Chapter 10
by @reza12
*MATAR MAZA*
_(Life story)_
*Chapter 10*
Washegari Mansur ya sake kiranta akan mai ta yanke game da soyayyar su. Tayi shiru, kusan minti ɗaya ta ce "Kazo gida muyi magana. Koda yazo ta masa tambayoyi akan mai yasa yake sonta yana saurayi tana bazawara, kuma harda yarinya, shi kuma bai taɓa aure ba. Ya ce saboda kawai yana sonta, kuma zai iya rayuwa da ita koda aure nawa tayi. Ta ce masa yanzu idan ya aurenta zai iya dawainiya da ita, kuma ko yanzu zai iya ji da dukkanin matsalolin ta?" Mansur yayi shiru domin dai ba wani kuɗi gareshi ba, amma ya ce zai iya, ya nuna mata cewar duk wata dawainiya tata zai iya muddin har ta amince. Ta ce "Tom shekenan, na yarda zan aure ka, amma bana so kowa ya sani tukunna". Ya ce "Kamar yaya kar kowa ya sani?" "Eh har sai mun tsyar da magana ni da kai, ma'ana sai mun san matsya sai mu shigar da manya ciki". Daga haka suka rabu, yana ta murna domin shi da gaske ne yake son Azima domin ita ɗin macen shiga taro ce, komai yaji daidai daga sama zuwa ƙasa, tabbas idan ya sameta to Ubangiji ya sallame shi ta wannan bangaren. Yau ko waje bata leka ba, tana jiran zuwan mai martaba, tana ta samun kira daga mutane har a kasuwa amma taki dagawa, birninta kawai yazo taji shin da gaske ne amma yake so ya cuceta. Number Abraham ce ta sake shigowa a karo da barkatai, kamar ba zata daga ba amma ta daga tana sallama ciki-ciki. Yayi dariya a hankali ya ce "Kyawun fuskar ki ya hana ni sakuni, kawai ke nake son gani Please". Ya faɗa da wata kasalliyar murya. Ta ce "Sorry sir kasan wacce ka kira kuwa?" "Yes, Azima yar kasuwa ƙawar Namra haka ne ko?". Ta sauke ajiyar zuciya kawai domin ta gane yasan ita ya kira. Ya ɗora da "I'm in love with you seriously Azima, ban taɓa jin hakan akan wata mace ba idan ba ke ba, Please ki saurare ni muyi magana". Ta ce "Sorry sir are you forget ho I'm? Nifa Musulma ce" Ya ce "So what, na sani, hakan ne ma yasa nake sonki ai". "O really? Ka sani kuma kake sona kasan ba soyayya a tsakanin mu?" Yayi dariya mai sauti yana gyraa zama domin jin muryarta kawai na harfar masa da farin ciki. Sosai ya dage mata, har abun ma na bata mamaki, duk ta inda ta shiga sai ya kamo ta, karshe dai ta haƙura taga ina zai je a wannan haukan nasa. Tuni ta manta da damuwar da take ciki na mai HIV. Sunyi kusan awa uku suna waya kafin ya katse bayan ta bashi uzuri. Bayan ta kashe ta nufi gida gurin Hajiya domin ta gaidata saboda jiya bata je ba. Bayan sun gaisa Hajiya ta ce "Ni wannan yawan naki Azima yana bani tsoro wallahi, ke baki jin tsoron ma a kira mai gidan naki a faɗa masa". Azima ta zauna tana dariya ta ce "Hajiya ai ya san ina fita, shine ma fa ya bani izinin zuwa ko ina fa". Hajiya dai bata sake cewa komai ba. Haka kawai hirar ta da Abraham ce ke dawo mata. Sai kawai taji tana murmushi ita ɗaya . Bata bar gidan ba har sai bayan la'asar wanda sai da tayi musu girki gaba ɗaya. Washegari kuwa misalin sha ɗaya ta isa ofishin Namra domin ta bata labarin yadda sukayi da Mansur. Har ta shiga ofis ɗin bata haɗu da Abraham ba, hakan yayi mata daɗi, amma sai take jin kamar wata zuciyar tata na son ta ganshi saboda maganun da yayi mata jiya. Bayan ta zauna ta ce "Wannan ofis ɗin naki