KOMAI YA YI FARKO

Episode 52

by @jikargarba001

52

Bayan dogon tunani da nazari, Intisar ta fahimci cewa yin magana da Nafisa kawai ɓata lokaci ne. Ta yanke shawarar yadda za a kawo ƙarshen abin da ke faruwa, sai dai tana tsoron ko hakan ba zai haifar da wata sabuwar matsala ba.
Ba tare da ta tuntuɓi Zee ko ta ji ra'ayinta ba, sai ta kira Hunaif, domin ta yi imanin shi kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen wannan baɗakalar.
Hunaif na kwance yana hutawa bayan ya dawo daga stadium lokacin da wayarsa ta fara ringing. Ya ɗauka yana faɗin;
“Hello sis.”
“Na'am Yaya, ina wuni?”
“Lafiya ƙalau. Ya kike?”
“Alhamdulillah.”
Shiru ya ɗan biyo baya kafin Hunaif ya tambaya;
“Akwai wani abu ne?”
Numfashi Intisar ta sauke.
“Yaya, akwai matsala fa.”
“Matsala? Allah Ya kawo mana ita da sauƙi. Menene?” ya tambaya yana gyara zamansa a kan gadon.
“Ƙawar Zee ce take yi mata barazana kusan wata ɗaya kenan. Ta tayar mata da hankali sosai. Gashi exams ɗinmu saura sati ɗaya kacal, amma babu natsuwa a tattare da ita.”
Fuskar Hunaif ta ɗan sauya.
“Wace irin barazana? Kuma wacece yarinyar?”
Intisar ta haɗiye yawu kafin ta fara bayani.
“Wata rana yarinyar ta je gidan Zee da lemu. Ashe ta saka mata wani abu a ciki, bayan Zee ta sha, ta fita hayyacinta, sai yarinyar ta yi amfani da damar ta kai ta wani hotel room, ta ɗauke ta hotuna da videos marasa kyau tana tsirara.”
Idanun Hunaif suka kaɗa.
“Me kika ce?”
“Daga baya ta fara amfani da videos ɗin wajen yi mata barazana, tana neman kuɗi. Har ta kai ga tura ɗaya daga cikin videos ɗin a class group ɗinmu, da sa'a course rep ya yi saurin gogewa kafin ya bazu sosai.”
Hunaif ya lumshe ido yana ƙoƙarin danne fushinsa.
“Yanzu fa Zee ta tara duk kuɗin da take da su, miliyan huɗu, ta tura mata. Amma har yanzu yarinyar ba ta daina ba. Yanzu tana neman ƙarin miliyan uku. Zee tana tsoron ka ji maganar saboda ba ta san irin kallon da za ka yi mata ba. Ni kuma na san kai kaɗai ne za ka iya kawo ƙarshen wannan abu, shi ya sa na kira ka ba tare da ta sani ba.”
Numfashi Hunaif ya sauke a hankali.
“Intisar, me ya haɗa Zainab ƙawance da irin wannan yarinyar? Me ya haɗa ta da toxic friend irin wannan? Me ya kaita shan lemun ƙawa, sai kace babu lemu a gidana. Wani kalar lemu ne matata za ta so sha da ba zan iya affording ba?“
“Yaya, don Allah ka yi haƙuri, ba wannan ne matsalar yanzu ba. Abin da muke buƙata shi ne mafita.”
Hunaif ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Ki tura min lambar yarinyar da address ɗinsu.”
“Yanzu zan tura maka.”
“Do that please.“
“Please Yaya, ka yi hankali da Zee, da ta san hakan zai faru da ba za ta taɓa ƙawance da Nafisa ba.”
“Ba komai sis. Amma wannan yarinyar sai ta yi regretting yi wa matata barazana.”
Hunaif bai sanar wa Zee komai game da maganar ba, da daddare ya kira ta suka yi waya, ya lura muryarta ta yi sanyi sosai, alamar tana cikin damuwa.
A ƙarshe Zee ta tambaye shi ko zai iya tura mata miliyan uku saboda tana son yin shopping.
Ya amince.
Bayan sun yi sallama, maimakon ya tura kuɗin, sai ya kira Yusuf.

