GIDAN YAWA

Episode 10

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

TALLAH TALLAH TALLAH

RC: 8578922

RABEJI

TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.

Connecting worlds, Building futures.

IATA Accredited Agent

NANTA

QATAR AIRWAYS القطرية

aero taking you safely

AIR PEACE ...your peace, our goal

MaxAir

SAUDIA السعودية

TURKISH AIRLINES

Kenya Airways The Pride of Africa

EGYPTAIR

AWA AFRICA WORLD AIRLINES

TRAVEL & TOURS

- Visa Facilitation

- Ticketing/Reservation

- Hajj/Umrah Packages

- Packaged Tours/Cruise

- Hotel Booking

- Chartered Flight

- Honeymoon Planning

- Car Hired Services Home and Abroad

- International Universities Admission & Facilitation

- Consultancy Services

OTHER SERVICES

- Furniture Making

- General Farming

- Properties and Real Estate

- Import and Export

- General Registration

- General Contracts

- Clearing and Forwarding

- Food and beverages

Office Address:

Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano

Email:

***

Phone:

***

***

Episode 10

ZAHRA POV

Zama Zahra tayi kusa da Umma kanta a k’asa ta ce.

“Baba gani”

Ya dube su duka yayi gyaran murya ya ce.

“Abunda yasa na kira ku shine na tabbaye ku shin kuna da ra’ayin wuce wa karatu?, sana kuma wacce makaranta kuke so wanne irin karatu kuke da sha’awar yi?”

Zahra ta gyara zama tana d’agowa ta dubi Baba da fara’a ta ce.

“Ni dai Baba ina son makarantar kiwan lafiya ina nufin ina son karatun daya shafi Health”

“Madallah insha Allah zansa wani abokina Jafar yana koyarwa a school dake Kankia irin wacce kike so karki damu Mmn”

Murmushi ta k’ara saki tana jin burinta na zama d’aya daga cikin ma’aikatan lafiya zai cika insha Allah .

Dawo da dubansa yayi inda Bahijja ke zaune ya dubi yanayinta yana girgiza kai ya ce.

“Saura ke Auta ina jinki”

Kanta k’asa ta ce.

“Ni dai Baba bana son karatun nan dan……

“Keeee Bahijja wato baki san karatu baki ji kunyarmu ba kike fad’ar haka?, to wai tsaya ma mi kike so shin?”

“Kashhh Mmn Yara ki bari nayi magana da ita mana, kowa fa ra’ayinsa na tabbaye shi ai”

Shiru kawai Umma tayi bak’in cikin halin Bahijja na rufe ta. Zahra ma da mamaki kawai take kallon Bahijjar wato da gaske take bata buk’atar karatun dai?.

“Eh Baba bana son karatu iya wadda nayi ya isheni”

Jinjina kai yayi zaiyi magana Umma ta rigasa cewa.

“Karatun ubanmi kikai Bahijja?, Secondaryn ne kinyi karatu?, da har kike tutiyar ya isheki?”

Umma ta fad’a a zafafe.

“Haba Mmn Yara ya kike haka ne?”

“Haba Mlm Haba Mlm ka barni da ita kawai, wannan yarinyar to mi take so ta zama ne shin wai?”

“Yanzu dai Shikenan. Ke Bahijja idan ba karatun ba mi kike so?”

Saddar da kanta ta k’arayi k’asa tana wasa da hannunta tayi shiru.

“Bada ke ake magana ba hala?”

Umma ta fad’a tana harararta.

“Autata ko dai aure ake so uhum?”

Baba ya fad’a da murmushi sosai akan fuskarsa yana binta da kallo.

Ai ko da sauri ta mik’e jin abunda Baba ya fad’a da raha ta shige d’aki. Wannan abu da tayi shine yasa Baba gane auren take buk’ata kawai.

Baki sake Umma tabi Bahijja da kallo da zallar mamakin wawtar da tayi yanzu, tana girgiza kai.

“Tashi kije Zahra”

Baba ya fad’a hakan yasa Zahra mik’ewa jiki a mugun sanyaye ta wuce.

