GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
Sadik ya ɗan yi jim! yana kallon wasu Ƴan Samari uku da suka zubo musu na mujiya, su ma dai basu da maraba da na ɗazu sai dai kamannin fuska kowa da nashi, daga ganinsu irin fitsararrun Yaran nan ne.
Kuma ga dukkan Alamu turo su aka yi don sa ido akan Motsin Hibban.
Ɗan numfasawa ya yi ya ce "Ku tashi mu wuce yanzu, don na ga ya sake turo idanunsa wajen" Raihana ta ce "Me kenan??" Cikin nutsuwa ya yi musu bayani ai kuwa Raihana ita ce a sawun gaba wajen ficewa.
Gidan su Raihana suka nufa kamar yadda Hibba ta ce, tana tsoron nufar gidansu kai tsaye don ta san bibiyarta ba wani babban abu ba ne, sai dai akwai haɗari gareta.
Sai bayan Magrib ta samu ta silale cikin tsoro da firgici.
Sai da ta ganta kusa da Maama sannan hankalinta ya kwanta, sai kuma ta fara tunanin abun da ya faru da wanda yake shirin faruwa.
Daga yanayin Misali da kuma ganin idonta in ta kintata daidai shi ne wanda ya zuba mata gasassun idanunsa ya kusa sawa ta faɗi ta fasa baki, ranar da taje taron Familyn su Maama.
Rasa ta inda za ta shawo kan lamarin ta yi gabaki ɗaya kanta ya yi murfi, sai ta yi kamar ta gayawa Maama sai ta fasa, bare kuma Hamdan da ta san faɗen ba abunda zai jawo sai damuwa da tashin hankali.
Haka nan ta cigaba da Ƙunshe abun a ranta,,, sai dai tunaninta da tsoro sun ƙara ninka na Da.
******************************
Ikram, Inaya
Fuska ɗauke da murmushi Ikram ta ce "Naji labarin wai Kabeer yana son wannan Matsiyaciyar" Kallon mamaki da kaɗuwa Inaya ta zubawa Ikram kafin ta kawar da kai tana cewa "Hauka ma kenan!" "Wallahi da gaske nake Muhsin ne ya gaya min, kuma kin ga ba a ɓoyewa Abokin cin Mushe wuƙa, wai har zuwa gidansu ya yi aka ce masa wai an kusa bikinta, sai ya haƙura amma fa don baya so ba, gashi kuma yana jin haushinta" ta ƙarasa maganar tana ƴar dariya.
"Cab! lallai ma wallahi na raina wayon Kabeer, shi me zeyi da wannan ƙazamar da bata kai ma ayi da ita ba?" "Uhm! kwantar da hankalinki, ni fa dama nasan tunda naga yadda Maza suka kiɗime wajen kallonta to dole za a samu haka, amma yanzu ina ganin an zo daidai inda zamu samu dama" "Kamar ya kenan?" Inaya ta faɗa a ɗan hasale, "Ke babu fa yadda za ai Kabeer ya so wannan Jakar, kawai dai abunda aka saba ne Sha'awa ce dai da jaraba irin tashi" "Kuma fa haka ne, to yanzu me kike gani?" "Zuwa zamuyi mu zuga shi ya koma, ta sanadinsa zamu samu damar ruguza duk abunda take taƙama dashi, mu tabbatar mun sa ya haye kanta ya baza komarsa, daga nan kin ga sai abunda muka ga damar yi mata, wulaƙanci da tozarci ya tabbata gareta, ke ni fa wallahi tun daga kallon farko naji na tsaneta "
Inaya ta saki wani shu'umin murmushi ta shala kafin ta ce "Gaskiya kina bada wuta!, ai ina ga duk tsanar da kikai mata bata kai wadda nai mata ba, don ni in da da kisa ma wallahi da na huta, ni takaicina ma ranar fa Hamdan har binta yayi cikin gida!" Ikram ta yi murmushin gefen baki a ranta tana cewa "Damuwarki Hamdan nima haka ne, ke dai ki tayani aiki kawai amma a ƙarshe ni zan yi Nasara"
Tattaunawa suka cigaba da yi akan irin Tozarcin da zasu yiwa Hibba.
