GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 22

by @nusybee143

Page 22



A kaikaice Shaheeda ta kalle ta, sannan ta ɗauke kai, Abba ya dubi Hajiya Ruƙayya fuska a ɗaure ya ce "kishi kike yi da ita?

Saboda ba ke kika haife ta ba?"tsam Shaheeda ta miƙe, Abba ya ce "dawo ki zauna Fatima"

Shaheeda ta girgiza kai ta ce "Abba wani uzuri zan yi yanzu zan dawo"ta yi saurin ficewa daga parlourn don bata son rigima, kuma ta san halin Hajiya Ruƙayya,a kaf matan gidan ta fi kowa rigima 

Tana zuwa bayan ta yi wanka ta yi shirin kwanciya kan gadon ta ta haye ta cigaba da chat da Arnold, wanda har yanzu take mamakin sabo da shaƙuwar da suka yi,kuma take matuƙar jin sa a ranta 

Shaheeda ta cigaba da rayuwarta yadda ta saba a cikin gidan,ba ta shiga harkar kowa,amma duk wanda ya shiga tata ba'a rabuwa lafiya,kuma Abba ya goya mata baya sosai

A ɗaya ɓangaren kuma shaƙuwarsu da ta ƙara ƙarfi tsakaninta da Arnold, wanda har zuwa wannan lokacin babu wanda ya san da zamansa, Ummeey dai ta kula ta sake liƙewa waya,amma bayan haka babu abin da aka sake ganowa 

Yawancin hirarrakin nasu akan abin da ya shafi course ɗin da suke karanta ne,na software engineering,ya koya mata abubuwa da yawan gaske,wasu kuma yana gaya mata yadda zata yi 

A haka ta cinye hutun session gaba ɗaya,sau uku Muyassar yana dawowa a wannan tsukin amma gaba ɗaya bata wani ba shi attention sosai

Ta cinye hutunta lafiya,sannan kuma ta koma don ɗorawa daga inda ta tsaya 

Ranar da zata tafi kowa ya yi mamakin yadda ta kasance cikin farin ciki da ɗoki,amma babu wanda ya zargi wani abu, musamman yadda suka san Shaheeda take son karatun nan nata 

Muyassar ne ya mayar da ita makaranta,abin da ya ba shi mamaki ganin mutumin da ya zo zai ɗauke su ya kai su makaranta,ba kowa bane sai Arnold,kallo ɗaya Muyassar ya yi masa ya ɗauke kai,shima dai kallo ɗayan ya yiwa Muyassar ɗin sannan yake tambayarta hanya

Tana murmushi ta ce"hanya lafiya ƙalau,mun dawo

Arnold ga yayana Muyassar,yaya Muyassar ga babban abokina kuma malamina Arnold"ta yi maganar cikin harshen turanci 

Murmushi Arnold ya yi ya miƙawa Muyassar hannu suka yi musabaha, Muyassar ya daure ya miƙa masa,suka gaisa, sannan Muyassar ya dubi Shaheeda da take ta murmushi ya ce "to Shaheeda,ni dai zan wuce ko? tunda kin ga kin samu mai raka ki"ya karasa maganar yana murmushin yaƙe 

Shaheeda ta ce"kai yaya!don Allah ka raka ni mana,mu je tare

Ka ƙarasa ladanka Please!"ta ƙarasa a shagwaɓe 

Ɗan murmushi ya yi kawai yana satar kallon Arnold da ya naɗe hannu yana kallon su yana lumshe kyawawan idanunshi,da hakan ya zamar masa kamar ɗabi'a, sannan ya kalli Shaheeda ya ce "wani uzuri zan ɗan yi ne,but I promise you zan zo nan da few hours"

Babu yadda ta iya ta jinjina kai,ya ce "to yayana,sai ka zo, Allah ya tsare min kai a duk inda kake"ya yi murmushi sannan ya tari taxi ya shiga ya bar wajen 

Su ma motar Arnold suka faɗa suka wuce zuwa makaranta,suna zuwa Shaheeda ta sauka ta wuce hostel ɗin su,shima ya wuce nasu

Da yamma Muyassar ya dawo kamar yadda ya yi alƙawari,suna zaune a wajen da ɗalibai suke zama karatu,suna ta kallon mutane da suke wucewa jefi-jefi Muyassar ya dubi Shaheeda ya jefo mata tambaya 

"Shaheeda menene alaƙarki da wannan arnen?"

