MUTUWAR AURE...! BOOK 1

01

by @aishatouuu

________________

*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
***



***
_________________



_EPISODE 1_

*Bawa baya wuce ƙaddararsa, rashin uwa masifa ce babba a rayuwar ko wanne da, ɗan da ya taso babu uwa ne kawai zai gane haka, shi kaɗai yasan zafi da ciwon rashinta, musamman mace, macen ma yarinya ƙarama data taso cikin so da Kaunar iyayen ta kamar dai Asma'u,  (Husnan Baba), duk daɗin uwar riko bata taɓa kaiwa uwa ba, musamman in uwar tagari ce, amma inada tambaya gare ku masu karatu.*

               _Shi me yasa kalmar kishiyar uwa wato (Matar uba) ta zama kalma mafi muni a society musamman na Malam Bahaushe, da kuma kunnuwan ƴaƴan da suka rasa damar zama da iyayensu Mata, irin Asma'u?_
_Hakan hallaya ce ko dabi'a?_
     _Ko wacce mace a duniya tana iya amsa sunan Matar Uba, amma me yasa muke da mugunta akan ƴaƴan daba namu ba?_
_Shin lefin Matan Uban ne ko kuma na ƴaƴan Miji?_


_*Masu binciken hallayar ɗan adama wato ( psychologist) sunyi hasashen cewa Mata cassa'in cikin ɗari basa son ƴaƴan daba nasu ba.*_

_*Wani fasihin masanin sirrin Rayuwa yana cewa "baka sanin asalin ma'anar babu saika rasa, baka sanin darajar tashi tsaye saika faɗi......duniya tafi ƙarfin gari bare a kirata gida, tafiya akwai daɗi musamman inda kyakkyawan guziri, sai dai lokaci baya jira, Zamani bashi da amana, Zuciya bata da murfi kamar yadda idanun dake buɗe basu da shamaki, sai dai wani ruwan yafi ƙarfin kashe ƙishi, karka yarda da ƙaramin tunani dan Allah keda lokaci........*_


_NI KUWA A'ISHA NACE "ALLAH YA RABAMU DA GANIN RANAR MAKAUNIYAR NADAMA WATO (KARƁAR TAIMAKON WANDA MUKA ƘUNTATAWA)."_




2009

KANO STATE NIGERIA.

Rimin kebe.
Unguwa ce ta masu ƙaramin karfi, yawancin mutanen cikin ta talakawa ne da masu rufun asiri mawadatan cikin unguwar basu da yawa, a cunkushe unguwar take da gidaje da tarin mutane tako ina, hayaniya kuwa abun ba'a magana.

               Gidan Malam Abdullahi Mai Kano yana ɗaya daga cikin gidajen masu rufun asirin unguwar ta Rimin kebe. Ginin gidan rabi ne mai ɗauke da dakuna guda uku da shago a ƙofar gida, sai Kitchen da bayan gida, a tsakiyar gidan akwai shukar ƙatuwar bishiyar Dirimi da tayiwa gidan runfa gwanin sha'awa, wannan yasa duk ranar da ake ƙwalawa baka rasa inuwa da iska mai sanyin daɗi a gidan, a sumince gidan yake har ƙofar gida.

