BARRISTER SUHAIL

44

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----44

Da yamma Zeenah ta shirya zuwa gidan mahaifinta

mami ta saka baba haladu ya kaita ganin tana ta kiran layin suhail baya tafiya wanda da gangan yayi hakan da baya san takurar zeenah ko wajen aiki ya tafi ta rinƙa kiransa ba tare da dalilin hakan 

wannan shine dalilin da yasa ya kashe wayar sa baki daya. 

zaune take a falon hajiya tunda. ta shigo gaisuwa kadai ta hadata da mahaifiyar ta samu waje ta jaɓe kan kujera sai ƙasƙas take da cingum din bakin ta

hakan bai damu Hajiya ba idan da sabo ta saba da halin zeenah indai ranta a bace yake zatayi fiye da Abinda tayi yanzu 

mahaifinta Alhaji ibrahim ya shigo falon iya kallon da yayi mata sa da tasa hantar cikin ƙada wa Alhaji Ibarhim baya wasa da zeenah tunda ya karanci halin yasa baya sakar mata fuskar shi kadai ne mutumin da ya isa ya ƙeta kara zeenah bata tsallaka ba 

Alhaji Ibrahim ya shigo falon.

Tun daga ƙofar falon idanunsa suka sauka kan Zeenah dake zaune kan kujera 

Alhaji ya shigo dauke da sallama a bakin sa Hajiya ta amsa 

Zeenah ta gaishe shi ha amsa ba yaɓo ba fallasa 

kallon ta kawai yake 

"Zeenah ina Suhail ya bar ki kika fito cikin Wannan shigar"

kare ma kanta kallo tayi ita bata ga aibun dressing din ta ba riga da wando ne kuma ta saka abaya a sama 

bata rai tayi ta ce"Abba what wrong with my dress dad'"

Alhaji Ibrahim ya girgiza kai

"zeenah you will never change ke kullum gani kike abinda kike kina kan daidai while is bad"

"ke matar aure ce ya kamata ki chanza dress dinki daga wanda kike anan"

Ya nuna ta da yatsa

nasha fada maki ki rage taurin kai,a iya shigar da kika yi ya tabbatar min da mijin naki ma baki girmamasa

zeenah ta hade rai 

"Abba yanzu dan nazo gaishe ka shine zaka tsitiyane da fada"

Alhaji ibrahim ya ce"To yaushe zaki taba ganin kuskuren idan ba a fada maki kar mi manta nan da kwanaki kadan you will be a Mother kinaso yaron ko Yarinyar ta taso da irin wannan tarbiyar taki Allah ya sani nayi baka cin ƙoƙarina a kanki"

Hajiya ta yi shiru tana saurarensu

Alhaji ya ci gaba da cewa

“Ki saurare ni da kyau”

“Suhail mutum ne mai hakuri sosai na san shi fiye da ƙima”

“Amma babu namijin da zai ci gaba da jure rashin kunya da gadara irin taki"

“Idan kina son aurenki ya dore, ki gyara halayenki"

Zeenah ta sunkuyar da kai.

Kalaman mahaifinta sun shiga zuciyarta fiye da yadda take son nunawa 

har ta fara tunanin ko Suhail ne ya kawo karar ta ga mahaifin ta Wata zuciyar na ce mata"Suhail could never to this kawai Abba yayi mata nasiha ne"

Alhaji ya mike tsaye.

“Ki ci gaba da wasa da aurenki idan kin so"

“Ranar da kika wayi gari kin rasa abin da kike takama dashi, lokacin ne zaki gane darajar ni’imar da Allah yayi miki ta zaba maki Suhail a matsayin miji"

Yana gama fadan Haka ya juya ya bar falon

Zeenah ta zauna cak.