“Amma Mlm Kamar Bahijja wai aure?, aurenma bata jin kunyarmu ba ko nauyinmu ba?”

Murmushi kad’an ya saki yana duban Umma sosai ya ce.

“Ni ta birgeni, gara data fad’i abunda ke ranta bata cuci kanta ba bare gaba taja mana abun magana, tunda ta nuna auren take so shikenan za’ai mata yadda take so”

“Amma Mlm nidai idan har hakane Bahijja bata da wayon zab’ar ma kanta miji mai nagarta gaskiya, inaganin ka zab’ar mata da kanka sai yafi gaskiya hankalina sai yafi kwanciya”

Ganin yadda Umma take a rud’e da maganar yasa shi amsa mata da cewa.

“Shikenan zanyi nazarin waye ya kamata na had’ata dashi”

“Waye ya kamata fa Mlm kaba Nura dama mana”

“Nura kuma?”

“Nura dai wadda kuka had’a kakanni da Mahaifinsa Nura d’an gidan Muhammad Bawa”

Shiru Baba yayi yana zurfafa cikin tunani sosai kamin ya d’ago da sauri ya ce.

“Tabbas hakane zamuyi magana da Mama Oto dama d’azu kamin na shigo gida ta kira ni tana son ganina gobe zanje daga nan sai muyi maganar da duk ta dace”

“Shikenan hakan yayi Allah yasa hakan shine alkhairi a gare ta damu baki d’aya”

Da Amin Baba ya amsa, ya mik’e domin jin kiran sallar Ishsha da akeyi ya fita zuwa Masallaci.

********** “Yanzu Bahijja abunda kika zab’a ma kanki kenan?”

Wani duba ta tayi ma Zahra datai maganar tana tab’e baki ta ce.

“Shi naga ya dace da rayuwata dan haka babu abunda ya shafe ki a ciki, rayuwata ce ba taki ba”

“Naji rayuwarki ce, amma ke kina da wadda zaki fitar ne a matsayin Mijin auren?”

“Wannan kuma bai shafe ki ba Mlm”

Umma ce ta shigo basu san da shigowar tata ba jin abunda Bahijjar ke fad’ama Zahra yasa Umma nunata da yatsa cike da takaicinta ta ce.

“Ai idan dai aure ne Bahijja gaki gashi nan za’ai miki yadda kike so, tunda ke baki da hankali ba kuma kasan abunda ya dace dake a rayuwa ba. Sana kuma ki sani baki isa kawo mana wani ba wai a matsayin shine kike so mun riga da mun yanke hukuncin aura miki wadda duk mukaga ya dace”

Gaban Bahijja ne ya yanke ya fad’i amma duk da hakan bata ce komai ba sai shiru da tayi tana b’ata fuska. Itama dai a wajan nata babu wadda take so bare ta fitar, dama ta zab’i auren ne dan a barta a hankali zata zab’o wadda taga yayi mata amma tunda sunce zasu zab’a mata ai Shikenan batai magana ba dai bare suce sun sauya shawara dan yanzu abinda ta tsana shine karatu kuma bata San dalili ba.

“Amma Umma da an barta ta kawo wadda dai yayi mata ko zuwa gaba”

“Mtswww ke bana cike da shashanci kema, wannan d’in za’a bari wai ta zab’o Miji da kanta?, wadda bata da cikakken tunani bare hangen abunda zai dace da rayuwarta?. Mu munsan abunda zamuyi kawai kuma nan bada dad’ewa ba za’ai auren kamar yadda take so tunda shashace ita”

Umma ta fad’a tana niyyar shigewa uwar d’aka, Zahra ta tsaida ita tana cewa.

“Umma ga wannan bak’ar ledar inji Mama Oto ta ce a kawo miki”

Amsa tayi bata ce komai ba saboda ranta da yake a b’ace sosai…………

Book d’in nan na kud’i ne akan 1k kacal domin na kusa gama free pages hanzarta Ka biya domin tafiyar da kai

Account number 👉 8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Sai Shaidar biya 👉 ***