                   Yarinyar da gaba ɗaya bazata wuce shekara goma sha ɗaya ba ta tsallako titin ɗorawa ta shiga babban layin dazai maida ita gidan su, tafiya take a hankali hannunta rike da dan ƙaramin farin botikin falla data siyo koko aciki, tana tafiya tana jujjuya botikin, sanye take da wata doguwar riga ta atamfa Java sai hula baka wacce aka saƙata da zaran lilo, kusan rabin gashin kanta a waje yake saboda bata cusa gashin acikin hular ba hakan yasa kitson kanta ya barbazo.
Kafafun nan nata kuwa sunyi furu-furu da ƙura, tafiya take tana wasa da hannun botikin exactly yadda yara keyi in aka aikesu. 
                          A bakin ƙaton kwalbatin dake gabanta ta tsaya tana ƙare masa kallo, tunanin yadda zata tsallaka kwatar take saboda tanada girma sosai gashi babu katako a tsakiya bare tabi takai ta wuce, kamar dai yadda ake sakawa saboda yara irinta wanda bazasu iya tsallakawa da kansu ba sai subi ta kan katakon su wuce. 
Zama tayi a bakin kwatar tasa Botikin kokon ta a gaba tana ƙare masa kallo, a ƙalla takai wajan minti goma a zaune a wajen amma  babu wanda yazo wucewa bare tace ya tsallakar da ita, ta riga ta shigo cikin lungunsu gurin kuma ba kamar bakin hanyaba da mutane ke yawan wucewa.
Tuno da kashedin Nana da yadda ta murɗe mata kunne kanta aikota siyan kokon yasata tashi da sauri tana zazzare ido kamar wacce taga wani abun tsoro, botikin kokon ta ɗauka ta fara ƙoƙarin tsallaka kwatar da kanta amma  saita kasa, tana cikin haka Allah ya kawo makocin su Abban su Bishira yazo wucewa ya ganta, yana isowa wajan kwalbatin yace “subhanallahi Husnan Baba me kikeyi tsaye anan ke kaɗai, ina Yayan naki?”
Jin ya ambaci ina Yayanta batasan lokacin da hawaye ya cika mata idanu ba muryar ta na rawa tace “Iyar ƙyauye ce ta koresu shida Mamana kuma kullum inna cewa Baba ya kaini wajan Mama da Yaya sai yace saina sake girma.” Tana faɗin haka sai ta fashe da kuka, kana ganin yadda take kukan kasan abun ba ƙaramin ci mata rai yake ba. 
Cikin lallashi Abban su Bishira da bai wani gane kan zancen nata ba yace “subhanallahi to yanzu dai kiyi haƙuri kinji, Baba zai kaiki wasa yake miki, yanzu ina zakije?” Ta share hawayen fuskarta tace “gida zani kuma bana iya wucewa” 
Saida Abban Bishira ya tsallakar da ita kwatar sannan ya bata botikin kokon suka karasa cikin lungun nasu a tare shi ya shiga gidansa dake kusa da nasu ita kuma ta shiga cikin soron gidan su a ɗarare.
A soron ta tsaya ta kasa shiga cikin gidan saboda tsoron faɗan Nana, tsakar gidan ta leƙa taga babu kowa. 
Tana nan a tsaye taji an bude kofar bandaki da sauri ta zabura tayi baya tana kallon kofar ban dakin dake kusa da soron.
 Ni’ima ce ta fito daga bandaki hannunta rike da buta suna hada ido da ta falla mata harara.
“shegiya munafuka jinin kafurai, dalla ni daina kallona da mayun idanun ki kona zo na kwakule su.” 
Nana na jiyo su ta fito daga daki tana gyara ɗaurin zani tace “Ni’ima keda wa nake jiyoki tun daga cikin ɗaki?”
 “wa kika sani banda wannan shegiyar Ma’un.” 
“Au wai dama ta dawo ta barni zaune ina jiranta?”
 Ni’ima tace “gata nan tsaye a soro .”
Nana tayi ƙwafa tace “lallai saina gyarawa yarinyar nan zama zamu shirya, kinsan tun yaushe na aike ta ɗorawa ta siyo min koko? shine sai yanzu ta dawo, kuma saboda iskanci ta tsaya a soro sai kokon ya gama gantalewa sannan zata kawo mini." 
Sai kuma ta ɗaga muraya cikin faɗa tace wa Husna "Zaki shigo ki kawomin ko sai Beyerabiyar uwarki ta dawo ta shigo dake, munafuka” 
Husna najin faɗan da Nana keyi ta sakeyin baya taƙi shigowa saida ta buga mata tsawa tare da cewa
 “aradu idan kika bari nasa aka dakko min ke sai na lahira ya fiki jin dadi.”
A darare Husna ta karaso ta miƙa mata botikin kokon kanta a kasa. Nana tasa hannu ta warci botikin da karfi take hannun botikin ya fita daga jikinsa saiga kokon yana gudu akan suminti. Ni’ima data zo wucewa tabi kokon dake gudu akan sumintin da kallo tace 
 “lallai Nana irin wannan asara haka da sanyin safiya?”
Nana tabi kokon da kallo sai kuma ta kalli Asma’u dake tsaye a gabanta idanunta harsun tara hawaye tace “wallahi kin yiwa kanki tunda mugunta tasa kika zubar min da kokon nan to saidai ki jira na rana yau baki da Karin safe a gidan nan, dan bazan ɗauki asara da mugunta ba.”
Husna najin haka ta kalleta da sauri, shar shar hawaye suka zubo mata dan wata irin yunwa takeji kamar taci babu saboda jiya haka ta kwanta da yunwa bataci abincin dare ba, Saboda Nana bata gama ba har tayi bacci.
 
