BARRISTER SUHAIL

43

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----43

Aunty Fauziya ta ji dadin ganin iman kullum idan Suhail yazo kaduna sai ta tambaye sa lafiyar ta 

ta tarbeta cike da kulawa ta hado mata breakfast a cikin wanda tawa abba kafin ya fita tare suka ci da Suhail dan shima baiyi breakfast din ba suka fito 

har yamma Iman na part din aunty Fauziya tare suka girka abincin rana duk tayi shara tayi mopping bayan sun gama cin abinci rana iman ta hada kwanunka zata wanke aunty Fauziya ta shiga Kitchen da sauri ta karasa wajen ta amshi plate daga hannun ta"iman ke baki gajiya ne,ki barshi zanyi da kaina"

murmushi Iman tayi ta ce"Aunty da kin bari na ida ma"

"a'a kije ki huta kafin Suhail din ya dawo ku tafi"

tana fitowa falon aunty Fauziya Suhail na shigowa kallo ta yayi ya ce"kin shirya mu tafi"

dakin aunty Fauziya ta koma ta dauko hijabin ta tayi  wa Aunty Fauziya  sallama suka wuce 

babu wanda yayi magana a cikin su motar har suka karasa wata babbbar plaza dake kan hanya kallon sa tayi cikin alamun tambaya kashe nata ido guda yayi ya ce"muje ciki ko"

tana biye dashi a baya har suka karasa shagon siyar da waya suhail ya samu waje ya zauna ya iman ya ce"take the one You like"

iman ta kallesa sa "ni"

"Eh,ke"

"yaya Suhail amman ai ina da waya"

"Dama bance baki da ita ba inaso ki riƙe wayar da mijin ki ya siya maki"
Murmushi tayi ta nufi wajen wayoyin

Ta tsaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

Ita ba wai sanin kansu tayi ba hakann yasa ta ƙasa zaba

Suhail ya lura da hakan da kanshi ya tashi ya zabar mata iphone 15 pro max 
 
ya biya kudin tare da kayan waya gaba daya Aka mishi packaging

Bayan sun fito daga shagon

Suhail ya ja motar suka ci gaba da tafiya 

ganin yabi wata hanyar daban bata gidan Malan ba ta dago kai ta ce"yaya Suhail ba gidan Malan zamu je ba"

"Suhail yace inaso ki rakani wani waje"
bata kara tambaya 

tafiyar mintuna goma sukayi yayi parking kofar wani gida

a buɗe ya samu kofar hakan yasa suka shiga kofar palor yayi knocking meerah ta bude masu kofa

Idanunta suka sauka kan Suhail matsawa tayi suka shigo tare da Iman suhail na riƙe da hannun ta

aunty Aisha ta fito daga Kitchen tana ganin Suhail ya washe baƙi "Barrister yau manya baƙi gare mu kenan"

murmushi yayi suka zauna kan kujera

aunty Aisha ta ƙaraso ciki 

suka gaisa cike da sakin fuska ta kallli iman ta ce"ya gidan naku"

ƙasa tayi dakai ta ce"lafiya qlau Aunty"

"suhail kunzo garin kenan,ina zeenah"

"tare muke tana gidan Mami"

aunty ta ce"ka kyauta suhail naji dadin zuwan ku"

ta kalli meerah da ta bada attension dinta gaba daya kan kallo ta ce"Meerah baki ga Suhail da iman bane"

hade rai tayi ta ce"nagansu Momy"

"meerah haka na zakice bazaki gaishe su ba"

"yaya Suhail ina wuni" ta faɗa kamar mai shirin fashe wa da kuka 

"lafiya Alhamdulillah"

ta juya momy ta ce"ita iman din bazaki gaishe taba"

wata irin kalar harara ta wurga Imann irin bata isa din nan ba ta ce"Momy,i should greet her fa kika ce while i'm elder than her"

momy ta ce"umarni nake baki ko haihuwar ta kikayi ai ya kamata ki gaishe ta tunda yayanki take aure"

turo baki tayi ita a dole baza ta gashe da iman ba 

suhail ya ce"Aunty ki rabu da ita kawai"


ƙwafa aunty Aisha tayi bataji daɗin abinda Meerah tayi mata ba gaban kowa sai ta nuna bata isa da ita ba kenan 

kallon tayi a karo na biyu "ki tashi ki kawo masu drinks idan shima bazakiyi sai na dauko masu marar mutunci kawai"

Suhail ya fara miƙewa ya ce"a'a ki barshi ma tafiya zamuyi"

"da wuri haka"

