10
by @aishatouuu
***
_________________
Tun kwanaki biyu da suka wuce akayi hutun makarantar Boko Baffa ya shirya kayan sa yace gidan Yaya Musa zashi hutu.
Safiya taso ta hana sa zuwa sai kuma tayi tunanin gwanda ma ya tafi hutun tunda gidan nasu yanzu babu daɗi ba wani sakewa yake yi ba Husna tafi kowa mitar tafiyar sa.
Da yamma Baffa yayi sallama da Maman shi da Husna ya tafi.
Washegari da safe Safiya ta fito da risho lungun dakin ta ta ɗora musu suyar dankali tana zubawa ta koma ɗaki danta dakko cokakin juyawa, tana fitowa ta tsaya turus tana kallon kan risho da taga an kifa kaskon sunyar akan sa mai da dankalin sun zube akai wasu kuma a ƙasa.
In ranta yayi dubu ya ɓaci dan tasan ba zube wa yayi ba zubar dashi akayi da gangan, tana tsaye Mai Kano ya fito ya ganta riƙe da cokali tana kallon risho.
Yace "Wani abune ya faru? A'a subhanallahi zube wa yayi?" Ya faɗa sanda yayi ido biyu da rishon da take kallo, ranta a ɓace tace "Ya zube ko aka zubar min, wai Abdullahi mene ne matsala ta da yan gidan nan?." Safiya ta faɗa bacin ranta na fitowa fili.
"Nice nan na zubar, sannan matsalar ki damu shi ne ki fita kibar min gidan ɗana."
Dije ta faɗa tana fitowa tsakar gida ta tsaya.
Mai Kano yana jin abinda Dije tace ya dafe kanshi yana ambaton sunan Allah a ransa, sai kuma yayi wajen ta yabar Safiya a tsaye.
"Iya dan Allah kiyi haƙuri ki daina wannan maganar, bafa wani abu tace ba, nina tambayi meya faru shi yasa kikaji tayi magana." Yayi maganar da fatan zata yi shiru zancen ya mutu iya nan.
Kamar wanda ya zubawa wuta fetur Dije ta dube sa sheƙeƙe tace "to baka isa ba, Mai Kano, nace baka isa ba wallahi, yau ba gobe ba wannan mara mutumcin matar da kake Aure saita bar gidan nan, kaji dai na faɗa maka."
Hayaniya da ruwan bala'in da Dije ke surfawa shiya fito da Nana daga ɗakinta ta cuge a ƙofa tana kallon su ɗaya bayan ɗaya .
Mai Kano ya tsugunna a gaban Dije kansa a ƙasa kamar mai neman gafara, tunda ta fara zazzaga masa masifar da ya kasa kane dalilin yin ta, yake durkushe yana bata haƙuri, duk abinda Dije take masifa tana lissafa wa ita kanta tasan ba'a yisu ba, san zuciya ne kawai da tsagwaron kin gaskiya.
Koda yake faɗan nata yayi kama da wanda ke jiran kaɗan ya sauke abinda ke ransa, in banda haka shi baiga abinda Safiya tace na tashin hankalin da zaisa Dije tana wannan maganganun ba.
"Na faɗa maka Mai Kano wallahi indai nice na haife ka yau saika saki wannan tsinanniyar arniyar mai baƙar ƙafa daka auro, wacce tunda ka Aure ta shekara goma sha biyu baka sake ajiye komai ba sai dai ka ƙare a gindin ta da ƴaƴan ta, gaka wahalalle, toba bawa na baifa miki ba, kinyi ƙarya wallahi sai naga bayan ki a gidan nan." Dije tayi maganar tana nuna ta da yatsa bakin ta na kumfa saboda masifa.
"Muguwa dangin jaraba, nifa dama shi yasa tun farkon kawo maganar Auran wannan mara cikakken musuluncin da kayi ba kaunar shi nake ba Aramma ne yafi ƙarfina amma da yaushe inaji ina gani kana cikakken Bahaushe zaka kwashi Beyerabiya? Shekarar ka goma sha huɗu da shigowa Birni neman kuɗi duk abokan ka da kuka fito nema tare sunyi gidajen kansu sun siyi gonaki sunada gidaje a kauye amma kai ka ƙare a gindin mace da ƴaƴan ta, saidai taci abinda take so tasa suturar da take so kai kullum kana tsaye kana nema ka kawo mata tayi yadda take so, har yanzu baka da komai sai a yawon haya ka ƙare, to wallahi tunda ita ba matar rufun asiri bace sai kun rabu, kai inma ƙaddarar rabon ce ta haɗa ku to daga yau na yanke ta, dama tunda tayi wannan abar ai bata sake haihuwa ba." Ta faɗa tana nuna Husna dake tsaye kusa da Maman ta, sai kuma taci gaba da faɗin.
