MUTUWAR AURE...! BOOK 1

09

by @aishatouuu

***
_________________


Babu daɗe wa akayi Auran Safiya da Mai Kano, a lokacin yaso ya kama musu haya sai Aminin sa Sale yace ya zo su zauna tare a gidan sa, da farko Mai Kano yaƙi amincewa da wannan shawara sai da Sale yayi ta roƙon shi sannan ya yarda zai zauna a gidan sa, kuma cikin ikon Allah zaman Safiya da matar Sale ba'a samu matsala ba, zama suke lafiya babu wata fitina dan dukan su basu da faɗa.
Bayan Auran ne Alhaji Ƙadiri ya sallami Mai Kano ya bashi ƙaramar rumfar shi kyauta yace ya bar masa ita duniya da lahira ya saka nasa jarin aciki yaci gashin kansa shima, Wannan abun Alkhairi da Alhaji Ƙadiri yayi wa Mai Kano Aramma har gida yazo yayi masa godiya.
           Mai Kano ya ƙara dagewa da neman na kanshi zaman sa da Safiya kuwa babu abinda zaice sai san barka.

Mai Kano irin mazan nan ne da ake kira da Mijin marainiya akwai sa da tausayin iyali, Safiya kuma akwai haƙuri da sanin ya kamata kwata-kwata abun hannunta bai rufe mata ido ba.
Zaman Aure suke na rufa wa juna asiri, abubuwa da yawa Mai Kano sai dai ya dawo ya tarar Safiya tayi su da kuɗin ta, da yake mace ce mai san ado da kwalliya kamar yadda ta taso a gidan su bata saka ƙananan suturu haka a gidan Mai Kano ma babu abinda ya canja, saka gold kuwa dama wannan kamar ajinin ƴan gidan su yake, suna san saka gold ɗan kunne sarka da abun hannu.
Wannan hali da dabi'u na Safiya ya ƙara wa zaman Auran su daɗi da fahimtar juna, tuni Baffa ya dawo wajen ta da zama kasuwancin ta yana tafiya sosai dan yanzu har shago gare ta a kasuwar Birget, sosai Mai Kano yake supporting ɗin ta tako wani ɓangare babu baƙin ciki babu ƙyashi tsakanin sa da Allah yake yi mata komai.
               Bayan Auran su ba dadewa suka je garin su Mai Kano, Safiya taga ƴan uwan shi ƴan uwansa sun ganta, Dije ta rinƙa bi waje waje tana nunata kamar kuɗi, Safiya takai musu abun Alkhairi har gidan Mariya taje suka gaisa, kwanan su biyu suka dawo, kansu dawo Safiya taso Dije ta basu Ni'ima su taho da ita amma fir taƙi Aramma yace su tafi su barta wata rana da ƙafarta zata zo musu haka kuwa aka yi suka koma suka bar Ni'ima.

Auran su nada Shekara biyu Safiya ta haifi yarta Mace, ta roƙi Mai Kano ya bari tasa Asma'u sunan Momma babu ja ya aminci ranar suna yarinya taci suna Asma'u Husna, Momma ta aiko da dan kunne da sarkar gold na takwarar da akayi mata dashi aka huda mata kunne.
Baffa yaji daɗin haihuwar Husna kusan yafi kowa murna da haihuwar duk abokan shi saida suka san yayi ƙanwa, in makaranta yaje tsarabar shi ta Husna ce, sosai take ganin gata tako wanne bangare dan Mai Kano bai taɓa riƙe ɗan kansa ba sai a kanta.

Rayuwa haka tayi ta tafiya shekaru suka fara ja har an sa Husna a makaranta, tun daga kan ta kuma Safiya bata sake haihuwa ba tun tana damuwa harta barwa Allah, duk bayan hutu suke zuwa garin su Mai Kano su kwana biyu ko uku su dawo.
Tunda Safiya ta fuskanci iyayen Mai Kano basu da ƙarfi duk zuwa saita tafi musu da abubuwan buƙata, kayan sawarta dana ƴan uwanta in zasu bayar duka su take haɗa wa ta kaiwa Mariya Autar su Mai Kano da matan Salisu da Lirwanu, haka Ni'ima bata rabo dayi mata ɗinki kayan yaran Aunty Femi in zasu bayar duka Ni'ima take kaiwa, kuma sosai kayan suke mata kyau tasha adon ta dasu, da yake kayane masu daraja kuma ba wani shan jiki suke ba ake cire wa.
Dije da Aramma kuwa bata rabo dayi musu saban ɗinki duk zuwan da zasuyi, haka in zasu tafi sai ta soya Jar Miya mai yawa da nama ko kifi ta kaiwa Dije, banda sauran abubuwan buƙata.
Hatta kayan su Abdussamad in zasu bayar haɗa wa take ta kaiwa Lirwanu da Salisu, Safiya sam bata da rowa ga haƙuri da sanin ya kamata.
Wannan halin kyauta na Safiya ya sake siya mata so da Ƙauna a wajen dangin Mai Kano.
Aramma tsakanin shi da ita sai addu'a, Dije ma babu lefi tana godiya saidai ita a nata bangaren gani take duk wannan abubuwan da Safiya ke yi musu da kuɗin Mai Kano take yinsa dan haka ba wani burgeta abun yake ba, In Safiya tazo garin kuwa ta rinƙa binta da kallo sama da ƙasa tana gyaɗa kai. 

