GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 21

by @nusybee143

Page 21



Washe gari Muyassar ya dawo,sun daɗe suna hira kafin ya yi mata sallama, Shaheeda tana murmushi ta ce"to yaya!

Yanzu sai yaushe?"

Muyassar ya ce"to kin ga dai yanzu karatu zan koma in sha Allah,ba zan ce kai tsaye ga lokacin da zan zo ba,amma kuma in sha Allah zan yi ƙoƙarin sake zuwa very soon,ke dai ki dage da karatu kawai, in sha Allah wannan little engineer ɗin sai ta zama hasken da zai haska Maliya family"

Murmushi sosai ta yi,ta ce"yayana abin alfaharina, Allah ya tabbatar da bakinka,ina matuƙar son na ga na amsa sunan nan"tana murmushi tana juya kai ta ce"zan buɗe Company na kaina,zan zama shahararriyar yar sarrafen computer,zan ƙirƙiri apps da yawa waɗanda za su taimaka a harkar internet,kuma....."

"To sarkin soki burutsu, Allah ya taimaka ya ba da sa'a kawai, I can't wait na ga wannan ranar "ya ƙarasa yana murmushi 

Ba su daɗe ba sosai suka yi sallama,ta koma hostel shi kuma ya tafi 

Kwana biyu zuciyarta ta kasa sukuni saboda wannan matashin Guy ɗin da ta gani, wanda tun ranar da Muyassar ya zo bata sake ganinsa ba 
Ta rasa yadda aka yi zuciyarta ta damu da tunaninsa,abin yana matuƙar damunta, har abin yake so ya shafi karatunta 

Kusan watanni uku kenan, karatunsu ya miƙa sosai,kuma suna daf da fara jarrabawar second semester, wadda daga ita ne zata tafi hutun session,zata koma Nigeria,gaba ɗaya yanzu bata da nutsuwa, kullum cikin karatu take da nazari,ita ce searching, practical, group discussion da sauransu 

Tana zaune a inda suke zama don karatu, hankalinta ya raja'a sosai,sai ga wasu samari sun zo sun zauna a kusa da ita suna kallonta cikin sigar rashin mutunci 

Sau ɗaya ta kalle su,ta cigaba da abin da take yi, ɗaya daga cikinsu ya ja mayafinta, ɗayan kuma ya ja handout ɗin hannunta ya yar a ƙasa, ganin abin nasu ba na ƙare bane sai ta miƙe,amma sai suka hana ta wucewa 

Kuka ta fashe da shi,suka kama dariyar izgilanci suna ta dungure mata kai,ta durƙusa a wajen tana kuka 

Ji ta yi sun yi shiru,tana ɗagowa ta ganshi yana miƙa mata hannu, ba tare da ya jira komai ba ya kama hannunta ya ɗaga ta suka bar wajen,bata yi masa musu ba ta bi shi tana kallonsa 

Wani waje dabam ya kai ta ya zaunar da ita,ya dube ta fuskarsa babu walwala, cikin yaren Dutch ya ce"ki rinƙa kiyayewa,ba su da kirki,za su iya yi miki wani abu da bai dace ba,ke mace ce,kar ki sake zuwa can"

Jinjina kai ta yi a hankali, cikin sanyin murya ta ce"na ɗan kauracewa mutane ne saboda na samu damar karatu sosai"

Shafa kanshi ya yi yana lumshe kyawawan idanunshi,ya ce"ya kamata ki kiyaye,ba a ko'ina za ki iya zama ba,sai anjuma"ya juya zai tafi,ta yi masa murmushi tana faɗin "na gode"ya ɗaga mata hannu ba tare da ya yi magana ba ya bar wajen

Duk da yadda tunanin Guy ɗin da ko sunansa bata sani ba ya so ya hana ta sukuni amma ta dage da ƙarfin hali ta cigaba da karatunta,har ƴar rama ta yi,su Alice da Olivia har sun gaji da tambayarta me yake damunta 

