mai farin gemu gorar maganin tace ‘girgiza ka shanye bashi da daci ko tsami, baurinsa kadanne sannan akwai dandanon zuma acikinsa’. Mai farin gemu yace ‘na sha yanzun kuwa? Domin fa taro zantafi Gusau ina fatan idan ansha ba’ayin gudawa’ Megari ta ce ‘ a’a mai farin gemu bawani gudawan da zakayi’ mai farin gemu yace ‘ to nawane sadakin?’ Megari tace ‘Dari Biyu ne babu tsada’ mai farin gemu ya dauki kudinta ya bata shi kuwa ya kafa kai ya shanye maganin’ abokan tafiyarsa suma suka siya suka sha. Megari ta dauki roba daya ta mika ma Lado direba Lado yace ‘lallai yau zansha maganinki amma sai na koma Zariya domin akwai wani shayi da nasha a tasha nasan har nakoma Zaria bani da matsala’ Megari tayi ciniki sosai a cikin motar domin babu fasinjar da bai siyaba. Wani ma har roba biyu yake siye. Maganin Megari ya shahara sabida shaharar sa nema yasa har gidanta ake zuwa asiya maganinta idan ta hau mota kuwa haka ake siyen maganin.
Fasinjar sukayi ta yi mata rashin kunya ganin ita mace ce, amma tana sayar da maganin maza da abinda ya shafesu. Babawo kuwa babu wanda ya fishi ranshin kumya acikin motar, amma da yake Megari ta saba da wannan shirmen nasu haka take mayar masu da martini ga duk maganar da suka yi mata. A haka taci kasuwarta kafin su isa garin Mairuwa tayi cininki mai yawa.
Koda suka iso mai ruwa sai Megari tace ‘Lado zan bayarda sako anan’ Lado yatsaya Babawo ya bude kofa sannan Megari ta sauka. Taje kofar wani shago ta bayarda wani daurin magani a bakar leda. Sannan suka danyi magana da mai shagon sannan ta dawo mota ta shiga suka tafi. Lado yace ‘Megari kinje kinci kasuwarki mu kuma muna tsaye muna jiranki’ Megari tayi murmushi sannan tace ‘Lado Direban Bus kenan, wani alkawarine na cika mai wannan shagonne zai aurar da diyarsa shine yace inyi ma yarinyar hadin amare, shine na hada na mika mashi’. Babawo ya balle da dariya sannan yace ‘Megari kin karo wulakanci wallahi’. Ko kunya ba kiji kiyi ta zayyano bayanai haka’ Megari tace ‘toh ya za’ayi yanayin sana’ar tamu kenan.’ Mai 3kwata yayi tsit sabida baya son hirar da akeyi da Megari, asalima ana yi ne yana jin haushi. Tun da ya siya maganin kasala ya mika mata kudinta bai kara ce mata komeba. Ya sun kuyar da kansa yayi shiru abinsa.
Bayan sun isa garin sheme sai Lado yayi fakin adaidai inda suka saba ajiye Megari. Sannan ta sauka sukayi sallama da ita Cinyare tace ‘nima nan zan sauka’ Lado yace ‘gara dai ki sauka mu huta da wannan gwarancin’ Babawo ya sauka ya ciro mata kayanta sanan ta leko barayin direba ta kai mashi duka don ta huce takaicin da yake ta cusa mata. Lado yayi sauri ya dage gilas suka tafi suna dariya. Megari kuwa ta shiga cikin gari kamar yadda ta saba.