             Nana ta zare mata ido tace “abinda kikaji shina fada, keda abinci a gidan nan sai da rana, shegiya munafuka mai zubin munafukai.”
Tana gama fada mata haka tayi shigewar ta daki ta barta nan tsaye tana kuka. 

Ƙasan bishiyar Dirimin dake cikin gidan Husna ta koma ta zauna ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka.
Tana nan a zaune Nana ta sake fitowa ta kunna ice ta dora dumamen tuwo.
 Husna ta bita da kallo harta ɗora tukunyar tuwon ta shige daki, bata jima da shiga dakin ba suka sake fitowa ita da Ni’ima. Inda take zaune Ni’ima ta kalla sai kuma ta kalli Nana tace “kiga munafukar nan inda ta koma ta zauna kamar wacce ubanta ya mutu salon Baba na shigowa ya fara tambayar me akayi mata, kai wannan mata ta Haifa mana masifa.”
Nana tayi tsaki tace “Babanku ai shida gidan nan sai dare, yace bazai dawo ba tacan zai wuce kasuwa dan haka sai dai tayi ta zama a wajan daga nan har dare.” 
Husna najin Babanta ya fita bazai dawo ba yasa ta sake rushewa da kuka, kanajin yadda take kukan kasan tun daga kasan zuciyar ta yake fitowa, dan irin kukan nan ne na rashin makama da tudun dafawa, kuka ne mai taɓa rai dasa mutum yaji babu daɗi. 
            Babu wanda ya sake bi ta kanta a cikin su Nana tayi wajen tuwon ta. 
Ni’ima tace mata “inma zaki tashi anan gwanda ki tashi dan yau keda ganin Baba sai dare in kinyi sa'a ya dawo da wuri.”

Nana ta sauke dumaman tuwo ta zubawa Ni’ima ita ma ta zuba nata, Ni’ima ta shiga daki ta dakko musu taburmar kaba ta shimfiɗa suka zauna suka fara karyawa sunaci suna hira, Husna na zaune tana kallon su suna cin tuwo suna zuba zance hankalin su kwance har suka gama cin dumamen babu wanda ya sake kallon inda take zaune.
            Wata irin yunwa ke taso mata cikin ta har wani kugi yake, dakyar ta iya tashi ta shiga dakinsu tana shiga dakin tabi katifarta da kallo da yanzu tafi karfin hawan ta ta zama ta kwanan Ni’ima.
Wajan shimfidar ta dake can karshen dakin ta kwanta tayi rufda ciki wai ko zata dena jin yunwar, amma sai taji kamar ƙara mata yunwar akeyi.
Kwanciyar taƙi daɗi ta tashi zaune ta dafe ciki ko ina ta juya babu daɗi, tana zaune akan shimfidar tana ƙarewa ɗakin kallo hawaye na zubo mata, Mamanta ce ta fado mata arai da Yayanta mai kaunar ta.
                   A hankali kamar Mama na kallonta, ta ɓata fuska sak irin yadda take mata in tana son tayi mata wani abu muryar ta na rawar kuka tace “Mama yunwa nakeji zanci abinci Baba baya sona, yanzu bana ginin shi, dan Allah Mama kice masa ya kawoni wajen ki da Yaya, Mama kicewa Yaya ina tajin yunwa kuma cikina ciwo yakeyi, jiya ma banci abinci ba nayi bacci yanzu kuma Nana tace ba zata bani tuwon ba saida rana,” 
Husna tana maganar tana kuka, yadda take maganar kamar tana kallon Mamanta dole ta baka tausayi, dan abune wanda bata saba da shiba wato zama da yunwa, sam bata san menene zama da yunwa ba, ta saba kafin ta tashi a barci Mama ta gama haɗa musu abun karyawa merai da lafiya dai-dai karfin su.
                 Husna bata san menene wahala ba, bata san wani abu wai shi zagi ko duka ba, yarinya ce abar soyuwa a zukatan iyayenta, cikin gata da tattali ta taso, duk da Mama bata ɗaukar shirme da rashin ji amma bata duka ko zagi sai faɗa, gwanda ma Yayan ta Baffa shikam tanayi masa shirme zai kwaɗeta, haka zatayi kukanta ta share ko kallo bata ishi Mama ba, dan in suna fada da Yayanta Mama bata saka musu baki saboda inka shiga ma kaine zakaji kunya daga baya.
Yanzu Husna zata tsokane sa ya kwakwkwade ta amma yana fita komai ya siyo ko yaci saiya kawo mata, tun daga soro kuma zakaji  yana kiran “Ma’un Mama gatan Baba”
 Haka Husna zata taresa da gudu su shigo gidan tare kamar ba shine wanda ya gama dukan taba.
                   Wannan yasa wani irin san juna ya shiga tsakanin su, kai hatta yan unguwa sun sheda Husna yar gatan Yayanta da Babanta ce, mutane da yawa a unguwar Husnan Baba suke kiranta. 
Amma yanzu cikin abinda bai gaza ƴan wasu ƙididdigaggun kwanaki ba komai ya canja, kana kallon ta kasan tana cikin wani hali mara daɗi, dan ba haka ta saba rayuwa ba, komai nata ya canja tayi wani iri babu kyan gani.
Yarinyar da suturar sawar tama ba irin ta sauran yaran masu ƙaramin karfi irinta bace, komai nata daban, haka koda yaushe cikin tsafta take gashin ta baya rabo da gyara da sabon kitso, sauda dama Mamanta kan ce “ya mace saida gyara in ba haka ba sai ta tashi ƙazama”
             