fa ina ga zai dawo gurin zuwa hutu na ne". Ta faɗa tana dariya. Namra ta ce "Wannan ai ba irin naku bane, ke ai nabbar kai ce, naku na sama". Gaba ɗaya suka yi dariya. Ta ce "Ba wannan ba, yanzu yaya zanyi da Mansur ne. Nan ta kwashe yadda suka yi da shi. Namra da taji daɗin hakan yasa ta ce "To wai meye laifin Mansur ɗin nan, kawai ki yarda meye a ciki, Gashi ma saurayi yaro danyen jini Hajiya". Azima ta ce "Laifinsa ɗaya shine talaka ne shi, ta yaya zan iya auran sa a haka, kinga nifa nazo ne ki bani shawara yadda zan kirkiro abun da zai min wanda zai sa dole ya kasa yace ba zai iya ba". Namra ta gyara zama ta ce "To me kenan, sayan waya ko mota ko me?" Azima ta ce "Ba waya ba, mota kuma tayi girma, abu dai mai muhimmanci da zai iya zama dole". Sukayi shiru. Ta ce "To ko umara ko Hajji, ko kuma ya kai ki shopping duk ki ƙarar masa da account". Azima ta ce "No ba shi ba". Namra ta ce "To ke kika sani kuma". Ta na rufe baki ta ce "Yes na samo". "Mene ne?" Ta tambaya. Ta ce "Zance masa ya biya kuɗin hayar gidan da nake da kuma kuɗin wuta da ruwa dama wannan watan zai kare sai na tura masa lissafi dan ubansa". Namra ta ce "Amma fa kuɗin da yawa, please kar ki talauta shi". "Ai shi yace zai iya, kuma me amfanin kuɗin nasu idan bamu ci ba, kuɗin Maza ai na mata ne, dole su nemo su kawo mana muna zaune". Namra ta bita da kallo har ta gama. Sosai suke ta hira har dai lokacin tafiyar ta yayi ta kama hanya. Tayi mamakin da bata ga Abraham ba har zata fita, kamar ta tambayi Namra ko yazo aiki ne, amma ta fasa. Ta shiga mota ta tafi gida tana jin ta wasai. Tana shiga cikin palon gidan nata taji wayar ta na ƙara. Tana dubawa taga Abraham ne. Da mamaki take kallon number, sai ta fara tunanin ko yaga shigar ta Campanian nasu ne. Ta daga a hankali. Kafin tayi magana ya ce "Na turo ɗan aike izuwa gidan ki, nan da minti biyar zai iya zuwa". Ta ce "Ban gane ba aike na me?" Ya ce "Idan yazo zaki gani". Ya kashe wayar. Ta tsaye a gurin tana mamaki, kenan dai ya ganta a Campanian nasa kenan ko me. Tana cikin haka kuwa taji ana buga mata palo, sai da ɗan tsorata kafin ta tambayi waye ya amsa mata ta je da sauri ta buɗe. Sai kuwa ga mutum tsaye da wata karamar jaka ta baya. Ya ce "Good evening Madam, oga Abraham ne ya ce a kawo miki". Ta amshi jakar bata iya cewa komai ba sai binta da kallo, shi kuwa ɗan aike ya juya ya tafi abunsa. Ta kara so palo tana auna nauyin jakar da abun dake ciki. Duk hasashenta ta kasa hasaso abun da zai iya kawo mata a cikin jakar. Ganin haka yasa ta shiga dubawa da sauri domin dai ganewa idanunta.
Da wani irin tashin hankali taja baya har wayar hannunta na subucewa saboda abun da ta gani, ta dafe kirji tana ja da baya zabar tsoro. Daidai lokacin kuwa wayar ta ta fara ƙara tana neman ɗauki, ta sunkuya ta daga tana kaiwa kunne ganin number sa ce. Ya ce "Nasan kinga abun da yake ciki, kar kiyi mamakin hakan saboda ɗazu na zo shiga ofishin Namra saboda naga shigar ki, sai na ji hirar da kuke yi, kince wannan watan kuɗin hayar gidan ki da wuta da ruwa zai ƙare, Sannan kunce kina son namiji mai Kudu, shine kawai na kawo miki wannan domin muddin saboda da kudi ne to ina da su baki da matsala, bana so ki guje ni saboda su".
