05
by @aishatouuu
***
_________________
Safiya da tayi kuka harta gode Allah tanayin ido biyu da Baba Habu yana shigowa cikin Falon riƙe da hannun Husna bata san sanda ta saki Murmushin jin daɗi ba, su kansu su Momma saida suka sauke ajiyar zuciya, dan gaba ɗaya sun ɗauka fita da ita da Abdulganiyyu yayi maida ita gidan su yayi.
Safiya nata bin Husna da kallo Maman Sama ta kamo ta ta cire mata hijabin ta barta haka jikin ya rinƙa shan iska, Kitchen ta shiga ta zubo abinci da shayi mai kauri da kanta ta zauna ta rinƙa bata abaki tausayin Husna na sake huda mata zuciya.
"Ai duk mun ɗauka gidan su kuka maida ita?" Momma ta faɗa tana kallon zaratan magidantan ƴaƴan nata.
"A'a ai ba zai yiwu mu mai da ita gidan su haka kawai ba." Baba Habu ya faɗi yana kallon Abdulgaffar yace "kiramin ɗan uwanka a waje, uban ƴan zuciya wato ba'a masa yadda yake soba shi ne yaƙi shigowa gidan ya tsaya daga waje."
Baba Habu ya bawa su Maman Sama labarin abinda ya faru Abdulganiyyu Bamfai yaje shigar da ƙara, da yadda suka yi da Mai Kano.
"Bai san anyi mata duka irin wannan ba tun jiya, anya kuwa Baba Habu baza'a sake shawara ba kawai mu riƙe Husnah a hannun muba? Dan ni wallahi naji tsoro da lamarin Matar Abdullahi." Maman Sama na rufe baki, Momma ta ɗora da cewa "gaskiya dai ya kamata a sake duba wannan magana."
Baba Habu najin iyayen nashi yana Murmushi, yasan me suke gudu kuma baiga lefin suba shi kanshi ya jinjina wa rashin imanin Matar.
Mai makon ya basu amsa saiya juya kan Abdulganiyyu daya shigo ya samu waje ya zauna yana sake cushe fuska yace
"Abdulganiyyu ka rinƙa danne zuciyar ka in kana cikin fushi, hanaka shigar da ƙarar da nayi ba yana nufin baza'a ɗauki mataki akan matar Abdullahi ba, amma ina so ka sani duk tsiya da lalacewar Abdullahi shine dai uban Husna, sannan ko munƙi ko munso dole shi surukin gidan mune, yin Shari'a da matarsa kuma kamar yin Shari'a dashi ne akan ƴar cikin sa, wallahi Abdulganiyyu kaji na rantse maka da Allah ko? yau da ace Abdullahi yasan anyi wa Husnah wannan dukan yayi shiru bai ɗauki wani mataki ba to wallahi da babu abinda zai hana mushiga Court dashi da matar sa, to amma Bawan Allah nan ku da kanku shaida ne, bai sani ba duk kunga halin daya shiga lokacin da yaga Husnah, amma inama uzuri Abdulganiyyu har yanzu kai kana da kuruciya sannan baka san halin makircin mata ba." Baba Habu ya ɗanyi shiru yana karantar reaction ɗin su, sannan yaci gaba da cewa
"Hakan da nayi kuma ba wai yana nufin baza mu ɗauki mataki bane, A'a? Zamu ɗauki matakin Shari'a akan Matar Abdullahi yadda nan gaba ko kuɗi aka bata akace da ɗora hannun ta akan Husnah wallahi baza tayi ba, amma fa ni nawa tsarin ba irin naka bane babu kotin da zamu shiga da ita."
Duk sai suka yi shiru suna sauran abinda zaice, sun sanshi farin sani, shi Mutum ne mai yawan kara ga haƙuri da ɗauke kai, wani abun in akayi ya ɗauke kai har sai ya baka haushi da mamaki amma fa fushin sa babu daɗi, maganar shi kuwa tasa wani ciwo daya tsaya a ƙirjin Safiya taji yana narkewa a hankali yana faɗawa cikin ta, shi kansa Abdulganiyyu da ranshi ya kai makurar ɓaci saida ya ɗago ya zubawa Yayan nasu ido.