Bayan sun kammala jarrabawa aka yi bikin fitar yan final year,an zaɓi wadanda za su yi speech a cikin ragowar ajujuwan,level one,two da three,a cikin waɗanda aka zaɓa a level one har da ita

Speech ta yi mai kyau akan abin da ya shafi course ɗinsu na software engineering, kusan kowa da yake wajen sai da ya burge shi, gashi da turanci aka yi, English accent ɗinta ya burge kowa,ta sha tafi da hotuna kala kala

Abin da ya bata mamaki a waɗanda suka yi speech na ƴan level three har da wannan matashin,wanda ta ji cikakken sunansa ARNOLD LIAM LAMBERT, wanda hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa ɗan ƙasar Belgium ne,ko kuma mazaunin ƙasar Belgium,a takaice dai haifaffen ƙasar ne

Shima ya yi speech mai kyau, yadda yake magana cike da jan aji da rashin son hayaniya ya yi matuƙar burge ta,don haka itama sai ta tsinci kanta a cikin masu tafa masa

An yi biki mai kyau,an ci an sha,an tashi taro kowa yana cike da farin ciki 

Tana zaune a inda take zama sau tari, musamman idan tana karatu,yau ta buɗe wayarta tana chatting da yayanta Muyassar da Ummeenta,tana sanar musu da zata koma gida gobe,ta ji an ce "Hi!"

Ɗagowa ta yi da sauri ta kalle shi,ya yi mata murmushinsa mai kyau,yana faɗin "good afternoon HERMOSA!"

"HERMOSA?"ta maimaita tana kallonsa,ya sake yin murmushi ya ce"HERMOSA means beautiful in Spanish,can I have a seat?"bata yi musu ba ta nuna masa waje don ya zauna,ya zauna yana kallonta 

Cikin harshen dutch ta gaida shi,ya amsa yana murmushi,shima ya gaishe ta,ta yi murmushi tana kallonsa,ya ce"Good speech!"

Da harshen dutch ta ce"kai ma ai ka yi magana mai kyau da ma'ana, tunda da alamu wata shekarar ku ne wadanda za'a shiryawa wannan bikin"

Murmushi ya yi ya ce "na ji an ce ke ce mai overall a set ɗinku,ina taya ki murna"

Kallonsa ta yi sosai ta ce"ya aka yi ka sani?"

Ya ce"a set ɗinmu ni nake yin overall duk shekara,na kan bibiyi masu yin overall duk shekara, wannan karon kuma sai ta faɗo akanki,na yi mamaki kasancewar ki yar Africa,hakan ya faranta min sosai,daga wace ƙasa kika zo?"

Kallonsa ta yi ta ce "kai ɗan africa ne?'

Ya jinjina kai ya ce"mahaifina ɗan ƙasar South Africa ne, mahaifiyata ce ƴar Belgium,sai dai saboda domestic violence da ya faru da iyayen nawa tun ban san kaina ba mahaifiyata bata taɓa kai ni South Africa ba,a takaice ma,ban taɓa zuwa Africa ba"

Shaheeda ta jinjina kai ta ce"Ni kuma haifaffiyar Nigeria ce,yar asalin ƙasar Nigeria "

Ya jinjina kai yana murmushi ya ce"ya yi kyau

Kenan ke ma za ki tafi ganin gida ne?"

Shaheeda ta ce"gobe ma nake so na bar ƙasar nan zuwa Nigeria, na gama shirya komai"

Ya jinjina kai ya ce"fatan alkhairi,zan iya samun numbernki?"tana murmushi ta saka masa,ji take yi kamar ta yi tsallen murna,kuma ta kasa gane dalilin hakan 

Washe gari jirgin su Shaheeda ya ɗaga zuwa Nigeria,farin ciki da ɗoki tamkar ta rufe idanu ta buɗe ta ganta a Nigeria,duk da bata so tafiya gaba ɗaya ba saboda sabon abokinta Arnold 

