Episode 8
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 8
“Ah ah Zahra ya naga kun taho daban daban ne yanzu naga Bahijja ta shigo sai kuma ke daga baya?”
Sauke lumfashi tayi tana aje ledar dake hannunta ta zauna kusa da Baba dake mata tabbayar yana zaune akan tabarma yana cin abinci.
“Baba ba komai, ai kasan halinta ita tayo gaba ne bata buk’atar tafiyar yau dan da kyar ma muka je da ita”
“Kira min ita”
Baba ya fad’a yana ci gaba da cin abincinsa.
D’akin Zahra ta shiga ta iske Umma na shirin sallah dan har an idar da sallar mangaruba suka iso lokacin Baban bai dad’e da dawowa daga masallaci ba.
“Kije inji Baba”
Bata kalle ta ba bata kuma amsa ba hakan yasa Umma dakatar da kabbara sallar tana duban Bahijja dake kwance akan kujera.
“Ba magana ake miki bane shin wai Bahijja?”
Turo baki tayi tana mik’ewa tsaye bata ce kanzil ba tayi waje.
“Kema karki zauna kije maza Kiyi alwala dan ita naga hutun sallah take”
“Eh yanzu dama zan tashi Umma”
Kabbara sallar Umma tayi ita kuma Zahra ta cire gyalen abayar ta aje da bak’ar ledar da Mama Oto ta basu kusa da Umma tana fitowa waje.
Fitowar tata taji Baba nama Bahijja fad’a abunda bai tab’a yi ba yana cewa.
“Bahijja bana son rashin had’in kan nan naku”
“Baba wani abun ta ce nayi yanzu kuma?”
“Ba wani abu ta ce kinyi ba, amma nasan halinki bana son irin hakan da kikeyi. Yanzu kun taho tare miya hana ku jero tare ku taho sai ace kuna tafiya daban-daban?”
Sosa kai tayi kanta kasa tana turo baki kamar yadda ta saba ta ce.
“To ni Baba uzuri ne yasa nayo gaba fa”
“Ni dai na gaya miki ku had’a kanku dan wata rana bamu bane, ya kamata kiyi hankali yanzu Bahijja”
Umma ce ta fito bayan ta idar da sallar, tana zama kusa da Baba ta ce.
“Ai wannan da kake gani babu ranar da zatai hankali”
“Haba dai zatai hankali ai ko yanzu k’urucciya ce ke d’awainiya da ita ai”
“Hmmm haka dai kake fad’a. Yawwa Mlm na manta ya maganar karatun yaran nan ne dan naji Yayansu Safiyanu ya ce an fara d’aukar d’alibai a makarantar su wai”
Shiru Baba ya d’anyi ya ce.
“Ina son dama nayi magana dasu ne Akan karatun nasu naji ra’ayin kowa”
Da mamaki Umma ta ce.
“Ra’ayi kuma Mlm? nake jin ai su duka suna son karatun nan ai ko?, kuma sana yanzu idan ba karatun ba miye zasu zauna suyi?”
“Ah aure mana Mmn Yara”
“Aureee dai?”
Umma ta fad’a da sauri dan ita gaskiya tafi son suyi karatun nan kamin azo ayi maganar wani aure duka nawa suke yaran?.
“Ni dai sai nake ganin da dai an barsu suyi karatun nan idan yasu ko suna cikin karatun ne idan mijin ya fito sai ayi”
“Hmmm A’a Mmn yara dan karatu insha Allah bazan hanasu ba, amma sai naji ra’ayin kowaccansu tukunna”
“Ai shikenan kaga gasu nan”
“Ke maza ki tashi ki kira Yayarki Zahra”
Tashi tayi ta shiga d’aki ta iske Zahra ta idar da sallah, tunda tayo alwala ta shigo tana jinsu gabanta sai fad’uwa yake Allah yasa kar Bahijjar ta kwafsa masu, to kodai Mama Oto ce ta kirasa ne?.
Bamai bata amsa hakan yasa ta sauke lumfashi mai zafi.
Shigowar Bahijja d’akin tana tsayawa akanta k’erere ta ce.
“Kizo Baba na kiranmu”
Tashi tayi tana duban Bahijja ta ce.
“Dan Allah Bahijja tsaya mu d’anyi wata magana dake”
Wani kallo ta jefa mata ta ce.
“Kinga Yaya Zahra ba wani abunda zaki gaya min ni naji sa a yanzu, kowanne ra’ayin zuciyar sa zaibi da abunda yaga shine dai-dai a tasa rayuwar, dan haka dan Allah please ki rabu dani da ra’ayina da nake akansa”
Tana idasa fad’ar hakan tayi waje abunta, Zahra tabi ta da kallon takaici, wato Bahijja bata da hankali wallahi kanta rawa yake. Sauke lumfashi Zahra tayi mai zafi had’e da girgiza kanta ta nufi wajan itama…………