"Wanne arne?"ta faɗa tana kallonsa da fuskar mamaki

Ya ce"yaron da ya ɗauko ki a airport ɗazu "

"Oh!wai Arnold?shine arne?

Kawai abokina ne fa,kuma yana koya min karatu, shikenan fa"

"To amma ko ma dai yaya ne ya kamata ki san irin mu'amalar da za kuyi da shi,ko da a ce shi ɗin musulmi ne, bana son wannan mu'amalar da take tsakaninku ta wuce misali Please"

Shaheeda ta ce "yaya na san me nake yi fa,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah"

Muyassar ya ce"to Allah ya sa"ta amsa da "Ameen"sannan suka sauya hira 

Kwanan Muyassar biyu a Belgium ya koma UK, Shaheeda kuwa ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali 

A hankali rayuwa take gungurawa Shaheeda a makaranta,tana cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali,a gefe guda kuma ba tare da ta ankara ba, soyayya mai tsananin ƙarfi ta sarƙe tsakaninta da Arnold,wanda zuwa lokacin hatta mamanshi ta san Shaheeda,don tana yawan kawo musu ziyara har makarantar 

Muyassar yana iya bakin ƙoƙarin sa na ganin Shaheeda ta rabu da Arnold don tuni ya fara ƙyanƙyaso kamar akwai soyayya tsakaninsu,hankalinsa ya tashi sosai,amma kuma da ya tuna babu aure a tsakaninsu sai hankalinsa ya kwanta 

Inda tashin hankalin yake shine lokacin da Arnold ya kammala karatunsa, Shaheeda ta tabbatar da cewa tafiya zai yi,sai kawai ta fashe masa da kuka 

Da ƙyar ya lallashe ta, cikin karsashi ya ce"ki kwantar da hankalinki, yanzu lokaci ya yi da ya kamata iyayenmu su san halin da muke ciki,mu sanar da su, saboda kin ga lokacin karatunmu yana ta ƙarewa,ni na gama nawa ma, saura naki"

Kallonsa ta yi da sauri,ta ce"ba zai yiwu ba,aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba Arnold"

Gabansa ya buga,ya zauna a kusa da ita a ɗan rikice yana kallonta, kafin a hankali ya ce"meyasa? menene dalilin da ya sa kika ce haka?

Ko kin daina so na?"

Kai tsaye ta ce"soyayyarka na tabbatar da ita zan bar duniya,sai dai aure tsakanina da kai ba zai yiwu ba, saboda bambancin addini da yake tsakaninmu da kai"

Shiru Arnold ya yi yana kallonta, kafin ya lumshe idanu a hankali ya buɗe ya sake zuba mata su , cikin sanyin murya ya ce"

"To me zai hana ni da ke kowa ya yi addininsa tsakaninmu?

Ni ban damu ba ma,ko haifar yara muka yi su bi addininki babu matsala,ni dai ina sonki"

Shaheeda ta girgiza ta mayar da kan nata jikin kujerar da take zaune tana sauke numfashi,a hankali ta ce"hakan ba mai yiyuwa bane Arnold,a addinina bai halatta na aure ka ba,alhali kai ba musulmi bane"

Arnold ya ce"amma akwai wata ƙawar mahaifiyata da ƴarinyarta ta auri musulmi"

Shaheeda ta ce"ai dama ga mu mata ne,ga maza kuma babu matsala sosai"

Arnold ya girgiza kai cikin ƙunar zuciya ya ce"kenan a musulunci ana tauye mace kenan?

