MUTUWAR AURE...! BOOK 1

04

by @aishatouuu

***
_________________


Mota ta sauke Safiya da Husna a ƙofar gidan su bululim bululim taja hannun Husna suka shiga cikin gidan ko ganin gaban ta batayi, a kofar gida ta wuce Abdulganiyyu da Abdulgaffar suna mata magana amma ko ganin su batayi ba bare taji me suke cewa.
"Wannan lafiyar ta kuwa?" Abdulganiyyu ya faɗa yana duban Abdulgaffar.
"Eh kamar dai da wani abu, ni kamar ma Husnah na gani a hannun ta fa."
"Husnah kuma ita da take gidan su?" Abdulganiyyu ya faɗa da ɗan kokonto, sai kuma ya miƙe yace "bari na duba naga ko lafiya, Allah dai yasa lafiya take wannan saurin kamar zata tashi sama." Yayi cikin gidan.

Safiya na shiga babban Falon gidan su ta saki hannun Husna ta zauna a kasan kafet ta ɗora hannu aka ta fashe da kukan da saida Maman Sama ta fito daga Kitchen da gudu hannun ta riƙe da ludayin miya, Wallahi saboda rudewa da ganin kukan da Safiya ke yi ko Husna dake tsaye a gaban ta bata gani ba ta wuce.

"Innalillahi Safiya lafiya? Ke Safiya lafiyar ki kuwa kike fasa kuka irin wannan? Meya faru?"
Maganganun Maman Sama da kukan Safiya ne ya fito da Momma daga ɗaki, saɓanin Maman Sama ita ta kula da Husna dake tsaye a gefe tana kallon Mamanta tana kuka sai dai ita nata sautin kukan baya fita.
"Subhanallah meya faru kuma? Husnah waya kawo ki?" Momma ta faɗa tana riƙo ta.
Safiya bata saurari lallashin da Maman sama ke mata ba bare tambayar da Momma keyi sai kuka take bil hakki, dan kuka ne da ta riƙe shi tun sanda tayi ido biyu da jikin Husna take so tayi shi.
Suna cikin haka Abdulganiyyu ya shigo falon, shima Safiyar ya fara tambaya da.
 "lafiya?"
Amma ta kasa bashi amsa sai kuka take babu ƙaƙƙautawa, ranshi har ya fara ɓaci dama shi kuma yana da zafi ga saurin zuciya, sai ayi abu yafi a irga a gidan ƙala baza kaji yace ba, in kuka sashi a zancen ku in bai masa ba yanzu zaice ba hurumin sa bane, a hali da dabi'a ya fita daban da sauran yan gidan amma fa in ka taɓo shi ta kwaɓe muku abun babu daɗin ji da gani, wannan yasa matan ke shakkar shi sosai dan baya wasa, su kansu mazan gidan tsakanin su dashi sai lallashi.
"Ke dalla Malama in baza kiyi mana bayanin meya same kiba kiyiwa mutane shiru, kin zo kinsa mu a gaba da kuka ana tambayar ki lafiya kuma kina dojin." Ya faɗa da tsawar data sake ruda Safiya, Maman Sama ta rungume ta tana hararar shi.
Safiya tana jikin Maman sama tana kuka tace "Yaya zasu kashe ta wallahi kashe ta zasuyi basa sonta dan Allah ku karɓo mini ƴata nizan riƙe ta da kaina." 
"Wa za'a kashe ɗin?" Abdulganiyyu ya jefa mata tambayar yana kallon ta sama da ƙasa dan bai gane kan zancen ba.
Maimakon ta basu amsa kawai saita tashi daga jikin Maman Sama ta kamo hannun Husna dake kusa da Momma ta janyo ta tsakiyar su, dukan su suka bita da kallo, a tsakiyar su ta tsaida Husna tasa hannu ta cire mata hijabin jikin ta.
        "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un." 
Momma ta faɗa tana ɗauke kanta da barin kallon jikin Husna daya farfashe.
Maman Sama sarkin saurin kuka saida ta fasa nata ihun sannan ta ƙwala kiran.
 "Husna! Husnah me nake gani haka a jikin ki? Meya samu jikin ki haka?" Maman Sama ta faɗa tana sake jijjuya jikin Husna tana ƙare mata kallo.
Abdulganiyyu ya bi jikin ƴar ƙanwar tashi da kallo kuma takwarar Momman su ya dubi Safiya yace "mene ne wannan a jikin ta meya same ta haka?"
"Duka ne Yaya Abdulganiyyu, dukan ta suka yi." 
Safiya ta fada tana rusa kuka sai kuma ta sake cewa "tun jiya na cewa Maman sama zanje naga Husna yau kanmu tafi amma na faɗa mata bazani gidan Abdullahi ba saidai naje gidan Umman Bishira nasa yara su kirata, ina shiga gidan su Bishira na ganta a haka, dan Allah kuga yadda na same ta a gidan maƙota."
Ran Abdulganiyyu ya ɓaci sosai amma sai bai ce musu komai ba ya ɗauki hijabin Husna ya maida mata ya ja hannun ta suka fita daga falon, Safiya na ganin haka ta ɗora hannu aka ta zunduma uban ihun kuka dan ita a tunanin ta fita da Abdulganiyyu yayi da Husna gidan su zai mai da ita.

