SIRRIN ZUCIYA

Chapter five

by @aysharano22

🤍SIRRIN ZUCIYA🤍

By Aysha Rano✨

🤍YOTA🤍

Book 1.

Ƙofar na buɗewa ya turata da leg ɗinshi ya shiga ciki, sai ga wani ɗan madaidaicin parlor wanda ba wani tarkace ne a ciki ba daga furnitures sai su tv da tv stand, sai curtains da ɗan decorative items kaɗan amma tsayawa faɗar kyawun da yayi ma is a waste of saliva.

Bedrooms biyu ne cikin parlon suna kallon juna amma akwai distance a tsakaninsu…anan parlor ya ajiye su school bag ɗinta sannan ya nufi one of ƙofofin dake cikin parlon ya tura ya shiga ciki sai ga bedroom shima madaidaici, kai tsaye kan gado ya nufa ya lallaɓa ya kwantar da ita kmr jaririya, ya zare mata hulan dake kanta nan take gashinta mai kyau da santsi sak irin nashi ya bayyana…tattare gashin yayi ya ɗaure mata shi wuri guda ya sake gyara mata kwanciya kafin ya mike ya rage kayan jikinshi sannan ya faɗa bathroom yayi freshen up ya fito sanye da bathrobe.

Cream ɗinshi kawai ya shafa haɗe da perfs sannan ya nufi closet ya ɗauko armless shirt da wando three quarter duk farare ya saka ya maida bathrobe ɗin bayi sannan ya dawo yana kallon Kiara and at the same time yana duba agogo sbd sanin da yayi ba lallai ta wani ci abinci mai yawa ba a school gashi kuma tana ta bacci.

Fita yayi zuwa parlor ya ɗau lunch bag ɗinta ya duba yaga da gaske kuwa ba wani cin abincin tayi ba don gashi nan ta dawo dashi gida, kawai sai ya girgiza kai tare da komawa cikin ɗakin…ɗagota yayi gaba ɗaya bayan ya zauna gefen gadon ya ɗorata a jikinshi yana ɗan jan siririn dogon hancinta yace

“Pookie Uto”
(Uto yana nufin wake up or get up)

Ganin kmr bata san me yakeyi ba ya sake jan hancin wannan karon da ɗan ƙarfi ya sake cewa

“Ut na Kiara tumhe kuch khaana parega.”
(Wake up Kiara you have to eat something)

Buɗe idanuwanta masu kama da nashi tayi a hankali ta saukesu kanshi, cikin muryan bacci sosai tace

“Appa.”

Miƙar da ita zaune yayi yana cewa

“Tashi muje ayi wanka sai azo a ci abinci.”

Ba tayi musu ba ta gyada mashi kai tana murza ido shi kuma baiyi wata-wata ba ya kinkimeta suka shiga bathroom.

Da kanshi yayi mata wanka sannan ya naɗota a towel ya fito riƙe da ita a hannu kmr ’yar jaririya sai wasa sukeyi kmr wasu abokai…zaunar da ita yayi kan wani small pink vanity stool da kana gani dama zaka san nata ne ya shiga shafa mata oil ɗinta a jiki.

Yana gamawa da oil ya shafe mata jiki da baby perfumes ɗinta ya gyara mata gashinta ya tufke mata shi, sannan ya ɗauko wani ɗan ƙaramin tracksuit ɗinta dogon wando da riga itama mai dogon hannu lemon green ya sanya mata sbd sanyin da yaji ana yi a garin.

Da ganin yanda yakeyi mata komai zaka gane ba ƙaramin sabawa yayi ba don duk wani abu da uwa mace zata iya yima yaro Ayaan ya iyashi kuma yana yi ma Kiara tun tana jaririya…yana sa mata hula a kai ya riƙe hannunta suka fita parlor daidai lokacin da take ce mashi

“Papa Uncle Lee bai dawo ba.”

Murmushi yayi sbd yanayin yanda hausar nata ke fita abin dariya ne yace

“He said he’ll be back a little late today…are you missing him already?”

Kai ta gyada before tace

“Yeah, and he said zai taho min da popsicle.”

