BUDURWAR ABBAN MU

PAGE 8️⃣

by @prettys01

PAGE 8️⃣

> “Ku biyun nan kune mutane masu muhimmanci a rayuwata, dan haka yarda da junan ku zai sa ku so juna.” ya faɗa yana raba hannunsu, take wannan sanyi ya ɓace sai dan ɗumin hannun Al-hussain dake hannunta. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla Al-hassan, sai idanunsu suka sarƙe da na juna, wannan haske ya ƙara gilma musu, sai suka kauda kai kowa ya mai da hankalinasa ga Al-hussain dake ta koro musu jawabai akan soyayyar juna...............

A ƙalla sun ɗau lokaci a haka kafin Al-hassan ya musu sallama ya wuce a motarsa dake wajen makaranta, Al-hussain kuma ya gyara zamansa a filin wajen suka dasa soyayyarsu da sam baya ƙarewa.

“Gaskiya Allah Allah ne, kamarku ta ɓaci, ƴan gidanku suna ganeku kuwa?.” ta tambaya tana wasa da hannunsa, sai ya yi gyaran murya sannan ya ce.

“Abbeey baya gane mu, Merry Kuma ƴar cinke take yi, mutum ɗaya ne tak a duniyar nan, a kallon farko take babbance mu.....”

“Wa?." Ta yi saurin tambayata.

“Momyn mu.” sai ta yi murmushi.

”Allah ya jiƙanta, sorry kaji." Sai ya shafa gashin kansa sannan ya ce.

“Mu je class." Ba musu ta miƙe suka fara takawa kwanon burgewa, dan kuwa Marwa da Al-hussain ba ƙaramin dacewa suka yi ba ta kowacce fanni.

Kamar yarda suka saba, bayan an gama lecture, suka zauna a school suka ci gaba da hira, da lokacin Sallah ya yi Marwa ke nufan massalcin mata shi kuma na maza, haka suke rayuwa ba gajiya da juna.

A nan suka ci abincin rana, kafin Marwa ta mai sallama dan tana so ta koma gida da wuri, sai kiran Baseey take amma ba ta ɗauka.

Hakan yasa suka yi sallama, kowa ya wuce nasu gidan cike da mamarin juna........

Direct ta nufa gida, in da ta iske motar Baseey a Compound, sai ta fito tana riƙe da jakkarta, a daidai nan, Fauza ta shigo wacce school box ya ajeta, sai Marwa ta jira ta ƙara so, oyoyo ta yi mata tana amsar lunch bag ɗin ta suka jera tana cewa.

“Ya school ɗin?."

“Wallahi ba daɗi, sai haƙuri kawai.”

“Hmmm to ke ai ko karatu ba ki fara ba, sai kin shiga jami'a za ki gane.” sai suka shiga parlourn a tare.

“Secondry school ya fi, kufa babu mai dukkan ku, in kunso kuje, sannan da kowani shiga, amma mu fa? White sock ma in baka saba tashin hankali ne."

“Hmmmm za ki kai lokacin ai, duk abin da zance ba za ki gane ba." Sai suka yi murmushi suna haura stairs.

Ba su rayu da Mom ba, amma suna ƙaunar juna fiye da misali, ba za iya natsuwa idan ɗayansu yana cikin wani hali, komai da suke yi kansu a haɗe yake, duk da kuwa suna samun saɓani da juna wasu lokutan.

Suna shiga part din su suka iske Basma ta tasa abinci a gabanta sai kallo abincin take yi.

“Ina wayanki? Tun safe nake kiranki amma kinƙi ɗauka, why?." Sai Basma ta ɗaga idanunta ta kalla Marwa sannan ta ce.

“Bana yanayin magana ne, shi yasa ban ɗauka ba.”

“Meke faruwa ne? Cewan Fauza tana zama daga gefanta.

“Ya kuka ƙare a Station?.”

“Sun kamashi, sun mai mugun dukka, kuma daga school na koma na duba shi, sannna na ce su ɓatar ta shi da na sati ɗaya, nan fa Shamsu ya haukace yana kuka yana roƙona, shine na ce su sake shi kawai, sai na kai shi asibiti na biya mai kuɗin magani na dawo gida.” sai Marwa ta yi murmushi, halin Basma sai ita, ga mugunta ga tausayi.

“To ɓacin ran nan na menene kuma?.”

