SIRRIN ZUCIYA

Chapter four

by @aysharano22

Kamar jira ake su fara tafiya, wayarshi dake ajiye kan dashboard ta fara ringing. Dubawa yayi sai yaga Bro🤍 akan screen. Connecting yayi da aux din cikin motar before yayi picking yana cewa

“Haan bol.”

Daga ɗaya ɓangaren wanda ya kira ɗin yace

“Oh come on Ayaan, how many times kakeso in faɗa maka am not Indian like you, am a Nigerian so kayi min mgn da either Hausa ko Yoruba don sune kaɗai yaren da na iya.”

Tsaki Ayaan ya saki jin yanda baya gajiya da mashi wannan complain duk da cewa ƙarya yake, yana jin Hindi maidawa ne kaɗai bai iya sosai ba amma duk abinda aka faɗa yana ji kuma yana ganewa. Kawai iskanci ne yasa duk yayi mashi mgn dashi sai yayi wnn complain.

Bari yayi ya gama complain ɗinshi sannan yace

“Ok Mr Nigerian, can you plss tell me why you called cox am driving?”

Daga ɗaya ɓangaren aka ce

“ka ‘dakko Pookie daga school?”

Yace

“Yeah na ɗaukota, gamu a hanyar gida.”

Kafin na ɗaya ɓangaren yayi mgn Pookie ta rigasu da cewa

“Uncle Lee!”

Sai da Ayaan ya runtse idanuwa sbd da ƙarfi ta faɗi sunan. Shima kanshi wanda ta kira Uncle Lee ɗin cewa yayi

“Arey yaar Kiara do you want to destroy my ear?”

Dariya sosai ta shiga yi tace

“Maaf kijiye Uncle Lee.”(forgive me uncle Lee)

Ɗan bata rai yayi daga can inda yake kmr tana gabanshi ne yace

“So you are also speaking to me in Hindi?”

Rufe baki tayi tare da ware blue eyes ɗinta akan babanta dake driving tace

“Sorry my Uncle Lee.”

Murmushi Lee ya saki jin wai shi yarinyar nan zata ma dadin baki yace

“It’s ok my princess... now tell me, me kikeso in zo maki dashi?”

Da saurinta tace

“Uncle Lee na yaso Popsicle and my plantain chips ya gama.”

Dariya sosai Lee ɗin ya shiga yi mata ta cikin wayar sbd yaren da yaji tayi yace

“Kiara inaso ake cewa ba nayaso ba... and when something has finished sai ace ya ƙare not ya gama.”

Dariyar itama ta shiga yi ma kanta tana kallon Ayaan da shima dariyar hausan nata yake. Shi har yanzu ya kasa gane soyayyar dake tsakanin Kiara da Hausa language, cox yanda take son yaren yana jin ko Hindi data iya sosai bata so kmr haka.

Yana jin wani sashe na zuciyarshi yana ce mashi

“Dole ta so Hausa sbd yaren mahaifiyarta ne.”

Nan da nan yayi fatali da tunanin don ko kusa baya son ko tuna abinda ma zai sashi tunawa da ita balle tunanin yayi tsayi.

Daga can ɓangaren bayan Lee ya gama dariyarshi yace mata

“Don’t worry I’ll get them for you.”

Da saurinta tace

“Thank you my Uncle Lee.”

Yace

“Welcome Miss Agnihotri.”

Dariya sosai take yi tana jin daɗi yace mata Miss Agnihotri don yanda take son a kirata da haka ko Kiara da yake sunanta bata so kmrshi.

Sai a sannan Ayaan yasa baki cikin mgnr nasu yana cewa

“Zaka dawo gida da wuri ne?”

Lee yace

“Gsky ba lallai ba.”

Gyada kai yayi before yace

“Alright then we’ll see at home.”

Lee ya amsa mashi da

“Yeah that reminds me, Linda called earlier... wai bazata samu shiga gym ba yau sbd bata da lfy.”

Shiru Ayaan yayi kmr ba zai ce komai ba sai can dai yace

“And who will manage the gym?”

Lee yace

“I called Victor to take over... yana can ma tuntuni.”

Kai Ayaan ke gyadawa yace

“That’s okay... sai ka faɗa mata ba sai ta damu kanta ta dawo da wuri ba, ta bari ta gama samun lfy tunda Victor yayi taking over.”

Murmushi Lee ya saki sbd duk duniya a yanzu bayan Kiara babu macen da take samun pity da kuma kindness ɗin Ayaan kmr Linda, wacce ta kasance itace take managing gym ɗinsu.