Lado yaci gaba da baza wuta akan hanya Tafiya sannu kwana nesa ahankali sukayi ta wuce kananan garuruwa da kauyaku, har suka iso garin Yankara. Ko da isowarsu sai Lado yayi fakin ya sauke mai nikafi wadda sai an sauka mijinta zai biya kudin motarta. Tace ‘bari in karbo maka kudinka kaga inda yake gashin namansa can wajen waccan tukuban’ Babawo yace ‘ba matsala’
Matar ta nufi wajen mijinta wani gajeren mutumne, kato mai matsakaicin haske shi ba bakikkirin ba shikuma ba fari ba. Kallo daya za kayi masa ka tabbatar da cewa shi jarumine. A gaba dayan layin masu naman shine ogansu, asalima har mukami yake dashi. Kowa a wajen yana shakkarsa sabida rashin hakurinsa. Amma matarsa kuwa bata raga mashi ubansa take ci. Gashi kuma yana bala’in sonta. Baya son abinda zai bata matarai. Amma kullum bata da wani aiki sai kirkiro masa sabuwar hidima, shi kuma sabida Allah Ya hore mashi baya damuwa hakanan yake kauda kai yayi mata abinda take so. Wani lokacin hakanan sai ta yi wanka taje wajen sa’arsa ta karbi kudi masu yawa taje ta sha shagalinta. Ko a wannan tafiyar, da zata tafi Zaria bukin sunar kawarta, sai da ya bata kudin motar zuwa da na dawowa wanda zai isheta da kuma kudin gudun mowa. Amma gashi yanzun ta tsayarda Direba tana son aba shi wasu kudin. Koda Sule ya hanko tahowar matarsa sai yayi murmushi na jin dadin masoyiyarsa tadawo. Lokaci guda ya batarai bayan ya tuna da cewa ‘da wuya idan ba wata hidimar zata dora mashi mashiba’. Koda Hauwa ta iso sai ta kalli Sule tayi murmushin mugunta Sule nama yace ‘masoyiya kin dawo ? wallahi na yi kewarki tunjiya nayi zaton zaki dawo sai naji shiru amma nagodewa Allah tunda Ya dawo mani dake lafiya’. Hauwatayi dariya sannan tace ‘duk ba wannan ba ‘ga direba can yayi fakin yanzu ya ajiyeni, jeka ka biya shi kudin motarsa’ Sule yace a fusace ‘wai meyesa kike yimani hakane? saida na baki dubu goma sha biyar sannan kika bar garinnan, yanzu kuma kin dawo sai kice ni zan biya direba kudinsa?’ matar ta kalli Sule ta batarai sannan tayi masa murgude. Da sauri yace da ita kada ki damu zan biya. Ai duk yadda kikeso haka za’ayi’.
Koda Babawo yaji shiru sai ya biyo bayanta domin kuwa ya ga inda ta nufo. Don haka bai bar kansa yayi murfi ba. Yabi bayanta yana zuwa yace, ‘ke naji shiru ne kinsan fasinjane acikin motar suna jiranmu’. Sule nama yace ‘kada ka damu ga kudin motarka’. Ya lissafo kudin ya bashi sannan ya yanka mashi nama ya bashi. ya kara yanka wani ya bashi yace ‘ka kaiwa direba kudan mayar da yayu sannan ku shaida naji dadi da irin kyautatawarku wa matata’. Babawo ya ansa yayai godiya sannan ya juya ya tafi. Sule nama yace wa matarsa ‘ke kuma wace tsoka tayi maki anan in yanke maki ita kisha shakalinki?’ Tayi banza dashi sannan tayi tsaki tace ‘sai ka iso gidan ni na gaji zanje gida in huta’. Har tafara tafiya sai ta waigo tace ‘kayi mana take away domin bazanyi girkiba’. Ta tafi abinta. Shi kuma ya hangame bakinsa yana kallonta kamar wani sakarai. Sannan yace a cikin zucuyarsa ‘kaji wata fitinar kuma wai bazata yi girki ba’ ya koma ya zanna yaci gaba ada aikinsa.
Bayan Babawo ya koma mota sai ya mika wa Lado nasa naman. Lado ya karba ya fara daukan daya ya sanya a bakinsa, dadin naman ya kai masa karo. Logaci guda ya tuna da kudin motar matan yace ‘Babawo dan uwarka badai nama ya bamu a madadin kudin motarmu ba’. Babawo yace a’a oga ya biya kudin mota, wannan ya bamune sabida yaji dadin mun mutunta masa matarsa’ Lado direba yayi dariya sannan yace ‘to yayi kyau’. Sannan ya taka motar suka tafi suna tafiya suna cin naman suna santi.
