MUTUWAR AURE...! BOOK 1

08

by @aishatouuu

***
_________________


Wannan abu daya faru tsakanin Mai Kano da Abdussamad shiya janyo hankalin shi ya samu yan uwansa yayi musu bayanin abinda ya faru sukayi ta mamaki.
Baba Habu ne ya kawo shawarar mai zai hana su samu Alhaji da maganar inya yarda kawai sai ya ɗauke shi aiki a rumfar sa tunda dama ya salami yaran shi.

Sosai jin haka daga bakin Baba Habu ya yiwa Abdussamad dadi  dama yanada plan din in aka kwana biyu suka gama lissafin tasu rumfar ya yiwa Yaya Ja’afar maganar su daukeshi aiki a wajen su yasan zai taimaka musu sosai.

Bayan gabatar wa da Alhaji Ƙadiri lissafin karshen shekara Baba Habu yayi masa bayanin Mai Kano da abinda suka yanke, Alhaji Ƙadiri yayi shiru yana tunani kamar yace musu a’a saboda shi yanzu lamarin yaran kasuwa ya fara bashi tsoro kowa ka dakko so yake ya karyaka ya kafa kanshi, amma dole yana bukatar mataimaki.
                 “kun yarda da Amanar shi?”
Alhaji Ƙadiri ya tambayi yaran shi yana kallon su.
“eh yana da kirki da Amana.”
Abdussamad ya fada da sauri, murmushi Alhaji Ƙadiri yayi yana kallon sa yace “nima na yarda yana da kirki Abdussamad amma ita riƙe amanar nizan baku labari in ya fara aiki dani.”
Sosai jin amsarshi ta yiwa Abdussamad daɗi, aransa yake jin Mai Kano ba zai bashi kunya ba in sha Allahu.

Abdussamad ya samu Mai Kano yayi masa bayanin komai, Mai Kano yayi shiru yana tunani har Abdussamad yaji tsoron ko ba zai amince ba, a hankali ya dafa kafadar shi yace “kayi tunani kanka yanke hukunci amma ina tabbatar maka aiki ne mai kyau zakaji daɗin zama da Alhajin mu indai ka kiyaye abinda baya so."
Murmushi Mai Kano yayi yana duban yanayin Abdussamad yace “karka damu zanyi magana da iyayena insun amince sai nama magana.”

                           Bayan kwana biyu Mai Kano yaje gida ya samu iyayen shi da maganar Aramma yayi shiru yana tunani dan gaskiya shi bai tura sa Kano neman kuɗi dan ya zauna gaba ɗaya ba, ya turashi ne yaje yayi rani kamar sauran samarin gari in damuna ta faɗi ya dawo gida yayi noma.
To amma Mai Kano mutum ne mai biyayya yasha yanke masa hanzari ya haƙura yasan duk ƴaƴan shi babu wanda zaiwa abinda yake wa Mai Kano ya zauna lafiya.
Numfashi ya sauke yana kokarin fahimtar yanayin dan nashi yace “kace mutumin Beyerabe ne kuma musulmi ko?”
Kan Mai Kano a ƙasa yace “eh musulmai ne?”
Kafin Aramma ya sake magana Dije tace “wai barin shi zakayi yaje wajen Yarabawa yayi musu aiki? Wanne musulunci ne a wajen yaren mutum? Musulinci ko suna yanzu haka ma basa sallah.”
Aramma da takaicin maganar Dije ya ƙume kawai saiya fuskanci Mai Kano yace “tashi kaje Allah yama albarka saika yiwa iyalinka bayani ta sani.”
Sosai maganar Aramma ta bawa Mai Kano mamaki danko kadan bai ɗauka zai aminnce masa ba. 
Aramma yabi bayan Mai Kano daya fita da kallo yana jin daɗi dabai hana shiba dan yana kula da yanayin sa yana son aikin kawai biyayyace tasa yake jiran umarnin su.
Wajen Dije data cika tayi fam Aramma ya maida hankalinshi ransa a ɓace yace “wayace miki duk yaren da ba Hausawa ba basa sallah? Su asalin Hausawan ba Maguzawa bane? To in baki sani ba ma na faɗa miki ako wacce ƙabila akwai Musulmi akwai wanda ba Musulmi ba.


