KOMAI YA YI FARKO

Episode 51

by @jikargarba001

51

Sosai Humaira ta kwantar da hankalinta ta mayar da dukkan tunaninta kan karatun JAMB ɗinta. Kullum za ka same ta a ɗaki rungume da littafi, ko dai tana solving past questions ko kuma tana karanta wani subject cikin nutsuwa. Har Abba sai ya rinƙa yi wa su Inara faɗa idan suna hayaniya, yana gaya musu su bar ta ta maida hankali sosai a karatunta tunda su ba za su yi ba.
Humaira ma ba ta ba su kunya ba. Duk wahalhalun da ta sha a rayuwa bai hana ta tsayawa tsayin daka wajen ganin ta jingine komai a gefe ta mayar da hankalinta a karatunta, wani lokacin ma har sai Mami ta tilasta mata ta sauko ta ci abinci ko ta ɗan huta.
Karatun nata ya biya ƙwarai kuwa.
Ranar da result ɗin JAMB ya fito, Humaira hannunta har rawa yake yi wajen checking result ɗin. Su Inara ma suna zagaye da ita cike da excitement domin duk sun duba nasu kuma ya yi kyau. Da result ɗin ya buɗe, na ɗan lokaci Humaira ta kasa magana saboda mamaki.
“280!” Inaya ta yi ihu tana fizgo wayar. “Kaiii Humaira!”
“Innalillahi! Humaira kin ci ubarmu wallahi!” Inara ta faɗa tana dariya.
Humaira kuwa sai kallon screen ɗin take yi idanunta cike da hawaye. Baƙin cikin da ta taɓa shiga, da ƙalubalen rayuwa, da duk wahalhalun da suka faru da ita suka faɗo mata a lokaci guda, sai kawai ta zauna a hankali tana goge hawayenta.
Mami da Abba na jin ihu suka fito da sauri.
“Me ya faru?” Abba ya tambaya cikin ɗan firgici.
“Masha Allah!” Mami ta faɗa tana karɓar wayar da Inaya ke miƙa mata. “280?”
Abba ma wayar ya kalla, sannan murmushi jin daɗi ya bayyana a fuskarsa. “Excellent!” ya faɗa cike da alfahari. “Humaira kin yi ƙoƙari and I'm proud of you.”
Humaira ta sunkuyar da kanta tana murmushi cikin kunya.
“Allah ya saka miki da alkhairi bisa ƙoƙarin da kika yi, This is just the beginning.” Mami ta faɗa tana rungumeta. 
Result ɗin Humaira ya yi matuƙar impressing Mami da Abba. Hakan ya ƙara sa Abba ɗaukar alƙawarin taimaka mata wajen ganin ta yi karatu mai zurfi kuma ta zama babbar mace a gaba.
Su Inara ma ba a bar su a baya ba. Inara ta samu 260, yayin da Inaya ta samu 244, wanda shi ma babban ƙoƙari ne.
Saboda farin ciki, Mami da Anty suka shirya musu ƙaramin party a gida. Ba wani party mai hayaniya ba, amma mai cike da so da farin ciki. An kawata dining area da balloons da flowers masu kyau, aka yi ordering cake mai rubutun:
“Congratulations Girls!”
Yaya Hamza ma bai tsaya a baya ba,  da ya ji labarin sakamakon da suka samu, musamman na Humaira, sai ya aika wa Anty Fiddausi kuɗi masu tsoka domin ta kai su siyayyan kayan da za su saka ranar party ɗin.
“Ki tabbatar kin siya musu abubuwa masu kyau, yaran nan sun cancanci a yi musu murna yadda ya kamata.”
Anty kuwa sai dariya take yi tana tabbatar masa da cewa za ta kula da komai.
Ya Hameed ma, duk da kasancewarsa ya yi busy ba zai samu damar halartar party ɗin ba, bai manta da su ba. Ya aika musu da saƙon taya murna tare da kyautar naira dubu ɗari ga kowacce daga cikinsu.
Lokacin da alert ɗin ya shiga wayoyinsu, Inaya har tsalle ta yi.
“Wallahi ni kam yau zan yi shopping sosai!” ta faɗa tana dariya.
“Inaya dai ki rage son kashe kuɗi,” Inara ta ce tana girgiza kai.
Humaira kuwa sai godiya take yi cike da jin kunya da farin ciki. Har yanzu ba ta saba da irin kulawa da ƙaunar da take samu daga wannan iyalin ba.
Yusuf ma ya nuna tasa gudummawar ta wata hanya ta daban. Da ya ga su ukun suna ta maganar yadda za su shirya, sai ya ɗauki waya ya kira wata fitacciyar mai make-up.
“Ku bar maganar make-up a kaina,” ya faɗa yana ɗaga girarsa. “Ni zan biya komai.”
“Kai Ya Yusuf!” Inaya ta faɗa cikin murna. “Allah ya ƙara maka buɗi mu love.“