Babawo yace ‘oga amma fa mutuminnan mijin tace ne. baka gansa ba gabjejen kato, wanda zai yi kyau da hudar doya. Amma sai abinda matar tace zaiyi’. Lado yayi dariya sannan ya dauki yankan nama daya yakai bakinsa. Ya sanya manyan hakoransa ya tauna ya hadiye sannan yace ‘Ai dama mata suke wahalshemu. Kuma lallai fiyayyen halitta Annabi Muhammadu S.A.W. Yayi gaskiya. Yace ‘ban bar wata fitina wadda take cutar da maza ba, face fitinar mata’. Babawo yace ‘Allahu akbar sadaqarrasulul karim’. Fasinja suka kwaqshe da dariya. Mai 3kwata yace ‘Da dai yanzun na shigo motar nan da sai ince santin nama kukeyi shiyasa kuke wadannan maganganun naku amma tunda ba yanzun na shigo ba nariga nasan irin diramarku tun farkon taso warmu daga Zaria’. Mai faring emu yace ‘kwarai kuwa Mai 3kwata maganar kahaka take. Kuma ni inda suke burgeni dukkansu sunsan mai suke yi sannan kuma dukda suna da shiririta awani fannin amma kuma basu bata wa kowa lokaciba domin da’alamu zamu isa Gusau akan lokaci ba tare da wani yayi korafi ba’. Tun da Lado da Babawo suka fara cin namansu basu kara tankawa kowane fasinja ba saida suka karar da naman sannan suka fara Magana da fasinja.
Tundaga yankara basu kara samun fasinjaba sai da suka isa garin tsafe. Suna shigowa cikin garin suka samu fasinjar Gusau mutum biyu suka dorasu sannan suka kara gaba. Lado yaci gaba da falfala wuta kamar wanda aka biyo da gudu.
Bayan sun fita garin Tsafe sai Lado yaji motar tayi barayi daya don haka yayi fakin Babawo yayi suri ya duba sai yaga tayarsu daya ta baya barayin mai zaman banza ta sauka alamar tayi faci. Lado yace wa Babawo ‘ya dakko jak a dage motar’ Fasinja suka bukaci su sakko amma Lado yace ‘kowa yayi zamansa acikin mota da yardan Allah bazamu wuce minti biyarba mun canja wata tayar. Sannan kuma gani da kakkarfan yaron mota mai zafin nama, kuma karfi banza faka-faka zaiyi sauri ya gyara kome’. Nan danan Babawo ya sanya jak y adage motar yacire tayar Lado ya ciro safayar ya mika ma Babawo ya sanyata shikuma Lado ya mayarda mai facin a wajen ajiye safayar. Sannan suka shiga mota s uka tafi.
Malam Sani yace wa mai faring emu ‘kaga amfnin safayar taya ko?’ mai farin gemu yace ‘kwarai kuwa inda basu da safaya da sai munjira ankai ta faci sannan adawo ya santa mutafi.’ Mai zama a barayin mai zaman banza yayi ajiyar zuciya sannan yace ‘gashi sai daka bar cikin gari kawai barayi su kada mu daji’ Sababbin fasinjan Gusau su biyu suka ce ‘ a’a nan bashi da matsala kuma inda ma yake da matsalar anfi samun matsalar da daddare’. Malam Sani yace ‘ya kamata mutane murika yiwa junanmu adalci musamman wajen fadin gaskiya. Sau da dama muna fadin abinda bamu Sani ba. Yadda ake yada rashin tsaron da yake damun jihar zamfara ya wuce yadda abin yake. A yadda ake fadin rashin tsaron ya isa ace yanzun an karar da mutanen jihar. Don rashin tsaro tabbas akwai karancin rashin tsaro ta fuskar sakaci da gazawar hukuma. Amma mafi girman lamari zamu iya cewa jarabawa ce daga Mahalinmu wanda kuma yayi bayani acikin littafi mai tsarki ALQUR’NI Yace ‘Duk abinda ya same ku mara kyau daga abinda kuka aikatane don haka sai mu duba mu gani irin laifukan da muke yiwa Allah mu tuba kuma mu gyara’. Fasinja suka ce wannan gaskiya ne Malam Sani’.
Adaidai wannan lokacin suka iso inda jami’an soji suka sanya get domin duba wadanda suke shige da fice a cikin jihar zamfara. Koda isowarsu sai wani soja ya umarci Lado da yayi fakin Lado yayi fakin agefe. Gabansa kuwa akwai motoci sama da ashirin bayansa kuwa sunkai goma wani soja yana binsu yana leka cikin motar idan yaga dama sai yace wa direba da fasinja su fito suje su gaishe da oga idan yaga dama kuma sai ya karbi wani abu wajen direba sannan ya umarce su da su tafi. Idan ya umarci mota su je sugaishe da oga to kowannensu sai ya nuna katin zama dan kasa sannan kuma ya bayarda dari biyar idan kuma bashi da katin sai ya biya dubu daya koma fiye.