Washegari Nafisa ta dawo gida daga siyayyan abaya da kuɗin da Zee ta tura mata.
Tana cikin shirya kayan a wardrobe ɗinta lokacin da aka fara knocking gate.
Kafin ma ta fito daga ɗaki, ta ji Mamanta ta buɗe ƙofar falon ta fita.
Da Mama ta buɗe gate, sai ta ga samari biyu da wata mace a tsaye.
“Ina wuni Mama?”
“Lafiya ƙalau.”
“Nafisa muke nema, ko tana ciki?”
Mama ta ɗan haɗe gira.
“Daga ina kuke? Kuma me yasa kuke nemanta?”
Macen cikinsu ta yi murmushi.
“Mu course mates ɗinta ne. Akwai wani course da ta fi mu fahimta, shi ya sa ta ce mu zo gida ta taimaka mana da tutorial.”
Fuskar Mama ta washe da jin daɗi.
“Ku shigo mana, tana ciki.”
Suna shiga falon, sai ta fara kiran;
“Nafisa! Ki fito, ga course mates ɗinki sun zo.”
Da sauri Nafisa ta fito tana murmushi, a tunaninta Zee ce ta kawo mata sauran kuɗin.
Amma tana fitowa sai ta tarar da baƙin fuskoki.
“Ke ce Nafisa?” matar ta tambaya.
Mama ta ɗan yi mamakin tambayar, amma Nafisa ta gyaɗa kai.
“Eh, ni ce.”
Nan take ɗaya daga cikin samarin ya ciro handcuff.
“You are under arrest.”
“Meye?” Mama ta faɗa a firgice. “Daga zuwa karatu sai ku zo kuna kama min ƴa?”
Mutumin ya yi murmushi.
“Hajiya, ba karatu muka zo ba, mu jami'an tsaro ne. Kama ƴar ki muka zo yi.”
Mama ta dafe ƙirji.
“Me ta yi?”
“An zarge ta da saka wa matar Muhammad Hunaif wani abu a abin sha, ta kai ta hotel room, ta ɗauke ta videos marasa kyau, sannan tana amfani da su wajen yi mata barazana da karɓar kuɗi.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!”
Mama ta fara kuka.
“Don Allah ku yi haƙuri. Ita kaɗai Allah Ya ba ni, za ta mayar da duk kuɗin da ta karɓa, har ma mu ƙara muku, amma don Allah kar ku tafi da ita.”
Sai a lokacin wani saurayi da ke zaune gefe ya miƙe.
Yusuf ne, ƙanin Hunaif.
“Ba mu da lokaci,” ya faɗa cikin zafin murya. “Officers, ku tafi da ita.”
Nan take jami'ar tsaron ta ja Mama gefe.
Aka sanya wa Nafisa handcuff.
Da ta kasa ko motsi saboda tsoro da mamaki, suka tasa ta gaba suka fice da ita.

Da dare bayan an gama dinner, Yusuf ya kalli su Inara.
“Mu je ku raka ni wani waje.”
“Ina kuma da daddaren nan?” Mami ta tambaya.
“Gidan Ya Hunaif ne, katarsa ba ta da lafiya.”
Inaya ta taɓe baki.
“Mu fa muna da exams gobe. Yanzu ma karatu za mu yi.”
Inara ma ta miƙe tana cewa;
“Ga Chemistry da uban wahala.”
Yusuf bai ce komai ba.
Sai ya mayar da kallonsa kan Humaira, wadda ke tattara plates bayan an gama cin abinci.
Kullum ita ce ke yin hakan duk da Mami na hana ta.
“Besty, ai ke za ki raka ni ko?”
Humaira ta yi murmushi.
“Ai ba sauri kake yi ba ko? Bari na gama tattara wajen nan sai mu tafi. Ni fa ban isa na ƙi maka rakiya ba.”
Ta ɗauki plates ɗin zuwa kitchen.
Inara ta bi ta suka haɗa tsaftace wajen wanke kwanukan.
Daga nan Humaira ta shiga ɗaki, ta buɗe drawer ta ciro dogon hijab ta saka a kan kayan baccin da ke jikinta.
Inaya ta kalle ta.
“Ba ki daddara da wulaƙancin da matar nan ta yi miki ba?“
Humaira ta yi murmushi.
“Rashin lafiya ya kore komai. Besides, saboda Ya Yusuf ne zan tafi.”
“To a dawo lafiya.”