Tafiyar awanni bakwai ya kawo Shaheeda Nigeria daga Belgium, farin ciki kamar me don zata ga yan'uwanta,bata damu da yadda babu wanda ya zo daukarta ba,don Abba ba ya Nigeria,yana can harkokinsa na kasuwanci, Ummeey kuwa ba zuwa za ta yi ba ta sani, Muyassar ba ya ƙasar,a gidansu kuwa kaf babu wanda zai zo,don haka ko a jikinta ta hau taxi drop ta tafi gida 

Da ihun murna ta shiga gidan na su, Ummeey dai ta kasa ɓoye farin cikinta,ta tafi da gudu ta faɗa jikin Ummeey tana murna, Hajiya Jamila da ta zamewa Ummeey ƴar'uwa tana kallonsu tana murmushi,ta ce"ba'a ganmu bane ɗaliban turai?"

Murmushi Shaheeda ta yi,ya durƙusa tana gaida su gaba ɗaya, Hajiya Jamila tana murmushi ta ce"ya karatun?

Kin yi kyau abinki,kin murje kin yi jiki kamar ba ke ba, Belgium ta karɓe ki alhamdulillah"

Cike da jin daɗi Shaheeda tana murmushi ta ce "alhamdulillah, Mummy ai karatun nasu da daɗi ba kamar a Nigeria ba"

Hajiya Jamila ta ce "kar dai ki bari Salma ta ji ki,kullum a cikin complain take yi karatu yana ba ta wahala"

Dariya Shaheeda ta yi ta ce"oh su Hajiya Salma manya, Ummeey bari na shiga ciki na yi wanka"daga nan ta miƙe ta shiga don yin wanka 

Bayan ta kammala hutawa Ummeey ta umarce ta ta je ta gaida matan gidan, babu damuwar komai a ranta ta sanya dogon hijabinta ta fice daga sashen 

Sashen Hajiya Atika ta fara zuwa,a matsayinta na babba a matan gidan,da sallama ta shiga,ta yi sallama ya kai uku amma babu amsa,duk da tana kallon Hajiya Atika a zaune tare da yaranta Safwan da Malika 

Kutsa kai ta yi ba tare da damuwa ba,tana zuwa ta samu kujera ta kame ta zauna tana murmushi, kafin ta ce "sannu Ammi,ina kwana?'

"Wanene ya ba ki izinin zamar min a kan kujera?

Malama tashi min akan kujera"

Murmushi Shaheeda ta yi tana taɓe baki ta ce"Ni zuwa na yi mu gaisa,an daɗe ba'a haɗu ba

To ya muka same ku?ya yaran?ya gida?"

A kufule Hajiya Atika ta ce"ba'a gida ɗaya muke da uwarki Zainab ba? Je ki tambaye ta mana,ko kuwa mu uban naki ya sa ki raina?"

Shaheeda ta girgiza kai ta ce"Ni yanzu na girmi faɗa,na bar wa marasa abin yi,kuma hankali dai daidai gwargwado na yi,na gaishe ki,bari na yi nan"

Hajiya Atika ta ce"gwara dai ki tafi kafin na naɗa miki shegen duka anan"

Shaheeda ta dakata daga yunƙurin fitar da take yi ta ce"a da ba'a daki Shaheeda ba sai yanzu da ta zama mutum?

Ai mai dukan engineer Shaheeda a yanzu dai sai dai ruwan sama"ta sa kai ta fice tana waƙa 

Kai tsaye ta nufi part ɗin Hajiya Ruƙayya,tana zaune ita da ƙanwarta Arfa suna hira ƙasa-ƙasa,a ranta ta ce"munafurcin ya motsa kenan!"amma hakan bai hana ta kwarara sallama da ƙarfi ba

Da sauri suka ɗago suna kallonta fuska a ɗaure,babu damuwa ta ƙaraso parlourn ta zauna tana kallonsu tana murmushi 

"Barkanku da dare,ya na same ku?ina wuninmu?"

