MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

Bayan kwana biyar da dawowar su Papan ya fara shirye shiryen gagarumar walima na sunan 'ya'yan nasa. Zuwa sannan labari ya karade ko Ina acikin Masarautar da wajenta akan batun ya dauko 'yar riqo daga America, duk da har zuwa wannan lokacin ahalin gidan basu yarda an bude zancen na cewar tsintar yarinyar akayi ba, sai mutane suka dauki zancen akan Papa ya taho da yar riqo ne, amma sanin daga gurin waye dinne kuma kowa ya kasa fahimta, duk qwaqwai din 'yan gulma a dangi haka suka fara hakura, dan ko Momma haka taja bakinta tayi shiru akan Fadwa dan abunda take binnewa a zucyarta kadai ya isheta. Ana gobe hidiman ne 'yan'uwanta Aina'u da Madina suka iso daga Abuja suma. Kasancewan isowar dare sukayi nan da nan Papa ya aika driver aka daukosu, bai shigo sashen ba har saida suka huta suna cin abinci, cikin mutuntawa suka gaisa sannan ya juya tareda nufan kofa ya fita sai Momman ta dan bi bayansa da kallo fuskarta a dinke, ganin haka yasa Aina'u ta ajiye spoon din hannunta tace "Banason wannan abun da kikeyi Binta, a bayyane yake abun naki ya fara wuce gona da iri" sai Momman ta sauqe riganta data daga tana shayar da Khadijan, sai da ta ajiye ta a gefenta nan kan kujera sannan tace "Ni me nayi kuma Adda?" Madina ta kalli Aina'un itama ta dan tabe baki bata bar cin abincinta ba, sai Aina'un tace "Kin fini sanin abunda kikeyi ai, ke abu baya wucewa a gurinki ne wai?" caraf Madina tace "Fisabilillah sai kar ta nuna bacin ranta bayan an mata ba daidai ba" nan Momma ta kalli Madinan tace "Ai ita Adda a kullum ko me za'a min a gidan nan bata taba ganin laifinsu sai nawa, bayan kuma a ko da yaushe ni ake duka sannan a hanani kuka. Meye nawa dan nayi kishin soyayyar mijina da ta 'ya'yana?" Aina'u na kallonta tace "Wannan son zuciya ne kawai Binta, ba wani kishin soyayya, kina magana kamar wadda mijinta ya qauracewa gaba daya a rayuwa" tace "A yanda muka dauko wannan hanyar ni dashi daf muke da shiga wannan fannin, Adda wai ni zai nunawa 'yar tsintuwa ta fini da 'ya'yana a idonsa" rai a bace Madina tace "Toh wai ni meya hanaki rabasa da yarinyar tun a can ne?" Aina'u ta banka mata harara sannan tace "Banason irin haka Madina, kema watarana in kina abu kamar kanki a kunce" Momma tace "Ai gaskiya take fada nima da nawa sakacin kuma zan dauki mataki nan bada jimawa ba dan bana hada soyayyar mijina da kowa bayan 'ya'yana a gidannan wallahi, ko Uwah haka tayi hakuri ta barni, dan haka baza'a fifita d'an wani data kasance bare akan 'ya'yana kuma akan Idona sannan nayi shiru ba" Ainau tace "Yanzun har yaushe ma  ya dauko yarinyar da zaki rinqa yin irin wannan maganganun? Grow up mana, it's high time ki rinqa tantance abunda ya dace da wanda be dace ba" tana kallon Yayartata ta wani hade fuska "Menene abunda bai dacen ba? Dan nace banason yarinyar?" Aina'u ta amsa da "Eh mana! Toh in kikace bakyason ta kina son kiga shima ya qi yarinyar ne, ya kike so yayi da yarinyar toh in ke baki jata a jikinki ba" Madina tace "it's obvious ai Adda, sai ya bada ita a wani wajen daban tunda matarsa bata so. Simple" Aina'u dake jin ranta na baci da qannen nata tace "Banason Ina magana kina saka min baki Madina, wannan raini ne kina jina? In bazaki tayani mu dorata akan hanya me kyau ba sai ki rufemin baki" sai Madinan ta juya kanta tana hade rai, can kuma ta ajiye spoon din hannunta ta miqe sai Momman tace mata "Me kikeyi har yanzu baki koma gidan ba?, aure da saura wata