                 Sunada shekara Shida da Aure aka ɗaga filin kusa da su za'a siyar Sale ya faɗawa Mai Kano in yana so ya siya, dan wajen yayi kyau da sauƙi, Mai Kano ya samu Safiya da shawarar yana son ya sayi wajen amma kuɗin hannun shi baza su kai ba yana ganin kawai zai saida mashin ɗin sa sai ya cika kuɗin ya siya.
Nan fa Safiya tayi fir tace ba zai saida mashin ɗin sa ba, yana fita ta ɗauki sarkar bikin ta da Alhaji Manu taje bakin asibiti ta siyar yana dawowa ta bashi kudin duka tace "gashi nan ka cika ka siya saimu fara tara na gini."
Mai Kano yayi mata faɗan saida sarkar ta kamar zai ari baki, amma Safiya sai ta ce "kayana fa namu ne Baban Husna kaje ka biya Allah ya bamu na gini."
Mai Kano yaji daɗin abunda tayi masa a ranshi ya ci alwashin biyan ta sarkar ta da wacce ta fita.


Wata rana!!!
Safiya nawa Husna wanka tana mata tsarki ta faɗa mata in suna wasa a ƙofar gidan Mallam Malam almajiran sa suna musu irin wannan.
Sosai hankalin Safiya ya tashi da dabara ta tambayi Husna da waye da waye suke saka musu hannu a wando, ta faɗa mata suda ƴar gidan Malam Malam in suna wasan ɓuya da almajiran suke saka musu hannu a wando, yaro ba wayo tsaf ta faɗa wa Mamanta wa'yanda suke musu haka.
Abinka da yare Safiya bata tsaya fadawa Mai Kano ba washegari tayi dumamen safe tasa a kira mata almajiran nan da Hausa ta lissafa mata su, suna zuwa ta juye musu abinci tasa musu a ɗakin Baffa murna da ishe su saida ta bari hankalin su yayi kan abincin sannan ta rufe ɗakin ta ɗauki wayar rediyo data adana ta tun jiya ta rufe almajiran nan da duka Umman Abba (Matar Sale) tayi bugu da roƙon duniya Safiya ta buɗe ƙofa taƙi budewa almajiran suna kuka da ihu amma Safiya bata kyale suba saida tayi musu dukan tsiya sannan ta buɗe ƙofa suka fita suna kuka.
Bayan fitar su babu daɗewa saiga Malam Malam ya shigo gidan neman ba'asin dukan almajiran sa da Safiya tayi, nan fa tayi masa banza yin Duniya akayi da ita taƙi yin magana.
Dama haka take akwai ta da haƙuri da ɗauke kai amma fa in tayi fushi abun baya kyau tana da kafiya.
Mai Kano yana dawowa tun daga waje Malam Malam ya tare shi yana masifar ba zai yarda ba sai yayi ƙarar Matar sa.
Hankalin mai Kano a tashe ya shigo gida ya tambayi Safiya meya faru hankalin ta kwance tace "yarinya na zasu ɓata min hannu suke saka bama a wando."
Mai Kano ya dafe kai yace "amma da kin min baya ni na samu malamin su, da baki ɗauki hukunci irin wannan ba."
Ai fa anan Mai Kano yaga asalin fitinar Safiya dan burkice masa tayi saida Sale ya shiga cikin maganar sannan ta mutu, nan kuma tace ta gama zaman Hotoro.
           Wannan shi ne dalilin barin Mai Kano Hotoro suka koma Rimin kebe.

Ni'ima na yawan zuwa tayi musu kwana biyu, sosai Ni'ima da Husna suka saba ƴan uwan Safiya babu wanda baisan Ni'ima ba.

           .......Suna da shekara huɗu da komawa rimin kebe har lokacin Safiya bata sake haihuwa ba.
Watanni biyu da suka wuce ne kuma Allah yayi wa Alhaji Ƙadiri rasuwa bayan doguwar jinya daya sha, wannan mutuwa ta daki ƴaƴan sa da jikokin sa kai harda al'ummar unguwa, ansha jimami da rashin daɗin zuciya, bayan sadakar arba'in suka raba gado, gidan su na Birget Baba Habu ne ya siya yasa aka sake maida shi ginin zamani sannan yace su Momma suci gaba da zama a gidan tsawon rayuwar su, wannan karamci da Baba Habu yayi saiya sake haɗe kansu waje ɗaya.