“Ku dama nake jira, a yi ta ta ƙare." Ta faɗa tana sa hannu ta ture plate ɗin dake gabanta zuwa ƙasa, take ya fashe abincin ciki ya zube, Fauza za ta yi magana, Baseey ta ɗaga mata hannu tana cewa.

“Kira Harira ta kwashe.” ba musu ta miƙe ta fita tana ƙwaɗa ma mai aikinsu kira.

“Harira! Harira!!.”

“Na'am." Cewan Harira tana fitowa daga Kitchen.

“Yauwa, ta wo da tsintsiya, glass plate ya fashe a ciki.”

“To gani nan zuwa." Da haka ta koma Kitchen da sauri, Fauza ta yi murmushi, dan kuwa Harira ta yi mata ɗari bisa ɗari, tana da tsafta ga iya aiki, sannan girki ma haka.

Tana shiga ta iske Marwa na ba Basma chips a baki, ita kuma tana amsa kamar anyi mata dole.

“Abba zuwa dare zai iso, me ya kamata a dafa mai?."

“Fauza irin kin iya girkin nan.....wai Allah ya ƙyauta, babu abin da na iya ta fannin Kitchen.” faɗin Marwa tana kallon Harira da ta shigo tana aikinta.

Duk wani motsin da Harira take yi akan idanun Basma, har ta kwashe ta goge sannan ta fita.

“Me kuka gani?." Cewan Basma tana miƙewa tsaye.

“A ina kenan?."

“Marwa kardai ki ce hankalin ki baya kanta?."

“Wa?.”

“Harira, yau za ta bar gidan nan.” ta faɗa a fusace.

Fauza da ta fito sanye da wata material ta zauna tana cewa.

“Sata take yi ko me? Yau fa kwana biyu da fara aikinta, akan me za ta bari Ya Baseey?.”

“Saboda bana son zamanta a gidan nan, idan da sata ne babu matsala dan kanta take cuta, amma da zarar idanuna sun sauka akan ta zuciyata zafi take mi." Ta faɗa idanunta suna sauya launi.

Sai Marwa ta dafa ta tana cewa.

“Me ta yi miki?.”

“Ba mason a yi ma Mom Kishiya, amma zaman Harira a gidan nan kaman mun kawo ma Abba mata ce har gida......bazawara ce, means ba ta aure, sannan tana da ƙyau mai sunan ƙyau, ga diri ga hips, jikinta tana aiki rawa yake sosai, a haka za ta zauna Abba ya dawo gidan nan ya ganta, wallahi ko hijab ta sa jikinta yana fitowa.” ta faɗa tana komawa ta zauna.

“To munce bamuson tsohuwa? An kawo dai-dai mu shima za mu ce bamuso?.”

“Eh Marwa.”

“Ta iya girki, ga matar da tsafta, in muka koreta wa za su kawo?.”

Sai suka kalla Fauza a tare.

“Mummuna ɓaƙa, gajera, wacce ba ta da shape sannan mai manyan pimples, yarda Abba ba ma zai so ganinta ba.”

“Tir Ya Basma, kuma sai ta yi girki mu ci? Wallahi a'a, ban yarda ba sam, kinsa zuciyata yana tashi." Ta faɗa tana miƙewa da nufan toilet da gudu, murmushi suka yi sannan Marwa ta ce.

“Muje na ƙare ma jikinta kallo, in tafiyar ba zai yiwuba ta yi gaba kafin ya dawo, dan Ni kaina ba zan so mu zama silar kawo ma Mom Kishiya har gida ba.” sai suka miƙe a tare sannan suka fita.

Ba ta Kitchen, Dan haka suka nufa in da aka sauke ta, a hankali suka yi sallama tare da shiga cikin ɗakin.

Babban gadone a tsakiyar ɗakin, sai kujeru biyu, wardrobe madaidaici da ɗan tarkacen abubuwa.

Basu sameta a ciki ba, amma akwai motsin ruwa a bayi, sai suka zauna Marwa na cewa.

“Harira muna jiranki ana.” ta faɗa da ƙarfi dan kar ta fito ta gansu za ta iya tsorata.

“To ganin zuwa." Ta faɗa da ƙarfi.

Suna zaune ta buɗe handle ɗin ƙofar ta fito, sanye da wata riga roba-roba mai laushi da bin jiki, sai ta yafo zani a kanta sannan ta iso in da suke ta zauna a ƙasa tana cewa.

