GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar

by @auntyindo

"Sai dai a sha giya! ayi ƴan zuƙe-zuƙe a kashe kuɗi a je yawo   in an gaji a Dawo,    ni tsarikana da Ɗabi'u har ma da halaye sun sha bamban sosai da na Iyayena da Ƴan Uwa, shiyasa ta wata fuskar nake shan wahalar rayuwa da su....."   

Hibba ta fahimci kalma ɗaya tak!  da ta furta ta tayar masa da damuwa ba iyaka, don haka ta katse shi ta hanyar kawar da maganar... "Labarin za ka cigaba da bani ne  kokuwa za ka sake ni    in Sama maka abunda za ka ci?"    Cikin salonsa na shagwaɓa ya ce "To ai Da ne nake jin yunwa, amma tunda kika tashi daga bacci  nake kallonki sai naji har na Ƙoshi"  Ta  ɗan murmusa gami da cewa "Haka ne?, nima  to na ƙoshi tunda kai ma haka, ka ga sai mu wuni muna kallon-kallo ko?"

Da sauri ya janye jikinsa daga nata yana waro  ido gami da cewa "Da  wasa nake fa!"     tuntsirewa tayi da dariya tare da miƙewa tana faɗin "Oh  to yanzu na ji magana!".
**************************

   Ismail.........  Yana kwance kan ɗaya daga cikin tausasan kujerun da aka ƙawata Falon dasu,,, sama yake kallo ƙuri!!  ya lula Duniyar tunani.

Hajja Halima da ta ƙaraso wajen tun ɗazu, take binsa da kallo ba tare da ya sani ba ta ɗan taɓo shi gami da kiran sunansa,  da sauri ya tashi ya zauna yana amsa kira.
Cikin tausayawa ta ce "Tun ɗazu Abby yake nemanka fa"   Amsawa yayi a taƙaice  tare da rafka tagumi.

Zama tayi a kusa dashi tare da dafa kafaɗarsa,  "Yarinyar da ta riga ta zama Ƙanwarka  ita ka zauna kana damuwa saboda wani ya Aureta?  Ba girmanka ba ne fa!"   "Am! ba tunaninta na....." katse shi Ummi tayi da cewa "Kar ka yi min ƙarya, kana cikin damuwa ne akan hakan Ismail,  So fa ba wasa bane  bare kuma ya haɗu da Ƙauna,   kuma kai ne fa ka zaɓi haka da kanka!"      ɗan jinjina kai yayi kafin ya ce "Haka ne Ummi, ba a son raina na damu ba, don ban ma san dalilin damuwar ba, ba wai tunanina  na rasa ta   ba,  kawai dai ina jin wani iri ne tamkar  nayi silar ....."     rasa kwatancen da ze yi mata  yayi don haka yayi shiru  gami da haɗiye wani ƙululun yawu  me ciwo....

Nazarin kalamansa Hajja Halima ta tafi yi, hakan ya bashi damar cigaba da cewa "Ba iya Hibba ba, shi kansa Hamdan jinsa nake tamkar Ɗan Uwa na na jini, Tamkar Ibrahim  ɗina da na rasa!"   kuka ne yake shirin kufce masa don haka yayi shiru da zancen.

Sosai zuciyar Hajja Halima ta karye, hawaye suka ciko idanunta,  tunanin Ƴaƴanta biyu da suka rasu ya shiga dawo mata,,, shakka babu indai Ismail ya ɗauki Hamdan da Hibba a wannan matsayin to fa ita kanta tasan  zai iya yin babbar Sadaukarwar da ta  fi wadda yayi,  don kuwa ba ƙaramar Ƙauna ce a tsakaninsu ba musamman  da Ibrahim.