Bayan dawowar Mai Kano Abdussamad yaji daɗin amincewar sa, babu ɓata lokaci ya gabatar da shi a wajen Alhaji Ƙadiri ya karɓe sa hannu bibbiyu sannan yayi masa bayanin komai yace washegari zai fara zuwa Rumfa, abin ƙarin jin daɗin kuma sai yace ya zo su rinƙa kwana da Abdussamad tunda bashi da wajen zama. 
Mai Kano yaji daɗin wannan karamcin da Alhaji Ƙadiri yayi masa,
Washegari Abdussamad ne ya rakashi har Rumfa sai da yaɗan zauna sannan yayi masa Sallama ya tafi dan su a Kasuwar Kantin Kwari suke nasu kasuwancin.

Rayuwa ta fara canjawa Mai Kano sannu a hankali ya fara zama da Alhaji Ƙadiri cikin ikon Allah kuma suna zaune lafiya, dan Mai Kano mutum ne mai sanin ya kamata ga ɗauke kai da rashin san abin wani.
Shima kuma Alhaji Ƙadiri sosai yake jin daɗin zama dashi, duk ƙarshen wata yake zuwa ganin gida yayi kwana biyu ko huɗu ya dawo.
Nan da nan Mai Kano ya fara canjawa dan zaici mai kyau ya sha mai kyau ya kwanta a mai kyau ga kuma kwanciyar hankali, gashi babu lefi Alhaji Ƙadiri yasan hakkin na ƙasa dashi, sosai yake biyan sa hakkin shi babu ƙyashi da mugunta.
Amintar su da Abdussamad sai ta ƙara karfi dan yanzu kusan komai tare suke yi dan ma Mai Kano yana da kama kai duk yadda Abdussamad yaso ya sake masa komai nasa shi yana yiwa kansa iyaka baya yarda ya wuce matsayin sa.

Cikin shekara ɗaya Allah ya sake sawa kasuwancin Alhaji Ƙadiri albarka wannan shekarar da Mai Kano ya kawo masa lissafin kuɗin Rumfa riba da adadin sauran kayan da suka rage sosai yayi mamakin ganin abinda aka samu, rabon da a samu riba irin wannan a rumfar sa tun sanda suke zama da Baba Habu.
Wannan ya sake yi wa Allhaji Ƙadiri da yaran sa daɗi, bakin Alhaji Ƙadiri yaƙi rufuwa saboda murna sai faɗi yake 
"Akwai albarka a hannun ka Abdullahi." Abdussamad kuwa yafi kowa farin ciki yaji daɗi kamar ya goya Mai Kano.


******Tun bayan dawowar Mai Kano gidan Alhaji Ƙadiri shakuwa ta sake shiga tsakanin shi da Baffa wani lokacin ma shi yake rakasa makaranta kanya tafi kasuwa.
Kullum inya tashi a kasuwa kuma saiya tsaya ya sayi alewa minti wacce yake rabawa yara sadaka, amma fa tsarabar Baffa daban take data kowa.
              Mallam Bahaushe yace wai mai ɗa wawa nan da nan mutumci ya shiga tsakanin sa da Safiya Autar su Abdussamad, harga Allah da farko bai san ita ce Maman Baffa ba dan bata fiya zama a gidan ba, sosai Safiya ke ganin mutumci da girmansa ko bai ganta ba indai ta ganshi saita ce 
 "Baba Abdullayi ina kwana?"