“Gani, ina fatan ba wani abu na aikata mara ƙyau ba?" Sai Marwa ta ce.

“Eh, ba ki yi komai ba, ɗauko wayarki ki ban account number ɗinki." Sai ta miƙe tana godiya sanan ta nufa gefan gado.

Tana tafiya zanin ya faɗi, manyan mazaunanta suka fara sama da ƙasa, duk akan idanunsu.

Ta ɗauko sannan ta dawo ta zauna ba tare da ta gyara zanin ba saboda ganin ai mata ne, ko bra ba ta saba, suna tsaye breast ɗin suna kallonsu.

Basma ta kai zuciya nesa sannan ta lumshe ido, dan in ta ci gaba da kallonta tsaf zuciyarta za ta buga.

“Yauwa na tura miki 100k ki fara sana'a, tafiya zamu yi dukka gida, ba lallai mu dawo nan kusa ba, ki haɗa kayanki, Driver ya mai da ke gida, mun gode." Da sauri Harira da Basma suka kalla Marwa.

Basma ta ja tsaki jin abin da Marwa ta ce, sai ta miƙe ta bar ɗakin.

“Ina za ku koma da zama?.” ta tambaya tana jin babu daɗi duk da ba jimawa ta yi da su ba.

“Tafiye-tafiye zamu fara ne saboda aikin Abba, karki damu muna godiya da nuna kulawa, sannan ki dauki duk abin da kike so a Kitchen na baki, sai dai 15mnt kawai ya rage miki.” da haka Marwa ta miƙe ta fice.

Wani farin ciki ne ya kamata dan kuwa ita gaba ta kaita, ai kafin ka ce me, Harira ta shirya tsaf, ta ko nufa Kitchen ta ɗiba abinci sosai, Dan bako guda biyu ta cika.

Tana fita tsakar gida ta shiga mota Driver a ransa ya ce ‘An kuma kenan’ ya ja mota yana nufan tasha da ita.....................

*Abba.*

Sai da ya makara sallar asuba saboda rashin barcin da be yi da wuri ba, bayan ya dawo masallaci ya kwanta amma barcin ya ƙi zuwa, har lokacin tunanin Najlah yake yi, murmushi na sau ba adadi ya kuma yi yana shafo gashin kansa.

Haka ya shafe tsawon lokaci yana abu ɗaya, sannan ya miƙe ya shiga toilet, buƙatarsa ya biya tare da yin wanka, yasan General 7:30am yake fita.

Be zo da wani kayan ba, amma da yake daƙin General ne sai ya duba cikin kayansa, ya fara dubawa a natse.

“Bara na sanya ƙananan kaya ko zan burgeta yau, dan sai na samu daman maganar da ita ko ta yayane.” ya faɗa yana ciro wani wando da riga.

Ba ƙwarya yarda kukasan danshi aka yi wannan kayan, Ash ɗin wando, sai light orange shirt, take ya dawo ɗan 30s, ya taje kashin ganka sannan ya daura agogo, p-cap ya sa tare da mask, sannan ya yi wasan turaruka a jikinsa kamar yarda ya saba.

A hankali ya fara tafiya cikin wannan kamalar ta sa, yana fita ya iske Yaya yana breakfast cikin sauri-sauri.

Kusa da shi ya zauna suna sake gaisawa.

“Ya na ga ka shirya da wuri, ba dai wucewa za ka yi ba?." Sai ya shafa kansa sannan ya ce.

“Uhmm dama kawai na shirya ne."

“Okay muje Barak kawai, ƙarfe nawa za ka wuce?."

“Da yamma."

“Kayi ƙyau sosai."

“Na gode Yaya." Ya faɗa yana kai Tea bakinsa.

“Matsalata da kai shine gaggawa, kana sauƙin hali da fahimta, amma in kana son abu baka bi a natse....... wacece yarinyar?.” ai saura kaɗan Abba ya ƙware, ya hau ɗan tari yana dafe ƙirjinsa.

“Ina lura da kai ai, ban gane wacece ba amma a ƴan rukunin ɗalubai ne." Da haka ya fara goge bakinsa yana kallon Abba dake kallonsa.

“Kai dai binciken ka yana yawa, har ka gane....oh Allah, kuma da kake cewa in da gaggawa, zafin nama ne kawai.”