Koda ya iso kofar motar Lado, sai Lado ya sauke gilas ya gaishe da sojan cikin girmamawa sannan yace ‘oga yau dai ni zan siya ma manjar gidanka’ sojan yace ‘ko direban Bus’ Lado yace ‘kwarai kuwa Lado ya ciro dubu daya ya mika ma sojan sojan yayi sauri ya karba ya kalmasheta sannan ya sanya ta acikin aljihunsa. Yace wa Lado ‘Bitanan ka wuce.
Lado yayi godiya sannan ya tafi abinsa. Mai faringemu yayi salati ya sanar wa ma’aiki sannan yacewa fasinja ‘kunga yadda sojojin kasarnan suka baci da ansar nagoro!’ mai Mai 3kwata yayi dariya sannan yace ‘baba ai kabar wani rufa-rufa, kace dai cin hanci kawai’. Ayan zun awanna kasar samun wanda baya damuwa da ansan cin hanci ko na goro adukkan fannonin ayyuka ko kuma hukumomin kasarnan to lallai da wahala’ Malam Sani yace ‘amma fa ba duka aka taru aka zama daya ba.’Mai farin gemu yace ‘gaskiya ne wannan amma dai sojoji sun lalace domin ada idan ka baiwa soja cin hanci aranan zaka gane kurenka domin kuwa zaka sha duka kamar jaki’
Lado yayi dariya sannan yace mukam akasar nan babu kalar jami’an tsaron da bamu ganiba, munyi gwagwarmaya da jami’an tsaro kala-kala, nayi kokawa da soja, na bugeshi ya bugeni mun ci uban juna ga dai babwo nan yasan komai’ Babawo yace ‘gaskiyane oga’ Lado yaci gaba da cewa dankuwa Dansanda Allah na tuba karamin alhakima’ Babawo yace ‘Gaskiya ne oga sai dakai wallahi’ Lado yaci gaba da cewa ‘shiyasa idan na hadu da yan kasteliya,kasrota,zarota ko kuma karota da yan sitika ubansu nake ci. Baku ga yadda nayi wa kasrota a Funtua na banke daya yafadi gefe nasan wallahi wannan sai an kaishi yaga likita’ Babawo ya yayi dariya sannan yace ‘oga ai ko birnin Zazzau baka raga ma yan kasteliyaba fasasu kayi kabi ta cikin su ka wuce dole suka waste kowannensu yayi nasa wajen domin ya tsira da rayuwarsa’ Lado yace ‘kai da kasan kome’
Daya daga cikin fasinjar wanda aka dakko a tsafe yace wa Lado ‘baka jin tsoron kada watarana su ritsaka su dauki mataki akan ka?’ Lado yayi dariya sannan yace ‘Ai kafin mubaro gida sai Tsohuwa ta shafa kaina tayi mani addu’a sannan na fito shiyasa kaga bana shakkar kowa, sabida natsuwa da kwanciyar hankali idan nahau wannan motar, ji nake kamar ina akan gadon matata.’ Fasinja suka sha dariya har ta ishesu.
Ahaka sukayi ta tafiya suna ajiye fasinja suna daukar wasu har suka isa garin kotorkoshi.
Koda isarsu sai Babawo yace wa Lado ‘oga’ Lado yace ‘Babawo ya akayine?’ Babawo yace ‘ga garin mutuminka’ Lado yace ‘wa kenan?’ Babawo yace ‘fasinja informer’ Lado yace ‘oh!, wallahi har na manta dashi. Dama Kotorkoshi yace zashi ko?’ Babawo yace ‘eh mana ogah’ Babawo yace ‘yanzun yana can ahannun jami’ai’
Lado yace ‘matsiyacin ba’. Adai dai loacinne Lado ya kunna radion motarsa don sauraron Prite Fm dake Damba a Gusau. Kunnawar sa keda wuya sai suka ji kaitattun labarai sun fara da maganar imfoma dan asalin Kotorkosh nka shi ahannun hukuma’Lado yace ‘kaji tun kafin musauka har labarin ya wade duniya’ Babawo yace ‘na tuna yayin da yake Magana da fillaci acikin mota’
Lado ya numfasa fasinja wadanda a gabansu akayi, tare da Babawo suka ji dadin cika alkawari da jami’an yan sanda sukayi. Ada sunyi zaton yansanda zasu ci amanarsu su sakeshi’.
