FreeArewaPen original
KOMAI YA YI FARKO
- 1views
- 55chapters
- 2audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Episode 1
Dare ya yi nisa, gari ya nutsu cikin shiru kamar ruwa a tafki. Gidaje sun cika da numfashin masu barci, fitilu sun mutu, hatta iska tana kaɗawa a hankali kamar tana jin tsoron tayar da kowa. Amma idanunta sun ƙi rufuwa, zuciyarta na ta bugawa a hankali, saboda wata damuwa da ta dame ta. A cikin duhun ɗakin, ta ji kanta kamar zai rabe biyu saboda tunani da ta sa a gaba, ta kasa samun nutsuwa, zuciyarta na ta kai komo tsakanin tunanin da ba ta so, amma ba zai daina tashi ba, ko ta rufe idanunta bacci ba ya zuwa, sai ma zuciyarta ta rinƙa haska ma ta abinda bata son tunowa.A hankali cikin gajiyar jiki da ta zuciya, ta tashi daga kan katifarta da ta suɗe ta koma kamar tabarma, laluɓawa ta yi ta fita daga ɗakin, da taimakon hasken wata da ya haske gari ta ɗauki buta ta ɗebi ruwa a randar da ke ƙofar ɗakin, ba tare da wani tsoro ba ta nufi banɗaki, tsarki ta yi ta fito, ta fara alawla, tana ji...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.