              Amma sai gashi tun da Mama da Yaya suka fice daga gidan komai na rayuwar ta ta canja, duk gayun nan da gata yanzu babu, da kaɗan da kaɗan komai nema yake ya zame mata labari. 
Tun dawowar ta gidan Baban ta ta tarar babu Mamanta ba yayanta zata iya rantsewa da Allah bata ƙara koshi ba. 
                 Duk da tasan duk muguntar Nana bata hanata abinci sai dai ta bata shi a wulakance, Ita dai barta da hantara da mugunta da zagin cin mutumci’ Amma tana bata abinci saidai ba akan lokaci ba, a gantale take bata, dan Nana bata gama girki da wuri, tuwon dare baya sauka da wuri sai takai wajan goman dare bata gama ba, haka abincin rana sai karfe hudu zata gama sa kafin ta raba ta bata kuwa sai wajan biyar na yamma, dan ko jiya bacci ne ya dauke ta kanta gama girkin dare, bayan ta gama kuma bata tashe taba wannan yasa ta tashi da yunwa sosai.

Wannan kuma wani sabon horo ne a wajan Husna dan bata saba zama da yunwa ba ko kaɗan, Mama ƙarfe ɗaya mai kyau ta gama abincin rana haka shida na yamma ta sauke na dare, wannan horon zama da yunwar yasa Husna cikin kwanakin nan gaba ɗaya ta rame tayi wani iri sai ido kake gani kamar wacce tayi ciwo.
                   Tsaftar jikin ta kuwa dama ba’a maganar ta dan tunda Mamanta ta tafi ita takewa kanta wanka. Shima wankan ba kullum ba saboda Nana tace bazata jure wasan ruwa da sabulu ba.
                     
              Husna ta sake juyawa akan taburmar kabar da ta shimfiɗa zatanin ta akai, nan ne yanzu kuma ya zama wajan kwanan ta, tun tafiyar Maman ta Ni’ima ta hanata kwanciya akan katifarta wacce Mama ce ta siya mata da kudin ta.
                 Tana nan a kwance tana juyi Ni’ima ta shigo dakin ta haye kan katifa tayi shame shame. 

Can taji muryar Nana na ƙwalla mata kira, jikinta na rawa ta mike ta fito tana hada hanya dan wallahi yunwa tasa bata iya ganin gabanta yadda ya kamata. 

                  “maza haɗa kwanu kan nan ki wanke su yanzun nan, yar hutu wacce ba yar wahala ba, kika wani shige ɗaki kika kwanta ga bayinki insun gama ki fito kici a sama, to maza tattara kwanukan nan ki wanke min su tas, kuma in kika yimin jiƙa jiƙa Aratakanni sai naci Uwarki yau a gidan nan, karkiga ina ƙyaleki, inna rikeki baza kiji da daɗi ba tam”
Nana ta fada tana zuba mata uwar harara. 
Husna ta fara haɗa Kwanukan tana kaiwa bakin makwarara inda suke wanke wanke saida ta gama tattare su duka sannan ta zauna ta fara wanke su a hankali dan jikin ta ya saki. Duk da yunwar dake cinta haka take wanke kwanukan tana share hawaye, kana ganin yadda take wanke wanken kuma kasan bata wani iya ba. 
Tana aikin tana tuna Mama ta tuna yadda in tace zatayi mata wanke wanke take hanawa, tace bata iya ba saita ƙara girma, in kuwa ta dage sai tayi to saidai ita ta wanke ita kuma tayi mata ɗauraya ko Yayanta na wanke wa tana masa ɗauraya.
         Tukunyar miya ta ɗago zata jika taga da sauran miya da irin kanzon dumamen nan daya kama, ruwan ta fasa zubawa a cikin tukunyar ta kankare kanzon tukunyar tuwo ta wanke sa da ruwa ta zuba a cikin miyar da tagani sun rage, da sauri sauiri take ci har ta cinye ƙanzon tas ta suɗe tukunyar, saida taga babu dogon miya a ciki kamar wacce tasa ruwa ta wanke sannan ta wanke ta.