Lado yaci gaba da baza wuta akan hanya babu sassautawa duk motar da sa ma kai sai ya shata, nan da nan sai ga Lado a farkon garin Gusau a kofar jami’a dake damba anan Mai 3kwata ya bukaci a sauke shi. Babawo ya cewa Lado ‘oga tsaya ka sauke mai Mai 3kwata’ Lado yace ‘Allah Sarki mai Mai 3kwata anan zamu rabu kenan?’ Mai 3kwata yayi dariya sannan yace ‘haka rayuwar take sai kuma idan da rabon zamu gana’ Lado yayi fakin sannan ya kalli Mai 3kwata yace’ya labarin Ihsan yar Funtua?’ mai tri kwata yace ‘wallahi wannan yarinyar da gaske nake sonta kuma zan je har gidansu. Kai ina mai tabbatar maka inkaga ban auri wannan yarinyarba sai dai idan Allah bai nufa ba’ Lado yaji dadin maganar Mai 3kwata hakanan duk fasinjar motar don haka mai farin gemu yace ‘kai Mai 3kwata to karike amana ka kuma ji tsoron Allah domin nasan halinku na yaran yanzu’ Mai 3kwata yayi dariya sannan yace ba kome baba in Allah ya yarda babu abinda zai faru sai alkhairi’ dukkan fasinjar tare da Lado da Babawo sukayi wa Mai 3kwata fatan Allah Ya tabbatar da wannan hadin. Mai 3kwata ya karbi lambar Lado sabida watarana. Babawo yace ‘anan kake karatu’ mai 3kwata yace ‘aa kani nane anan janje dubiya ni kammala nawa tun shekarar 2015 yanzun ni likita ne a asibitin koyarwa na Ahmadu Bello dake tudun wada a Zaria. Dukkan fasinja suka yi mashi fatan alkhairi, Sannan suka yi bankwana. Lado ya cigaba da baza wuta. Babawo ya cewa fasinja ‘Daga nan bazamu kara tsayawa ako in aba sai mun isa tashar Lalan fasinja kuwa duk suka yi shiru alamar sun gamsu da maganarsa’ adai dai lokacin da suka isa rawul dake daf da isowa Lalan Lado yana tafiya ahankali saboda cunkoson ababen hawa sai dai yaga ancillo masa wani katon karfe agaban motarsa karfen yana da wasu manyan kusoshi a jikinsa an samar da shi ne sabida idan aka jefashi a kan titi babu Direban da da zai iya yin kasadar takashi dolensa ya tsaya an kama shi. Lado ya barka wata iriyar ashariya sannan yace ‘wane dan wahalanne?’ jami’in yace fito ka ganshi dan uwarka’.
wani dan sitika ne sanye da kayan aikinsa bakinsa yana makale da sigari ya sha dammara. Mutanen yankin sun dade suna jin haushinsa sabida yadda yake aikinsa ba tare da bin ka’ida ba. An dade ana yi masa fatar Allah Yasa wani yayi maganin sa. Tirkashi yau dai kam Allah ya hada sile dan sitika da Lado Direban Bus.
Lado tare da Babawo suka fito a fusace kowannensu cikin matsanancin fushi kamar zasu cinye sa. Koda suka fita sai Babawo ya nufin inda Saminu dan sitika ya sanya karfen da yayi masu get, ya ciccibeshi yay a jefar dashi gefe daya. Sule dan sitika ya kai ma Babawo wo duka da karfin tsiya Babawo ya duke sannan ya sanya tafin hannunsa ya bangaji Saminu dan sitika a kirjinsa. Dan sitika ya tafi tabaya yayi taga-taga kamar zai kai kasa amma sai Lado ya tarbeshi, ta bayan sannan shima ya sanya hannunsa ya mangareshi da karfin gaske. Dan sitika ya ga wata iriyar wuta ta gilma, Saminu dan sitika ya sanya hannu ya dafe kansa domin kuwa ya daina gani sai wani irin duhu mai kaloli da yake yi masa yawo. Lado da Babawo suka hau mota suka gudu. Saminu dan sitika ya gangara cikin wata rumfar kwano wan wani dattijo ke kasa kayan miya ya zauna yana jinya. Jama’ar dake wajen babu wanda baiji dadin abinda ya faru ba. Dama Saminu dan sitika ya takurawa mutanen yankin da rashin mutuncinsa.
Bayan Dan sitika ya wartsake sai ya tashi yana borin kunya ‘wallahi wadannan zasu san sun taba hukuma, sai na dauki mumunan mataki a kansu.
