27
by @rufaidaumar
ALWASHI
52
Washegari aka yi walima a gidan wanda duk Hajja ce ta shirya. Mami babu tanadin da ta yi n tarbar Laila. Ta ajiye tanadinta ga Kausar wacce za ta tare nan da sati guda. Sam Mami da yaranta ba su san da shi ba, sun dai ji ƙishin ƙishin daga bakin Afrah wacce tace kamar ta ji Lubna suna zancen. Har wani decoration aka yi a tsakar gidan. Komai ya yi kyau, Hajja har da su kayan rabo ta yi. Babu zantuka dake yawo a bakunan ƴan uwan Laila irin na mutunci da kirkin Hajja. Sai yabonta suke. Laila dai uffan ba ta ce musu ba don ba ta gama tantance kirkin ba.
Gaba ɗaya ita gajiya ke ɗibarta ba. Ga shi a yammacin ranar su Haseenah suka tattara suka bar Katsina. Zakiyya kuma ta yi gidan aurenta bayan ta mata alƙawarin zuwa nan da kwanaki biyu.
Kafin a watse sai da Anti Shafa wata cousin ɗinta ƴar Maiduguri ta ƙara yi wa kayanta kabbasa, ita kanta sai da ta saka ta yin wanka. Ta tabbatar ta shirya tsaf cikin wani lallausan leshi ruwan madara mai adon baƙaƙen furanni da stones. Sai mayafin da ta fiddo mata na amfani. Kuka kam ta sha shi har da ruƙunƙume Haseenah wai to ita ta zauna ta bari sai gobe. Tun Haseenah na dauriya har itama ta fashe da kukan. Sai da aka tsawatar musu kafin daƙyar su rabu. Areef ya zo sun gaisa amma ba ta ma bari sun haɗu ba. Amanar Laila wata Gwaggonsu ta damƙa masa da tunasar da shi haƙƙoƙinta da ke kansa. A ƙarshe ta jaddada masa cewa ya ji tsoron Allah wurin yin adalci tsakaninsu da Amaryarsa. Ya kuma riƙe amanar kowaccensu. Sosai ya ji daɗin nasihar kuma ya yi godiya. Kuɗi mai yawa ya ajiye musu wai su yi guzurin hanya. Daga nan ya musu sallama ya wuce bai ko waigo don amsa kiran ya zo ya ɗauki kuɗin da suke mishi ba a cewarsu abun ai sai ya yi yawa. Ga Abba shima ya basu nasa. Zakiyya dai lokacin ne ma ta ƙarewa Areef kallo don rabonta da shi a zahiri tun haɗuwarsu ta farko a ɗakin Maminsa sadda ta yiwa Marigayiya Sameera rakiya kitso a gidan.
Ba ta manta me Zakiyya ta ce mata ba kafin su rabu.
"Wallahi Laila guy din nan abinsa da ɗaure kai, wane irin mummunan rayuwa ya tsunduma kansa a ciki haka? Ki gan shi fa a nutse kuma kyakkyawa na yaɗawa duniya da ma alfahari ga matar da ta aure shi. Amma kyan ya zama na ɗan maciji. Kaico. Laila Allah ya baki sa'ar yaƙarsa, saboda na kula yana da fuska biyu. Ke kya rantse ko kiyashi ba zai iya zalunta ba balle kuma ɗan adam. A gaskiya ki bi komai a sannu kuma ki yi takatsantsan don na lura yana da mugun wayo da iya taku. Sannan ki tabbatar ko yaya kina sakin jikinki da shi, kamar yanda muka faɗamaki, zai yi wahala ki fahimce shi ko ki san wasu harkokinsa matuƙar ba ki saki jiki da shi ba. Yanda kika danne kika aure shi, yanzu danniyar taki ta fi ta baya yawa. Sai kin sake da shi ko yaya za ki ci galabar sanin makamar aiki. Haka Hajja ta faɗamaki itama. Kin tuna komai dai ko?'
Ajiyar zuciya ta sauke, a lokacin ta amsawa da Zakiyya da Eh, amma ita kam duk wayon Areef tana ji a ranta sai ta yi nasara.