Abraham na gama faɗa ya kashe wayar. Ita kuma ta cigaba da kallon kuɗaɗen ta kasa magana. Gaba ɗaya yau an goge mata hadda, mai yake nufi da ita, anya wannan mutumin kirki ne, ko dai an turo shi ne ya jarrabata. Tunanunnuka ne barkatai suke tai mata rufdugu, ganin haka yasa ta karaso ta sake duba kuɗin da kyau. Kuɗaɗe ne masu yawa sabbi a cikin jaka rafa-rafa miƙaƙƙu. A fili ta ce "O ni Azima, harda Kirista kuma yau na rarumo, Allah kana gani, ban san abun da zuciyarsa ba". Ta kwashe kuɗin ta ajiye su gefe ba tare da irga su ba. Ta kira shi ya daga. Ta ce "Nifa ban ce maka bani da kuɗin biyan haya bane, kawai gyan ne ya dame ni zan masa haka domin ya rabu da ni, Kuma idan ma haka ne kuɗin sunyi yawa fa". Ya ce "Na san kina da kuɗi, kawai nayi hakan ne domin nima kar watarana a kore ni saboda matsalar kuɗi kawai". Tayi murmushi ta ce "Kana bani mamaki yadda keke abu Kamar baka san matsayin mu ba". Shima yayi murmushi yana tabbatar mata da cewar ya sani, kuma shi auranta zaiyi. Sun dade suna hira har ta shiga kichn tayi girki suna hira. Bayan ta gama cin abincin tayi wanka tabi lafiyar gado cike da alfahari da kanta, yadda yanzu take da dama da kuma buri, sannan babu wani dan iska da zan bata umarni ko ya rainta, abun da taso take yi a duk lokacin da taso, ga kuɗaɗe a account da gida, kawai ta tuno da irin rayuwar ƙuncin da suka yi bayan rasuwar Baba, tabbas ta yarda cewa babu Maraya sai rago.
Kaman yadda suka tsara kuwa haka ta fadawa Mansur, shi kuma yace mata nawa ne kuɗin. Koda yaji nan take yace bashi da kuɗin amma ta ɗan bashi lokaci zai haɗa ya biya mata. Daga haka ya ɗan bata damar shan iska. Suna tsaye da Billa bayan ya gama jin tuhumar da take masa wai shine mai cutar ƙanjamau. Yayi dariya ya ce "Waye ya faɗa miki wannan maganar, kuma a ina yake?" Ta ce "Ai wanda ta faɗa min ba zata min karya ba, dan haka wallahi ina tsoro ba zan iya ba". Bilal ya ce "Ikon Allah, ke kuma daga faɗa miki abu sai kawai ki yarda babu bincike babu lissafi ko?". "Haba Bilal ana karya da irin wannan ciwon ne, kawai dai nayi mamakin yadda baka faɗa min bane kake kuma son muyi aure a haka, gaskiya ba zan iya ba". Sosai fa ta dage ta ma ki tsayawa yayi mata bayani. Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ya dinga mata rantsuwa da bata hakuri amma taki, karshe ma yace mata ta zaɓi duk asibitin da take so suje ayi masa gwaji amma tace ita kawai a rabu saboda dama ita tana tsoron yin aure a gidan sarauta, sosai yake sonta, kuma da aure da zuciya ɗaya. Babu abun da bai ce mata ba amma ta dage. Haka dai ya bar gidan ba tare da yana jin zai hakura da ita ba.