"Eh Akwai inda zamu biya ne"

har bakin gate ta masu rakiya ta dawo ciki ta samu meerah Cikin faɗa ta ce"Ameerah yanzu abinda kike kin kyauta kenan ko"

shiru tayi ba tare da tayi msta fada ba aunty Aisha ta mata fada sossai daga karshen ma ta tashi ta bar mata falon 

suhail ba kara tsayawa ko ina ba sai kofar gidan Malan bayan yayi parking ya jima yana kallon iman kafin ya dauko wayar ya mika mata masa tayi tana juyata a hannu 

"thank You so much my councel"

daga sama yaji sunan da ta kira sa da shi 

Wani lallausan murmushi ya bayyana a fuskar Suhail.

Murmushin da rabon da Iman ta gani tun kafin shigowar zeenah Rayuwar su 

Iman tayi maganar ba tare da kunya ba 

suhail ya ce"mi ki kace"

kalllon sa tayi ido cikin ido "my councel"

indai har iman zata cigaba da kiransa da wannan sunan tabbas yanzu ne ya fara faranta ta mata 

cikin kashe kudin da ya yake ma zeenah ko kwatar su bai kashe wa akan Iman, Amman she is wondering yadda tayi appreciating dan kawai ya siya mata waya

katse mata tunani tayi da cewa"yaya Suhail please ka barni na kwana anan"

jim yayi kafin ya ce"naji zan barki under one condition"

"shiru tayi tana sauraren sharadin"

"Sai idan kin yarda zanzo muci Abinci dare tare ki dafa min dambu da zogalen na da iske ki kina yi ranar nan"

dariya tayi ta ce"zan dafa maka"

ta bude kofar motar ta fita tana daga masa hannu har ya bar layin 

da sallama ta shiga gidan su babu kowa taskar gidan hakan yasa ta nufi daki Ammi 

Ammi na zaune a kan kujera da gudu iman ta faɗa jikin ta cike da murnar ganin Mahaifiyar ta

Ammi ta janye ta daga jikin ta ganin tana ƙoƙarin karya mata kafa 

Iman ta turo baki cike da shagwaba "ammi shine zaki ture ni"

"to Iman ba ba dole kina ƙoƙarin karyamin kafa"

Iman ta gaishe da ta cike da girmamawa da kuma kewar ganin junansu 

hira suka fara Ammi ta ce"Ina abokiyar zaman taƙi"


iman har ta manta da wata zeenah ban da yanzu da Ammi ta tambaƴe ta hade fuskar tayi ta ce"tana chan gidan su yaya Suhail,maman sace bata da lafiya shine ya kawo mu fa duba ta" 

Ammi ta ce"subuhanallahi miya same ta"

Iman idan ta ce ga Abinda ya sami mami tayi karya hana rantsuwa taga ana mata dressing a kafar ta hakan yasa tayi tunanin ko ciwo taji"


iman ta ce "taji ciwon ne a ƙafar ta Amman da sauki" 

"Allah ya bata lafiya,ya kamata aje a dubata"

gaban iman ne ya fadi sakamakon furucin Ammi na zata je duba maman suhail,duk abubuwan da mami keyi mata bata taɓa fadawa wa kowa ba ta bar Abin ne kawai a ranta 

bataso Ammi taje gidan a mata irin abinda ake yi mata batasan kowa a danginta ya gane Mami bata santa ko Suhail bata taɓa gaya masa ba duk da ma wasu abubuwan anayi a kan idon sa 

hakan yasa ta ce"Ammi bafa wani ciwo bane,tama warke"

murmushi Ammi tayi ganin yadda Iman ta nuna bata so taje




IMAN DA SUHAIL FA LOVE SAI GABA YAKE SHIYASA BA A SHIGA TSAKANIN MATA DA MIJI🤣😩KUNA ZAUNE ZASU BAKU KUNYA KAMAR YADDA IMAN TABA FANS DIN TA🏃🏼‍♂️🤪


AYI COMMENT AYI LIKES HAKAN KE KARFAFA MANA GWIWA MU CIGABA DA SAMBADO MAKU UPDATE 

MUNA DA UZURI AMMAN HAKAN YASA KULLUM MUKE KOKARIN TUROWA BADAN KOMAI BA SAI DAN MU FARAN TA MAKU AMMAN KU KASA BADA MINTI UKKU WAJEN YIWA MARUBUCI COMMENT HAKAN ZAI SA MARUBUCI YA RAGE. KAIMI ZAIYI TUNANIN KO LABARIN BAYA BURGEWA

KHADIJA WRITES TAKU CE 🤟🏼