"To ya isa haka ta fita taje can wani wajen ta shimfiɗa musu iko da baƙin halin ta amma ba a nan ba." Dije ta ƙarashe maganar bakin ta da babu haƙoran kirki fal da goro yayi ja duk ya furfurzo waje saboda masifa, a tsaya take akan shi har yanzu yana durkushe a gaban ta sai zufa yake saboda tashin hankali.
Tunda Dije ta fara ɗibar albarkar ta Safiya na tsaye a ƙofar ɗakin ta sanye da ƙaramin hijabin Sallah, Mai Kano dake durkushe kawai take kallo cike da tausayin sa, jira kawai take taga ikon Allah, dan halin masifar Dije har yau ganin sa take kamar a mafarki.
"Ka tashi ka sake ta yanzu a gabana basai anjima ba inba haka ba wallahi sai na ɗaga maka Nono." Dije ta sake faɗa tana gyara ɗaurin tsangalallan zaninta, da sauri Mai Kano ya dago yana kallon Dije idanunsa sunyi jawur a ransa yake maimaita kalmar "Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, wannan wacce irin masifa ce.."
Fech fesch fesss....Dije ta fache majina sai kuma tasa hannun zani ta goge hanci, ƙananun idanunta da tsufa da masifa suka sake ƙanƙantar dasu ta ware akan Safiya tace "to wallahi ubanki Ƙadiri ma yayi kaɗan bare ke ƙaramar haki, wannan ƙafafun nawa da kike gani babu inda basu shiga ba, nasha gaban ki a biye biye, fes nake kallon ki tunda yaƙi sakin ki ta arziki zansa ya sake ki ta tsiya."
Tunda Dije ta fara zuba masifar ta Safiya bata ce mata ci kanki ba sai yanzu da ta ambaci ubanta, take taji ranta yakai ƙololowar ɓaci to dama ran nata a ɓace yake, meya rage nacin mutumci da wulaƙanci wanda Dije bata yi mata ba? Babu sai wanda ta manta, tunda Dije take ci mata mutumci ta zageta ta tsine mata albarka a gidan nan bata taɓa zuwa inda take jin ba zata raga mata ba sai yau dan haka a fusace cikin ɓacin rai da Hausar ta da kana jinta kasan yare ce ta furta.
"Wallahi bazan yarda kina zagin iyayena ba dan ina auran ɗan ki, Abdullahi ka sake ni dan Allah nima na huta da masifar Mamanka."
Cikin Mamakin kalaman Safiya ya ɗago kai ya kalle ta sai kuma ya taso da sauri yazo gaban yace "haba haba Safiyya ba halinki bane maida magana, kiyi hakuri zan lallaɓa Iya zata haƙura dan Allah karki sake yin magana kinji?"
Nana da taji abinda yake cewa Safiya cikin izgilanci da zuga ta karkace ta rangaɗa buɗa, sai kuma tace "Ah lallai Iya kin mori Haihuwa."
Dije kuwa tunda Mai Kano ya tashi daga durƙuson da yayi a gabanta ya tafi wajen Safiya ta bisa da kallo baki hangame tace "kan uban nan, Mai Kano daga gaban nawa ka tashi ka tafi lallashin kafurar Matar ka?"
Kafin yayi magana Safiya tace "wallayi kina ganin kafurci a dangin ki amma mu duka iyayen mu babu kafurai." Ta faɗa tana rushewa da kukan baƙin ciki, itama Husna dake gefan saita fashe da kuka ganin Mamanta nayi.
Dije kuwa najin abin da Safiya tace sai ta ɗora hannu aka ta rusa ihu kamar wacce aka yi wa mutuwa tana faɗin.
"Mai Kano yanzu har nayi lalacewar da matar ka zata zageni a gaban ka kuma ka tsaya kana kallon ta?"
Sai kuma tsangal tsangal tayi hanyar ɗakin data sauka ta fara tattara kayanta a bakko tana faɗin.