In ban dama na shaka magani wallahi nafi karfinsu. Shi kuma abokin aikina tun dazu daga aikenshi ya kai mani kayan miya, ya tafi yayi shiru’ Jama’a kuwa duk sun kewayeshi suna kallon ikon Allah. Ya ciro wayarsa ya fara kiran wayar ofishinsu ya sanar dasu abinda akayi masa.
Nan take daga ofishin nasu aka daga wayar. Bayan ya kora masu bayani sai akace ‘ka dauki lambar motar? Saminu dan sitika yace ‘aiko ban dauki lambar motarba’ nan take mai gana da shi yace ‘aikin banza ka da ka kara kira na kabar wa Allah’ jama’an da suka ji wayar da Saminu dan sitika yake yi, sai suka fashe da dariya. Babu yadda ya iya da su hakanan ya tafi ya kyalesu. Shi kenan jama’a sun fara raina shi.
Bayan Lado direba yayi nisa daga wajen sai yace ‘kaga daga yau idan ya gammu sai ya kara sa mana get, bulala zan sanya mashi’. Fasinja suka fashe da dariya har ta ishesu. Adai dai lokacin Lado ya isa tashar lalan kai tsaye ya sunkuya cikin tashar mai tsaron get yabiyo shi da gudu ya miko mashi rasit Lado ya karba sannan ya ciro dari biyar ya mika mashi yace ‘karbi’ bayan ya karba sai Lado yace ‘dan wahala kawai’ Lado ya nufi layin yan Zariya yayi fakin. Fasinja sukayi godiya ga Allah da Ya kawosu lafiya. Sannan ko wannensu ya sakko akayi ban kwana da juna sannan suka san inda dare yayi masu. Adai dai lokacin karfe 1:15 am mai farin gemu yace da Malam Sani kaga yanzun har zamu isa Gadabbaga sannan muyi Sallar karfe Biyu mu fita wajen daurin aure’ Malam Sani yace kwarai’.
Suka nufi gefen titi domin su tarbi kekenape suhau sannan su karusa Gadabbaga. Adaidai lokakacin malam sani ya ciro wayarsa ya kira Malam Sale yayi mashi jaje na hadarin mashin da dansa yayi yabama mai faringemu shima yayi mashi jaje. Malam Sale yace ‘kun isa wajen bikin?’ Malam Sale yace yanzun muka sauka tashar Lalan kasan Direban dan shiriritane’ Malam Sale yace ‘na sani kwarai’ Malam Sani yayi dariya sannan yace ‘Ai baka san kome ba sai mundawo zaka sha labari, wannan Direba da yaron mota kamar wasu aljanu ba suji wallahi’ malam Sale yace ‘To nagoda sai kun dawo’. Suka tsallaka titi mai kekenape ya tsaya ya dauke su, suka tafi.
Lado da Babawo suka nufi wajen wata Inya mura mai sayarda abinci, Lado yasa aka kawo masu shinkafa da nama da lemo mai sanyi. Suka koma gefe suka ci suka sha sukayi hani’an.
Kafin su bar wajen sai ga wata mata tazo wajen tana neman Lado Direban Bus Lado yace ‘baiwar Allah lafiya?’ Matar tace ‘Lafiyar kenan, dama akwai wasu kayane da za’a daukan mani zuwa Zaria’ Lado yace ‘kayan meye?’ Matar tace ‘kankana ne da kuma gwanda tunjiya ya kamata akaisu to amma direban da zaikai mana motarsa ta lalace shiya sa bai samu zuwaba’. Lado yace babu kome zamu kai maki nawa zaki biya mu matar tace ai ya kama ta kuga kayan tukuna’ Lado yace ko komun gani ko bamu gani ba maganace ta biyan kudin mota gaba daya don haka muyi ciniki kawai’ nan take suka shirya ta dauki rabin kudin ta basu sannan suka dauki matar suka tafi inda kayan suke. Koda suka iso get sai mai tsaron get yace ‘Lado kudin lodi’ Lado yace ‘uwarka ce lodi, leko ka gani’. Mutumin ya leka baiga kowa ba sai matar nan ita daya don haka sai yace ‘Duk da haha ana biyan kudin kamasho sabida a tasha aka sameka’ Lado yace ‘kai Danfulo zanyi maka rashin mutunci dan ubanka matsa kabana wuri’ Dan fulo yayi dariya sanan yace ‘Lado baka sauki acikin lamuran kudi, wuce a sauka lafiya. Lado ya taka motar tayi kyashi ya ci taya sannan ya fita a tsiyace.