Da gaske ne bata da ikon yin abin da take so sai namiji?"

Shaheeda ta yi saurin girgiza kai,ta ce"aure a musulunci yana nufin namiji ne shugaba, shugabancin nashi bai tsaya iya bayar da Umarni ba,har ɗauke dawainiyar auren duka,don haka ya wajaba ga macen ta yi masa biyayya a abin da bai saɓawa Allah ba,to tun fari idan ta auri wanda ya kasance ba musulmi za'a iya samun gagarumar matsala, shine dalilin da ya sa"

Arnold ya jinjina kai a sanyaye,ya ce"na fahimta 

Yanzu menene abin yi?

Fatima kin san ina sonki sosai,kuma ba zan iya rasa ki ba,kuma bana fatan na ga wannan ranar a rayuwata,ki taimaka min Fatima,kar ki guje ni "

Shaheeda ta girgiza kai tana goge hawayenta ta ce"ba zai yiwu ba na gaya maka, muddin ba ka musulunta ba na tabbatar ba zai yiwu na aure ka ba"

Shiru ya yi na wasu seconds, kafin ya ce"to idan na musulunta zan iya?zai yiwu ki aure ni?"

Da sauri ta kalle shi cikin tsananin mamaki,ya jinjina kai cike da ƙwarin gwiwa,ya ce"soyayyar da nake yi miki zan iya sadaukar miki da komai,ciki har da addinina ma"

Ihun murna sosai ta yi tana godewa Allah, cikin tsananin farin ciki ta ce"na yi maka alƙawari,muddin ka musulunta ni kuma kai ne zaɓina,kaine komai nawa,ina sonka,ina matuƙar sonka Arnold"shima murmushi ya yi jikinsa a sanyaye,ta gyara zama ta ce"wanne suna za ka koma idan ka musulunta?"

Kai tsaye ya ce"duk wanda kika zaɓa min a shirye nake na karɓe shi "Shaheeda ta miƙe tsaye tana murmushi ta ce"tukunna dai, akwai wani course mate ɗina,yana karantar da mu addini sosai,zan kai ka ya ba ka kalmar shahada zuwa anjuma in sha Allah, welcome to the religion of peace sweetheart!"ta karasa faɗa tana murmushi, sannan ta miƙe tsaye,ya raka ta har bakin hostel ɗin su,sai murmushi suke yi cikin tsananin farin ciki 

Muyassar ta fara sanarwa da cewa Arnold zai musulunta,bai nuna mata komai ba a wayar,ya yi masa fatan alkhairi kawai, sannan ya sanar mata da zuwansa zuwa gobe don ya mayar da ita gida 

Bayan magriba da kanta ta zo har garden ɗin makarantar inda ɗalibai masu nacin karatu suke yawan zuwa,inda Arnold ya saba zama,ta ja shi suka tafi wajen Sheikh Mukhtar,wani course mate ɗinta ɗan asalin ƙasar Oman don a laƙanawa Arnold kalmar shahada 

Da kanta ta yi wa Sheikh Mukhtar bayani, shi kanshi ya yi mamakin yadda Arnold ya yarda zai musulunta saboda Shaheeda farat ɗaya,don ya san su Arnold iri su ne waɗanda suke da tsananin tsauri a addinin kiristanci 

Hakan bai hana shi farin ciki ba, ba tare da ɓata lokaci ba ya karantowa Arnold kalmar shahada, Arnold ya maimaita, aka ɗauki kabbara cikin farin ciki 

Daga nan kuma aka tambaye shi sunan da yake so a saka masa,tana murmushi ya nuna Shaheeda, wadda take jin kamar an yi mata gafara saboda tsananin farin ciki, Shaheeda tana murmushi ta ce "a sanya masa suna MUBARAK!"