"Gwanda na tafi na bar maka gidan ka tunda Safiya ta fini na barka da duniya da Safiya."
Kan Mai Kano yayi masa dum ya tsaya ya rasa inda zai saka kanshi saboda tashin hankali. Ganin Dije ta fito riƙe da bakkon ta a hannu mayafinta a kafaɗa tana kuka yayi wajen ta da sauri yana cewa
"Iya dan Allah ki rufamin asiri karki jamin zagi da fushin Allah, yanzu in kika tafi me kike so mutane suce a kaina?"
"Ka kori Uwar data haifeka akan Kafurar Matar ka." Dije ta faɗa, kanta rufe baki Safiya ta sake cewa.
"saidai kece Kafura Wallahi."
Nana ta ware Idanu tace "wallahi Mai Kano kayi asara agaban ka Matar ka ke zagin mahaifiyar ka harta kirata Kafura kanaji kana gani, hmmm lallai ka shawu."
Baiibi takan maganar Nana ba yaci gaba da ƙoƙarin hana Dije tafiya.
Ran Safiya a mugun ɓace ta shige ɗakin ta Husna ta bita a baya, bata jima ba ta fito ta canja hijabi Husna dake kuka na biye da ita a baya suka fice daga gidan ko kallon inda Mai Kano yake bata yi ba.
Kamar ta hana Husna binta sai kuma tayi tunanin inta hanata binta gunwa zata koma, wajen Nana da babu alkairi a bakin ta ko wajen Dije da take ji kamar ta sasu a wuta ta ƙona ita da Husnan, hannuta ta kama sukabi ta bayan layi.
Safiya taso ta wuce Birget gidan su sai kuma tayi tunanin yau Sunan Yaya Kemi gwanda taje gidan sunan tasan yanzu duka ƴan uwanta suna can, itama tun jiya da yamma taso taje ta kwana Mai Kano ya hanata, daidai transformer Ali Babur suka sauka, tana riƙe da hannun Husna har digan Yaya Kemi tun daga relar gidan ta fara cin karo da yaran ƴan uwanta suna ganin ta suka fara gaishe ta bata amsa ba ta shige cikin gidan.
Tawakallatu da Aunty Mansura dasu ta fara cin karo a bakin Famfo suna wanke hanji, afujajan suka ganta ta shigo idanunta sunyi ja sun kunbura, gaban Aunty Tawakallatu ya faɗi ta tare ta da sauri tana cewa "Ke Safiya lafiya kuwa daga ina kike haka?"
Aunty Mansura ma sakin wanke naman tayi ta dauraye hannunta suka taru a kanta suna tambayar ta lafiya, maganar Aunty Mansura tasa Safiya fashewa da kuka ta rungume ta.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, Safiya daga ina kike haka? Meya faru? Ina Husna? Wani abu ne ya samu Abdullahi?"
Ba ƙaƙƙautawa Tawakallatu ta jero mata tambayoyin lokaci ɗaya, kukan Safiya da hayaniyar su Aunty Mansura ya jawo hankalin sauran mutanen suka fito da sauri, ganin abinda ke faruwa su Aunty Sakina da suka fito daga ɗakin Yaya Kemi suka zagaye Safiya dake kuka sosai suna tambayar ta lafiya, Yaya Kemi ce ta kula da Husna dake tsaye a gefe tana kuka ta kamo hannunta tace "A'a Mamana zo nan, Sakina kama ta muje ciki."
A tsakiyar falon Yaya Kemi suka zaunar da Safiya dake kuka kamar ranta zai fita, Aunty Momi data fito daga uwar ɗakin Yaya Kemi hannuta riƙe da jariri tayi turus gaban ta ya faɗi tana kallon ƴan uwanta da suka zagaye Safiya, Tawakallatu ta cire mata hijabi ganin tana zufa, Aunty Mansura ta ƙara gudun fanka Yaya Kemi ta zauna a gaban Safiya sauran ƙannen ta suka zagaye ta.
"yi hakuri Safiya ki faɗa mana maiya faru, duka hankalin mu ya tashi."