A bakin Abdussamad ya  samun labarin ita ce ta haifi Baffa amma sun rabu da mahaifinsa tun yana jariri, tayi Aure da wani babban mutum mai suna Alhaji Manu Kwabo ɗan asalin ƙabilar Margi ne, Auran soyayya suka yi, Alhaji Manu Kwabo ɗan kasuwa ne sosai a Kantin Kwari yana cikin Manyan ƴan kasuwar Kwari, sun haɗu da Safiya ranar ɗaurin auren Abdulganiyyu yazo wajen ɗaurin aure ya ganta.
Yana da mata wacce suka yi Aure tun bashi da komai har yayi arziki saidai tsawan shekaru basu taɓa samun haihuwa ba, dangi sunyi sunyi dashi ya ƙara Aure  yaki sai dai ya kama ƴaƴan ƴan uwa ya riƙe har yayi musu Aure.
Alhaji Manu Kwabo mutum ne mai kirki da zumunci.
Farkon auren sa da Safiya ba'a samu wata matsala a gidan sa ba sosai ake zaman lafiya tsakanin Safiya da uwargidan sa Hajiya Turai, dama kuma Safiya bata taso taga ana faɗan kishi a gidan suba wannan ya sake taimakawa wajen zaman su lafiya da Turai, sosai Safiya take bin Hajiya Turai, haka bata da matsala da yaran da Alhaji Manu yake riƙo saboda akwaita da kama kai ga kyauta, bayan Auran ta da Alhaji Manu Alhaji Ƙadiri ya bata jari mai tsoka kamar yadda yaba sauran ƴan uwanta mata.
Da shawarar Alhaji Manu ta fara kasuwancin saida atamfofi da laces kuma sosai take samun alkhairi saboda tallafawar shi da kuma yaran sa da suke shiri sosai da ita, ana kawo kayan da za'a samu alkairi suke faɗa mata, wani abun ma suke ce mata 
"Mama Safiya ki gwada siyan wannan zaki samu alheri." Wannan yasa sosai take jin daɗin zama da su.

An fara samun matsalar zaman Safiya da Hajiya Turai ne lokacin da ciki ya bullo a jikin ta, nan fa Hajiya Turai tace ina wuta ta jefa ta, kishi take da baƙin ciki da fitar cikin Safiya sosai.
Wutar kishinta ta sake ruruwa ganin susucewar da Alhaji Manu da dangin sa suka yi akan cikin Safiya.
Ansha fama da tashin hankalin Hajiya Turai amma da yake Safiya bamai fitana bace kuma Alhaji Manu Kwabo tsayayyen mutam ne a gidan sa saiya taka mata burki, cikin Safiya ya shiga wata takwas Hajiya Turai taga dai da gaske fa tana zaune shekara da shekaru da Alhaji bata haihu ba wata data zo daga sama zata haihu dashi ta barta da kale, wannan mugun tunani ya sake rikita mata lissafi, nan fa ta shiga neman mafitar yadda zataga bayan Safiya da abinda ke cikin ta.