Murmushi ya yi yana kallonta, Shaikh Mukhtar ya cigaba da yi masa bayanan abubuwan da suke Shari'a ne,bayan ya gama ya dubi Shaheeda ya ce"malama Fatima za ki iya ƙarasa yi masa sauran bayanin,don na san kin san abubuwa da yawa, Allah ya saka miki da alkhairi"Shaheeda ta yi murmushi, Sannan ta yi musu sallama suka tashi ita da Arnold suka tafi 

Har bakin hostel ɗin su ta kai shi tana murmushi,shi ma murmushi yake yi,ta ce"I'm proud of you Mubarak!

Kuma ina tare da kai duk runtsi,na san tarihin soyayya ba zai manta da mu ba"Mubarak yana dariya ya ce"na san sai an sake updating Romeo da Juliet,kuma mu za mu zama updated ones ɗin"dariya ta yi sosai,suka yi sallama,ta tafi shi kuma ya shiga hostel ɗin su 

Washe gari tun safe suke a tare,tana sake wayar masa da kai akan abin da ya shafi addinin Musulunci, kasancewar ya saka kanshi sai gashi yana ganewa sosai 

Ko da Muyassar ya zo don tafiya da ita kiri-kiri ta shaida masa ita ta fasa tafiya,ba zata koma Nigeria yanzu ba,da ya tambaye ta dalili kai tsaye ta ce "yaya ka ga Mubarak jiya ya karɓi musulunci,yana buƙatar koyon al'amuran addini sosai,kuma ka ga ni ya sani,ya kamata na zauna na koya masa"

A kufule Muyassar ya ce "Shaheeda yarinta tana damunki wallahi!

Ina malamin da ya ba shi shahadar?ki kai shi wajensa mana,ko shi bai san yadda ake koyarwar bane?sai ke uwar iyayi da neman suna?"

Tana kumbura baki ta ce"ni dai yaya gaskiya ba zan tafi na bar shi ba,ba gaya maka yana buƙatar kulawata, sannan yaya ka daina ce min yarinya, I'm matured enough, eighteen years nake don haka don Allah a daina ce min yarinya"

Gaban Muyassar ya faɗi sosai, don ya fara hangen wani abu dabam,ya daure ya ƙaƙaro murmushi yana faɗin "da alamu dai baby sister ta kamu ko?"

"Yaya kamuwa kamar yaya?"ta jefa masa tambaya 

Kai tsaye ya ce"kin kamu da soyayyar abokinki mana,gashi nan da yake ta karɓe ki har ƙiba kike yi abinki "

Ga mamakinsa sai gani ya yi tana murmushi sosai, ta ce"yaya soyayya akwai daɗi,kai ma ya kamata ka samu wadda zata dace da kai, you Will enjoy it ina gaya maka"

Tashin hankali! Muyassar ji ya yi kanshi yana juyawa,amma ya dake ya kalle ta ya ce"ai ni tuntuni na sami tawa sahibar zuciyar "

Shaheeda tana murmushi ta ce"wow!

A ina take yaya?tana da kirki?"

Kai tsaye ya ce"anan take,kai tsaye ma zan ce gata nan, ƙanwata,abar so na da alfaharina,farin cikin raina FATIMA SHAHEEDA!!!"

shiru ta yi na ɗan lokaci tana bin Muyassar da kallo idanu waje kamar ta ga wata sabuwar halitta, kafin ta yi ta maza, murya a dashe"yaya ka san me bakinka yake faɗa kuwa?"

"Na sani sosai Shaheeda,ba ki sani ba ko?

To da soyayyarki na rayu,tun daga lokacin da na fara riƙe ki a hannuna kina jaririya a raina nake jin na samu matar da nake so, kowacce daƙiƙa ta rayuwata tunda kika zo duniya da tsananin soyayyarki nake bugun numfashi Shaheeda,ke ce farin cikina,ke ce ruhina,don haka Please Fatima, don't break my heart Please, I love you so much my Queen!"




#Nusy_bee