Safiya sai tayi kamar zata danne kukan ta amma inta tuno maganganun Dije sai baƙin ciki ya taso mata ta sake fashewa da kuka, ganin haka yasa hankalin su Yaya Kemi sake tashi, tabbas duk abinda yasa Safiya kuka irin wannan ba karami bane, sunsa Safiya tanada hakuri ga zurfin ciki, ita ce ƙarama a cikin su amma duk ta fisu haƙuri sanyin hali da rashin san fitina, jikin su a sanyaye suka fara rarrashin ta da ban haƙuri da kalaman kwantar da hankali, ganin hankalin ƴan uwanta ya tashi ta daina kukan sai haɗiyar zuciya, ruwa Aunty Mansura ta bata tasha ta ɗan nutsu Yaya Kemi ta cewa Aunty Momi.
"kai Husnah wajen su Maamah kice su lallashe ta su bata abinci dan bana jin sun karya, itama Safiyar Tawakallatu haɗa mata shayi ta karya."
Muryar Safiya a shaƙe tace "ku bari bazan iya shaba."
Maimakon su bari ɗin kamar yadda tace sai Aunty Mansura ta miƙe ta haɗa mata shayin Aunty Momi kuma ta kama hannun Husna suka fita. Wajen yaran Yaya Kemi takai ta tace su kula da ita, sannan ta koma bangaren Yaya Kemi.
Da ƙyar Safiya tasha rabin kofin shayi amai ya taso mata saida ta amayar da shayin da tasha tass sannan ta wanke bakin ta Tawakallatu na dafe da ita suka dawo falon Allah sarki Yaya Kemi duk isakar falon saida ta haɗa dayi mata fifita da muhuci.
Saida tadan sake samun nitsuwa sannan tana share hawayen daya zobo mata ta kalli yan uwanta murya a karye tace "Maman Abdullahi ta sani a gaba, wallahi tunda ta dawo da Nana bani da kwanciyar hankali, Maman shi ta hana ya kwana a ɗakina saboda nace bazan iya cin girkin matar shi ba, ta hana sa shiga wajena, tace inya sake shiga ɗaki na ko bayan idonta ne Allah ya isa bata yafe masa ba, in inason magana dashi sai dai na fito mu haɗu a cikin gida shima tana jin fitowa ta zata fito ta tsaya a wajen wai karya kwashe kuɗi ya bani nayi girki tunda nafi ƙarfin naci wanda Nana tayi, ta hana mana kwanciyar hankali duk abun nan da take bana kulata tunda inada komai na amfani ko Abdullahi bai bani kuɗi ba yasan zanci abinci amma duk da haka tasa ni a gaba safe dare da rana masifa take, ita lallai bata yarda ba dole shi yake bani kuɗi a ɓoye, Husna bata isa taje kusa da Baban taba saita kore ta sai dai Matar shi da Ni'ima, komai ya kawo inya bawa Husnah sai ta kwace ta rage tace yayi yawa ita ce ƙarama wai danme zai bata kai ɗaya da yayarta, Matar nan ta hanani zama lafiya kullum masifa babu dare babu rana amma haka na haƙura saboda tausayi Abdullahi yake bani, wallahi duk ya rame saboda damuwa.
Safiya tashare hawaye tace
"Yauda safe......ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta faɗawa yan uwanta.
Aunty Mansura da tafi sauran saurin hawa da zuciya ta miƙe a fadace tace "ku tashi muje wallahi basu isaba."
Yaya Kemi ta kalli Aunty Mansura tace "kinga koma ki zauna muyi magana a nitse gidan nan da mutane kar kusa hankalin su ya dawo kanmu."
Jin labarin halin da Safiyya take ya ɓata ran su kowa ka kalli fuskarsa babu walwala ko kaɗan, babu abinda yafi ci musu rai irin yadda Dije ke zagin ubansu dake kwance a kabari da kiran su arna Kafurai, Shawara suka yanke, Tawakallatu Aunty, Momi da Aunty Sakina su raka Safiya gida ta dakko abunda take buƙata daga gidan sunan saisu wuce Birget gidan su dole Mai Kano yazo su Baba Habu su shiga maganar a yiwa Safiya tsakani da Nana da Maman sa. Wannan shawara ta Yaya Kemi tayiwa kowa dai-dai banda Aunty Mansura da taso suje suci ƙaniyar Nana da Dije daman ita akwaita da zafi ga faɗa, badan taso ba Yaya Kemi ta danne ta da faɗin.