“Da alama yanzu kun fara sona ne saboda kuɗi,” ya faɗa yana dariya.
“Eh mana!” Inara ta ba shi amsa ba tare da wata-wata ba, wanda ya sa duka suka fashe da dariya. Humaira kuwa tace; “A'a Ni ko ba kuɗinka ka san ina sonka.“

"Shiyasa nima na fi ji dake ai.“
Ya rage kuma Yaya Hunaif.
Da Mami ta kira shi ta sanar da shi sakamakon da yaran suka samu da kuma party ɗin da suke shiryawa, sai ya taya su murna sosai.
“Contribution ɗinka fa?” Mami ta tambaye shi cikin wasa.
Hunaif ya yi murmushi a ɗayan ɓangaren wayar.
“Mami, ku bar maganar contribution, Ina da wata kyauta da nake son yi musu.”
“Wace irin kyauta?”
“Nan da kwana biyu za a kawo musu mota gida.”
“Mota?” Mami ta maimaita cikin mamaki.
“Eh. Za ta riƙa ɗaukarsu zuwa makaranta da islamiyya da duk inda suke buƙatar zuwa.”
Na ɗan lokaci Mami ta yi shiru saboda mamaki.
“Hunaif, kana hidima da ƙanenka dayawa.”
“Ba yawa ba ne Mami. Yaran sun yi ƙoƙari, kuma sun cancanci a ƙarfafa musu gwiwa.”
Da Mami ta sanar da su labarin, su Inaya suka yi ihu har gidan ya kaɗa.
“Mota?” Inaya ta maimaita kamar ba ta yarda ba.
“Ina nufin motar tamu?” Inara ta tambaya.
Yusuf kuwa ya girgiza kai yana dariya.
“Ku fara samun admission tukuna kafin ku fara planning yawon gari.”
Humaira kam ta yi shiru tana murmushi kawai.
A zuciyar Humaira, ta kasa daina tunanin yadda rayuwarta ta sauya cikin watanni kaɗan, daga yarinyar da ba ta da kowa sai baƙin ciki da tsoro, zuwa ga yarinyar da ke zaune cikin iyali mai cike da ƙauna, kulawa da kuma mutanen da ke murnar nasararta matuƙa.
A karo na farko cikin lokaci mai tsawo, Humaira ta ji kamar itama ta dace ta yi farinciki.
Da yamma, bayan kowa ya shirya cikin sabbin kayan da aka siya musu, gidan ya cika da annashuwa da farin ciki. Aka kunna music mai daɗin sauraro, amma ba da ƙara sosai ba, just a cool music.
Yusuf ne ya zo da shawarar a yi dancing competition domin ƙara wa taron armashi.
“Yau ba wanda zai tsira,” ya faɗa yana dariya. “Kowa sai ya nuna abin da ya iya.”
Nan take aka fara tafi da ihu. Su Inaya suka fara fitowa suna nuna ƙwarewarsu, suna sa kowa dariya da tafawa. Inara ma ta shiga, ita kuma tana wani dancing cikin nutsuwa amma mai kayatarwa.
Humaira da farko ta ƙi fitowa saboda kunya, amma da suka matsa mata sai da ta fito. Duk da ba ta yi wani abu mai yawa ba, murmushin da ke fuskarta kaɗai ya isa ya nuna wa Mami tana cikin farin ciki, ba ta taɓa ganin Humaira tana walwala haka ba.
Abin mamaki kuwa shi ne lokacin da Yusuf ya ja Mami da Anty cikin filin gasar.
“Kai Yusuf!” Mami ta faɗa tana dariya. “Mu kuma me muka sani?”
“Ba zaku tsira ba yau,” ya amsa yana tafa musu hannu.
Dole suka shiga. Mami ta yi iya ƙoƙarinta, amma Anty ta ba kowa mamaki. Ta shiga dancing ɗin da kuzari da walwala har sai da kowa ya fashe da dariya da tafi.
“Ina kika ɓoye wannan talent ɗin ne?” Abba ya tambaya yana dariya.
“Wasu abubuwa sai lokacin da ya dace ake fito da su,” Anty ta amsa tana dariyar jin daɗi.
A ƙarshe, bayan ƙuri'ar da aka yi cikin raha da wasa, Anty ce ta lashe gasar rawar, Ta ɗaga hannunta sama tana murna kamar wacce ta lashe kofin duniya.
Dariya da tafi suka sake cika falon.
Daga baya aka koma kan abinci, Kowa ya ci ya ƙoshi, ana hira da raha tsakanin 'yan gidan. Abba, Anty da Mami suna kallon yaran cikin farin ciki, suna jin daɗin ganin yadda gidan ya cika da walwala.
Da dare ya yi sosai, taron ya watse a hankali. Kowa ya koma ɗakinsa domin yin wanka da shirin kwanciya.
Yayin da Humaira take tafiya zuwa ɗakinsu tare da su Inara, ta ji zuciyarta cike da wani irin natsuwa. Yau ba ta kwana da kuka ba, ba ta kwana da tunanin abin da ta rasa ba. Amaimakon haka, ta kwanta tana tunanin mutanen da Allah Ya kawo mata a rayuwa, mutanen da suka rungume ta ba tare da sun haɗa jini da ita ba.
______

