Episode 9
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Episode 9
“To idan baccin ma rainin wayo ni zaki aje na tsare miki sanwa?”
“Ke kam Habi da waye kike haka tun d’azu ina jiyo ku a d’aki?”
Cewar Inna Ramatu data fito daga b’angarnsu. (Matar Kawu Sama’ila kenan).
Tab’e baki tayi tana nuna Mama dake zaune har lokacin tana hidimar sanwa bata kuma sake magana ba a wajan.
“Da waye nake fa idan banda Binta data gama ganin inda nake kwana?”
“Miya faru to wai?”
Inna Ramatu ta fad’a tana zama akan wani benci dake tsakar gidan kusa da Inna Habi.
“Wai fa tazo ta iske tukwanyar data d’ora akan murhu ta jirkice, a’a shine danmi bazan gyara mata ba?, saboda ga y’ar aiki ta aje a wajan ko?”
“Hmm Lallai ko ai raini ne ma hakan, shi ayo mutum sai kilbibin tsiya?”
Inna Sakina ce ta fito kishiyar Inna Habi (Matan Kawu Bature) tana cewa.
“Ni na rasa gane kanku a gidan nan, kun tasa baiwar Allah a gaba a rink’a duba gaba dai, ana kama girma don Allah”
Tashi Inna Habi tayi tana duban Inna Sakina bakin ciki cike a ranta ta nuna Sakina da yatsa tana cewa.
“Ban tab’a ganin wacce bata san kanta ba irinki, bari na gaya miki ki daina shiga harkata na gaya miki, bada ke nake ba nafi k’arfinki wallahi Sakina”
“To ai naga duk gidan nan dai kun matsa ma Binta miye ta tare maku ne ni ban gani ba?”
“To wai ke shin yaushe ma kika fara shigar ma Bintar fad’a ne ai bamu da labari uwar son a sani?”
Hararar Inna Ramatu Inna Sakina tayi tana cewa.
“Ai dad’in abun duk gidan nan bana shiga harkar kowacce mata kowacce gulma da k’ananun magana babu ni a ciki, dan haka ni banga abunda Binta ta tsare maku ba”
Tabbas Inna Sakina bata shiga k’ananun maganganu na cikin gidan batta dai da shegiyar rowar tsiya da bak’in kishi idan har abu ya had’u ta da kishiyarta Inna Habi sai anji kansu. Ko yanzu danta ga ita ce gaba-gaba wajan yadama Mama magana tun d’azu tana jinsu ta kasa hak’uri ta fito tana shiga maganar dan kawai ta bak’antama Inna Habi d’in, kuma tayi nasarar hakan.
Inna Dije data fito da turmi zatai dakan yaji ta dubi Inna Sakina ta ce.
“Rashin wayo ke damunki Sakina da alama da bak’in kishin banza irin naki wato dan Kinga Habi a cikin wannan maganar shine kikai tsalle kika dire kika shigarma waccar sumimi kasau d’in?, ai gaki ga ita, mu dai d’uwawu ne dole a zauna damu a’ato”
Duk abunda suke da maganganun da suke duk tana ji tana mamakin irin abubuwan da suketa fad’a akanta wadda ba gaskiya bane.
Sauri take ta gama abunda take ta bar tsakar gidan dan maganganun sun fara isarta sosai.
Da kyar ta mik’e saboda cikin jikinta daya k’ara girma sosai ta d’auki tukwanyar data gama abincin ta kai d’aki gaba d’aya ta dawo ta kashe wutar, duk abunda zatai anfani dashi ta d’auka ta shige d’aki tabarsu a tsakar gidan har lokacin suna sukarta da bak’ak’en maganganu………