Basu tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan matar. Sukayi fakin sannan suka fito suka bude but. Matar ta bude get din gidan. Kankanece da gwanda zankare. Matar ta kirawo yaran gidan suka taya Lado da Babawo lodin kayan har kan kujera mota ta cika tayi makil babu sauran wuri inbanda wajen Direba da dan tsakiya da wurin mai zaman banza.
Bayan sun gama lodin sai Babawo ya dakko gwanda guda biyu lafiyayyu ya ajiye a kujerar gaba sannan yace ‘wadannan a ajiye su anan sabida tsaro.
Lado yace ‘Kai dan uwarka guda biyu sunyi kadan karo biyu’ Babawo yace ‘ala bar mani Ogana’ ya koma ya karo biyu. Itako matar tana tsaye tana kallon ikon Allah. Tace acikin ranta ‘Yau kuma na hadu da yan dirama’
Wani daga cikin yaran gidan yace ‘Aunty Talatu zan biki Zaria’ Talatu tace ‘kabari da Sallah Mamanka zatazo dakai kaji yaron yace toh’
Bayan sun shirya sai Lado yace ma matar ‘munshirya sai tafiya’ matar ta kulle get sannan ta janyo kofar gidan ta rufe sannan ta baiwa yaran gidan key ta hau mota suka tafi.
Talatu ta zauna barayin mai zaman banza sai kuma Babawo a tsakiya yayin da Lado yake jan ragamar tafiyar. A haka suka hau titi suna tafiya suna fira suna kuma shan gwanda. Suka wuce rawul din da Saminu dan sitika yake, bashi a wuri babu labarinsa. ‘Babawo yace ya tafi hutun dole’ Lado yayi dariyar mugunta sannan ya kara takar motar tayi gunji ya fita aguje.
Babawo yaga Talatu tayi shiru bata Magana sai yace da ita ‘Baiwar Allah kina mace amma kina sana ar gwanda da kankana, kama ta yayi ki wakilta mijinki a wannan sana’ar’ matar tayi dariya amma bat ace kome ba’ Lado yace ‘kacika shishigi ina ruwanka tana da aure ko bata da shi, kaSani ko bazawarace’ matar ta batayi niyyan cewa kome ba sabida barkwanci Lado da Babawo dole sai da tayi dariya sannan tace ‘Ba sana’ar na keyi ba, jiyane yayanmu ya dakkota daga mafara koda ya iso nan sai motar ta lalace shine aka juye kayan anan dayake anan yayata take aure ni kuma ina nan nazo hutu shiyasa sai ya bar mani sallahun kayan.Gida dakaga babu kowa sai ni da yara matar gidan wato yayata ta tafi wajen aiki ne dayake mai kaciyar lafiya ce a asibitin FMC Gusau. Sannan kuma niba bazawara bace kuma ba matar aure ba’.Ko da ka ganni haka girman jiki ne kawai amma yarince karama ban wuce shekara sha takwas ba’
Babawo yace ‘ashe kanwa tace amma dai duk da haka kin mugun sauri girma wallahi’
Lado yace ‘kai Babawo zo ka tuka motarnan ni ma inji dadin shan kankana da gwanda’. Yayi fakin ya sauka Babwo ya tsallako ya fito sannan Lado ya shige ciki sannan Babawo ya shiga ya tuka motar shikuma Lado ya zama makwafcin Budurwar. Babawo ya fahimci Lado sarai cewa ya koma kusa da matar ne, don ya samu damar yin mata Magana.
Koda Lado ya dawo kusa da ita sai ya fara sakin zance yana yimata hirar duniya wani lokacin idan taji abinda ya bata dariya sai ta kwashe da dariya. Duk da dadin hira Lado bai yi kasa a gwuiwa ba wajen sanya karamar askarsa yana yanko gwandar da ke hannunsa sannnan ya sanya acikin bakinsa na Salati. Acikin hirartasu har yake bata labarin wani irin tukin ganganci da yayi jiya kan hanyarsa ta zuwa Gusau daidai garin tsafe.