__________Shirye-shirye Biki suna ta ƙara kankama a cikin ɗan rukunin Dangin Hibba Yayyen Babanta da Ƴaƴansu sai Maama da Abokiyar Zamanta wato Matar Abba da sauran Ƴaƴansa.
Duk da ba taro zasu yi ba ba gayyatar kowa ba hakan bai hana su zagewa wajen gyara amarya ba, haka zalika sun fitar da ɗan Anko iya nasu wanda zasu saka ranar wuni maganin ma kar Maƙota su ce basu san Hibba tayi Aure ba.
Yau Saura kwana Uku Ɗaurin Aure, Maama, Khalil, Anti Habiba, Hibba , Raihana, su kaɗai ne a gidan.
Hibba da Raihana suna ɗaki suna hira akan abunda ya shafi Auren, kamar yadda Hibba tai alƙawarin faɗa mata asalin a yadda aka ƙulla shi.
Su Maama kuwa suna tsakar gida suna nasu Taɗin, sallama suka ji anyi a soro ba tare da jira ba kuma aka danno kai.
Maama ta saki baki tana kallon Kabeer zuciyarta na bugawa, Anti Habiba ta ce "To!! wannan kuma fa daga ina?"
Maama tayi murmushin yaƙe tana cewa "Ɗan Yayana ne!" maida kallonta tayi kansa ta ce "Kabeer ziyarar bazata haka?" ɗan tsugunni yayi a gefe yana ɗan fara'a ya gaisheta, amsawa tayi cikin sakin fuska gami da tambayarsa Ƴan Uwa da Iyayensa, ya amsa tare da jan baki yayi shiru.
Sai da ƴan mintuna suka shuɗe kafin ya gabatarwa Maama asalin abunda ya kawo shi.
Cikin sa'a kafin Maama tayi magana Anti Habiba ta ce "Allah sarki bawan Allah, dama an ce komai rabo ne, matar Mutum ƙabarinsa!, ai Hibba wancan satin da ya wuce aka yi Aurenta yanzu tana Ɗakin Mijinta, kai ma Allah ya haɗa ka da rabonka wadda ta fi ta"
Kamar an soka masa Mashi a ƙirji haka yaji kalaman nata, lokaci guda duk ɗan ƙoƙarin fara'ar da yake ya dena, wani irin yanayi wanda ya shafi ruɗani, haushi, rashin nasara, kishi, kaɗuwa, ya bayyana akan fuskarsa.
Maama ya kalla cikin rashin yarda da maganar Anti Habiba yabce "Wai da gaske ne abunda nake ji?, anya kuwa tasan akan wa nake magana?" Murmushin ƙarfin hali Maama tayi tabce "Ƙwarai kuwa, in baka manta ba ai na taɓa gaya maka dama an kusa, to ai lokaci yayi tuni!" "Yanzu kenan banida wata dama?" ya ƙara tambaya cikin wata muguwar damuwar da bai san ma tsushenta ba.
"Nema cikin nema ma haramun ne fa Kabir bare kuma har an ɗaura Aure, kayi haƙuri kai ma Allah zai baka taka Abokiyar !" Lokaci guda jikinsa yayi wani bala'in sanyi, jinjina kai yayi tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, zuciyaraa cike da saƙe-saƙe.
Sai da Anti Habiba ta leƙa ta tabbatar ya tafi sannan ta dannawa Ƙofa sakata ta dawo ciki tana cewa "Ji wata sabuwa kuma" Maama ta ce "Ai na gode miki, kin min daidai donn bamu da abun cewa wanda ya wuce haka" Anti Habiba tance "Yo ina dalili!, ni sai naga ma be burgeni ba wallahi, kuma na tabbata dai tunda har aka gama magana da wancan har Aure ya kusa ai ba za a ture shi a kawo wani ba"
Hibba da Raihana suka fito suna tambayar waye da kuma yadda akai, Anti Habiba ce ta fara zana musu tare da ƙarin sharhi akai.
Da daddare....