Haka ta zauna shiru bayan tafiyarsu har aka yi kiran sallar Magriba. Lokacin ne saƙon abincin dare daga Hajja ya iso. Ta yi wa ƴar saƙon godiya ta rufe ƙofar ta koma ɗakinta. Bayan ta idar da sallah ta yi nafila, zaman addu'a ta yi yanda ta saba a gida. Sosai ta yi addu'a kan Allah ya shiga lamarinta ya ba ta ikon yin yaƙi da Areef. Ya kuma ba ta nasara a kansa.
Koda ta idar ma, gefen gado ta yi zamanta don ba wani yunwa take ji ba. Dab da tafiyar su Haseenah ta samu ta ci abinci. Wayarta ta ɗauka da zummar kiransu ma ta ji ya hanya. Nan ta ci karo da saƙon Mama ta whatsapp, da sauri ta buɗe cike da kewarta. Ba su yi wata cikakkiyar sallama ba, sannan tun zuwansu ko ta kira ta ba ta ɗauka balle ta amsa mata saƙon whatsapp. Wannan na daga cikin ƙarin damuwarta da ƙunci. Hakan yasa ta jin daɗin ganin reply ɗin Mama Kubra. Ta buɗe dogon saƙon muryar ta saurara.
"Assalamu alaikum Laila, ina fatan komai lafiya? Su Shafa kuma sun tafi ko? To Allah ya kai su lafiya. Dama ina son samun nutsuwa ne kafin na ce maki komai, yanzun kuma Alhamdulillah don ɗazu muka iso Maiduguri. Laila, Laila, Laila, sau nawa na kira sunanki? Ki ji tsoron Allah, ki ji tsoron Allah Laila. Ki sani duk wani abu da za ki shuka a gidan aurenki, a gaba shi za ki girba koda kuwa a cikin zuri'arki ne. Jikina ya kasa aminta da cewa kin auri yaron nan ne domin ɗanki, na fi tunanin wannan banzan Alwashin da kika taɓa ci tun rasuwar ƴar uwarki, shi ya hana ki cigaba da taki rayuwar, ya datse duk wasu burikanki ko? Hum! Laila ni na haifeki, na raine ku tare da abokiyar haihuwarki, babu wani abu da ban sani ba a halayyarku. Idan ko dukkan wannan abu hasashena ne, to ki ƙaryata ni Laila, ki ƙaryata ni wajen yin mijinki sau da ƙafa. Bin umarninsa da kaucewa ɓacin ransa tunda shi kika zaɓa. Ban ma san ya aka yi kuka ƙoƙarin convincing iyayensa suka aminta ba. Allah ya kyauta, ke kuma Allah ya sa ki ji maganata."
Anan muryar Mama ta ɗauke, voicenote din ya ƙare. Zuwa lokacin ta ji kukan ma ba fita yake ba, jikinta ya yi sanyi. Mama na son ɗaure ta da jijiyoyin jikinta sai dai wannan ɓangare na zuciyarta mai shegen kafiya ya ture dukkan nasihohin Mama ya ajiye a gefe.
'Ki yi haƙuri Mama, ki gafarce ni. Na san duk abin da zan aikata kema za ki ji daɗinsa a gaba. Ki bari na koyawa azzaluman mutanen nan masu son zuƙatansu hankali.'
Wannan maganar ita ce matsayar Laila. Daidai nan kuma ta ji alamun motsi a falon. Kafin ta yi yunƙurin miƙewa don rufe ƙofar ɗakin har ya ɗaga labule ya shigo da sallama. Shi kaɗai ne, hannunsa riƙe da ledoji. Yana sanye cikin wani arnen men lace sky blue colour, ya ɗora hula a kansa duk da hular ba ta rufe cikar sumarsa ba dake kwance luf-luf. Kallo ɗaya ta masa ta kauda kai, ya ƙaraso ciki ya zauna gefen gadon nesa da ita kaɗan, ledojin ya ajiye a gefe ya ƙara kallonta da ɗan murmushi a fuskarsa yayin da nata fuskar a ɗaure tamau. Duk da kanta yana ƙasa tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta da suka sha lalle ja da baƙi, hakan bai sa ya kasa fahimtar yanayinta ba. Amaren da suke lulluɓi su zauna sai Ango ya buɗe musu fuska ita babu ma rufin, kwalliyarta ya mishi kyau ya san babu damar nunawa.