Ta na shiga gida ta kira Sadiya, sai dai tana ɗagawa taji tana kuka, cike da furgici take tambayar ta abun da ya faru. Amma ta kasa magana, hakan yasa ta fito da gudu bayan ta saɓo gyale ta nufi gida hankalinta a mugun tashe. Tana zuwa kofar gidan taga Mansur saurayin Sadiya ɗin tsaye shima hankalinsa a tashe. Yana ganinta kuwa ya nufo gurin ta yana kiran sunanta. "Mai ya faru Mansur, ina Sadiya ɗin?" Ta faɗa ta na karasowa gabansa. Kafin ma yayi magana sai ga mahaifiyarsa ta fito daga cikin gidan a fusace. Ganin Azima yasa ta faɗin "Yauwa ai ga asalin banllagazar ta iso, na san dama zata zo saboda ta zama uwar sai abun da tace, to nazo ne na jawa kanwarki kunne akan ta fita sabgar ɗana, bana son ganinta da shi, domin ba zamu so mu haɗa zuri'a da karuwai wanda suke asirce maza kuma marasa zaman Aure ba, na faɗawa ita uwar taku da ita yarinyar, yanzu kuma ga ki, to a bar min ɗana haka aje a samo wasu, idan ma a nono kuka sha maita da asiri to ni na bawa dana Lahaula maganin baki". Tana faɗa ta dakawa Mansur tsawa haɗi da zagi akan ya wuce su tafi. Sai dai me. Ina ai uwa bata fi uwa ba, yau da akan iya kanta aka tsaya zata iya jurewa amma azo har gida a zagar mata uwa a kirata da maiya a gabanta, sam bata yi wannan lalacewar ba, ko a baya da bata da ƙarfin iko bata yarda ba bare yanzu da take jin zata kara da uban kowa a faɗin Nigeria. Duk da cewar taci albarkacin ɗan ta shi yasa taso ta kyale ta ta, amma tunda ta saka Hajiya a ciki wallahi sai ta mayar mata da amsa domin dai uwa uwa ce. Azima ta ce "Ai idan ana neman babbar ballagaza ke za'a sama da har kike iya takowa kizo gidan su budurwa wai ta fita daga sabgar danki, kin nunawa duniya cewa baki isa da shi, domin shine zaki faɗawa haka saboda shi ya ganta yake so kuma har yake zuwa gidan su, wallahi munfi ƙarfin muje gidan saurayi, kuma kalmar maita da kika ambace mu da ita ki shirya amsa kiran koto, zamu je ki bada tabbacin hakan". Matar ta fashe da kuka tana kallon Mansur da yake ta kallon Azima. Ta ce "Kana dai gani ko a ganka take kira na da ballagaza, har take zagi, Allah ya wadaran wannan gidan da kazo neman aure, kuma wallahi ko bayan raina idan ka sake ko kallon yarinyar nan Allah ya isa, ban yafe". Azima ta ja tsaki ta shige cikin gidan tana kara jaddada mata zuwa kotu.
Tana shiga gidan ta tatar da Sadiya na ta kuma Ummi na taya ta. Ga Hajiya ma a gefe ɗaya da alamu dai lamarin bai musu dad'i ba. Ta kalli Kanwar tata a hankali ta ce "Ta shi kizo, kiyi hakuri Sadiya Allah zai shiga lamarin". Ta faɗa cike da lallashi domin tasan yadda take mutuwar san Mansur, domin shi ɗin ya cancanci aso shi, kuma tasan tayi mugun sabawa da shi, dole abun yayi mata zafi. Hajiya ta ce "Duk wannan laifinki ne Azima, yau da kina zama a gidan mijinki waye ya isa ya mana wannan maganar, wallahi na gaji, watarana halinki zai iya yin ajalina, idan kuma haka kike so to shi kenan kici gaba". Ta ƙarasa tana kuka. Sosai ran Azima ya sake ɓaci. Ta ce "Mai tace muku da taza?" Ta faɗa tana binsu da kallo. Hajiya tayi saurin faɗin "Duk ma abun da ya faɗa ai gaskiya ne, Dan kuka shi ke kawowa uwarsa jifa, kuma idan na isa dake daga yau karki ƙara barin gidan mijinki, ko nan da waje karki fita, kiyi zamanki duk abun da kike so ki ƙara shi ya kawo miki idan kuma Baya nan ga Sadiya ko ummi wata ta koma ta yata ki zama". Ta faɗa cikin fushin da ta dade ba tayi magana ba. Azima ta kalli Sadiya, a ranta tana jin yanzu da Hajiya tasan cewar Azima bata da aure tun tuni mai zai faru...📝