Numfasawa tayi  sannan ta ce "Allah yayi maka albarka Ismail, ka cigaba da miƙa lamuranka ga Allah damuwarka zata dawo farinviki   in sha  Allah,   tashi mu je wajen Abbyn ka ji?"    gyaɗa kai yayi sannan ya tashi suka rankaya,  Ummi na riƙe da hannunsa.
********************************

    Muhsin, Kabeer....
Cike da takaici Kabeer  yace "Ina ganin kawai ƙyale batun yarinyar nan yafi, ba zan zauna wahalar da kaina akan ma wadda bata kai ba wallahi"
  "Aikin gama ya gama ai,  kuma an dai sallame ka" Faɗar Muhsin yana dariya...

Dogon tsaki Kabir ya ja kafin ya ce "Wallahi indai kana min irin wannan sai ka gane   bambancin dake tsakanina da kai!,  kawai don kaga ina saurarenka shikenan ka samu Ƴancin yi min duk abunda ka ga dama?,  shi yasa Daddyna fa yake cewa da   Ɗan Uwa gwara Bare wallahi, don na tabbata inda ban haɗa baƙar alaƙar nan da kai ba sai kafi ɗaukar damuwata matsayin taka"

  A Zafafe Muhsin ya ce "Kai!? me kake tunanin ka fi ni?   Kuɗi ko Gata zaka nuna min?,    in fa zafin kai kake ji dashi nima ina ji dashi wallahi!,  kar nake kallon kowa tun daga kanka har Ƴan Gidanku don haka kar ka fara zo min da rainin hankali, ni  ba sa'an yinka ba ne,  kafin ma ka ce wani abu ni na gama kawo ƙarshen Abota da kai, don ban ga amfanin lusarin Namiji  irinka ba"     "Ni kake faɗawa haka?"  Kabeer ya faɗa yana nuni da kansa.

"Na gaya maka ka yi maganin abun, banza maye!  kawai jaraba ta ciyo ka   ka rasa abar rage zafi sai ka zo ka ƙare a kaina, to ni  ba Matsiyaci ba ne da zaka taka ni ka zauna lafiya"
  Ido Kaber  ya zuba masa yayin da kalamansa suke karakaina a ƙwaƙwalwarsa, "Wai saboda na saba  neman Mata   shi ke nan ba dama in kamu da son Wata sai a ce Sha'awa ce?  kenan yanzu ba ni da Daraja kamar ta kowane Namiji me Ƴ
ƴancin Auren Mace don Ƙauna?"   Tambayar da zuciyarsa ta jefa masa kenan sai dai ba shi da amsarta...

Yayi ƙwafa,  a ƙufule ya ce "Na ji ka  dena Abota dani, mu zuba Shege ka fasa, dani da kai zamu ga kuma waye Matsiyacin!"    Muhsin ya ce "Kai ne mana!, ai kowa ya sani, kuma ka sani daga yau babu Mutunci tsakanina da kai!"   kafin ya kai ƙarshen maganar Kabir ya ce "Ubanka ma bai Mutunta Ubana ba, don haka ba zan ji komai ba don  ka ce  haka,  dama ai rayuwar da ake kenan a Familyn rayuwar Ƴan Bariki, babu mutunci babu mutuntawa, wanda ya fi Kuɗi shine Mutum shine aka fi so ake mutunta shi,  ka ga hakan ba baƙona bane, kuma ka tattara kayanka ka bar min Gida kafin na dawo!"  yana kaiwa nan ya fice fuuu!.
Muhsin ya bi shi da wani mugun kallo me cike da manufofi iri daban-daban.
_________________________________.

Bayan Ƴan kwanaki......

  A kowane ɓangare rayuwa na tafiya daidai da yadda kowa ya tsara tashi, masu baƙin ciki nayi, masu bita da ƙullli nayi, masu shirin ƙulla tasu nayi, haka masu farinciki nayi.

A ɓangaren su Hamdan rayuwar Ƙauna me cike da tsantsar farinciki  suke kamar su haɗiye juna saboda tsantsar kulawa da nuna Ƙauna. Tuni Hamdan ya fara mantawa da rigimar Ƴan gidansu don kuwa ya riga ya rungumi abar ƙaunarsa...........