Zainab na kwance a kan doguwar kujera da ke falon, kanta ɗaure da ɗan ƙaramin scarf, idanunta sun kumbura saboda rashin bacci da yawan kuka. Duk da Yusuf ya kirata a waya ya sanar da ita an kama Nafisa, ya kuma yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali, har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya, sake-sake take yi na inda Yusuf ya ji labarin, sai kuma abinda ya fi ɗaga mata hankali shine ƙilla Hunaif ma ya sani
Sallamar Yusuf da Humaira ce ta katse mata tunanin da take yi.
Da sauri ta ɗago kai.
“Yusuf...” ta kira sunansa cikin rauni.
“Yaya jikin?” Yusuf ya tambaya yana ƙarasa shiga falon.
“Da sauƙi.” Ta amsa tana ƙoƙarin murmushi.
A lokacin ne idanunta suka sauka kan Humaira da ke tsaye a bayan Yusuf cikin dogon hijjab.
Humaira ma ta gaishe ta cikin ladabi.
“Yaya jiki?”
“Da sauƙi.” Zee ta amsa tana kallonta.
Wani abu game da Humaira yana ba ta mamaki duk lokacin da ta gan ta. Nutsuwa da kamun kai irin nata ba abu ne da ake yawan samu a cikin mutane masu shekarunta ba.
“Ku zauna mana.” Zee ta faɗa.
Suka zauna a two seater tare.
“Ya Hunaif ne ya ce na zo na duba ki,an ce ba ki da lafiya.”
Zee ta ɗan gyara kwanciyarta kafin ta amsa cikin raunanniyar murya.
“Eh, zazzaɓi ne yake damuna.”
“Sorry. Allah Ya ƙara sauƙi.”
“Aameen.”
Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu.
Can Zee ta ɗaga kai ta kalli Yusuf.
“Errrm... Yusuf, ya aka yi ka san maganar Nafisa? I mean, ya aka yi ka san abin da ke faruwa?”
“Yaya ne ya kira ni jiya da dare, ya faɗa min komai, sannan ya turo min lambarta da address ɗinsu. Ya ce na tabbatar an kama ta kuma an hukunta ta.”
Fuskar Zee ta ɗan canza.
“Wani Yayan?”
“Ya Hunaif mana...”
Kafin ma Yusuf ya ƙarasa maganar, wani irin tari ya sarƙe Zee, ta fara tari mai ƙarfi babu ƙaƙƙautawa.
Da sauri Humaira ta ƙaraso kusa da ita tana bubbuga mata baya a hankali, Yusuf kuwa ya miƙe da sauri ya ɗauko mata ruwa daga dining area ya kawo. Da ƙyar Zee ta karɓa, amma tana shan ruwan ta fara amai.
“Subhanallah!” Humaira ta faɗa cikin damuwa.
Su biyun suka yi saurin taimaka mata.
Humaira ta kama ta zuwa ɗakinta, sannan ta shigar da ita bathroom ta taimaka mata ta tsaftace jikinta.
Bayan ta gama, ta dawo da ita ɗaki ta kwantar da ita a kan gado.
Daga nan Humaira ta fito zuwa falon ta fara gyara wajen da Zee ta ɓata.
Yusuf kuwa ya ɗauki wayarsa ya kira Hunaif ya sanar da shi halin da Zee ke ciki.
Bayan ya yi masa bayanin komai, Hunaif ya ce;
“Ka ba ta wayar.”
Yusuf ya shiga ɗakin ya miƙa mata wayar.
A hankali Zee ta karɓa.
Tana ganin sunan Hunaif a screen ɗin wayar, sai ta ji wani sabon yanayi ya mamaye zuciyarta, wani irin tsoro da kunya suka sake dabaibaye ta.
Sai dai ta daure ta ɗora wayar a kunnenta.
“Hello Zee, kina jina?”
Kai ta gyaɗa kamar yana gabanta, sannan ta tuna ba zai ganta ba.
“Eh...” ta amsa a hankali.
“Good. Yanzu ki cire duk wata damuwa a ranki, ki kwantar da hankalinki, kar ki bari damuwa ta jefa ki cikin wata ciwo. Be fine, okay?”
“Uhmm...”
“Yanzu me ke miki ciwo?”
“Zazzaɓi nake ji.”
“Kin sha magani?”
“A'a.”
“Zan kira doctor yanzu ya zo ya duba ki.”
Shiru ta yi na ɗan lokaci.
Sai kuma cikin murya mai rauni, kamar mai shirin fashewa da kuka, ta ce;
“I want to go home.”
Hunaif ya yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya amsa cikin nutsuwa.
“No. Ba za ki tafi gida yanzu ba. You need to rest first, ki kwantar da hankalinki, you will be fine, In Sha Allah.”
Wani sanyin zuciya kalamansa suka saukar mata, duk da cewa tana jin wani kunya da tsoron abinda zai iya yi, amma kashi casa'in na abinda take ji ya rabu, ganin yadda ya yi magana da ita kamar ba komai.
Bayan sun yi sallama, Yusuf da Humaira suka ci gaba da zama tare da ita, bai wani daɗe ba doctor ta iso.
Ta duba Zee sosai, ta auna zafin jikinta tare da tambayar wasu bayanai.
Daga ƙarshe ta rubuta mata magunguna, ciki har da paracetamol da maganin malaria.
Kafin ta tafi ta ce;
“Da safe ku kai ta asibiti. A yi mata cikakken bincike, saboda ba zazzaɓi kawai nake zargin yana damunta ba. Tana buƙatar a duba ta sosai.”
Yusuf ya gyaɗa kai.
“Toh Doctor.”
Bayan doctor ta tafi, Humaira ta taimaka wa Zee ta sha maganinta.
Cikin mintuna kaɗan bacci ya fara ɗaukarta.
Yusuf da Humaira suka kalli juna cikin damuwa, kafin su bar ɗakin a hankali domin ta samu ta huta.


#Jikargaba
***