Duk inda suka bi don a kashe maganar da Nafisa ta tayar, amma ta ƙi yarda. Ta nace cewa sai Zee ta biya kuɗin da take nema, in ba haka ba kuma za ta cigaba da fallasa ta.
Tsabar yadda hankalin Zee ya tashi, kuma tana neman mafita cikin gaggawa, sai ta ajiye girman kai a gefe ta kira Intisar.
A lokacin, Intisar na kitchen tana haɗa lunch, ƙanwarta Kubra ta shigo riƙe da wayarta a hannu.
“Ya Inti, ana ta kiran wayarki.” Ta faɗa tana miƙa mata wayar.
Da Intisar ta karɓa, kiran ya riga ya katse, tana duba screen ɗin wayar, sai ta ga missed calls uku daga Zee.
“Zee?” Ta faɗa cikin mamaki.
Ba ta gama mamakin ba, sai ga wani sabon kiran nata ya sake shigowa. Intisar ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta.
“Hello, Intisar...” Zee ta kira sunanta cikin raunanniyar murya.
“Na’am.” Intisar ta amsa a taƙaice.
“Intisar, please, I need your help. Ki taimaka min, ban san yadda zan yi da Nafisa ba, tana da videos da pictures ɗina da babu kyaun gani, Jiya ma ta turo min su da idona na gani, don ta tabbatar min cewa ba ƙarya take yi ba, wallahi hakan ya tsorata ni sosai.”
Zee ta ɗan yi shiru tana ƙoƙarin haɗiye kukanta.
“Duk da Sarah ta yi ta jan kunne na kada na tura mata kuɗi, na kasa saurararta saboda tsoron kar Nafisa ta tozarta ni, na tura mata miliyan huɗu, amma yanzu ma ba ta haƙura ba, har yanzu tana neman wani miliyan uku. Wai miliyan ɗaya ne cikon abin da take so, sauran miliyan biyun kuma wai saboda lokacin da na ɓata mata.”
Nan take Zee ta fashe da kuka mai ban tausayi.
“To ni kuma me ruwana da wannan sabgar?” Intisar ta tambaya cikin ko in kula.
“Intisar, please...” Zee ta roƙa. “Ke kaɗai ce ƙawar da na san za ta iya taimaka min da gaske. Don Allah kar ki juya min baya.”
Intisar ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce,
“Zainab kenan, kin manta ni ɗin dangin miji ce fa?”
“Don Allah, Intisar. Mu manta da duk abin da ya faru a baya please... ina cikin matsala. Babbar matsala.” Ta share hawayenta da sauri. “Ban taɓa tsoron wani abu kamar wannan ba a rayuwata.”