"Ya gajiyarki?"
Ta ɗan ɗago jajayen idanunta da suka kumbura tsabar kukan da ta sha a yau ta watsa mishi kafin ta yamutse fuska cike da tsiwa ta amsa.
"Gajiyar me kuma? Me ma ya shigo da kai nan? Me ka shigo ka yi min Areef? Ko abin da ka fara za ka ƙarasa? Ai ina tunanin ka gama cire duk wani mutuncina kafin isowar ranar nan ko?"
Ta ƙarashe tana dubansa tsakar idanu, yanayin kallon da yake watso mata ya sa ta kawar da kai. Zafin kalamanta na ƙarshe ya ji ainun, miƙewa ya yi duk a son ya haɗiye zafin zantukan kar ya aikata abin da ba shi ba. Miyau ya haɗiya cikin ɗan kaushin murya ya ce.
"Sai da safe."
Ya sa kai ya fice. Ta bi bayansa da harara gami da jan tsaki. Ita fa ba ta jin za ta iya sassautawa mutumin nan.
Sanin da ta yi ma ba zai taɓa dawowa ba ya sa kawai ta yi sallar isha'i sannan ta rage kayan jikinta ta ɗauko na bacci, sai da ta ƙarewa farar rigar kallo wacce ta sha turarukan kabbasa, santsi ne da ita mai hawa biyu ce. Gaba ɗaya tsawonta a gwuiwarta ya tsaya. Ta tufke jelar kitsonta ta saka hularta fara ta rage fitilu. Text din Haseenah ya shigo wayarta tana sanarmata tun ɗazun sun isa gida. Ta aikamata martanin saƙon sannan ta tuna ba ta rufe falon ba. Fitowa ta yi ta rufe ƙofar da muƙulli, ta iske ma duk ya kashe mata fitilun falon. Don haka koda ta shiga ɗakinta kawai rufowa ta yi ba tare da sanya muƙulli ba, har ranta ta sani babu abin da zai maido shi wurinta.
***
"Ka san da cewa Adam mahaifin Laila matarka ma raye? Ka san cewa Laila da Sameera are two diffrent identities. Tare aka haife su, ƴan biyu ne. Mahaifinsu kuma shi ne Adam Yaƙub Kibiya, mutumin da Alh Affan ya sa aka tsare shi tsawon shekaru goma sha takwas. Mahaifiyarsu wacce aka ce sunanta Haj Kubra Hammad Yusuf, ta bar Yobe tare da jariran twins ɗinta, Sameera da Laila, sakamakon korar kare da ita uwar mijinta da yan uwansa suka yi mata sanadiyyar ɓacewar Adam. Wannan shi ne bayanan ranka ya daɗe, ina kuma kyautata zaton Matarka Laila ɗiyar Adam Kibiya ce."
Areef ke sauraron dogon saƙon murya da Ma'aruf ya aikomasa ta whatsapp bayan dogon rubutun da ya yi mishi bai samu ya duba ba. Lokaci guda zufa ya jiƙa shi. Ya saurara ya kuma karanta don gani yake tamkar bai ji daidai ba. Ya buɗe sababbin hotunan Adam Kibiya da Ma'aruf ya aiko mishi ya ƙurawa Adam idanu. Ya hangi Sameera a fuskarsa, haka kuma ya hangi Laila. Kamannin tas a sama fuskarsa.
Miƙewa ya yi tsaye yana safa da marwa a ɗakin, wayar ya ɗauka ya ƙara kiran Ma'aruf. Ko sallamarsa bai amsa ba ya ce,
"Kana da tabbacin duk abin da ka faɗa min hakane?"
"Komai sai da na yi bincike ranka ya daɗe. Ba na tunanin akwai ƙarya a zancen nan."