biyu" saida ta zauna akan kujeran dake kusa sannan tace "Sai nan da sati hudu zan koma, mitan Mama dayawa wallahi, komai sai tayi fada akai" Aina'u tace "Sai kace bamusan halinki ba" sai Madinan ta kalleta tace "Adda ki fito fili kice in bar miki gidanki kawai" tace "Meyasa zance ki bar gurina Madina, kema kinsan duk fadan da nake miki suna bayan soyayyar da nake miki ne" Momma tayi murmushi tace "Madina duniya, da sai ince to kizo nan muyi zaman mu kawai" Aina'u tayi saurin cewa "Ai saidai bayan Idona zaku zauna guri daya a irin wannan lokacin, sai ta zauna ta tayaki uzzirawa mijin naki kenan" sai duk suka fashe dariya Madina har da kyakyatawa, nan kuma twins suka shigo tareda Kasim da shima yake sa'ansu, Imran na ganin Madina ya fara murmushi sai ta daga masa hannu da nufin suyi shake tace "My boyyy" yana dariya ya miqa hannunsa sai Kasim kuma ya zauna a gefenta. Idon Aina'u na kan Imam tunda ya shigo har ya zauna a kujerar dake dan gefe dasu yayi kwanciyarsa dan daman sun gaisa tun zuwansu, sai tayi murmushi tace "Imamu ana nan da hali dai" Momma ta juya tana kallonsa itama, tace "Sai ki rasa me yake dannewa a cikinsa da bazai fitar ba, ayi mutum sai dan banzan zurfin ciki" sai ya juyo yana kallonsu bai ce komai ba, Aina'u ta sake yi masa wani murmushin tace "Kaci abinci?" ahankali ya amsa da "Eh" ta sake cewa "Me yake damunka?" sai gani sukayi ya dan yi murmushi tareda girgiza kansa, Madina na kallonsa tace "Allah ya baki daya Adda Binta" nan ya miqe tareda nufan gurinta yace "Kai Anti" ta dan turesa tana dariya tace "Ni ka matsa min daga nan jare, kana ganina ai ka dauke kai" bai fasa kwanciyan a gefen nata ba sai ta kyalesa ta cigaba da hiranta tareda su Imran da Kasim.
Can suna zaune daya daga cikin hadimar Momman ta shigo Mai suna Laure dalilin kiran da uwar dakin nasu ta mata, sai da Momma ta gama lissafo mata abubuwan da zata mata sannan ta kalli Yan uwan nata tace "A kawo muku ita ne?" Aina'u tace "Jinjirar?" ta gyada kai sai Madina tayi saurin cewa "Mezamu mata in mun gantan Adda?" Kafin Momman ta amsa sai Aina'un ta dubi Laure tace "Ki kawo ta kinji" da haka Lauren ta amsa a ladabce sannan ta juya ta fice. Bata dade ba ta dawo falon dan sanar musu an kaita gurin Uwah, Momma ta tabe baki batace komai ba ganin yaransu na zaune dasu agurin. Suna cikin hiran Aina'u ta miqe a sannu zata shiga dakin Momman, dan itama cikine a jikinta na wata shida, 
Sai Maimuna ta shigo falon hannunta riqe da yarinyar ta mai suna Sajida dake da shekara daya da wasu watanni, komawa tayi ta zauna da fara'arta dan sun san juna kuma suna zumunci da juna a Abuja. Maimuna ta qaraso ta zauna sai Twins suka mimmiqe har Kasim din suka fice. Saida suka gama gaisawa sannan Maimuna tace "Anti Binta sai hakuri fa, naji maganganu na tashi akan lamarin yarinyar nan" Momma tace "Uhm, kuma babu yanda aka iya dani ba, masu maganan sai su karbi riqonta ai ba laifi" Aina'u ta dan dafa kafar Momman amma sai tayi biris zata cigaba da maganan, nan da nan Aina'u tace "Ai dama sha'ani irin haka sai an hada da hakuri" Madina ta gyara zama tana tabe baki a fakaice, dan itafa tun kafin ta ga yarinyar ma taji ta fita ranta sanadiyar matsalan da yayarta ke samu akanta. Maimuna bata bar sashen ba sai da Momma ta fada mata kusan duk abubuwan da suka faru tun a Houston, Aina'u dai miqewa tayi daga qarshe ta shige dakin Momman dan tayi uzurinta, dan in ta cigaba da zama tasan tsaf zasu hau sama su fado itada qannen nata, kuma agaban faccala.