"Nasa Ja'afar ya samo mana Lauyan da zai fitar mana da agreement paper da sahalewar Court wanda za ayi wa Husnah tsakani da Matar Babanta, sannan Abdullahi zai kawo Matar shi muma zamu kai Husnah zata saka hannu ƙarƙashin yarjejeniyar babu ita babu sake ɗora hannu akan Husna da sunan duka, koda kuwa da wasa ne, duk randa ta sake haka kuma kotu zata kamata tare da ɗaukan mummunan mataki akan ta. Sannan bayan komawar Husna gidan su duk sati ɗaya ko biyu Abdulganiyyu, Abdulgaffar ko Abdussamad ɗayan su zai rinka zuwa yana duba ta, dalilina nayin haka kuma shine dan Matar Abdullahi taji a ranta cewa da gaske fa ake mata ba da wasa ba, sannan na zaɓi Mazan su rinƙa zuwa duba Husnah ne saboda inna tura su Mansura su rinƙa zuwa suna duba ta wata rana za'a yi batacciya dasu.
Kowa a falon sai yayi shiru yana juya hukuncin da Baba Habu ya yanke, in akwai abinda bai yi wa wasun su daɗi ba shi ne cewa da yayi Husna zata sake komawa gidan Babanta, amma basu da wani zaɓi dole sai dai su bita da addu'a.
Safiya kuwa duk da bata so akace Husna zata sake komawa gidan Babanta da zama ba amma sai ta ji abunda Baba Habu yace yayi mata daɗi, sosai taji sauƙin tsoro da fargabar data hanata sukuni da kwanciyar hankali tsawan kwanakin data rabu da gidan mijinta.
Baba Habu ya miƙe yana duban agogon hannun sa, su Momma suka saka masa albarka shida sauran ƙannen sa, wanda tun bayan rasuwar mahaifin su Alhaji Ƙadiri suka sake zame musu gata musamman ma shi daya ɗauki nauyin uba ya ɗora a kansa.
Kan Baba Habu ya fita daga gidan saida ya sake faɗawa Safiya lallai ta gama shirin ta da wuri dan gobe jirgin Safe zasu bi zuwa Lagos, gaskiya ta so ya tafi ya barta ta taho daga baya, bayan an gama case ɗin Husna da Nana amma sai Baba Habu yaƙi amincewa yace zaman nata me zai yi, Husna zata ci gaba da zama dasu Momma har zuwa lokacin da zasu gama yin abinda ya dace. Dole badan Safiya taso ba haka ta amsa wa Baba Habu da "to."
******Mai Kano ya iso ƙofar gidan sa kamar zai tashi sama mashin ɗin ma bai masa packing ɗin kirki ba ya afka cikin gidan kamar wanda aka koro.
A tsakar diga ya wuce Nana da Ni'ima "fuuuuuu." ya shige ɗaki Ni'ima na masa sannu da zuwa bai amsa ba.
"Ikon Allah lafiya kuwa?" Nana ta faɗa tana miƙewa tabi bayan sa.
A tsakar ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa, tana shigowa suka haɗa ido yayi kanta da masifa kamar zai rufeta da duka yake faɗin.
"Ke ashe dama baki da mutumci ban sani ba? Ashe muguwa ce ke annamimiya mara imani wacce bata yarda da Allah ba?" Numfashin sa na sama da ƙasa saboda ɓacin rai yake nuna ta da ɗan yatsa kamar zai kai mata duka.
"A'a wai Baban Ma'u menayi maka ne kazo kana min ɗiban albarka da rana tsaka?"
Nana ta faɗa tana komawa baya dan wallahi ta tsorata da yanayin sa data ganshi dan tunda take aure da Mai Kano zata iya rantse wa da Allah bata taɓa ganin fushi da masifar da take hanga a cikin idanunsa ba yau.