Intisar ta yi shiru na wasu sakanni, tana sauraron sheshsheƙar kukan Zee daga ɗayan ɓangaren wayar.
A zuciyarta, ta tuna yadda Zee ta yi ta raina shawarwarinta a baya, ta tuna yadda ta yi ta jan kunnen ta kan wasu abubuwa amma Zee ta ɗauka kamar hassada ce ko tsoma baki take yiwa abinda bai shafeta ba. Amma duk da haka, wani tausayin Zee take ki a ranta.
“Kin faɗa wa Hunaif?” Ta tambaya cikin nutsuwa.
Da sauri Zee ta girgiza kai, kafin ta tuna ba za ta iya ganinta ba.
“A'a! Wallahi ban faɗa masa ba. Idan ya gani kafin na faɗa masa ban san abin da zai faru ba.”
“Sarah fa?” ta tambaya don ta san ita ce ta ukun su.
“Sarah ce ma ta fara ƙoƙarin shawo kan Nafisa, amma ta ƙi. Wai sai na cika mata kuɗinta.”
Intisar ta sauke numfashi.
“Kin yi kuskure da kika fara tura mata kuɗi.”
“Na sani, wallahi na sani yanzu. Amma na tsorata ne.”Zee ta amsa cikin kuka.
“Yanzu kina da wani proof na threatening ɗin da take yi miki?”
“Eh. Messages ɗinta suna nan. Har voice notes ma tana aiko min.”
Intisar ta yi shiru na ɗan lokaci tana tunani.
“To kar ki sake tura mata ko sisi”
“Amma...“
“Na ce kar ki sake.” Intisar ta katse ta. “Domin ko kin tura mata miliyan goma ne, ba za ta tsaya ba. Mutum irin Nafisa idan ya ga kina tsoro ƙara matsa miki za ta yi.”
Shiru ya biyo baya.
“Yanzu me zan yi?” Zee ta tambaya cikin sanyin murya.
“Da farko ki kwantar da hankalinki. Na biyu ki turo min screenshots ɗin duk messages da voice notes ɗinta. Kar ki goge komai.”
“Toh.”
“Na uku, idan ta sake kiranki ko ta yi miki magana, ki yi ƙoƙarin kada ki nuna mata tsoro.”
Zee ta yi murmushi mai ciwo.
“Intisar, kina ganin za a iya warware wannan matsalar?”
“Ban sani ba tukuna, anma zan yi tunani.“
“Please kar ki faɗa wa Hunaif.” Zee ta furta a hankali.
“Kina neman taimako amma kina son ki zaɓi yadda za a taimake ki?”
Zee ta yi shiru.
“Zan ga abin da zan iya yi. Amma ba zan yi miki alƙawarin ɓoye komai ba idan abin ya kai wani matsayi.”

“Na gode, Intisar.” Zee ta faɗa tana goge hawaye.
“Kar ki gode min yanzu, ki turo min komai da kike da shi sannan ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya a gida. Kuma idan Nafisa ta sake neman kuɗi daga gareki, kar ki tura mata.”
“Okay.”
Bayan sun katse wayar, Intisar ta tsaya tana kallon screen ɗin wayar na wasu daƙiƙu.
Wani irin nauyi ta ji ya sauka a zuciyarta.


#JIKARGARBA.
***