                    Wata ranar juma'a Safiya ta fito tattaki cikin gida kamar yadda ta saba Hajiya Turai ta shammace ta ta kamata da kokwawa Safiya tayi iyaka ƙoƙarin ta danta kwaci kanta amma ta kasa, babu imani Hajiya Turai tahau ruwan cikin ta tana duka har saida Safiya ta suma jini ya fara zuba sannan ta kyale ta, Safiya na cikin wannan halin Allah ya kawo Musa babban Yaron da Alhaji ke riƙo, Alhaji manu ya aiko sa kawo cefane yazo ya tadda wannan tashin hankali.
Da taimakon mutanen unguwa ya kai Safiya asibiti saida Likitoci suka karɓe ta sannan ya samu damar kiran Alhaji Manu ya sanar dashi abunda ke faruwa.
Hankalin shi a mugun tashe yazo cikin asibitin Murtala, lokacin haihuwar ta baiyi ba amma dole likitoci suka bada shawarar ayi mata aiki a cire abunda ke cikin ta inba haka ba  za'a iya rasa ta ko ɗan cikin ta.
                     Alhaji Manu ya kira wannan labari da mummunan zance take  yasa hannu aka shige da Safiya theater room.
             Labarin halinda Safiya ke ciki ya iske  dangin ta babu ɓata lokaci suka cika asibitin har Alhaji Ƙadiri saida ya zo.
Cikin ikon Allah aka yiwa Safiya aiki successfully aka ciro mata ɗa namiji lafiyayya  kato kamar ubansa, Alhaji Manu yasha murna bakin sa yaƙi rufuwa, Norses ɗin da suka yi aikin sun sha kyauta, take ya sawa yaron sunan mahaifinsa Muhammadu Inuwa (Baffa) sai lokacin Musa ya faɗa musu ainahin abinda ya faru da halin da yaje ya tadda Safiya.
Babu wanda ya sani su Aunty Mansura suka tafi gidan Alhaji Manu suka yiwa Hajiya Turai dukan tsiya da ƙyar makota suka kwance ta a hannun su.
Sunsha faɗan abinda suka yiwa Turai a wajen Alhaji Ƙadiri yayin da Alhaji Manu yace sunyi masa dai-dai dama tunanin hukuncin da zai mata yake yi akan abinda tayi dan haka sun saukaka masa, ita ma taji ajikin ta, duk da haka sai da Alhaji Ƙadiri yayi musu faɗa sosai.

              Iftilaƙin rabuwar Safiya da Mijin ta uban ɗanta Alhaji Manu Kwabo ya faru ne randa ta cika kwana huɗu da haihuwa Alhaji Manu  yazo asibitin da sassafe Maman Sama tanawa Baffa wanka ya shigo ɗakin ko gaisuwa basu yi ba ya bata takardar sakin Safiya ya kuma ce Baffa ba ɗansa  bane Safiya ta nemi uban ɗanta.
Wannan mummunan labari yayi mutukar tayar da hankalin Alhaji Ƙadiri, abun da ya faru sosai ya taɓa Safiya.
Ƴan uwan Alhaji Manu Kwabo har gida suka zo suka bawa Alhaji Ƙadiri hakuri tare da tabbatar masa da aikin asiri ne amma su sun tabbatar da Baffa ɗansa ne.
Tabbas a lokacin Alhaji Ƙadiri yaso yayi ƙarar 
Alhaji Manu amma sai yan uwan shi suka hana tare da Alkawarin zasu tsaya da Baffa har zuwa lokacin da Alhaji Manu  zai dawo cikin hayyacin sa.
              Wannan shi ne abinda ya raba Safiya da  mijinta na farko Alhaji Manu Kwabo.


****Rayuwa taci gaba da juyawa abubuwa da yawa suka yi ta canjawa, Mai Kano na kula da matar sa da iyayen shi sosai komai nashi nasu ne.
                 A Wani zuwa ganin gida da Mai Kano yayi rigima ta ɓarke tsakanin sa da Nana tayi rantsuwa sai dai Mai Kano ya tafi da ita Birni inba haka ba sai ya sake ta, abun ya bawa Mai Kano mamaki dan zuwan shi na karshe lafiya lafiya suka rabu.
Bai kula taba yaci gaba da sabgogin sa babu wanda yasan mai yake faruwa a tsakanin su sai randa ya shirya zai dawo Kano Nana tace sam bata san zance ba, shi kuma ya ƙyale ta ya fito amma sai ta biyo sa har wajen Dije tana masa diban albarka ta inda ta shiga bata nan take fita ba, har maƙota suka fara shiga zancen anata bawa Nana haƙuri amma taƙi haƙura da Dije tayi mata magana sai cewa tayi.
"Dan Allah kiyi shiru ai da sanin ki Mai Kano yake zaman dadiro a birni amma kuka yi shiru kuka kyale sa to wallahi ban lamunta ya sake tafiya ya barni ba saidai ya tafi dani, indai yana da gaskiya, in kuma yaƙi to sai dai ya sakeni dan bazanci gaba da zama da Mai zaman dadiro a gidan Yarabawa ba."