"Abun kazan na ubanki kika yimin, nace abu ta kaza da Kazar uwarki kika yimin, ƴar iska mara mutunci, munafuka muguwa makira annamimiya, ke mara imani ce, ke azzaluma ce, ke maha'inciya ce, wacce bata san Allah, ba bata san ma'aikin Allah ba, bata yarda da ƙaddara da ikon Allah ba, to wallahi baki isa ba danni ba mutumin banza bane, niba lalataccen namiji bane, ke kinsan nafi ƙarfin kimin iskan ci da rashin mutumci, dan haka maza maza ki haɗa yanaki yanaki ki barmin gidana yanzun nan ba sai an jima ba, gidana ba gidan kisan kai bane, ba gidan ƴan dambe marasa imani bane."
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, Mai Kano kana cikin hankalin ka kuwa? Kasan me kake faɗa min kuwa? Iyayena fa kake zagi." Nana ta faɗa tana rushewa da kuka hankalin ta na mugun tashi.
Mai Kano jikin sa har rawa yake saboda ɓacin ransa daya taso masa yace "shaye shaye nake, ko baki jiba nace haukacewa nayi, ke banda ina gudun nayi abinda bai kamata ba wallahi yau da saina miki irin dukan azabar da kika ganawa Husnah."
Nana najin ya ambaci sunan Husna saita tsaya cak tana kallon shi kukan da take yi ma sai ya tsaya saboda mamaki tace "au yanzu dama Mai Kano duk wannan cin mutuncin da zagin ƙare dangin da kake yimin akan na daki Ma'u ne?"
Itafa har ranta bata ɗauki irin dukan data yiwa Husna a bakin komai ba, bata ma ɗauke shi a wani abu da har zai zo yana mata irin wannan masifar akai ba.
Ran Mai Kano ya daɗa ɓaci dajin abinda tace, kallonta yake zuciya na cinshi, wallahi yadda yake jin kanshi inya biye mata saiya illata ta.
"Haɗa kayan ki ki barmin gida na nace ko baki ji bane?"
"Wallahi bab.........."
"Idan kika sake magana baki fita daga gidan nan ba wallahil azeem a bakin igiyoyin Auran ki." Dif.......maganar da Nana ta ɗebo zata yi ta ɗauke daga bakin ta kamar an ɗauke wutar nepa, zufa ta yanko mata tsoro da fargaba suka shige ta.
"Karfa wankin hula ya kaini dare ni Nana, in Mai Kano ya sake ni yanzu ai na shiga uku." Nana ta ayyana haka a ranta sai kuma tayi wuru-wuru a tsakar ɗakin ta rasa me zata ɗauka, Ni'ima na tsaye a ƙofar ɗaki tana jinsu tana rusa kuka dan duk abinda ke faruwa a cikin ɗakin akan kunnen ta ya faru.
Mai Kano ya fito daga ɗakin Nana harya wuce Ni'ima ya dawo ya ciro kuɗi a aljihun sa da baisan nawa bane ya kama hannun ta yasa mata kuɗin amma sai ya kasa ce mata komai ya juya ya fita daga gidan.
Yana zaune a kofar gida ya dafe kanshi da ke masa mugun ciwo Nana ta fito Ni'ima na biye da ita a baya suka wuce shi, da ƙyar ya iya ɗaga kansa dake masa ciwo kamar zai rabe gida biyu yabi bayan su da kallo yana jin takaici da baƙin cikin abinda Nana ta aikata masa.
Yasan halin Nana bata da daɗi amma bai taɓa sanin bata da imani ba sai yau, kai ko a mafarki wani yace masa Nana zata iya yiwa ɗan mutum irin wannan dukan data yiwa yarsa wallahi ba zai taɓa yarda ba, ashe shawarar da ta rinƙa basa kwanakin baya da daɗin bakin tada rinƙa yi masa akan Husna duk na ƙarya ne da yaudara.
Ƴan uwan Safiya sunyi masa halacci, ya saki yar uwar su da ƙaramin ciki bayan uwarsa ta gama ci mata mutumci, yanzu kuma ace matar shi na neman illata ƴar su amma duk da haka basu bari anci mutuncin sa anci na iyalan saba, to shi yanzu da wanne ido ma zai kalle su? Me ma zaice musu?.
Alhaji Ƙadiri Mai Shinkafa ya shaideshi yayi masa halacci yayi masa gata ya mutumta shi amma dubi abinda ya saka masa dashi bayan baya nan, wannan wacce irin masifa ce haka? Wai dama shi mutuwar Auran haka yake zame wa mutum tashin hankali da masifa ko kuwa nasa ne yazo da haka?