A bakin gate suka haɗu da Abdulgaffar daya ji shirun tayi yawa ya biyo baya, yace "A'a ina zaku haka?"
"Policetation." 
Abdulganiyyu ya faɗa yana yin gaba riƙe da hannun Husna, sai Abdulgaffar ya zama lost.

"policetation kuma?"

Ya tambayi kanshi sai kuma ya biyo bayan Abdulganiyyu da sauri yana masa magana amma tuni harya ɗora Husna a mashin yaja sun tafi, dai dai lokacin kuma motar Baba Habu ta iso Kofar gidan, yana fitowa ya tadda Abdulgaffar a tsaye da baki a buɗe.
"Ya aka yi ne?" 
Baba Habu ya tambaye shi.
"Wallahi Abdulganiyyu ne yanzu ya tafi da Husnah policetation, ina tambayar shi lafiya bai bani amsa ba ya wuce." 
Ai Baba Habu beyi jinkiri ba ya koma cikin motar sa ya cewa Abdulgaffar "zo mubi bayan shi, kasan halin sa in ranshi ya ɓaci bai iya yanke hukunci ba."

.......Direct Bamfai Abdulganiyyu ya tafi da Husna, bai samu tsaiko wajen samun ganin DPO ba dan kananun ƴan sandan dake aiki a wajen sun san shi.

"Na rasa meke damun wasu matan indai akace yaro ɗan kishiya ne sam basu da imani akan shi." Dpo ya faɗa bayan ya gama sauraren duka bayanan da Abdulganiyyu yayi masa, ya sake kallon jikin Husna yana girgiza kai cikin takaici yace 
"Tun yaushe ne ta dake ki?" 
Cikin lallashi DPO yake tambayar ta tana bashi amsa rabe a jikin Kawun ta.
"Jiya ne." Ta faɗa a karye.
Yace "Kiyi hakuri kinji? In sha Allah bazata sake dukan kiba." DPO ya sake faɗa cikin yanayin san kwantar Husna hankali sai kuma ya maida indansa kan Abdulganiyyu yace "Anyway zamuyi duk abinda ya dace in sha Allah." 
Sai kuma ya jawo takardar gaban shi ya fara rubutu, ya ɗago zai miƙawa Abdulganiyyu takardar suka haɗa ido da Acp Ja'afar Mai shinkafa daya shigo office ɗin kai tsaye babu knocking bare jiran a bashi izinin shiga, Abdulganiyyu daya bawa Ƙofar shigowa baya bai san da shigowar Yaya Ja'afar ba saida yaga DPO ya miƙe ya sara yana faɗin.
"Morning Sir." 
"Morning Rano." Yaya Ja'afar ya faɗa yana zagayowa da sauri DPO Sunusi Rano ya matsa ya bashi waje ya zauna a inda ya tashi Yaya Ja'afar yana fuskantar ɗan uwanshi daya ɗauke kai kamar bai sanshi ba yace "Rano"
"Yes Sir."
"Please excuse us."
"Okay Sir."  
DPO Rano ya amsa tare da girmama wa ya juya ya fita daga office ɗin ya rufo musu ƙofa yana tambayar kanshi ko Acp Ja'afar Mai Shinkafa yasan mai ƙarar ne, saida ya fito waje yaji wani ɗan sanda na faɗin ai kanin Oga Ja'afar ne.