                 Wata rana da Safiya ta kira da baƙar rana a tarihin rayuwar ta, suna zaune a soro ita da yaran ta sai sukaji dirar mota a ƙofar gida, Baffa ne ya leƙa da Dije ya fara cin karo yace "Lah Mama Iya ce tazo."
Safiya najin haka ta miƙe Dije ta shigo Wasu mata na biye da ita a baya, Safiya tace "kumu shiga ciki sannun ku da zuwa."
Matan suka amsa da fara'a Dije kuwa fuska a ɗinke tace 
"Yawwa."
Safiya bata Kawo komai aran taba suka shiga cikin gida, ɗakin kusa da ita ta buɗe musu dan yafi girma kuma a gyare yake suka shishshiga tasa Baffa ya karɓo musu ruwan sanyi a wajen Umman Bishira ta zauna suka gaisa tace "bari a ɗora muku abinci." Sukace "a'a yanzu zasu wuce."
Wata dattijuwa a cikin matan ta gyara zama tace "to yarinya ga Nana nan Allah ya sake yi mata dawowa gidan Mai Kano tunda zama bai ƙare ba, dan Allah kuyi haƙuri ku zauna lafiya."
Da rashin fahimtar inda zancen matar ya dosa Safiya ta kalle su da matar da aka nuna a matsayin Nana sai kuma tace "Mama ban gane inda zancen ya nufa ba?"
Da mamaki sauran matan suke kallon juna, to kamar ya ya bata gane ba? Kafin su sake magana Dije tace "ai ba zata gane ba dan ni na hana Mai Kano ya faɗa mata Nana zata dawo gidan shi, ni nace masa zan faɗa mata da kaina bayan Nana ta tare a gidan sa dan bana son ya faɗa mata Nana zata dawo a ɓata abun da biye biye."
Dije tayi maganar a gadaran ce, sauran matan da suka rako Nana duk sai suka saki baki dan basu yi tunanin jin haka ba.
Safiya kuwa sai ta bi Dije da ido dan harga Allah duk da taji mai suka ce tunani da ƙwaƙwalwar ta basu taɓa kawo mata Mai Kano zai yi Aure bata sani ba.
Miƙewa tayi ta fice tana ƙoƙarin gane abinda ke shirin faruwa, tana fitowa daga ɗakin tayi turus tana kallon mutanen dake shigowa da katifa da sauran tarkacen mu na mata.
Ɗakin ta ta shige ta bawa Husna kayan islamiyya tasa, tace "Maza kira Yaya kuzo ku tafi lokaci yayi."
Da sauri ta fice kiran Baffa ita kuma ta ɗauki waya ta kira Mai Kano amma har kiran ya katse bai daga ba, haka tayi masa kiran duniya baya ɗauka, abun ya bata mamaki dan abune da bai taɓa faruwa ba, wayar ta ajiye ta fito ta ɗora girkin dare Dije ta fito suda sauran matan nan ta buɗe musu ɗakin gefe suka shiga ciki suka zauna, ɗakin da suka fito kuma aka fara shiga da kayan Nana.
Gaban Safiya sai faduwa yake wani tashin hankali take ji yana taso mata amma haka ta danne cikin awa ɗaya ta gama jallof ɗin taliya ta zuba ta kai musu har ɗaki, matan jikin su duk a sanyaye suka karɓa suna godiya.

Karfe shida na yamma saiga Mai Kano da Sale Abokin shi kusan a tare suka shigo dasu Husna,  kamar yadda Mai Kano ya saba yau ma saiya ɗaga Husna ya dora ta a saman wuyan shi suna dariya suka shigo gidan, lokacin har sun gama gyara ɗakin Nana,  ɗakin baƙin suka shiga aka gaisa Safiya najin su daga ɗakinta ana masa alasanya alkairi sai lokacin taji wani gumi na zubo mata.
"Da gaske dai Aure Abdullahi yayi?"
Ta faɗa a fili tana kallon kofar shigowa ɗakin, zuciya na ce mata ta fita tayi masa rashin mutumci shida baƙin sa wata zuciyar kuma na hana ta zuwa.
Akan idon ta yayi sallama ya shigo ɗakin, ta kafe shi da ido, kansa a ƙasa ya kasa kallon ta, da kyar ya iya ce mata "Ki fito ku gaisa da Sale." Yana gama fadar haka ya juya da sauri ya fice daga ɗakin.