"Ko babu komai Mansura saimu duba Abdullahi yana da kirki kuma duk munsan yadda yake son Safiya da kula da ita, duka Mazajen mu sunfi sa rufun asiri nesa ba kusa ba amma cikin mu babu wanda ya kai Safiya kwanciyar hankali da samun kulawar Miji, to kodan wannan muyi masa uzuri mu bari su Baba Habu su fara shiga cikin maganar komai zai yi daidai."
Wannan magana ta Yaya Kemi tasa duk jinkin su yayi sanyi dan duk sun sani sun kuma shaida Mai Kano na kaunar Safiya su kansu suna jinjina wa ƙoƙarin sa dan mutum ne mai wadatar zuci ga kirki da haƙuri, ko baka ganshi ba inya ganka saiya ma magana ya ma alheri inda yaro a hannuka baya rasa abinda zai basa koba yawa, haka baya gajiya da zuwa gaida iyayen su tun Alhajin su na raye, kuma har bayan mutuwar sa bai daina zuwa ba, duk lokacin da yaje gaida su Maman Sama baya rasa mezai kai musu dai-dai karfin sa, kai ko Mazajen su da suka dame shi a wadata da samu ba zasu nuna masa Alkhairi ba, baya gajiya Mazan su da matan su sun san haka sau da dama sukan ce "Safiya ke dai Allah ya dube ki yaga baƙin cikin da kika shaƙa a baya a gidan Alhaji Manu shi yasa ya wanke miki zuciya da miji irin Abdullahi, ko suce Allah ya baki Mijin marainiya." sun sha faɗa wa Safiya haka har basu san adadi ba, dan haka suke girmama shi.
Ƙaddara ta riga fata
..........Wannan komawa ta Safiya da ƴan uwanta gidan Mai Kano ita ce mafari silar faruwar komai.
Ita ce mabuɗin Ƙaddarar Husna
Ita ce dalilin wahala, mafarin shigar wani sabon lissafi cikin rayuwar Husna.
Wannan komawa ita ake kira da rashin sani wanda yafi dare duhu, tsautsayi wanda ba'a saka masa rana, tabbas da Safiya da ƴan uwanta sunsan da guzurin da zasu dawo daga gidan Mai Kano da basu jeba, da basu taka ƙafafun su a Rimin kebe ba.
Saidai masu iya magana sun ce "ita ƙaddar ta riga fata, haka bawa baya wuce ƙaddarar sa"
Wannan zanen ƙaddara ita ce ta faru da Rayuwar Safiya alokacin da ta saka ƙafafun ta a gidan Mijinta uban yarta Husna....
Da Sallama suka shiga gidan Aunty Sakina ce a gaba Safiya da Tawakallatu a baya, a tsakar gida suka tadda mutanen gidan Nana na zaune tana cin tuwo, Dije na kan taburma Mai Kano yana zaune a gefan ta.
Shi kaɗai ne ya amsa Sallamar jikin shi a sanyaye.
"A'a Baban Husnah kana nan ashe baka fita kasuwa ba." Aunty Momi ta faɗa.
"Um ina nan Aunty yanzu nake shirin fita, sannun ku da zuwa." ya faɗa yana kallon Safiya data wuce ɗakin ta.
Su Aunty Sakina kamar su wuce basu gaida Dije data haɗe rai kamar taga mutuwar ta ba sai kuma wata zuciyar ta tuna musu ko babu komai fa Uwar Abdullahi ce, Abdullahi kuma mutum ne harda ƙari dan haka taci darajar ɗanta da shima bai taɓa kin gaida nasu Iyayen ba.
Aunty Momi ce ta fara cewa Dije "Sannu da Zuwa."
Dije ta ɗago ƙananun idanunta fal masifa da bala'i ta kalle su goron data gama gogawa ta afa a baki sannan tace "nida gidan ɗana za'a yiwa sannu da zuwa? ko kuma Matar gidan Nana da gidan Mijin tane? Ai ku sannu da zuwa ta kama dangin naci da jaraba."
Mai Kano ya dafe kai kunya ta rufe shi kamar ya nitse saboda abinda Dije tayi, tabbas Iyaye iyaye ne musamman uwa da Allah da Annabi suka ce abita, bashi da yadda zaiyi da Dije sai dai yayi addu'ar Allah ya raba su lafiya.
Ran Tawakallatu a ɓace ta cewa sauran ƴan uwanta "dan Allah kumu je ciki."
"Bansan kinji haushi ba sai naji saukar duka shegiya Fatakarkara."