Karon farko cikin lokaci mai tsawo tana jin tsoron kalaman da Abba ya fada mata 

Amman bataji alamun karaya a tattare da ita ba

iman na kwance kan cinyar ammi firgit ta tashi tunawa da tayi tawa Suhail Alkawarin dafa masa dambu gashi har la'asar ta wuce kallon ammi tayi ta ce"Ammi kina da tsakin masara"

"tsaki kuma iman mi zakiyi dashi"

"yaya Suhail ne yace na masa Dambu anjima zaizo yaci"

kallon da Ammi keyi mata yasa taɗan ji kunya saukar da kanta tayi ƙasa tana murmushi 

Ammi ta ce taje Kitchen ta duba cikin Sa'a ta samu 

nan da nan ta fara hada wuta tana tsaka da aikin malan ya shigo da mamaki ya ga iman tana girki 

ya ce”iman daga zuwa kuma Sai girki ai kya ma Bari ki huta ko”

Ammi dake fito wa daga daki ta ce"malan ai girkin tane"

malan ya kalli iman

"girkin ta kuma"

"eh mana wai Suhail zata wa dambun"

murmushi malan yayi yace"ohh nagane"

bai kara magana ya koma daki Ammi ta gyara mata zogalen 


karfe shidda ta kammala komai ta jera abincin cikin sabuwar kulla da Ammi ta dauko mata a gefe kuda kuma ta hada masa lemun kankana da Malan ya aiko

bayan sallar isha'i motar Suhail tayi parking kofar gidan Malan 

malan na zaune tare da dalliban suna darasi ya nufo su cike da girmamawa ya gaishe da kowa 

tare suka shiga ciki da malan Ammi na zaune tsakar gida ta gama Sallar tana karatun Alkur'ani suka shigo ciki 

suhail har ƙasa ya risina ga gaishe da ita ta amsa cike da fara’a Ammi har mamakin ladabin Suhail take 

 A dakin Malan ya zauna Ammi ta shiga dakin iman fitowar ta Kenan daga wanka ta shirya tana saka wani blue lace Tana Shafa powder Ammi ta shigo “Idan kin gama kije dakin Malan Suhail na jiranki”

“To Ammi”

A gaggauce ta ƙarasa shiryawa bata san so adadin nawa ta kai tana duba agogon tana zaman jiran Suhail ba 

hijabin ta sa har kasa ta dauki kular Dambun zuwa Dakin malan cikin tafiyar mai kama da pareti 

Tun daga ƙofar ɗakin idanun Suhail suka sauka kanta

Blue hijab ɗin da ta saka ya ƙara fito da hasken fuskarta 

a gaban sa ya ajiye abincin har lokacin bai sauke idanun sa daga kan taba 

waje ta samu ta zauna ta gaishe ya amsa 
Ganin yadda idanunsa suka ƙi barin kanta yasa ta sunkuyar da kai tana wasa da gefen hijabinta

Rabon da ya ga Iman cikin irin wannan annurin tun watanni da suka shuɗe

ganin taƙi magana ya ce"iman You counsel  missed You"

hannu tasa ta rufe fuskar tana murmushi 

kular Dambun ya daga kamshin zogalen ya cika hancinsa take ya lumshe idanun sa

spoon ya dauka ya fara kaiwa bakin sa daɗin girkin ya hanasa fadar abinda yayi niyyah baisan lokacin da ya cinye kusan rabin kular ba 

Iman sai kallon sa take idan yayi wani abun har dariya yake bata 

sai yaci ya koshi ya soma santin abinci  

“Amman dai Ammi ce tayi girkin Nan”

Murmushi tayi ta ce Ba wata Ammi ba, Yaya Suhail Ka dai ce girkina ya yi maka daɗi.

"You said my mind”

Wani irin natsuwa yake ji duk lokacin da yake tare da ita

hira sukayi sosai da iman daga bisani ta dauko wayar ta ,yayi mata setting abubuwa 

bashi ya bar gidan Malan sai karfe tara na dare ya fito kenan yaya Mubarak na shigowa hannu ya bashi suka gaisa duk da ba hakan ya saba masa ba 

yaya Mubarak tun sanda Suhail ya kara aure yafi kowa jin haushin sa shi kansa Suhail ya lura da chanjin fuskar da ya samu wajen yaya Mubarak 

Iman ta buɗe kalli yaya Mubarak ta ce"sannu da zuwa yaya"

"yawwa" kawai ya ce ta shiga ciki 

Suhail bai samu damar yima Ammi sallama ba har kofar gida iman ta raka sa ta dawo ciki 

A dakin Ammi ta iske yaya Mubarak yana sauke Kayan sa tana lura da  yadda walwalal sa ta ragu lokacin da ta rako Suhail 



Like 
Comments and share