Tirƙashi Nana ta kawo inda Mai Kano ya kasa haƙuri ya ɗago kai ya kalle ta ranshi a mugun ɓace yace "to baki isa ba in zaki zauna ki zauna in kuma bazaki zauna ba kiyi gaba."
Wannan magana ta sake tunzura Nana ta ɗora hannu aka ta fasa ihu tana zage zage gashi Aramma baya nan sunje wajen jana'iza a Baragon.
           Ko takan Nana Mai Kano bai sake biba ya dau jakar goyan shi zai fita Nana tasha gaban sa tace bai isa ya tafi ya barta ba.
Shedan da ɓacin rai suka sa a nan take yayi mata saki ɗaya ba tare daya sake kallon kowa a ba ya kada kanshi ya fice daga gidan.
           Wannan ke nan. 


****
Shekaru sun fara nisa Kasuwa babu abinda zasu cewa Allah sai godiya, duk damuna Mai Kano yake tura kuɗin da za'ayi noma gida. Yanzu baya yawan zuwa ganin gida kamar da.
Kusan cin sa da Alhaji Ƙadiri da ƴan gidan sai abinda ya karu, yanzu ya zama ɗan gida, shida Safiya kuwa sosai suke shiri yanzu shine yake karɓo mata kayan ta in yazo daga Lagos tana kiran sa komai yake yi zai bari ya tafi ya karɓo mata.
Haka Baffa komai ya ce Baba ne ya siyamin Kaza Baba ne yaban Kaza.

Anata zuwa neman Auran Safiya tako wanne bangare amma taƙi yarda ta bawa kowa fuska, sam bata kula kowa abun harya fara zama rigima tsakanin ta da Yayun ta Maza dan zuwan ƙarshe da Baba Habu yayi yace  in bata fidda Miji ba har ya sake dawowa duk wanda yaga dama shi zai bata.
Safiya da Mai Kano sun daɗe suna son juna amma kowa sai ya shanye abinda ke cikin zuciyarsa saboda sanin tsari da tsaurin ra'ayin Alhaji Ƙadiri akan Auran  Bahaushe.
           Masu iya magana suka ce wai in rabo ya ranste....!


Wata ranar Laraba da Mai Kano da iyalan gidan Alhaji Ƙadiri baza su taɓa mantawa da ita ba.

Kamar wasa Alhaji Kadiri ya kira Mai Kano Falon shi yace ya bashi auran Safiya.
"Alhaji Auran Safiya nidin?"
Murmushi irin na manya Alhaji Ƙadiri yayi sai kuma ya sake fuskantar Mai Kano da mamakin sa yaƙi ɓoyuwa yace "Ni nasan kana son Safiya ita ma kuma nasan tana sonka Abdullahi sanin wane ne ni da tsarina yasa bazata taɓa nuna wa ba, Abdullahi na yarda da kai da tarbiyyar ka inada labarin dalilin da yasa kuka rabu da matar ka Abdussamad ya faɗa min komai.
                Amana guda ɗaya ce kuma na yarda kanada ita na amince maka na baka amanar yata Safiya in dai iyayen ka sun amince maka zan Aura maka ita."
Harga Allah Mai Kano harya yiwa Alhaji godiya ya baro falon shi jin zancen yake kamar a mafarki, shi dai Mai Kano shi Alhaji Ƙadiri zai bawa Auran ƴar sa bayan yana da sahihin tarihin tsaurin ra'ayin sa da kafiyar sa akan bada Aure ga Hausawa.
Tabbas labarin ya girgiza ahlin Alhaji Ƙadiri sosai kuma suka ji maganar kamar daga sama, Abdussamd kusan yafi kowa murna dajin wannan zance.

Lokacin da Mai Kano yaje gida da maganar Auran ƴar mai gidansa bai samu matsala da Aramma ba amma Dije taso bashi matsala saida Aramma da Salisu suka yi mata bayani sosai sannan ta yarda amma duk da haka gani take kawai Mai Kano arniya zai Aura tunda Beyerabiya ce....