       Ƙarar  iska gami da sanyinta  ke  karaɗawa a hankali, yayin da duhun Dare ya mamaye Ko'ina,  shiru ne ke famar karakaina a cikin  Motar yayin da duk su biyun suka lula Duniyar tunani....
  Yau ma kamar kullum Yawon da suka saba fita a duk dare shi suka fita,  sosai hakan ke yiwa Hibba daɗi damuwarta takan ragu sosai fiye da in tana gida, kuma hakan na ƙara shaƙuwa da sabo a tsakaninsu.

   Hibba ce ta katse shirun da cewa "Am... kamar ina jin Daddy na nemanka ko?"      ɗan kallonta yayi ba tare fa ya bata amsa ba, ganin zasu shigo cikin gari inda haske da mutane suke rututu yasa shi  rufe glass ɗin motar, kamar ba zai magantu ba sai kuma ya ce "Ba baƙon abu bane ai, kullum cikin  haka ake"
"Amma duk da haka wannan tafiyar taka zata zo musu abaibai, ba tare da wani babban dalili ba sannan ba wata ƙasa me nisa ka tafi ba,  dole fa zasu sha jinin jikinsu"     "Yanzu dai in na fahimta korata kike ko?"   murmushi me ciwo tayi gami da cewa "A'a, inda son raina ne wannan farin cikin  namu ya ɗore, mu kasance a Inuwa ɗaya mu rayu tare har ƙarshen numfashi,  amma ina tsoron mu je neman gira mu rasa ido, na san indai aka gane akwai alaƙa tsakaninmu to fa ranar rabuwar mu ta zo" ɗan jim tayi tana zuba masa idanunta da suka ciko taf da ruwan hawaye, cikin rawar murya ta ce "Ni kuma ina matuƙar sonka Yaya Hamdan!" 

Nasa kaifafa idanun ya zuba mata, yana binta da wani kallo me wuyar fassaruwa,   ɗan murmusawa yayi sannan ya ce "Da alama har yanzu ba ki san waye Mijinki ba"
kawar da nata idon ta yi gefe saboda yadda kaifin nasa ya danne duk wani tasirinta.

zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan murmusa ta ce "Ban gane azancin nan naka ba,  na sanka na tsawon lokaci duk da ba me tsayi bane, mun rayu a matsayin cikakken Ma'aurata har tsayin kwanaki fiye ma da sati biyu,  ina ganin yanzu ba wai saninka ne ban yi ba, sai dai ko ban fahimci rayuwarka ba"
  Murmushi me sauti kawai yayi ba tare da ya bata amsa ba.

Har suka isa Gida babu wanda ya ƙara magana...
Hibba ta lura  halin Miskilancin nasa ne ya motsa don haka ta wuce Bedroom ɗinta domin kwanciya saboda wata muguwar gajiya da kasala da take ji tun daga cikin Ƙashinta.

Har ta kintsa ta kwanta ko motsin Hamdan ba ta ji ba sai da bacci ya fara kwasarta sannan taji shigowarsa  cikin taku me kama da sanɗa.
Ko motsawa ba ta yi ba tayi Lakur! tare da tafiya Duniyar tunani akan ƴar rayuwar da sukai ta Mako biyu.

  Hamdan ya shigo rayuwarta kamar afkuwar walƙiya, ya cika rayuwarta da ƙauna, kuma yayi nasarar zama Sarki a cikinta,  babu zato babu tsammani ya maida ita cikakkiyar Matar Aure wadda ta amsa sunanta,   wannan tunanin takeyi  idanunta a lumshe yayin da murmushi ya gama karaɗe fuskarta ba tare da ta sani ba.

Kusa da ita ya zauna gami da yaye lulluɓar da tayi  yana zubawa kyakkyawar fuskarta ido, zuciyarsa na bashi wasu saƙonni iri daban-daban a lokaci ɗaya,    ƙara runtse idon tayi  tana ɗan turo baki gaba.