Hibba da Hamdan na zaune a Falon Maama suna ɗan taɓa hira.
Hamdan ya ce "Wai da gaske kike ba zaki je ko ina ba cin Amarci?" gyaɗa kai ta yi ta ce "Eh mana, a nan dai Ƙasata kuma a Garin da aka haife ni, nafi son komai ya fara daga nan!" "To ni kam tayaya za a yarda in yi kwanaki a wani gurin bayan ba wata Ƙasar na tafi ba?" yayi maganar cike da shagwaɓa, ta ɗan murmusa tana cewa "Zaka iya mana cikin sauƙi ma, ba dole sai ka tafi ƙasashen masu jan kunne fa shine kayi balaguro ba, kuma ba sai kayi ƙarya da su ba" Gyara zama yayi yana zuba mata ido gami da cewa "To ya za a yi kenan?" "Kawai ka ce zaka je wani garin Hutu ko aiki, akwai Garuruwa da dama masu daɗin Ziyarta a Nigeria, ina gani idan hakan ne ma babu wanda ze damu da abunda ka je yi, tunda na fahimci kamar in abunda ya shafi Business ɗinka ne to Daddy fa yasan komai, haka kuwa kaga kowa ze ɗauka ka ɗan fita ne ganin gari"
"Kuma fa haka ne! zance ya ƙare kawai, yadda kike so haka za a yi Hamdana!" ya yi maganar cike da farincikin samun mafita.
Murmushi ta sakar masa gami da cewa "Amma dai ka sanarwa Daddy kana son yin tafiya ko? ba sai ranar ba" "Eh to ban faɗa ba kuma, amma tun da mun samu matsaya yau ɗin nan zan gaya masa in sha Allah" gyaɗa kai tayi ba tare da ta ce komai ba, nan take zuciyarta tayi tsalle ta faɗa duniyar tunani.
Ido ya zuba mata yana jin matuƙar tausayinta na ratsa dukkan kafofin zuciyarsa,,,, ɗan numfasawa yayi kafin ya ce "Idan kina murmushi kin fi kaiwa Maƙura a kyau Hibban Hamdan!, bana son ganin ko alamun damuwa a tare da ke" ta saki wani lallausan murmushi gami da cewa " Bana cikin damuwa a yanzu saboda saura ƙiris ya rage in zama Matarka, ina cikin matuƙar farinciki wanda baya barin damuwa ta yi tasiri a kaina!" Ya Lumshe ido gami da sauke wata zazzafar ajiyar Zuciya sannan ya ce "Fatana farincikin nan ya ɗore har Abada Hibbah, kuma in sha Allah Hakan za ta faru".... ....... ....
Hira suka cigaba da yi cike da ƙauna da kulawa, har na ɗan lokaci sannan Hamdan ya yi mata sallama ya wuce Gida.
Koda ya sanarwa Daddy yana son yin tafiya yayi sa'a ya samu goyon baya ɗari bisa ɗari, ba iya Daddy ba har Ammy ba su kawo komai a ransu ba.
Hakan yayi masa daɗi sosai kuma ya ƙara bashi damar yin kyakkyawan shiri, yadda duk ƙwaƙwa da nacin mutum be isa ya gane ina zai je kokuma yake zuwa ba, har Mota da Mashin ya siya sabbi gal yayi musu number tasu wadda ba a san shi da ita ba, sannan ya ajiye a gidan da zasu tare, yadda ma ko ina zai shiga babu me cewa ya gane Motar.
Bayan kwana Huɗu.....
An ɗaura Aure dangin Amarya sun yi ƙwarya-ƙwaryan bikinsu daga nan aka raka Amarya ɗakinta, kowa ya watse tare da jan bakinsa ya tsuke.
Tun a Talatainin daren ranar Hamdan ya ƙara ɗibarta daga wannan Gidan zuwa asalin wanda ya tanadar mata, don kuwa ko Danginta bai yarda su san a inda zata zauna ba .
Kamar a mafarki take ganin abun don kuwa a ƙalla ɗayan daren ta wuce, tuni ta fara baccin gajiya.