                       Rayuwa ke nan Husna da bata shiri da miyar kuka ko kadan  bata san miyar kuka amma yau itace ta shanyeta hankali kwance babu kyama babu kukan bata so saboda tsabar yunwa, lallai gaskiyar malam Bahaushe da yace in kaji mutum yace bai iya kuka ba to uwarsa ce bata mutu ba. 
Tana gama wanke wanken ta kwashe kwanukan takai kitchen ta ajiye, Tana aje kayan wanke wanke kuma ta fito ta koma dakinsu dan tunda Nana ta bata aikin itama tayi shige warta nata dakin ta kwanta.

Husna ta samu Ni’ima har tayi barci, wajan kayanta taje ta bude jakar sama ta ciro wani coffeen hijabi tasa ta maida zip ɗin ta zuge  bai gama rufuwa ba ta barshi a haka ta saka Hijabin ta fice daga gidan.

Husna bata zuwa ko ina daga gida sai makaranta amma yau kanta tsaye ta tafi gidan makotan su ta shiga gidan su kawarta Bishira. Da Sallama ta shiga gidan Umman Bishira na zaune tana wanki ta amsa tana mata murmushi tace “a’a Husnan Baba ce yau a gidan mu da safe, ina makarantar?” Saida Husna ta gaisheta sannan tace “Baba ne ya tafi bai raka niba kuma ni bana iya zuwa da kaina, jiyama banje ba, kwana da yawa ma fa bana zuwa.” 
Umman Bishira ta girgiza kai tana jin wani iri a ranta rayuwa ke nan lallai riƙon dan wani da uwar wani babu daɗi.
 “kiyi hakuri kinji Husna daga yanzu ki rinƙa zuwa nan kuna tafiya tare dasu Bishira kinji ko?” kanta kawai ta ɗaga ba tare da tace komai ba ta samu waje ta zauna a kusa da Umma, da yake gidan babu kowa duk abokan wasan nata sun tafi makaranta sai Umma ita kadai. 
Husna na zaune Umman Bishira  ta kalleta taga yadda duk tayi wani wuri wuri da idanu bakinta ya bushe, jikin nan nata yayi fururu kamar wacce tayi sati bataga ruwa ba. 
Umma ta girgiza kai a ranta tace “wai Husnan Safiya ce ta zama haka saboda rashin uwa a gida, tunda Allah ya haɗa su zama da su zata iya rantsewa da Allah bata taɓa ganinta da datti ba amma yanzu dubeta kamar wata mara galihu. 
          “Husna na zuba miki abinci zaki ci?” da sauri tace “eh Umma zanci dama yunwa nakeji banci tuwon ba Nana tace saidai na jira na rana.” 
Umma ta rasa bakin magana saboda mamakin halin wasu matan akan ƴaƴan daba nasu ba, ji wani mugun zance wai “sai dai ta jira na rana hmmm!" 
Kai ta gyaɗa kawai tana sake bin jikin Husna da kallo kwallar tausayin ta ta cika mata ido.
“babu komai zai wuce”
Umma ta faɗa a ranta tana tuna yadda Maman  Husna ke aiko musu da abinci wasu lokutan musamman randa ta canja kirki, haka kawai zata aiko kiran Bishira tace tazo inji Mama suci abinci, tun Umma na faɗa harta haƙura dan Mama har gida tazo tayiwa Umma magana akan ita bata son halin Hausawa yaro na kowa ne, suna wasa tare sai kuma aci abinci daban daban. 
               Umma ta sake tuna wani lokaci da Baban su Bishira ya samu matsalar aiki zata iya rantsewa da Allah kusan Mama ce ke basu abinci safe rana da dare, saboda tun randa Baban Husna ya bata labarin an rufe kamfanin su Malam Idi kullum safe rana da dare saita saka Baffa yakai musu abinci.
Gashi dai ba wata ƴan uwan taka bace ta jini a tsakanin su ba amma Safiya tayi musu alkhairin da naka ma saiya gajiya dakai.