Kansan dake masa mugun ciwo ya dafe, sai kuma a hankali tunani da ƙwaƙwalwar sa suka fara tuna masa da baya, can wani tsohon tarihi.
Safiya! Safiya!! Wani suna mai daraja, girma da ma'ana a cikin tarihin rayuwar sa, tabbas tahirin rayuwar sa bazai taɓa cika ba in aka cire sunan Safiya.
Haƙika yaga karamci, sannan yaga halacci da sanin ya kamata a wajen ta, tabbas ɗan halak yana gadon halin kirki da mutumci daga wajen iyaye sa amma na Safiya bayan gadon harda ƙari da tukaici a nata halin.
Wani sashe na zuciyar yace "Haƙika Mai Kano ka rushe yadda da amincin dake tsakanin ka da Alhaji Abdulkadir Mai Shinkafa."
Mai Kano saiya rufe idanun sa da sauri yana sauraren bugun zuciyar sa.
Haƙika har abada bazai daina tuna randa Alhaji Ƙadiri ya kira sa har cikin falon gidan shi ya zaunar dashi a gaba sa ya kuma mutumta shi ya girmama sa tare dayi masa abun da bai taɓa zata ba, bai kuma taɓa tsammani ba, tabbas Alhaji Ƙadiri yayi mishi Alfarmar da bai taɓa yiwa kowa ba, bai kuma taɓa amincewa kafatanin ƙabilar Hausawa akan taba, duk kuɗin ka duk ikon ka indai sunan ka Malam Bahaushe to a wajen Alhaji Ƙadiri baka isa ba, baka kai ba, kayi kaɗan haka kuma kayi tsararo yayi maka wannan alfarmar, sai dai ka nemi wani abun daban a wajen sa amma ba wannan ba, alfarmar data bawa ƴaƴan shi da matan shi da sauran mutanen gari da suka sanshi suka san tsatstsauran ra'ayin sa mugun Mamaki.
Akan sa Alhaji Ƙadiri ya aje aƙidar sa tsarin sa da tsatstauran ra'ayin sa naƙin bawa Bahaushe Auran ƴaƴan sa, shi Mai Kano Alhaji Ƙadiri ya rufe ido ya wanke yarshi mafi soyuwa a ransa ya bashi Auranta alokacin da shiba kowa bane face Yaron rumfar shi maici a ƙarƙashin sa, bai duba talaucin sa ba, bai kalli babunsa da ƙyauyen daya fito ba, bai kuma kalli bashi da komai ba, sai tsagwaron tsabar yarda da amincin dake tsakanin su kawai ya duba yayi masa wannan Alkhairi.
Sai dai kash ya kasa ya kuma gaza, yau yayi watsi da wannan aminci na Mai gidan shi Ubanshi a duk faɗin garin Kano kuma Surukin sa, ya karya alkawarin sa ya kuma lalata amincin sa alokacin da baya nan, yayi nesa da wannan Duniyar tamu gaba ɗaya, ƙasa ta daɗe da rufe masa ido, yaci Amanar shi ya sakar masa Safiya a wulaƙance.
Yaci amanar Mutumin daya amince masa ya fifita sa ya kuma ɗaga darajar sa akan duka Hausawan Duniya.
Abdullahi yayi nisa cikin tuna hannayen sa dafe da kansa idanunsa a buɗe suke yana kallon ƙasa amma wallahi sai jinsu yake kamar a rufe dan baya ganin komai baya iya hango komai sai fuskar Ubangidan sa dattijon arziki Alhaji Abdulkadiri Mai Shinkafa a shekarun baya alokacin da ya shigo cikin Birnin Kano neman kuɗi shi kaɗan shi bashi da komai, daga shi sai rigar jikin sa da tsohuwar ledar kinsuwai baƙa riƙe a hannun sa wacce Dije ta basa yasa wuƙa da laujen yankan rake sai riga da wandon sa kala ɗaya. Gani yake shekaru da lokutan na gifta masa kamar yanzu ne abunbuwan ke faruwa....