        Bayan fitar Rano yaya Ja'afar ya kalli ɗan uwanshi da Husna yace "meya faru ka baro gida da ita babu wanda ka nema? kuma daka zo nan me yasa baka kirani ba?" 
Sam Abdulganiyyu bai so suka haɗu da Yaya Ja'afar ba shi yasa bai neme shiba tun farko daya shigo saboda baya son sumai katsalandan yafi so sai ya gama komai sannan kowa ma yaji dan baya son a kawo masa wani tsari na daban.
"kowaye ya faɗa masa yana nan ma oho?"
"Tambayar ka nake baka ce komai ba?" Kanya bashi amsa wayar Yaya Ja'afar tayi ringing, yana ganin mai kiran ya ɗaga.
"Hello, eh na ganshi muna tare."
"Okay gamu nan zuwa." Baba Habu ya faɗa daga can bangaren.
Ran Abdulganiyyu a ƙuntace yayi wa Yaya Ja'afar bayanin abinda ya faru kamar yadda Husna ta faɗa musu, sai kuma ya cire mata hijabi ya nuna masa jikin ta, shi kanshi yaya Ja'afar ganin dukan da aka mata ba karamin ɓata masa rai yayi ba... Dan haka baice komai ba ya jawo wata paper yayi rubutu akai.

                  Baba Habu yayi shiru yana jijjuya abinda ya faru bayan sun gama yi masa bayanin komai shima ya ga jikin Husna, a gaskiya a wannan karon ranshi yayi mugun ɓaci kuma ko bai faɗa ba yan uwan shi sun ga alama saboda furucin shi daya biyo bayan  gama sauraren komai daya faru shine.
"yanzu wani mataki zamu ɗauka a hukumance Ja'afar?"
"Eh na riga na shigar da ƙorafi, so yanzu zan tura a kawo min Mai Kanon, ina so naji wanda ya bawa matar shi daman dukan mutum haka.." yaya Ja'afar ya faɗa ranshi a mugun ɓace.
Murmushi Baba Habu yayi dan yasan za'ayi  rigima akan abinda zaice musu yanzu amma kuma dole hakan za'ayi dan ya fuskanci yadda suka hau dokin zuciyar nan inya biye musu batacciya za'ayi wacce zata iya kaisu ga nadama nan gaba, dan haka ya fuskance su yace
"Babu wanda zaka tura su ɗakko Abdullahi, turawa a taho dashi wannan cin mutunci ne babba, kuma duk yadda abubuwa suka kai ga lalacewa dole shi ne uban Husnah bamu isa mu canja wannan ba, sannan kar fushi yasa ku manta waye shi a wajen maihaifin mu, haka koba komai shi surukin gidan mune, mu kuma tarbiyyar gidan mu bama sharri bama cin mutunci kamar yadda bama bari aci mana mutumci, dan haka ni zan kira shi da kaina nasan zai zo, in har da sanin shi matar sa ta yiwa Husnah wannan dukan ina mai tabbatar muku da kaina zanyi karar shi har sai naga abinda ya turewa buzu naɗi, in kuma babu sanin shi ma'ana bai sani ba to zamu duba masalahar da tafi dacewa da yanayin" Baba Habu ya faɗa ba tare daya jira cewar suba ya dannawa Mai Kano kira.