"Ke tsagera,iskancin da kike yi idan kin ga a baya na ƙyale ki wallahi a yanzu kika kuskura kika ce za ki yi mana wani rashin tarbiyya sai kin gane kurenki "

Taɓe baki Shaheeda ta yi tana yi mata kallon banza, kafin ta ce"ke yanzu idan banda abinki wane ya ce miki idan kika ce za ki dake ni zan tsaya kamar itace ina kallonki?

To kaf danginku babu wanda ya isa na yi masa wannan alfarmar don ki ji da wai

Ni fa zuwa na yi don na gaishe ku na gaya muku na dawo,don kun san yanzu duba handout ma da tunanin assignment kawai ya isa ya sa na manta Allah ya halicce ku a duniya"

Arfa tana yi mata kallon banza ta ce "karatu dai,ni wallahi ban yarda karatun ake yi ba,na fi zargin wata baɗalar ake yi da sunan karatu ana raina mana hankali "

Dariya Shaheeda ta yi har tana kwarewa, kafin ta ce"to ai gwara ni,sai da na fake da karatun sannan ƴan iska irinki suke zargina,kar dai ki manta a gabana aka fito da ke daga ɗakin gardi,kar ki manta na san abubuwa da yawa,don haka ki yi rayuwarki nima na yi tawa,idan ba haka ba kuma allura ta tono garma"tana kai wa nan ta miƙe don ficewa daga ɗakin kafin ranta ya ɓaci a yi mara daɗi 

Arfa ce ta yi wuf ta shaƙo ta,bata yi wata-wata ba ta sauke mata mari, sannan ta hankaɗe ta,ta fice daga sashen 

Ko da ta koma sashen Ummeey ma bata sanar da ita yadda suka yi da matan uban nata ba,ta cigaba da harkar gabanta 

Ta ji daɗi sosai lokacin da ta buɗe Whatsapp ɗinta ta ga Arnold ya ajiye mata message,ta yi murmushi ta yi masa reply,bisa Sa'a yana online, suka cigaba da hira, wadda galibi ta karatunsu ce

Washe gari ma Ummeey ta ce ta je ta gaida kakarta innayyo,bata yi musu ba ta je,amma baya sauya zani ba,don yadda suka saba wulakanta ta yau ma haka suka yi mata,ta ja tsaki ta fice daga parlourn 

Mummy ce ya finciko ta tana faɗin "ke!

Wa kike ja wa tsaki?"

Shaheeda ta yi murmushi ta ce"yi hakuri"sannan ta janye mayafinta ta fice daga parlourn 

Ko da ta koma gida ma bata yi wa mahaifiyarta batun komai ba, kamar dai jiya,ta cigaba da sabgoginta 

Tsawon kwanaki biyar da dawowarta kafin Alhaji Yusuf ya dawo,a tsakiyar gidan ta daka tsalle ta ɗane shi tana ihun murna,ya rungume ta cikin tsananin farin ciki da kewar ƴar tashi 

Hannunta ya kama suka nufi sashensa,matansa da sauran yaran suka rufa musu baya,matan kowacce da abin da take wassafawa a ranta 

Kamar yadda ya saba suka baje a babban parlourn shi da kuma yaranshi da matan ana hira,amma sai ya fi karkata akalar hirar ga ƴar gold ɗinsa Shaheeda, wadda ta taƙarƙare tana ta ba shi labarin karatunta da rayuwarta ta Belgium 

Ba su juma sosai ba suka amshi tsarabarsu kowa ya tafi,amma ban da Shaheeda da take sake buɗe sabon topic na hira 

Hajiya Ruƙayya da take da girki ranar ta dube su fuska a ɗaure ta ce"Alhaji ya kamata fa a ce ka sallami yarinyar nan, kowa ya tafi ita me take yi har yanzu?"

Kai tsaye Alhaji Yusuf ya ce"hira da ubanta mana"

Hajiya Ruƙayya ta ce"to sai ta tafi sai da safe ko?

Don gaskiya saboda wannan ƙatuwar yarinyar ba za'a shigar min lokaci ba,dama dai ƙarama ce sai na yi uzuri"





#Nusy_bee