“Uhmmm amma dai ina fatan babbace duk da yara na gani, kuma kai ba yaro bane." Ya faɗa yana miƙewa, da sauri Abba ya miƙe ya bi bayansa yana cewa.

“Ko jinjira ce ina ruwanka in dai za'a bani." Sai Yaya ya juyo ya kallesa yana mai murmushi.

A lokacin Matar Yaya ta fito riƙe da jakkar Yaya, ta miƙe mai.

“Allah ya tsare, a dawo lafiya..........Kai masha Allah, anya ba zaka ruɗa ƴam mata ba idan kaje, sam baka tsufa Abba." Sai suka yi dariya, Abba ya yi gaba yana duba wayarsa, Yaya kuma ya kalla matarsa cikin so da ƙauna ya ce.

“Karki ƙara fasa mai kai, dan naga yana hayaƙi, ki dai tayamu da addu'a kaman akwai yarinyar da ya gani." Sai ta zaro ido, za ta yi magana ya rufe mata baki yana cewa.

“Sai na dawo, ki kula." Sai ta ɗaga kai tana fatan Allah ya sa da gaske ne.

A motar sojoji suka nufa Barack, sai dai kowa aikin gabansa yake yi.

Suna iska General ya nufa ɓangaren sojoji, Abba kuma ya shiga office ɗin Yaya ya kwanta, yana ji kamar ya yi tsuntsu ya ganshi a gabanta.

Tun yana jiran Yaya har ya ji ya fara ƙosawa, ya kira wayarsa amma ya ji ta a kashe, tsaki yaja yana tashi ya isa gaban fridge ya buɗe, sai dai youghout kawai ya gani, sai ya ɗauka yana cewa.

“Coming." Ya faɗa jin ana buka ƙofa da ƙarfi.................

*Najlah*

Kamar kullum haka aka tashe su fitar dare, ai kuwa ta doje ta ƙi fita, ta ci gaba da barci, ashe Sir J, ya lura babu Najlah, tunda ita ke zuwa na farko kusan kullum, hakan yasa ya tabbatar tana barci, be bi ta kanta ba sai bayan da suka gama horo gaba ɗaya, sannan ya sa a kira mai ita, ko da suka koma suka isketa tana sallah, nan fa suka ce sir J na na nemanta.

Ta riga tasan hakan zai faru, sport wear blue ta sa, sannan ta fita zuwa wajen Sir J, in da kowa yake bin ta da kallon tausayi.

A office ɗin sa ta same sa, tana shiga ya rufeta da faɗa sosai, sai dai Najlah ta ƙame ƙam tana jinsa, bayan ya gama ya ce da ita cikin harshen turanci.

“What did you sit and do during the night lesson?” sai ta ɗago fararen idanunta ta kallesa sannan ta ce.

““I am performing Qiyam al-Layl" Ta faɗa tana turo baki.

“Do you mean night worship?”

“Yes Sir J.”

“Yesu..........so you are someone who worships a lot.”

“Yes.”

“So those of us who went out don’t worship, or what?.”

“Sir J, that’s not how it is. You are an unbeliever, that’s why you don’t have its blessings." Ta faɗa tana cizon leɓenta.

“Hmm, really?.” ya faɗa yana haɗe fuska, ita kuwa bata lura ba ta ko kuma cewa.

“Very much, so You know our religion is the true one, not yours—you stand in front of idols and pray."

“Najlah, quiet? Don’t you have sense, waiting for Jesus like a mad person?." Take ya miƙe tsaye yana jin zuciyarsa na mai zafi.

Najlah kuwa danasanin faɗa ta yi duk da tun ba yau ba take so ta sanar mai da ya dena bauta ma *Jesus Christ* sai yau Allah ya ba ta dama.

Hannunta ya fiza sannan ya yi waje da ita, ba tare da ya ce da ita komai ba, ya nufa Barack da ita, suna shiga ta haɗiye miyau tana mai ci gaba da binsa ba tare da tace komai ba.

Idanunta ne suka sauka kan Ya Adam dake ɗaga karfe a nesa da ita, sai ya mata murmushin *za ki ci ubanki,* baki ta murguɗa mai, tana ganin sun nufa office ɗin babban General, take cikinta ya hautsina dan bashi da sauƙi.