Ansha hidima sosai dan 'yan uwan Momma sosai suka zo gurin taron daga Bauchi. Ganin yanda kowa in yazo yake tambayar jinjirar da aka taho da ita yasa Uwah ta aika hadimarta zuwa sashen su Momman aka taho mata da Fadwan dan ta matsar da ita daga idon mutane, dan har zuwa sannan idanuwanta a bude suke tana lura da yanda al'amuran yarinyar zai tafi a gidan d'an nata, saboda zuciyarta taqi aminta da cewar matarsa ta karbi yarinyar kamar yanda ya fada musu. Wunin ranar sai ya zamto ita ta kula da yarinyar da taimakon babbar hadimarta Laraba. 
Har aka gama hidiman aka watse Momma bata nemi sanin inda aka kai Fadwan ba haka zalika ko da yan uwanta sun tambayeta inda Yarinyar take bata dogon zance akai. 
Sai washegarin ranan su Aina'u suka fara shirin tafiya, sai da suka gama kintsawa tace da Madina "Muje muyi sallama da Uwah yanzu" da haka suka fito Babban falon sashen sai suka hadu da Papa da shima shigowarsa kenan tareda Abdulrahman a biye dashi, gaisawa sukayi dan rabonsu dashi tun daren da suka iso sai dai Momma taje sashensa sannan ta koma wajensu, sai gamuwar tasu tayi wuya. Da fara'arsa yace "Mun gode da hidima fa Maman Kasim" ya kalli Madina "Mungode Khadija"  fuska a sake Aina'u tace "Ba komai mune da godiya, Allah ya raya zuri'a" yace "Amin, an kawo muku yar'uwartata kun ganta kuwa?" cike da waskewa tace "Eh mun ganta, Allah ya taya riqo ya bada lada", sai Papa ya amsa da "Amin summa Amin, ba dai ayau zaku koma ba" nan ma tace "Yau ne, zuwa anjima in Allah ya kaimu" sai yace "Okay Kamal zai kaiku" ya juya ga Abdulrahman dake bayansa yace "See to it please, yazo da wuri kar su jirashi" ya amsa da In sha Allah sannan su Aina'un sukayi godiya, Papan ya sake cewa "Agaishe da Honorable da Allah, mungode sosai" ta amsa sannan suka fice shikuma ya nufi nasa sashen. A falon Uwah suka sameta tareda wasu matan dattawa guda biyu, bayan sun gaisa aka kawo musu kayan ciye ciye sannan tace da Laraba ta dauko musu Fadwan. Da ta fito da yarinyar sai ya zamto Madina ce ta kusa da ita amma sai ta kafse taqi karbanta wanda yasa Aina'un miqa nata hannun da sauri ta karbi Fadwan dake nannade a towel tana bacci, da fara'a tace "Ma sha Allah, Uwah kinga yarinya tas da ita" fuska a sake Uwah tace "Sai Ma sha Allah" tace "Allah ya taya riqo yasa ta zamo cikon addinin muslinci" Matan ne suka riga Uwah amsawa sannan itama tace Amin tana lura da Madina da tace "Allah ya raya".