‘Wasu titrloli guda Biyu suna tafiya Daya biye da Daya. Ni kuma ina biye da su. Koda naga sun dade basu buda mani hanya ba sai na cusa kai. Na sauka daga kan sholda, na sanya masu kai, sai da na wuce daya, sai na hangi wata motar tanka kamfani conoil ta sanyo kai zata bi ta kaina. Hankalina ya tashi narasa yadda zanyi domin kuwa babu inda zan bi in kauce narasa inda zansanya kaina. Na sallama na sadakar mutuwa zanyi lokaci nane yayi.Dole inyi ban kwana da duniya. Nayi Kalmar shahada na runtse idanuna. Sai da nayi dakika talatin idanu na suna a rufe amma naji shiru babu abinda ya faru. Sannan na bude idanu na, naga babu wata mota a gabana. Nayi ajiya zuciya. Nace ‘alhamdu lillahi’ fadar hakan ne yasa fasinjar suka kalleni cike da mamaki sannan wani daga cikin su, ya tambayeni abinda ya faru nayi hamdala’ na kwashe labari kab na gaya masu suka cika da mamaki.
Talatu tace ‘lallai bazaka mantaba domin kuwa da tuni kazama tarihi.’
Babawo yace ‘Oga nifa alokacinnan ina tunanin shaken da kayine ya bugaddakai’ Lado yace kai yau dai kam sai ci uban ya ronnan tsaya yi fakin’ Babawo yayi ta bashihakuri amma Lado yaki hakura Babawo yayi fakin yafita Lado ya fito ya cakumi Babawo da fada sukayi kai wa junan su duka Talatu tana zaune cikin mota tana kallon ikon Allah suka ci uban junan su. Lado yayi sa’a ya cira Babawo sama Babawo yayi tabashi hakuri yana fadin ya tuba bazai kara ba. Talatu ce ta ceci Babawo da kyar a hannun Lado. San nan ta lallashe su suka koma cikin mota aka tafi.
Kamar basuyi fada ba su sukayi ta hira suna nishadi duk inda suka isa wajen jami’an tsaro sai Babawo ya kewaye ta cikin gari domin boye masu tunda yasan suna da laifi a wurin Jami’ai.
Suka iso Zaria misalin karfe 04:30pm Suka kaiwa matar kayanta har gidanta. Tayi masu godiya sannan suka hau motarsu suka koma tasha sukayi fakin. Lado ya karusa wajen mai shayi ya jinjima masa sannna yace masa ‘yanzu haka ji nake kamar akara yi mani lodi in koma Gusau ina jin karfi sosai’ Mai shayi yace ‘ai na gaya maka wannan shayin babban shayi ne amma kayi mani gaddama’ Lado yace ‘a gafarceni naga zahiri don haka asanya mani shayinnan acikin leda in tafi da shi gida’ mai shayi ya kyalkyale da dariyar cin nasara sannan yace ma Lado ga shayi na baka kyauta kaje ka ji dadin ka’ Lado yayi godiya ya karba. Sukayi sallama. Ya kira babwo ya anshi key mota sannan ya sallame shi yace ‘Idan Allah Ya kai mu gobe ka fito da wuri’ Babawo yace ‘toh oga’ Ya nufi gida dayake basu da nisa daga Bus stop ya taka a kasa ya tafi.
Shi kuma Lado ya bar motar anan cikin tasha ya nemi mai mashin ya hau ya tafi gida.
Bayan wata daya da yin wannan tafiyar sai mai 3kwata ya kirawo Lado suka gaisa sannan ya gayye ceshi daurin aurensa da Ihsan yar Funtua. Abin ya bama Lado mamaki, ya dauka irin dai shirmennan ne na yara fasinja sai gashi abin ya zama gaskiya. Ranar dauri auren Lado da Babawo dasu aka dakko amarya. Lamarin ya kayatar sosai mai 3kwata yaji dadin amsa gayyatar da Lado da yaronsa Babawo sukayi aranar daurin auren basuyi kasa a gwuiwaba sai da suka gaisa da amarya Ihsan tana cikin farin ciki sosai kuma tayi murna da ganinsu har tasa akayi masu hotuna sabida tarihi. Suka yi mata fatan alkhairi.
Mai karatu anan na kawo karshen wannan Littafi mai suna ‘Direban Bus’ Ina rokon Allah Ya sa wannan Littafi ya amfanar da duk wanda ya karanta shi.
Nine naku
YUSUF ISMAIL GIWA
Mu hadu a wani littafin nawa mai suna
Zaman hakuri
Littafi ne mai dauke da labarin nishadi, sannan kuma yana kunshe da darussa masu kyau. Kada ku bari abarku abaya, kuyi maza ku neme shi ku karanta. Zai fito a watan august da yardan Allah.
Phone: ***
Gmail:***
Facebook: Yusuf Ismail Giwa