Ƙofar Sir J. ya hau duka ba tsayawa, jin an bashi Umarni, ya shiga ciki yana tura Najlah, har sai da ta faɗi ƙasa, sai ta gyara zamanta ta haɗe kai da gwiwa.

A natse Abba ya juyo ya zuba ma Mutumin dake tsaye ido, sannan ya kalla yarinya a zaune ta haɗe kai da gwiwa.

“General yana ina?.” cewan Sir J cikin Hausarsa wacce ba ta fita.

“Ya fita amma anjima zai shigo.” Abba ya faɗa yana zama daga kan kujera.

“Ok....tashi ki kama kunne kafin na dawo, yau sai na an karya ƙafafunki, an cire miki haƙoran rashin kunya, nonsense." Da Haka ya juya ya fice.

Tana ji ya fita ta ɗago ta kalla ƙofa sai ta yi murmushi sannan ta juya dan ganin wake zaune a office ɗin nan General A.A.

Idanunsa yana kanta, tana jiyowa suka haɗa ido, take zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi.

Najlah kuwa fuskarta ta fara kallo, take ta saki murmushi tana bin sa da kallo, a cikin ranta kuwa cewa ta yi.

‘Wow, Guys ɗin nan ya haɗu.’ tare suka shagala da kallon junan su, kafin Najlah ta sauke idanunta ƙasa tana baya wannan mutumin.

Ita a rayuwa tana son ganin Namiji babba, wanda ya manyanta, gashi ya ɗau wanka.

Sai da ya yi jarumta sosai kafin ya haɗo kalamai daga bakinsa ya ce.

“Me kika yi mai ne?.”

Cikin kuzari da sauri ta yi ƙundumbala sai ga ta gabansa tana murmushi, ita har cikin ranta ta ji ya burgeta, ga muryarsa da ta ji mai sanyi daɗi.

“Abokai.....zamu iya zama abokai a farko kafin na yi magana da kai?.” ta faɗa tana kafasa da idanunta. Sai ya miƙa mata nasa hannun yana cewa.

“Abota." Sai ta yi ɗan dariya sannan ta ce.

“Kawai dan na ce bautan Allah shine gaskiya, ba wanda suke yi ba, kawai ya kawo Ni nan, so yake ya sa General A.A ya karya Ni, kuma shi ɗin mugune wallahi.” ta kai nan tana rage murya.

Hmmm Abba dai jinsa ya yi a gajimaren soyayya, dan kuwa zazzaƙan muryan Najlah ya sa ya yi fiffike ya koma wata duniyar.

“Me yasa za ki faɗa mai haka? Ke idan aka ce miki haka ai ba za ki daɗi ba.” sai ta jinjina kai.

“Da wallahi sai yanka yiwan mutum.”

“Uhmmm shi yasa nima jiya kika min alaman za ki yanka Ni Ko?." Ya faɗa yana kallon fuskarta da suke ta sheƙi, idanunta ta ɗan zaro tana cewa.

“Wayyo wallahi na za ci irin ƴan raunin wayau ne ashe dai Ɗan saurayi ne, Dan simulmulun Gaye ne.” ta faɗa da zuciya ɗaya.

Abba kuwa dariya ya ɗan yi, yana ganin ƙarfin halinta, duk da kuwa hakan ya mai daɗi.

“Ko dai idanunki suna da matsala ne? Tsoho Ni ai, ba saurayi ba?."

“Kaiii kar ka yi saɓo mana, Zuƙeƙen santalelen saurayi nake gani nikam.” ta faɗa cikin wani irin yanayi da yasa Abba jin kaman ana tsirga mai al'aura.

“Hmmm wai, kalleni fa da ƙyau ƴam mata." Ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Da sauri ta ce.

“Dan yi tafiya na gani." Ba musu ya yi step one - two sai ya tsaya cak yana kallonta.

“Wow...Wow.... Wow, gaskiya ka iya tafiya cikin salo, Gaye kenan har wani ƙunɓo kake fa." Ta faɗa tana lumshe ido.

Abba wani nishadi ya ji ya kamashi, ya ji kansa ya fashe, wai shine Zuƙeƙen saurayi. Sai ya koma ya zauna yana cewa.

“Kina da saurin sakewa da mutane, baki Sanni ba amma kina magana da Ni."

“Hmmm to Ni me mutum zai iya min nikam, kuma ai kuma kama da General A.A, kai yaron sa ne ko?." Ta tambaya tana kuma mai murmushi.