  A hankali ya ɗora babban yatsansa kan kyawawan laɓɓanta yana ɗan shafa su a hankali,  cikin nutsuwa ya ce "Hamdah!"    sai da ta sauke wani gwauron numfashi kafin ta iya buɗe idanunta da suka fara alamun bacci ta zuba masa,  cikin murya dake bayyana rauninsa da kuma tsantsar ƙaunarta ya fara magana  "Kiyi haƙuri da irin rayuwar da muka tsinci kanmu a cikinta!"  ya ɗan yi shiru sannan ya cigaba da cewa  "Zamu dena kwana tare, zamu dena wuni a tare,  kasancewarmu tare sai  wasu ƙayyadaddun lokuta, wanda nayiwa laƙabi da lokacin Rayuwata!"

  "Kar ki ɗauka hakan rauni ne ga Soyayyarmu,  ki sa a ranki ko a wane hali Mijinki yana tare dake,  domin rayuwata ta ginu a tare dake na Aureki ba don rabuwa ba Hibba!,     kar ki yi tunanin ƙaramar hatsaniya ko babba zata sa in rabu dake"   

  Shiru ya ƙara yi na ɗan wucin gadi sannan ya ce "Idan kowa ya nuna kansa yake so, ni kuma zan nuna Ke kaɗai nake so fiye da kaina, fiye da duk wani abun da nake Taƙama dashi kafin yanzu!,,   da gaske kin fiye min Komai  Hibba!, fatana ɗaya kar tsoro da rauni na Mata yasa ki juya min baya, don kuwa na bawa kaina yaƙinin ba zaki min haka don son zuciya ba!" 

   Yawun bakinta da ya tsaya cak! yaƙi gaba yaƙi baya ta samu ta haɗiye shi muƙut!  ta lumshe idanunta kafin ta ƙara buɗe su akan Hamdan  wanda take kallonsa tamkar wani haske dake  lulluɓe da Duhu,  a hankali ta ɗora hannunta akan nasa ta ɗan damƙe     tana ɗan murmushi,     ta yunƙura  ta zauna tana ɗan yatsina fuska  don kuwa jinta take tamkar ana mata dahuwar ƙashi.
     cikin sassanyar murya ta ce "Wasu matan fa, wata da watanni suke yi ba tare da sun ga Mazajensu ba,  ba kuma rashin Ƙauna bane, kawai rayuwar ce kowa da yadda Allah ya tsara masa tashi,   ni kuwa fa aƙalla kullum zan dinga ganin Mijina,   ka ga ba sai an bani haƙuri ba, da kaina zan rarrashi kaina sannan in dinga yiwa Mijina Addu'a"    ɗan jim tayi kafin ta ƙara murmusawa ta ce "Idan  na zaɓi rabuwa da kai, to fa sai nayi jinyar zuciyata,  kaga babu riba, gwara  in rayu ƙarƙashin inuwa mafi daɗi gareni" 
Ido ya zuba mata gami da wani ƙawataccen murmushi, shakka babu yana bala'in jin daɗin ƙwarara masa guiwa da takeyi.      Dukkan damuwarta kawar da ita take  ta ɗora farinciki akai domin ta ga    ta kore masa damuwa ko rauninsa.   

Hannunta dake riƙe da nashi ya damƙe gami da janyota jikinsa ya ƙanƙame!, ajiyar Zuciya ya sauke a jere   yana lumshe idanu,   cike da ƙauna yac e "Allah ya yiwa rayuwarmu Albarka Matata!,  haƙiƙa ke babbar Kyauta ce Allah ya bani, kuma ina roƙonsa ya bani ikon kulawa da ke   da dukkan ƙarfina!"      "Amin"  ta amsa tana murmushi,  ɗago fuskarta yayi  yana zuba mata wani narkakken kallo, ita kam lumshe ido tayi tana murmushi a hankali ta ce "Ni kam ina son in ga Maama, na daɗe ban ganta ba"  ya ɗan murmusa  gami da yin magana cikin muryarsa da ta fara canja salo "2 Week kawai?"  ta ɗan gyaɗa kai, ya ce "Oh! za ki ganta, but after 3 months"  da sauri ta  zaro ido, ta buɗe baki zatayi magana yayi saurin rufe shi da nasa cikin wani salo me cike da zunzurutun ƙauna!......

*Aunty INDO*