Idanun Areef nan da nan suka sauya kala. Kansa har wani sarawa ya hau yi. Murya a dusashe ya ce,
"Nagode, i will call you back."
Daga nan ya katse ya ajiye. Yanzu ya zai yi? Babban abinda ya rikita masa lissafi bai wuce tunanin to wace ce ya aura ba.
Ya tuna da sunan Laila aka ɗaura aure, ta ce masa Sameera nickname dinta ne, Laila ne real name ɗin. Don haka ya kira ta da Laila gaban kowa nasa ma.
'If she is Laila, then where is Sameera?'
Ya jefawa zuciyarsa tambayar.
'Ko ta rasu ne bayan abin da ya shiga tsakaninku? Ko ta rataye kanta ne ma? Idan kuma ita ce ka aura fa ba Laila ba?'
Duka tambayoyi ne da ba shi da amsarsu sai ma ƙarawa kai damuwa da ya yi.
Daƙyar ya miƙe ya shiga banɗaki don daman wanka zai yi ya kwanta. Gajiyar da ya soma ji ma sai ya nema ya rasa. Ɓacin ran da maganganun Laila suka haifar masa, su ma sun yi ɓatan dabo, yanzun ya shiga ruɗani, ruɗani mai yawa.
Koda ya yi wankan ya sanya fararen pyajamas ɗinsa. Kasa kwanciya ya yi, neman amsoshin tambayoyinsa yake. Zumbur kawai ya miƙe daga saman gadon ya kunnen bedside lamp ɗinsa. Sumar kansa ya shafa, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa. Babban ƙullin da yake son warwarewa bai wuce na fahimtar Laila yakr aure ko Sameera ba. Da wani tunani ya faɗo a ransa, bai ba da damar ya yi tunani na biyu ba, kawai ya yanke hukuncin da ya zo ransa. Ya kashe fitilarsa ya zura ɗan flat takalmin da ke haɗe da pyajamas ɗin ya fice daga ɗakin.
***
Gajiya, tunani da damuwar da ba su bari ta runtsa a kwanakin nan ba, su ne suka yi sanadin da a yau din da ta ji ta fara ɗana baƙin ciki a zuciyar Areef, bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita. Don haka ba ta ji motsin buɗe ƙofar da rufewa ba, kamar yanda ba ta ji motsin hayowarsa kan gadon da buɗe bargon da ta rufa da shi sakamakon sanyin AC ba.
A hankali ya fara shafa ta tun daga kafafunta har ya ƙaraso tudun ƙirjinta. Ya zo ne domin bambance abubuwa da dama a yau, ba da niyyar sha'awa ba. Sai dai nan ɗin da hannayensa suka kai, ya ji ya taɓa su kai tsaye ba tare da wani abin kariya ba kamar rigar mama. Ya ɗimauce, ya kuma shiga yanayin da tunda ya zo duniya, ban da wancan kuskuren da ya afka ba a hayyaci ba, bai taɓa jin irin na yanzun ba. Wannan kai hannun da shafar ne ya sa Laila motsawa, farko ji ta yi tamkar mafarki, kamar kuma ba da gaske ba, can da ta ji hannaye biyu damƙe da ƙirjinta duka biyun, sai ta ware idanunta a tsananin gigita. Daga yanayin yanda ta motsa ya ba shi tabbacin farkawarta ga uwa uba hasken fitilar gefen gadon da ba ta kashe ba. Idanunsu ya shiga cikin na juna, ta tsorata da babban lamarin da ta ga nasa ƙwayar idanun a ciki, hanjin cikinta suka kaɗa. Wannan ba Areef ɗin da ta sani mai zuwa wurinta ba ne, wannan wani daban ne mai ƙananan idanu jajaye cike da jaraba. A gaggauce ta sa hannayenta biyu a ƙirjinsa da nufin hankaɗa shi, sai dai kamar motsin ma ƙara tayar da hankalin Areef ya yi. Ta buɗe dukkanin bakinta za ta kwara ihu, ba ta yi zato ba kawai ta ji ya sakar mata nauyinsa a jiki sannan ya haɗe bakunansu wuri guda.
©Rufaida Umar