            Umma ta zubowa Husna dumamen shinkafa da wake da kunun tsamiyar da suka karya dashi ta kawo mata. 
Jikin Husna har rawa yake ta karba ta fara cin abincin da sauri sauri.
             Umma ta ci gaba da wankinta zuciyarta cike fal da tunanin rayuwa.
           Tas Husna ta cinye abincin ta shanye Kunun sannan tace “Umma nagama nagode.” 
“to kin koshi ko a ƙara miki? saida Husna tayi murmushin jin daɗi sannan tace “na koshi, Umma nagode.” 

Wannan kuma tarbiyar Mama ce duk abinda kayi mata sai tace maka ta gode walau babba ne ko yaro, dan haka Husna da Yayan ta Baffa suka taso da tarbiyar komai kayi musu sai sunce maka sun gode duk kankantar sa kuwa. 
Saida Umma tayi murmushi sannan tace “ to ungo wannan zanin kidaura saiki cire kayan jikin ki na wanke miki duk sunyi datti.” 

Husna ta karɓi zanin ta daura ta cirewa Umma kayan jikin ta. Tuni ta ware ta hau yiwa Umma hirar Mama da Yaya, har Umma ta gama wankin ta zuba ruwa ta wanke mata kanta fes sannan tayi mata wanka tace “tom ki zauna idan kayan naki ya bushe saiki saka ko?” 
Husna ta washe mata baki tace “to Umma nagode.” 

Anan ta shantake har Umma ta gama girkin rana, suna zaune suna hira, su Bishira suka dawo daga makaranta, Bishira na ganin ta tace “lah Husna Uncle Abba yana ta tambayar ki.”
 Husna najin haka ta bata fuska cikin rashin jin daɗin rashin zuwanta makarantar tace “ai dan Mamana da yaya basa nan ne shi yasa ban jeba. Amma Umma tace na rinƙa zuwa muna tafiya daku tunda Baba yanzu ya daina rakani.” 
Umma tayi sauri ta katse zancen iyaka nan ganin har ta fara kuka. 
“yi shiru Husna kinji, kuma na faɗa miki Babanki bai daina raka kiba, aiki ne yayi masa yawa.”
 Sai kuma ta juya wajan su Bishira tace “ku kuma maza kuje ku cire uniform azo aci abinci.” 

…….tare dasu Bishra Umma ta zuba musu abinci bayan sun gama ci suka fita kofar gida kasan katuwar biyar Darbejiya suka kafa dabar ƴar carafke da sauran yaran makota. 
Husna ta sake sosai a cikin yara, kamar yadda babu wanda ya neme ta a gidan su haka ita ma bata sake komawa gidan ba tunda ta fito, gaba daya saita manta da Nana da matsalolin ta, sosai ta sake a cikin yara sunata yar carafke ana zuba uban musu. 
Can wajan karfe biyu da rabi na rana taji ana ƙwala mata kira tana ɗago wa taga Ni’ima ce mai kiranta tana tsaye a ƙofar gidan su, Husna ta taso ta biyo Ni’ima tana cewa su Bishira “ina zuwa.”
 Ganinta da ɗaurin zani a ƙirji Ni’ima tabi jikinta da kallo sannan tace “kika tsaya min aka, Nana ce ke kiran ki tana dakinta.” 
Tana gama faɗin haka  tayi ficewarta daga gidan dama gidan su ƙawarta zata. 
                                    