Zuciya nata ingiza Safiya karta fita dan wallahi ganin abun take kamar a mafarki, gani take kamar ba da gaske ba ne, Abdullahin ta data sani ko duniya ce ta taru tace mata zai yi mata haka bazata taɓa yarda ba. Amma bari ta fita daga iya gudun ruwan su.
Hijabin Sallar ta tasa ta fito cikin gidan dai-dai lokacin kuma matan da suka rako Nana suka fito zasu tafi dattijuwar ɗazu ta sake ce mata "yarinya kiyi haƙuri kinji? Allah ya baku zaman lafiya."
Sauran matan suka amsa da Amin Dije ta raka su har wajen motar data kawo su saida motar su ta tafi sannan ta dawo cikin gida.

"Safiya ƙaraso nan magana zamuyi."
Sale ya faɗa yana fuskantar ta.
Akwai mutumta juna sosai tsakanin ta da Sale dan mutum ne shi ba abokin yarwa ba.
Kan taburmar da suke ta  isa ta zauna daga gefe kamar wacce ta zauna akan ƙaya, sale yace "Safiya sai kuma kika ga Nana ta dawo ko?" Bai jira cewar taba yaci gaba da cewa 
"Wallahi Safiya abun ne yazo haka katsam babu shiri, ni shaida ne Mai Kano bai san da maganar ba, umarnin iyayen sa ne babu yadda zai yi dole yayi musu biyayya, kiyi haƙuri Safiya nasan ba'a kyauta miki ba amma kiyi haƙuri haka Allah ya tsara."
Bata san lokacin da ta dago ta yiwa Sale wani mugun kallo ba dan ita tama rasa taƙamaiman abinda yake son cewa.
Basu ji isowar Dije wajen ba saiji sukayi tace 
"Au saboda ka dawo da tsohuwar matar ka uwar ƴaƴan ka shine ka dakko Sale yake bata haƙuri Mai Kano? To saɓo kayi daka dawo da Nana ko wani mugun abu? da kake bata haƙuri haka sai kace wata uwarka."
Safiya a mamakan ce ta ɗaga kai tana kallon Dije dan ita tsawan zaman ta da Mai Kano bata san wannan fuskar ta Dije ba, "to dama haka take ko kuwa duk acikin shirin ci mata mutumcin ne ta canja hali?"
Safiya ta tambayi kanta, sai kuma ta miƙe tsam Sale na mata magana tayi ɗaki ta barsu anan.
                Mai Kano ji yake kamar ya haƙa rami ya bunne kanshi a ciki tsabar kunyar Safiya data rufe sa.

Idon Safiya ya bushe sai baƙin ciki dake cin zuciyar ta, Husna data fara bacci ta tasa tasa ta cire uniform ɗin ta tace taje tayi Alwala tazo tayi sallar Magarba, bata tambaye ta Baffa ba dan tasan yana rakota gida yake komawa sai anyi sallar isha'i yake dawowa gida saboda suna zaman hadda a masallaci.
              Tunda ta shige ɗaki bata sake fitowa ba Mai Kano yazo kanta yayi mata maganar duniya amma ko kallan inda yake batayi ba, da safe su Baffa na tafiya makaranta ta shirya ta kulle ɗakinta ta fice daga gidan.
                   Mai Kano sai fitowa yayi yaga ɗakin ta a kulle. Yayi shiru kawai yana kallon ɗakin, dama yasan za'ayi haka dan shirun Safiya yasan babu alkairi a cikin sa gwanda ma tayi faɗan yasan komai ya wuce amma sauda dama in tayi shiru irin wannan to abun baya kyau.
          Lokacin da Safiya taje gidan su da labarin abunda ya faru buɗar bakin Momma sai cewa tayi "haƙuri zakiyi ki koma ɗakin ki dama maza suna haka Safiya, wannan ai ba komai bane a shafukan halin ɗan Namiji."

Anyi dirama an kai ruwa rana saida su Baba Habu suka shiga cikin maganar sannan Safiya ta yarda ta koma gidan Mai Kano dan cewa tayi wallahi ta gama Auran sa, amma saboda dattako da riƙe alkawari irin na Ahlin Alhaji Ƙadiri suka danne ta ta koma, a ranar ne kuma tayi kukan rashin mahaifinta, dan gani take da yana raye bazai bar wannan cin fuskar da aka yi mata ba.
           Rai babu daɗi Maman Sama ta mai da ta ɗakin ta bayan ta sake bata haƙuri dayi mata nasiha.

Nan fa aka fara saban zama, farkon zaman Safiya tana ta ganin lefin Mai Kano da baƙin sa sai a hankali kuma ta fara gane ko kaɗan bashi da lefi, sannan duk abunda yasan zataji babu daɗi ƙoƙari yake ya kiyaye sa, wannan yasa Dije ta sashi a gaba da masifa kala-kala ta hana su zaman lafiya, tunda ta dawo da Nana bata barsu sun sarara ba kwanciyar hankali kuwa tuni tayi musu nisa a gidan....