Bayan kwana biyu Uwah ta kira Papa zuwa sashenta da dare, ita kadai ya samu zaune riqe da Fadwan a hannunta tana jiran isowarsa, sai da suka gaisa sannan  ta fara magana cikin nutsuwa "Ban kasance mai kai idanuna acikin gidanka ba sai wannan karon da yazama dole, da farko banyi niyyan saka hannuna a lamuran da suke tafiya da iyalinka ba amma gudun sai ta baci azo ana dana sani yasa zan yi magana" sai Papa yayi shiru yana sauraronta har ta sake gyara zama ta yi masa tambayan dake ranta tun dawowarsu qasar "Shin da amincewar matarka ka dauko marainiyar Allah'n nan kamar yanda ka fada mana?" da fari shiru Papa yayi sai kuma ya d'an sauqe numfashi sannan yace "Har yanzu muna fahimtan juna akai tukunna" sai itama tayi shiru tana kallonsa. Tasan za'ayi haka dan tun ranar zuwansu taga hakan shimfide a fuskar matarsa amma sai ta kawar da komai. Jin shirun nata yasa Papa yace "Babu matsala in Allah ya yarda, nasan zata kula da ita" sai ta dan hade fuska tace "Shine har aka gama waliman aka kwana biyu bata nemi yarinyar ba?, Yau kwana uku kenan jinjirar nan tana hannuna, ai ko ba komai sai ta biyo bayan 'yarta indai har ta karbeta a matsayin hakan" nan kuma Papa yayi shiru yanajin bacin rai na taso masa, ta sake cewa "Amma ba damuwa, yarinya dai in har riqonta zai zamo da mishkila sai ku bani ita in riqe ai" sai lokacin ya dago yana kallon mahaifiyar tasa, a nutse yace "Da yardar Allah za'a gyara hakan" sai tayi murmushi sanin cewa a kaikace yake fada mata bazai iya bata yarinyar ba, ganin haka sai shima ya sake cewa "Inason ta taso cikin 'yan'uwanta ne su shaqu, a ganina ta hakan ne zasu samu hadin kai da junansu batareda sun wareta ba" kadan ya rage Uwah bata tabe bakinta ba saboda a yanda tasan matar d'an nata zuwa yanzu ma ta ware yarinyar daga cikin 'ya'yanta, sai kawai ta danne komai tace "Allah ya rayasu gaba daya" ya amsa da Amin. A daren ranan tasa aka maida Fadwan sashen nasu gurin Habiba ta cigaba da kula da ita.

Bayan sati biyu Papa ya shirya tafiya Abuja, a inda babban companynsu yake aiki. Tafiyarsa America yasa Abdulrazaq daya kasance daya daga cikin executive directors yake running a gurbinsa while Abdulrahman kuma yake running branch dinsu na Kano. Sai yanzu da dawowar shi Papan tasa zai cigaba daga inda ya bari dan shine President a Empire din nasu sannan Mai martaba kuma chairman gaba daya. A ranar da zai tafi sai da ya sake maganan kulawan Fadwan da Momma, suna zaune tana tsiyaya masa tea dinda hadimarsu ta kawo masa while shi kuma yana duba wasu takardun da zai tafi dasu gurin aikin. Sai da ta gama zuba masa sannan ya ajiye takardun ya karbi Khadijah dake riqe a hannunta daya, sai tace "Da ka fara da tea din tukunna" bai amsa ba ya cigaba da wasa da Khadijan, sai can ya dago yana kallonta yace "Fatima, fadamin ya zakiji in ace yau ba kya raye kuma aka rasa mai kula mana da Khadijah" sai ta hade girar ta cikin rashin fahimta, ya sake cewa "Ina miki kwatancen hakan ne da yanda har yau kika kasa karban Fadwa a qarqashin kulawarki" sai ta dinke fuska tace "Koda 'yan'uwanka basu kula dasu ba nasan nawa 'yan'uwan bazasu taba barin 'ya'yana a wulqance ba" ya sake danne komai sannan yace "Kika sani ko ita tafi namu 'ya'yan gata amma Allah ya rabota da kowa nata" sai ta dan juya kanta rai a bace ba tace komai ba, anutse ya sake cewa "All I'm saying is that, sai ka taimaki wani sannan Allah zai dubi naka a rayuwa Fatima, Think about it. Banason yarinyar nan ta taso ta fahimci tun tana da qarancin kwanaki a duniya kika gujeta da duk abunda ya shafeta, bamuda tabbacin me Allah ya ajiye mata a gaba, me zata zamo agaba, ko kuma wani irin kaddarar ce a harde tsakaninki da ita. Akwai mutanen da ko baka son kusancinsu a gareka sai Allah ya barsu a kusa dakai na har abada babu rabuwa, wanda babu yanda zakayi in baka so su ba. Ki fara taming zuciyarki tun yanzu a kanta in ba so kike Allah ya gwada ikonsa a tsakanin ki da yarinyar nan ba" da haka ya dauki shayinsa ya fara kurba amma har sannan bata juyo da kanta ba tana kallon Tv dake aiki a falon.

Free page 

Bintu Musa ✍️