Kai kawai Ayaan ya gyada mata daidai lokacin da ya buɗe deep freezer dake cikin kitchen ɗinsu ya shiga kallon abincin da suka masu saura a ciki before ya dawo da kallon ga Kiara da itama sai leƙa freezern takeyi yace

“Me zakici?”

Kmr jira take ya rufe bakinshi cikin sauri kuma da ƙarfinta tace

“Pastaaa.”

Jan bakinta yayi da hannunshi cikin kwaikwayon muryanta shima yace

“Pastaaa.”

Kai ta sake gyadawa tana murmushi tace mishi

“Yes.”

Dauko container da pasta ɗin ke ciki yayi ya debo daidai wanda yasan zai ishesu su biyu, yasa a microwave yayi setting sannan ya maida sauran cikin freezer ya rufe sannan yaja hannunta suka koma parlor, sai bashi labarin school take yana biye mata.

Bayan few minutes ya koma kitchen ya duba abincin da yasa a microwave yaga yayi sannan ya fito dashi yayi musu dishing, ya haɗa da chilled pulpy orange duk ya haɗa musu a tray ya sake komawa parlor.

Kan coffee table ya ajiye abincin, tun ma kafin ya kirata ta matso kusa dashi tana kallon abincin daya ajiye ɗin tace

“It looks yummy Papa.”

Gira ɗaya ya ɗage yana dubanta yace

“Really?”

Tace

“Haan.”

Yace

“Theek hai lets eat.”
(Theek hai means ok)

Ba musu ta sauko ƙasa ta zauna kusa da table ɗin shima yayi exactly irin yanda tayi ya tura plate ɗin abincin gabanta ya miƙa mata fork dake hannunshi, ta amsa kenan zasu fara cin abincin aka turo ƙofar parlorn daga waje.

A tare suka maida blue eyes ɗinsu kan ƙofar daidai lokacin da wani saurayi da zaiyi kmr 28 years ya shigo cikin parlon sanye da kananun kaya kana ganinshi kaga cikakken bayerabe.

Wara idanuwa Kiara tayi ganin wanda ya shigo lokaci ɗaya kuma ta mike da gudu ta nufi inda yake tana ihu sbd murnar ganinshi tace

“Welcome my Uncle Lee.”

Ɗagata yayi cak ya shiga juyi da ita cikin parlorn yana cewa

“Thank you Pookie, I missed you so much.”

Tace

“I missed you too, where’s my popsicle?”

Ledan dake hannunshi ya ɗago yana nuna mata yace

“Here.”

Ihu ta ƙara saki zata amsa ledan daga hannunshi yace

“No, not now… sai kin ci abinci.”

Ba musu ta gyada kai tana ci gaba da smiling ɗinta tace

“Theek hai.”
(Ok)

Pecking forehead ɗinta yayi yana cewa

“That’s my girl.”

Kallonsu kawai Ayaan keyi da blue eyes ɗinshi yana ta sakin smile sbd ganin wannan bond dake tsakanin su biyun nan da duk faɗin duniya a yanzu bashida wanda ya fisu, sune duniyarshi gaba ɗaya.

Sai da suka gama rungume-rungumensu suka shigo cikin parlon yana ɗauke da ita.

Yana ganin abincin da har yanzu ke gaban Ayaan untouched ya wara ido tare da ƙarasawa wurin ya zauna da sauri ya ɗauka fork yana ƙoƙarin fara cin abincin yace

“Kamar kasan yunwa nake ji.”

Daga haka yakai loma ɗaya na abincin bakinshi har wani lumshe ido yake yana girgiza kai.

Janye abincin Ayaan yayi daga gabanshi yana zabga mashi wata harara yace

“Why did you lied when I asked ko zaka dawo gida da wuri?”

Harara shima Lucas ɗin ya watsa mashi yana cewa

“I didn’t lie I was just teasing you.”

Ya ƙarasa mgn yana kashe mashi ido ɗaya before ya sake cewa

“And plus am missing my baby.”

Ya ƙarasa mgn referring to Kiara dake jikinshi yayi pecking head ɗinta.

Ayaan bai sake cewa komai ba ya ajiye musu abincin akan table aikam da sauri Lucas ya cigaba da ci…itama Kiara tasa fork ɗinta suna ci tare.

