Episode 2
SAUYIN KADDARA
......................................................,.......................
Writing by hauwau armayau 🥰
(Jidder 💘 💘)
BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM DA SUNNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN Kai
.............................................................................
Episode 2
Sosai yake kallonta Yana so ya fahimta a wani yanayi take dagowa yayi ya kalle Wanda ya shigo,
likitane ya shigo sai nurses biyu biye da shi ko wacce kayan aikine a hannunsu,
kallonsa likitan yayi yace Farooq kar ka daga hankalinka komai yayi farko zaiyi karshe koma dukkan tsananin yana tareda sauki,
murmushi da ya fi kuka ciwo Farooq yayi yace bazaka ganeba ina cikin matsannacin damuwa daba kowa zai fahimtaba,
yau ace waini ka duba a duniya bayaga nahaifiyata babu wacce ta tsaya ta fahimceni yau idan babu ita bansan ya rayuwata zata kare ba,shima likitan kallonsa yayi yace Farooq komai a duniya hakuri akeyi sannan ba ko wani yanayine yake dawwamaba ka duba tundaga farkon duniyanan har zuwa yanzu komai canxawa yakeyi,
wani murmushi ya komayi yace Bilal bazaka fahimce abunda na ke tunaniba,
dafashi Bilal yayi yace Farooq nasan kana cikin damuwa koma Hakan bazai sa ka kasa zuciyanka cikin damuwaba Farooq,
Allah ya baka ko wacce irin dama da ba kowa ke samu ba kana da kyau kudi hade da nasaba babu indai kake da nakasu,
akwai cewan Farooq akwai indai na Gaza Bilal ya karasa maganar cikin karyewan zuciya cikin rarrashi Bilal ya cigaba da bashi Baki,
Wai nikan TAHAREEQ da yaushe zaka koma office ne cewan mamy,
kallonta yayi yace yanzufa zan koma Mamy,
Amman kasan abun magana baya kadan a gidan yanzu zaa iya kiranshi ace an ganka a gida wai me yasa duk abunda zai zama abun magana kake son shine iyya ta karasa maganar cikin hasala,
kiyi hakuri Mamy kawai yace ya tashi ya fita gurin motanshi ya tafi shiga yayi Bai tsaya a ko inaba sai cikin ka tafaren campanynsu ,
Wanda suke hada ko wani nau'i na dinner set kama da kwano plate hade da kofuna sosai gurin hadu ko ina ya gifta gaishe ake yi Amman da hannu kawai yake amsawa,
ABEERA ABEERA ABEERA wai ni Kam ABEERA Bata nan,
gani baba au dama kina jina shine zunzurutun iskanci kika mun shiru ko kallansa ba tayi ba tace na fara baccine,
okay ina kikaje da'a ka tashe ku da makaranta,
dazu Kara kallonsa tayi a karo na biyu tace babu, kenan maganar Da ake fadamun gaskiya Kun fara bin Maza Dake da Yan uwanki nasu Bai fito na kine ya bayyana wato kin dawo mazinaciya dawani irin bugawa kirjinta yayi Wanda Yana da nasaba da kalman da baba ya fada a kanta,
ba magana nake miki ba dago ki kalle ni,
ba dagoba Kuma Bata ba bashi amsaba har Ya gama surutunsa da suki burutsusa Bata kula shiba Saida ya ce mata tashi ta tafi tukunna, gaske Saida a fara bin hotel ko Kuma ke ki bisu,