Dije ta faɗa tana furzar da goron bakin ta.
Suna shiga ɗaki suka tarar da Safiya harta haɗa kayan da zasu buƙata ita da Husna.
"Wallahi badan darajar tsufa da Abdullahi ba da sai naci mutuncin matar can." Aunty Momi ta faɗa ranta a mugun ɓace.
"Barta da Allah Duniya ce kanta take wa."
Cewar Aunty Sakina da jikin ta yayi sanyi da tijarar Dije, tabbas ɗazu labari Safiya ta basu yanzu kuwa da idan su suka gani.
Abdullahi naso yaje ya bawa su Aunty Sakina hakuri amma tsoron abinda Dije zata ce ya hana shi dama tunda Safiya ta fita yake lallaɓa ta da ƙyar ya samu ta haƙura da zancen tafiyar da tace zata yi shima saida ya mata alkawarin zai saki Safiya sannan ta dawo ta zauna, tabbas ba tafiyar tata yake tsoro ba sai abinda duniya da ƴan gari zasu ce a kanshi, alkawarin sakin Safiya kuma yayi mata ne kawai amma badan yanajin zai cika ba saidan ya samu ta fasa tafiyar.
Safiya ta fito hannunta riƙe da jakar goyo irin ta matafiya, Dije na ganin fitowar su ta miƙe tsaye tace "Mai Kano sake ta ta tafi gaba ɗaya bana son ta sake tako kafarta a gidan nan da sunan matar ka."
"iya yanzu muka gama magana nace miki zan sake ta amma ba yanzu ba." ya faɗa hankalin shi a mugun tashe.
"Saboda ita ta haife ka bani bako? Nonan Safiya kasha ba nawa ba ko?"
"Subhanallahi"
su Aunty Sakina da suka ji saukar zance wani iri suka faɗa.
"Mai Kano inka bari Safiya ta fita daga gidan nan baka sake taba Allah ya isa Nono na daka sha, Allah ya isa zaman da kayi a cikina, Allah ya isa renon ka da nayi bazan taɓa yafe maka ba duniya da lahira."
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! innalillahi wa inna ilaihirraju'un!! Innalillahi wa inna ilaihirraju'un!!!" su Aunty Momi suka faɗa da ƙarfi wani irin tashin hankali da tsoro na shigar su lokaci ɗaya, Safiya data ɗaga kafarta zata sa a soron gidan da zai kaita waje ta dawo da ita baya ta tsaya a wajen ƙam kamar wacce aka dasa, ita kanta Nana tuwon data saka a bakinta dawo dashi tayi, Mai Kano kuwa wata irin muguwar zuface ta karyo masa lokaci ɗaya kuma mummunan Zazzaɓi yayi masa mugun kamu idanunshi har rufewa suke saboda tashin hankali.
"Mai Kano saika zaɓi ɗaya ni ko Safiya da masifun cikin duniya?"
Dije ta sake jifan shi da muna nan maganganun ta.
Mai Kano da ƙyar ya samu ya miƙe jiri yana diban sa yayi taga....taga kamar zai faɗi cikin ikon Allah ya dafe bishiyar Dirimi da sauri ya tsaya kan ƙafafun sa, da taimakon Allah ya kawo kanshi inda Safiya ke tsaye idanunta sun bushe, tsawan minti biyu ya kasa magana jin kanshi yake kamar ana juya shi saida ya ambaci Allah sannan ya ɗauke idan sa akan ta a rarrabe kamar mai matsalar harshe ( Stammering ) yace "ki....k...ki gafarce ni." Sai kuma yayi shiru zufa na yanko masa kamar an zuba masa ruwa, saida yasa hannu ya yarfe gumin sannan ya sake kallon Safiya dake binsa da kallo kamar manyan idanun ta zasu faɗo ƙasa yace "Na...n.....na....sakeki saki ɗaya."
Yana rufe bakin shi Safiya ƙafafun ta suka sare ta kusa faduwa ƙasa ƙyauran ƙofar soro ta riƙe tana murmushin ƙarfin hali ta cewa Mai Kano "Inada ciki wata biyu."
Ita kanta bata zaci zaiji abinda ta faɗa ba bare ƴan uwanta dake bayan su, a zabure ya ɗago ya kalli cikin idon ta yana zare ido yace "ci....ci.....ciki dai na haihuwa Safiyya?"