BARRISTER SUHAIL

42

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----42 

Suhail ya jima riƙe da wayar a hannunsa bayan Hafsat ta katse kiran 

Kalaman ta ne kawai suke yawo a cikin kansa

A hankali ya ajiye wayar tare da lumshe idanunsa

Karfe goma na dare ya nuna bathroom ya shiga yayi kwanka ya saka wasu white pajamas ya nufi part iman 

Kai tsaye ya nufi bedroom ya tattar da ita tsaye bakin closet tana jera kayan ta 

waje ya samu ya zauna ta ɗago kai ta kallesa 

suhail ya jima yana tunanin ta inda zai fara ba iman hakurii har ta kusa kammala aikin gaba daya 

"Iman Na san ban cancanci ki saurare ni ba a yanzu amman nazo na baki hakuri akwai abinda ya faru Na cuce ki Na yi sakaci da haƙƙinki Na sa kina jin ke kaɗai ce alhalin kina da miji 

Ya matso kusa da ita

bazan tursasaki akan dole ki yafe man ba amman ina so ki bani dama a karo na biyu na wanke laifina a wajen ki 

Hannunta ya kamo cikin nutsuwa ya ɗora a ƙirjinsa.

“Feel it…”

Muryarsa ta yi ƙasa.

“Feel how my heart is beating for you.”

Idanunsa suka sauka cikin nata.

“I love you, Iman.”

“Wallahi ban taɓa sanin irin muhimmancin ki a rayuwata ba sai da na fara ganin nisan dake tsakanina da ke.”

“Ke alkhairi ce da mahaifina ya zaɓa min.”

“Ke ni’ima ce daga Allah.

“Kuma idan akwai wanda ya fi ni son ki a duniya, su ne Malam da Ammi kawai"

Hawayen da yake ƙoƙarin dannewa suka cika idanunsa

karon farko da iman taga hawaye a fuskar suhail zuciyar ta yi rauni 

Hawayen da take dannewa suka zubo.

Wani ɓangare na zuciyarta yana son yafe masa.

Wani ɓangaren kuma yana tuna mata dararen kuka, kaɗaici da rashin kulawar da ta sha.

Hakan yasa ta kasa ɗaukar kowace shawara

Tun daga ranar Suhail ya fara ƙoƙarin gyara komai

Ya fara raba kwana cikin adalci.

Idan ya yi kwana biyu a wajen Zeenah, zai yi kwana biyu a wajen Iman.

Sai dai abin mamaki…

Duk lokacin da yake tare da Iman zuciyarsa tana samun natsuwar da bai taɓa samu a ko’ina ba

Amma a wajen Zeenah kuwa
Kullum wata sabuwar matsala
Kullum wata sabuwar ƙorafi
Kullum wata sabuwar gardama
Har ya fara tambayar kansa ko wace irin rayuwa ya jefa kansa ciki.
Shi kansa bai san lokacin da ya fara gajiya da halayen Zeenah ba

Amma abu ɗaya ya sani

A hankali zuciyarsa tana komawa ga matar da ya taɓa watsi da ita wato iman 

wata kula ta musamman iman ke samu daga wajen suhail fiye da wanda yake yi mata a baya 

zeenah tun tana damuwa har ta daina ta lura da Suhail kullum hankalin sa na wajen iman duk da ba wani sakin jiki tayi da shi ba

tun zeenah na neman wayar yusrah har ta hakura gaba daya zaman alfarmar kawai tare da Suhail wanda yasha fada mata yana mata ƙara ne akan soyyayar data nuna masa a  baya 

a na haka har aka shafe sama da wata shidda suhail ya fadawa matasan akan su shirya zasu je kaduna kaduna duba mami bata da lafiya farin ciki ya kasa boƴuwa a fuskar iman zata je kaduna taga Ammi da malan Kimanin wata takwas kenan rabon da ta sasu a idonta duk da ba wani nisa ke tsakanin su ba

yau Assabar a yau ne aka shirya tafiyar zasu kwana daya su dawo Lahadi saboda aikin Suhail

suhail ya fara fitowa cikin sani navy blue din yadi yayi matukar kyau zeenah ta biyo bayansa sanye take da wani white laces dinkin doguwar riga ta yafa wani dan karamin mayafi a samar kanta tun daga nesa Suhail dake jikin mota ya hango ta koda ta karasa ya ce"Zeenah look at you dress a haka zamu fita"

"Suhail mi shiga tayi kuma,miyasa kullum kake ƙoƙarin sai ka fito da laifina ne"

shiru Suhail yayi bai kara cewa komai ba ya na kallo ta buɗe front seat ta shiga 

iman ta fito daga karshe sanye take da hijab ash color har kasa jaka da takalmin na Companin bella sun dace da shigar ta ba ƙaramin kyau tayi cikin shigar ba duk da ba wata kwaliya tayi a fuskar taba

 bayi mamakin ganin Zeenah zaune a front seat ba hakan yasa ta buɗe back seat ta shiga suhail ya ja motar suka bar gidan 

cike da nutsuwar daya saba yake tafiya kan titi gaba daya hankalin sa yana kan Iman da tun shigowar take game cikin wayar ta 

zeenah kuma sai taunar cingum dinta take fuskar nan ba walwala

koda suka shigo garin Kaduna kai tsaye Suhail yayi parking kofar gidan su horn yayi baba haladu ya bude masa gate lokaci guda ya ma sa sannu da zuwa 

a compound din gidan yayi parking tare suka nufi part din mami suhail na gaba zeenah na biye dashi a baya sai iman a chan nesa 

a haka suka karasa cikin falon mami na zaune tare da mai aikinta tana mata dressing a ciwon da taji a kafa abinka da mai diabeties gaba daya kafar dai ruwa take fitar wa daga cikin ta"

mami na ganin Suhail da zeenah ta fara murmushi tare da gyara zama lokacin guda mood din fuskar ta ya sauya ganin iman a bayan su 

waje suka samu suka zauna Suhail ya fara gaishe ta tare da yi mata ya jiki tun sanda taji ciwon ta kirasa ta fada masa lokaci zuwa lokaci yake zuwa dubata dalilin na kawo su zeenah kenan su duba ta 

zeeenah ta daga baki kamar bata so "Ina wuni"

washe baki mami tayi "lafiya qlau zeenah ya gidan naki"

"lafiya kawai ta ce ga cigaba da dan na wayar ta"

Iman dake gefe ta ce"Mami ina wuni ya jikin naki"

yi tayi kamar bata ji taba Suhail ya ce"mami Iman na magana"

sai lokacin ta dago ido tun shigowar ta kalleta "ita da ta gaida ni yadda taga dama bata yi laifi ba kenan sai ni da ban amsa ba idan uwar ta ce zata gaida a haka tana magana ciki ciki sai kace Dole"

Mamaki ya kama Suhail ganin Zeenah ya kamata mami taga laifi yadda ta amsa mata  gaisawa cike da ranin data saba amman ita da yake yar Attajiri  ce Bata laifi sai iman dashi bai ma ga laifin da tayi ba"

shiru ya ratsa falon ba wanda ya sake magana sai karar taunar cingum din zeenah bayan an gama wa mami dressing ta kalli zeenah "muje ciki ko kici Abinci ko"

ta kalli jummai mai aiki ta ce"ki kawo mata breakfast bedroom"

haka ta tashi tana dingisa kafar zeenah tabi bayan ta sai ya tsina fuska take kamar mai ƙyamar wani abu 

suhail ya kalli iman da tuni hawaye ya cika idanunta ya ce"kije dakin Aunty Fauziya ki huta anjima sai nazo na kai ki gidan kiga malan da Ammi"