            Da sallama Husna ta shiga ɗakin Nana na zaune a bakin katifar ta da wata mata da bata santa ba, da alama bakuwa tayi. Nana da bakuwar ta suka bi Husna da kallo a wulakance babu wanda ya amsa mata sallamar bakuwar tace “au wai dama wannan ce Ma’un? Yo ni ai na ɗauka ma wata uwar mata ce da naji kinata maganar ta, yanzu Nana akan wannan abar kike mita da ɓata bakin ki, kai amma wallahi kin bada ni. Hmmm! Wannan da batafi ƙarfin na zaune ta ba, duka duka ma nawa take wannan yarinyar?”
Nana ta tari numfashin bakuwar ta da cewa “kayya Zahira dan bakisan munafunci da makircin wannan yarinyar bane, in kikaga kaɗifiri da uwar matan da yarinyar nan take yi in taga ubanta abun saiya baki mamaki, yadda kikasan Beyerabiyar uwarta saida ta karanta mata komai kafin ta fice.
           “la la ni bana mamakin duk abinda akace wannan abar tayi, hmmm! Ke bakisan illar irin wa ƴan nan ƴaƴan ba, to wallahi in bakiyi da gaske ba wannan da kike ganin ta a raine a raine saita koreki daga gidan nan, ke zaman kano gaba daya saiya gagare ki, yawwa nadai fada miki gwanda kisan abunyi tun wuri.” 
              Nana na jin ance zaman Kano zai gagareta ta dafe girji tare da zare ido waje “me kika ce Zahira? Ina wannan bazai yiwu ba.” 
“a to nadai fada miki.” 
           Husna dai na tsaye tana jinsu da kallon duk abinda suke yi, Nana ta kalleta a wulakance tace “gidan uban wa kika tafi tun safe? Oh gani shegiya ko kin fasamin botiki da sanyin safiya na kyale ki, shine kika fice tun safe baki sake shigowa ba sai yanzu da aka kiraki.” 
Husna dai ba ta ce komai ba sai kanta data sunkuyar ƙasa. 
Wani mugun tunani ne ya fado ran Nana, shedan ya kitsa mata "kawai ki fara aiwatar da shawarar Zahira tun yanzu, inba haka ba da gaske zaman gidan nan saiya gagareki."
Nana ta ɗan sanyaya murya tace  
             “Hmmm! Kinga ni maza cire wannan zanin na jikinki ki saka kayanki gasu can kizo na aike ki ɗorawa.” 
Husna taji maganar wani iri dan ita dai tasan bata da kayan sawa a ɗakin Nana amma ganin rigarta a gefan katifar ta saita tsaya tana kallon Nana. Ita kuma a zabure tace  “zaki cire wannan baƙin zanin ki ɗauki kayan ki kisa ko saina taso.” Nana ta daka mata tsawa tana nuna mata doguwar rigarta data ajiye a gefan katifar ta. Ko yaushe tazo nan ɗin kuma oho?
                    Abinka da yarinta ga tsoro da rashin wayo, kawai Husna sai ta kunce daurin kirjin da Umman Bishira tayi mata dazu.
 Daga ita sai pant ta karasa wajan kayan tasa hannu zata dauka ke nan taji an fincikota tayo baya kanta gama fahimtar meke shirin faruwa taji saukar bulala a bayan ta, ta buga tsalle ta juyo tana sosa baya tayi ido biyu da Nana tsaye da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu, ko a ina ta same ta oho? Dan ita dai tasan Babanta bai taɓa siyo dorina ba.
 “badai ke tantiriyar mara mutumci ba, yau zanci uwarki a gidan nan.” 
Nana ta faɗa tana sake yowa kanta. Husna na ganin haka ta kurma uban ihun neman taimako.
Nana ta fincikota ta kayar a tsakar ɗakin ta fara lafta mata dorinar babu tausayi babu duban shekarun ta, jibgarta take kamar wacce Allah ya aiko ta, da ƙyar Husna ta mike a rude tayi cikin ɗakin da gudu tana ihun kuka tare da neman gurin ɓuya, amma ina babu matsira Nana ta bita tana duka suka rinƙa zageye ɗakin tana  gudun neman ceto ita kuma tana binta tana duka, wajan bakuwar  tayi da gudu tana roƙon ta cece ta dan Nana ta rufe kofa ta hanata fita daga ɗakin, tana zuwa jikin bakuwar ta tureta gefe tana faɗin 
“kinga yarinya zata kayar dani dan Allah matsa can” 
Ta hankaɗata tsakar ɗakin, Nana ta sake yin kanta da duka, tun Husna na kuka da ihun neman taimako har ta gaji ta kwanta a tsakar ɗakin muryarta ta dashe saboda ihun data rinƙa yi, saida Nana tayi mata lilis ta farfasa mata jiki san ranta sannan ta kyale ta a yashe a tsakar ɗaki. 
         Ta daga katifa ta saka Dorinar hannunta tana maida numfashi tace “shegiya gobe ma inna aikeki ki ƙara yimin mugunta, munafuka jinin masifa da bala’i, zaki tashi ki barmin nan ko saina sake turmusheki.” 
Zahira tayi dariyar nishaɗi tana jinjinawa Nana tace “a’a  barta haka karkiyi kisa kija mana masifa, ai ko yanzu ta daku ina faɗa miki gobe kome kikace mata haka zatayi miki shi babu musu, kuma duk abinda kika hanata bazata sake yi ba, ai bakiyi mata da wasa ba, kuma haka shine dai-dai dan irin waɗan nan yaran saida haka, ƴaƴan miji ai masifa ne, Nana tsaf zasu fidda ka daga ɗakin ka in bakayi da gaske ba, sai da irin haka ake bi dasu.”
Tsawa Nana ta sake dakawa Husna da har jikinta yayi zafin zazzabi, da kyar ta iya jan jikin tabar dakin, mai makon ta shiga ɗakin su kawai saita fice daga gidan a halin da take ciki, tana tafe tana sauke numfashi da ƙyar dan azaba ta hanata kuka, jikinta banda zafi da raɗaɗi babu abinda yake mata, ji take kamar ana zuba mata yaji a jikin ta babu ma kamar bayanta da take jinsa kamar wanda ta kakkarce. 
Umman Bishira na zaune a tsakar gida tana aiki kawai sai ganin Husna tayi ta shigo tana layi daga ita sai ɗan pant kamar wacce aka koro, hankalinta a mugun tashe tayi kanta tana salati.
“ke yar nan meya sameki haka?”
Husna ba baki sai hawaye da wata irin ajiyar zuciya da take sauke wa, Umma nayin ido biyu da gadan bayan Husna ta kurma ihu tana faɗin 
 “na shiga uku ni Barira Husna waye yayi miki wannan dukan?” 
Umma tayi tambayar tana kankame hannun ta, Husna naso tayi magana amma kuka da zafin da takeji a bayanta da jikinta ya hanata tayi wa Umma bayani.
 Suna cikin haka su Bishira suka dawo daga aiken da Umma tayi musu, suna ganin jikin Husna suma suka fara kuka, cikin abinda baifi minti biyar ba jikin ta yayi wani irin budir budir bayan ta kuwa gaba ɗaya ya farfashe babu kyan gani, haka hannayenta da cinyoyinta duka shatin bulala ne a kwakwakwance kamar zanen layi. 
Ita kanta Umma share hawaye take, ko takan aiken da tayi wa su Bishira bata biba tace wa Fa’iza kanwar Bishira maza ta ɗakko mata wayar ta a daki ta kira Baban su.
         Akan taburma ta kwantar da Husna da jikinta yayi zafi sosai. Lokaci ɗaya kuma zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta.