Sai Asbah ta buɗe ido ta ga kamar ba nan ne inda ta fara gani ba.
Tunda tayi Sallah ta koma bacci sai 9:00am ta farka, cikin sanɗa ta sauka daga kan gadon wanda ya ji shimfiɗar Alfarma, ido ta shiga zazzarewa tana ƙarewa ɗakin kallo.... "Sannu da tashi Matar Hamdan!" muryarsa ta ratsa kunnuwanta,,, cikin sauri ta kai dubenta inda ta ji muryar tashi, yana tsaye a gaban Madubi yana gyare-gyaren Suma, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin wani lallausan murmushi.
Cikin tattausar murya ta ce "Yawwa, ashe ka tashi da wuri" ya gyaɗa kai kana ya ce "Na tashi, gashi nayi wanka na rasa kayan da zan saka" ta ƙara faɗaɗa murmushinta gami da cewa, "Za ka jira in yi wanka sai in zaɓo maka?" "Eh mana haka nake nema ai" ta amsa masa tana ɗan murmushi gami da nufar banɗaki.
Suna gama kintsawa suka fito Falo Hibba ta fara hasashen inda Kitchen yake, sai yanzu ta tuna ma ashe akwai batun karin kumallo.
Cikin shagwaɓa Hamdan ya ce "Yunwa nake ji fa, kuma gashi ban iya Girki ba!" "Tunanin inda Kitchen ma yake nake yi, ina shirin tambaya, nnnnin banda rigima ta sabon Ango ai dama Girki aikina ne ba naka ba" ta ba shi amsa, Kwantar da kansa yayi kan kafaɗarta yana murmushi ya ce "To ai naji ance Amaren yanzu Ango ne yake yin Abinci musamman breakfast, da gaske ne ko?"
Tana ƴar dariya ta ce "Wannan ba zahiri banne a Labarai aka fi jin haka, ni kam ko ana yi ma ba zan bari ka yi ba, gwara ka huta!"
"Ai kuwa ban iya ba ne da sai nayi" ta ɗan saki baki alamar mamaki kafin ta ce "Ko dan ba abun mamaki ba ne don baka iya dafa koda Tea ba"
Ɗan murmushi ya yi yana ƙara rungumeta, cikin ransa yana tunanin irin rayuwarsa ta baya kafin ya ƙarasa zama Mutum, cikin tattausar murya ya ce "Um! ba mamaki, don kuwa ko lokacin cin Abinci bana bawa Muhimmanci a Da, tsakanina da shi sai dai a dinga bani a baki, ni kuma ina Karatu ko Lissafe-lissafe, bayan haka kuwa sai gani daga nesa"
Yanzu kam da ta saki bakin bata haƙura haka ba sai da ta juyo don ganin fuskarsa sosai, ɗago kai yayi shi ma yana kallonta fuskarsa ɗauke da wani sirrintaccen murmushi mai ɗauke da sinadaran tsananin ƙaunarta da ke ƙunshe a zuciyarsa.
Kyawawan idanunsa ya zuba a cikin nata yana cewa "Za ki iya rufe bakin ko in rufe miki shi da Nawa?" da sauri ta juya tare da rufe shi ruf!, sai kuma ta ce "Tab! ai fa naga alama ana nuna maka So har ya wuce Ƙa'ida, shiyasa shagwaɓarka tayi yawa"
Sosai Maganar ta soki zuciyarsa ta tayar masa da tsohon mikin danke maƙale a cikinta.
Ɗan jim! yayi kafin yayi wani murmushi me ciwo, hannunta ya riƙo yana zubawa Adon baƙin lalle da ta sha Ido, cikin sanyi ya ce "Ba laifi in kin ce haka, don nima na sani!, ni na tsarawa kaina rayuwata daidai yadda naga ta burgeni, da na taso kan turbar da iyayena suke rainona akanta da ba zan kasance kamili ba, sai dai in kasance kamar wasu daga cikin Ƴan Uwana, irin su Hairaan"
Ya ɗan jinkirta gami da jan wani dogon numfashi ya sauke shi tare da nannauyar ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa................
*Aunty INDO*