Shi dai miƙewa yayi don yasan bai zama lallai abincin ya ishesu ba kai tsaye ya shiga kitchen don yayi warming wanda zaici.

Ya gama diban abincin kenan yana ƙoƙarin sakawa a microwave ya jiyo Kiara na coughing daga parlor…baisan time daya saki plate dake hannunshi ya koma parlon da sauri ba.

Tari sosai yaga takeyi sbd shaƙewa da tayi da abincin, Lee na riƙe da ita yana ƙoƙarin bata drink a baki amma kmr numfashinta zai ɗauke…da gudu ya isa inda suke yayi wani irin sufa ya zube a ƙasa cikin hanzari ya janyota jikinshi shima ya shiga buga bayanta yana cewa

“Hey Pookie relax…take a deep breath okay?…take a breathe.”

Ba ta ma san me yakeyi ba sbd tsananin tarin da takeyi…lokaci ɗaya hankalin Ayaan ya tashi duk ya gigice ya ma rasa yanda zaiyi da ita.

Ɗago idanuwanshi da suka cika taf da ƙwalla yayi yana kallon Lucas da shima nashi hankalin ke tashe yace

“Do something Lucas, she’s not breathing.”

Karɓanta Lee yayi daga hannunshi ya ɗauki ruwa da sauri ya shiga ƙoƙarin bata a baki…da rarrafe Ayaan ya matso kusa dasu ya miƙa hannunshi bayanta ya cigaba da shafawa yana ɗauke hawayen dake ƙoƙarin zubo mashi da ɗayan hannunshi.

Tana shan ruwan kuma kmr haɗin baki sai tarin ya ɗan lafa mata, ya zamana ta daina yinshi da ƙarfi kmr yanda takeyi dazu…a haka har sai da ta daina gaba ɗaya sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya kmr wacce taci kuka ta ƙoshi.

Rungumeta Lee yayi a jikinshi yana kallon yanda Ayaan ke ta faman kai hannu yana ɗauke hawayen da ke ta sake ciko idanunshi…nan da nan blue eyes ɗinshi sukayi jajir haka tip of his nose abinka da farin mutum, wai don ma ba fa kuka yayi ba kawai hawaye ne.

Kallonshi kawai Lee keyi da ganin yanda ƙirjinshi ke heaving zaka gane ba ƙaramin bugawa zuciyarshi keyi ba…hannunshi ɗaya ya miƙa ya ɗora kan ƙafarshi sannan yana dubanshi cikin son ya kwantar mashi da hankali yace

“Relax, she’s fine now.”

Kasa cewa komai yayi kawai yana girgiza mashi kai, daidai lokacin Kiara data gama dawowa cikin hayyacinta ta ɗago daga jikin Lee idanuwanta da sukayi jaa suka sauka kan babanta da yayi saurin yin ƙasa da nashi idon sbd ko kaɗan baya son taga hawayen dake cikinsu.

A hankali ta matsa kusa dashi ta kira sunanshi, ganin bai kallonta tace

“Appa.”

Kasa cewa komai Ayaan yayi kawai ya jata jikinshi ya rungume tsam yana jin yanda faɗuwar da gabanshi keyi yana raguwa a hankali.

Lee yayi relaxing yana kallonsu yana murmushi as duk tsahon shekarun nan basu sa ya daina mamakin wannan son da Ayaan ke ma yarinyar nan ba…ƙwarewa kaɗai idan tayi fita daga hayyacinshi yake balle ace yau Kiara na kwance ba lfy haka zaiyita jinyarsu su biyun don kusan haihuwar guzuma akeyi wai ’da kwance uwa kwance, ita ba lfy shima ba lfy.

Bayan kusan mintuna goma tayi bacci a jikinshi sai a sannan ya ɗagota yana goge mata oil ɗin abinci da yayi saura a bakinta.

Miƙewa Lee yayi ya amsheta daga hannun Ayaan ɗin ya kama hanyar bedroom yana cewa

“Let me take her inside.”

Da kallo kawai Ayaan ya bisu har suka shiga bedroom ɗinshi, sai ya koma yayi relaxing jikin kujera tare da lumshe ido. Har yanzu bugun zuciyarshi bai gama dawowa daidai ba.