*****
_ABUJA_
Duk yadda yankin na Zuba ya kasance wajene ma tattarar jama'a, ƴanci rani maza da mata masu saida abinci da sauran mutanen gari da baka rabasu da wajen ko dare ko rana, sannan ga tashar hawa mota wanda hakan ya sake taimaka wa wajen cikowa da haɗa gosulon ababan hawa sosai, duk da babban titine wajen baya rabo da gosulon ababan hawa saboda yawan kaiwa da kawowar mutane, zaka samu yankin na Zuba cike da jama'a sunata harkokin su, yankin ya zama Bariki (Kazo nazo)......amma yau duk wannan cunkoso na Zuba babu shi yankin yayi fayau, saboda abunda ya faru ɗazu bayan sallar isha'i tsakanin jami'an tsaro,  da masu lefi, da kuma mazauna wajen.

             Bayan sallar isha'i kaɗan mutane sunata harkokin gaban su, sukaji ihu da gudun ababan hawa, masu lefi sun kutso cikin mototin mutane da gudun gaske jami'an tsaro kuma sun rufo musu baya, mutanen da kekan titi sunata ƙoƙarin sauka su bawa jami'an tsaron da suka koro masu lefin hanya su wuce, jin tsahin harbin bundugu da masu lefin keyi yasa mutane suka sake rudewa tuni suka fara fitowa daga cikin motocin su suna guduwa don neman mafaka, jin tashin harbin ya sake rikita mutane dan wasu harsun fara taka fararen hula da mototin su, ganin motar masu lefin ta sauka a titi ta kutsa cikin mutane da masifar gudu yasa Jami'an tsaron na NDLEA cin wani mugun burki saboda ganin muguwar barnar da masu lefin ke yiwa mutane, babu imani suke bi takan duk abinda ya tsaya musu a hanya su wuce, ganin haka jami'an suka tsaya basu ankara ba motar bayan su tazo ta wucesu fit da mugun gudu ta mike titi sai kuma ta sauka a hanya da alama shan gaban masu lefin take son yi ganin haka suma sauran motocin suka fara kokarin bin bayan waccan motar amma abun mamaki duka tayoyin motocin nasu sai suka sace lokaci ɗaya, abin yayi mugun basu mamaki dan lafiya suka tsaida motocin sannan basu taka komai ba, amma abun mamaki tayoyin harda wanda suka fashe kamar ansa abu mai kaifi an yanka, nanfa hankalin su yayi mugun tashi dan dole suna buƙatar bin bayan jam'in su da yabi bayan masu lefin akan lokaci.....