Yasan kuma duk sbd Kiara ne cox itace take kula musu da ita duk abubuwa suka musu yawa ko kuma duk wani abu ya taso wanda zai zama duk su biyun basa gida to Kiara zata kasance tare da ita a gym har sai sun gama abinda suke sun dawo.

Tana sonta sosai kuma bata taɓa yi mata wani abu na mugunta ko na rashin ganin idonsu ba shiyasa tayi gaining trust ɗin Ayaan. Duk da cewa yana da trust issues amma ita dai yana ɗan yadda da ita tunda har yake iya barinta da ’yarshi.

Amma fa ko a ina yake indai yasan suna tare to bini-bini zaka ga ya hau duba CCTV cameras ɗin cikin gym ɗin da yayi connecting da wayarshi. Nan zai ga komai da suke yi kuma bai taɓa ganin abinda bai yadda dashi ba shiyasa har yanzu yake iya barinta tare da ’yarshi.

Jin shirun yayi yawa Ayaan yace

“Wnn da kayi shiru I hope cat did not got your tongue.”

Tsaki Lee ya saki yana ɗan girgiza kai yace

“Look I don’t have your time now... see you at home... bye.”

Yana gama faɗan haka bai jira amsarshi ba yayi disconnecting kiran. Shima Ayaan maida tashi wayar yayi ya ajiye inda take.

Kmr jira Kiara keyi su gama wayar tace

“Appa what happened to Aunty Linda?”

Ɗan kallonta yayi for some secs before ya maida idanunshi ga tuƙi yace

“She’s just a little sick... but she’ll be fine in no time... don’t worry.”

Murmushi ta saki tana gyada mishi kanta tace

“I wish her a very speedy recovery... may she get well soon.”

Hannu yakai ya shafa kanta yana duban murmushinta dake sanyashi faɗuwar gaba sbd irin na mahaifiyarta ne sak yace

“Ameen Kiara... muahh.”

Ya ƙarasa mgn tare da hura mata flying kiss itama tayi mishi the same daga nan kuma ya maida hankali ga tuƙinshi.

Ba su suka isa gida ba sai bayan kusan one and half hour sbd traffic daya riƙesu cikin gari. Ayaan sai tsaki yake yana duban time, shi har yanzu ya kasa sabawa da wannan traffic ɗin na Lagos.

Jikin gate ɗin wani ɗan madaidaicin building yayi parking. A jikin wall ɗin wurin akayi drawing all sorts of gyming machines sannan in italics aka rubuta Get Fit With Us, kana gani dai zaka gane gym ne wurin.

Buɗe motar yayi ya fito ya buɗe gate sannan ya koma cikin motar yaja ya shiga da ita cikin ɗan madaidaicin compound ɗin. Daga can gefe yayi parking motar yabar ɗan space sbd mutane masu shige da fice a wurin.

Tun daga kan ƙofar shiga gym ɗin zuwa gaba ɗaya front view ɗinshi is made up of glass, don haka kana iya hango yanda mutanen dake ciki kowa nata workout ɗinshi, har wani ɗan sound ne ke tashi na music da suka kunna a ciki.

Ayaan ya saki tsaki daidai lokacin da yake fitowa daga cikin mota shiyasa shifa ko kaɗan baya son harka da Victor ɗin nan sbd shegen son jin music gareshi kmr ya haɗa jini da Dujal, duk yabi ya cika musu wuri da hayaniya.

Sai da ya fara ɗaukan school bag da lunch bag ɗinta ya rataya a left shoulder ɗinshi, sannan ya buɗe side ɗin da take itama ya ɗauketa ya rungume da right hand ɗinshi don tuni tayi bacci. Dama duk traffic ya riƙesu sai dai aga tayi bacci itama har yanzu ta kasa sabawa da traffic ɗin.

Wani lungu yabi wanda zai sadashi da bayan building ɗin bayan yayi locking motar. Yana zagayawa kuwa sai ga wani staircase ta wurin. Nan ya shiga takawa har sai da ya haura sama sannan ya zaro key daga aljihu ya shiga ƙoƙarin buɗe ƙofar dake wurin har yanzu kuma Kiara na rungume a jikinshi.



Masu buƙatar siya zasu tura 500 zuwa 0013569116 Aisha Ahmad Tijjani Jaiz Bank, sai a tura min receipt ta ***.










Rano✨