                   Tsayawar Mai Kano ke nan a Birget ƙofar gidan surukin nashi yaji wayar sa na ringing, wallahi saida gaban shi ya faɗi sanda yaga me kiran, amma saiya dake ya daga wayar da sallama, yayi shiru yana sauraren abinda Baba Habu ke faɗa masa.
"innalillahi wa inna ilaihirraju'un" ya faɗa bayan ya gama jin abinda Baba Habu ya faɗa.
"In same shi a Banfai kuma?" 
Ya sake maimaita maganar a fili yana sauke wayar daga kunnen sa.
Bashi da zaɓi dole ya hau Mashin ɗin sa ya tafi Bamfai ɗin yana tafe yana sake-sake a ranshi, amma ko wanne tunani ya ƙulla sai ya kunce dan har ya isa gate ɗin shiga ciki Bamfai tunanin shi bai hasaso masa dalili da abinda zai sa Baba Habu yace ya same shi acan ba.
Tun daga bakin gate ɗin shiga ƴan sanda suka tare shi da tambayoyin ina zashi, wa yazo nema? Meya kawo sa? Amsar ma saiya rasa wacce zai basu.
Yaya Ja'afar yasan za'ayi haka shi yasa ya turo Abdulgaffar da wani ɗan sanda su shigo da shi. Yana tsaye an hana shi shiga su Abdulgaffar suka iso gate ɗin suka yi wa ƴan sandan wajen magana suka barshi ya wuce.

           Sanda Mai Kano yayi ido biyu da jikin ƴar shi Husna mutuwar zaune yayi Baba Habu da su Yaya Ja'afar suka zuba masa ido suna son karantar reaction ɗin sa, Husna kuwa yin duniya akayi da ita taje wajen Baban ta amma taƙi zuwa, Lokacin da ya shigo ma tana ganin shi ta fashe da kuka ta sake ƙanƙame Abdulganiyyu.
"Husnah waya dake ki haka? A ina aka yi miki wannan dukan rashin imanin?" Mai Kano ya faɗa yana zuba mata idanunsa da suka canja kala. 
Husna ba amsa sai kuka, hankalin Mai Kano yayi mugun tashi, Yaya Ja'afar ya kalle shi duba irin na jami'in tsaron da yasan aikin shi yace "Matar kace ta dake ta baka sani bane?" 
Mai Kano yaji saukar maganar ta Yaya Ja'afar a cikin kunnuwan sa kamar saukar aradu.
"Nana ta daki Husnah irin wannan dukan? To ta ya ya? da yaushe? Me ta yi mata? " 
Saboda tsabar ruɗanin da Mai Kano ya shiga su da suke jiran amsoshin duka wadannan tambayoyin daga bakin shi amma su yake jerowa tambayoyin da amsar ta suke jira daga gare sa.
Duk sun karanci Mai Kano, sun kuma gane baisan da dukan ba, to amma ta ya ya? Bayan Husna tace jiya akayi mata dukan ba yau ba.
"Bai ganta ba tun jinya ke nan?"

"Dan Allah kawai a haɗa information ɗin abinda ya faru a shigar da kara Court koma waye yayi dukan da yadda akayi dukan da dalilin da yasa yayi dukan, duka ayi mana bayanin su a gaban Alkali."

Baba Habu yayi murmushi na wanda ya fi Abdulganiyyu sanin duniya da fahimtar ta, sai da Baba Habu ya gyara zama yana fuskantar Mai Kano da daya kasa zama da kyau saboda ruɗani yace "Abdullahi zamu ƙarasa wannan case ɗin a gida, Ja'afar a rufe case ɗin nan, Abdulganiyyu kama Husnah mu koma gida."
Wani mugun baƙin ciki Abdulganiyyu yaji ya zo ya tokare masa a wuya, dama yasan tunda Baba Habu yazo ya shiga maganar saiya hana ayi abinda ya dace, bai kula kowa ba ya fice daga office ɗin fuuuuuu a zafafe ya doko musu ƙofa ji kake "bummmm."
Baba Habu ya bishi da kallo yana girgiza kai, Yaya Ja'afar bai dubi kowa ba ya rufe case ɗin Abdulgaffar ne ya kama hannun Husna suka fito daga office ɗin.
Mai Kano da ƙyar ya iya miƙe wa ya biyo bayan su yana jin kanshi na sara wa da ciwo saboda tunani, basu sake ce masa komai ba shima bai sake cewa kowa komai ba ya hau kan mashin ɗin sa ya kama hanyar gida, yana tafe a titi yana saƙa yadda zasu yi da Nana, yana tunanin me ya kamata yayi mata ne dan ya huce wannan cin mutunci da tayi masa...