A cikin ran Abba ya ce ‘Me yarinyar nan ta mai da nine? Ko dai da gaske kama da samari nake?.’ a zahiri kuwa cewa ya yi.

“Ƙaninsa ne Ni, sannan ina da Yara ma.”

“Haba.....kar ka ce ka yi aure? Amma ka yi da wuri gaskiya, ko kuma wasu tun a 20s suke aure.”

“Yarana uku mata, kuma Ni ba ɗan 20s bane ɗan 40s ne.”

Sai Najlah ta lumshe ido, yau dai ta ga irin Namijin da take buri, dama ta faɗa haka ne ta ji mai ze ce.

“Wow masha Allah, amma Ni dai a Aboki na sanka, ba ruwana da age ɗin ka.” sai ya ɗaga mata kai yana jin daɗin firan nasu.

“Na tambaye ki mana?."

“Ina ji.”

“Shekarunki nawa?.” sai ta kallesa.

“A ganinka nawa nake?.”

“uhmmmm 20yrs haka.” sai ta miƙe tsaye tana ja baya sannan ta tsaya cak.

“Saboda Ni siririya shi yasa ba'a ganin Age ɗina amma 25yrs nake." Sai ya yi murmushi.

“Ƙarya babu ƙyau...............” maganar sa ta tsaya cak jin an buɗo ƙofa an shigo.

Najlah dake tsaye ta ƙame da ƙyau tana sama ma General, sai ya daga kansa yana nufan wajen zamansa, take Sir J. ya shigo fuskarsa a ɗaure.

Sir J. Ya faɗa ma General komai, dan haka cikin tsawa ya ce.

“Neeldown." Ai da sauri ta yi tana ɗaga hannunta sama tare da rufe idanunta sai gashin sama suka kwanta masu tsayi da laushi.

Take General ya shiga ba Sir J. haƙuri sosai, sannan ya ce.

“You can go, a nan za ta wuni dan kuwa wajen Segent George zan miƙa ta." Sai Sir J. ya yi godiya sannan ya fita.

Yana fita Abba ya kalla General ya ce.

“Wiyanta zai yi ciwo a haka fa.”

“Ba zai yi komai ba ko na 3h ta yi, ai punishment ma sai Segent George, Amma Najlah akan me za ki ce mai haka?." Yana sauke numfashi ta ce.

“Sir I'm joke."

“Shout up, ba'a wasa da addini, dan haka zan sa a horaki na yau, ina zuwa." Ya faɗa a zuciye sannan ya fita, sai Abba ya ce.

“Oh Allah, yanzu daga wanna abun sai horo?.” sai ta yi sauri ta katse sa, cikin salo da masifa ta fara cewa.

“Aboki karka damu, mun saba ai, soja ake mana haka rayuwar mu take, Ni duka ne kawai bana so, amma shima George ɗin muna da case da shi, wallahi in aka kaini wajensa, sai na yaga mai fatar fuskarsa, sannan na fara yaƙushinsa ina ciwonsa kamar ƙura, haka zan kama wannan kan nasa na yaga nasha mai jini, na fitar mai da haƙora, na ƙwaƙule idanunsa masu kama dana China, sananne na karya........."

“Shout up!?.” a razane ta buɗe idanunta sai suka sauka akan General A.A da Segent George, sai ta mai da idanunta kan Abba, da ya rufe baki alamun yana riƙe dariyar sa.

“Na shiga ukuna yau.” ta faɗa tana kallon yarda Segent George yake huci kamar zaki, da sauri ta mai da hannayenta sama dan kuwa da su take bayani tana wasa da zara-zaran yatsunta kamar wata mayya............✍️

END

> 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣

> Najlah sannu fa

> Baseey boom 🥰

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book

📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book

📙 *BARRISTER* Paid book₦300

📕 *THE SLAVE* free book

📒 *ZAMU HAƊU* Free book

📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300

📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300

📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500

📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book

📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_

📔 *YAUDARA ZALLA ❤️* _Free book_

📒 *ƳAR NOLLYWOOD 🔥* _Paid ₦500_

HIKAYOYI kuma sune :

*SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥*

*SARKIN MU🤣*

*MOHINA DA MATSAFIYA💀*

*RAMUWA💀🔥*

#LIKES👍

#SHARE👌

#COMMENTS☹️