Lee na shiga ɗakin ya kwantar da ita kan gado ya lullubeta da duvet yayi pecking forehead ɗinta sannan ya juya ya fita ya rufe ƙofar a hankali gudun kar ya tasheta.

Parlor ya dawo ya iske Ayaan har yanzu jingine jikin kujera ya lumshe ido…a hankali ya ƙarasa kusa dashi ya zauna ya janyo table da abinci ke kai ya ajiye a tsakiyarsu kafin yace

“Oya lets eat.”

Buɗe idanuwa Ayaan yayi yana kallonshi, zaka rantse wani ɗan baby ne if you see yanda yayi da face ɗinshi.

Murmushi Lee ya saki yace

“Come on now…lets eat.”

Girgiza kai Ayaan yayi kmr baya son mgn yace

“I..lost my appetite.”

Kallonshi Lee ya cigaba dayi kmr bai fahimci abinda yake nufi ba lokaci ɗaya kuma ya shiga girgiza kai tare da buɗe hannayenshi yana dubanshi da murmushi a fuskanshi yace

“Alright come here.”

Tsuke baki Ayaan yayi yana kallonshi kmr wani baby.

Lee ya sake ware hannayen yana dariya ƙasa-ƙasa yace

“Come noww…I know it’s what you want, so come.”

Bai sake mashi gardama ba ya cikashe gib dake tsakaninsu ta hanyar shigewa tsakanin hannayen nashi yayi hugging nashi so tight kmr yanda shima Lee ɗin yayi hugging nashi yana ɗan shafa bayanshi in a consoling manner, don yasan abinda yakeso kenan shiyasa yake making such faces.

Haka nan suke tun tale-tale Lee bai taɓa gajiya da consoling ɗinshi ba duk yake cikin yanayi irin wannan musamman daya kasance Ayaan ɗin mai raunii ne sosai dole yana buƙatar kulawa ta musamman.

A waje za’a ganshi very strong ba’asan he’s actually very soft and fragile ba from the inside, he’s always emotionally dependent on Lucas.

Har yanzu smile bai bar fuskar Lee ba yace

“It’s ok, common small chock ɗin ka ke ma wannan abun.”

Shi dai Ayaan bai iya ce mashi komai ba, shima bai damu yace ɗin ba ya cigaba dayi mashi bayani

“Abincin da take ci ne yayi choking ɗinta kuma gashi yanzu ta ware har tayi baccinta ma kai kana damun kanka.”

Sauke ajiyar zuciya Ayaan yayi kafin murya a raunane yace

“I almost got a heart attack.”

Lee na cigaba da shafa bayanshi yace

“I know…sorry.”

Wani ajiyar zuciyan ya ƙara saukewa kuma har yanzu yana rungume dashi ya kasa sakinshi yace

“Kuma tayi bacci ba taci abincin ba.”

Lee yace

“Don’t worry idan ta tashi sai a bata tea.”

Ajiyar zuciyan dai ya ƙara saki karo na ba adadi, cikin ranshi kam gode ma Allah yake daya haɗashi da Lee cikin duniya da baisan ya rayuwa zai kasance mashi babu shi ba.

He’s been his biggest supporter kuma comforter a duk lokacin da yake buƙatar hakan…he’s always there for him and his child he never gives up on him, he never turn his back on him, he never judged him…honestly speaking Lee is among the best things that has ever happen to him in his life, nobody will understand how much he means to him.

Girgiza kai Lee ya shiga yi jin shirun da yayi, yana dariya yace mashi

“You know sometimes I use to wonder how could somebody like you have a baby when you are also a baby.”

Dagowa yayi yana kallonshi, lokaci ɗaya kuma ya bata rai yana ɗan turo bakinshi yace

“Am not a baby.”

Tun bai rufe baki ba Lee yace

“Oh yess you are…my dear you are just a baby look at yanda ka gama min kuka yanzu.”

Hannunshi Ayaan ya kama ya shiga dubanshi da dukkan seriousness yace

“Thank you so much Lee..I dont know what I’ll do in this life without you.”

Hannunshi Lee ya riƙe yana ɗan bugun shoulder ɗinshi da nashi shoulder ɗin yace

“C’mon will u stop that already…you know I gat you.”

Kai Ayaan ya gyada mashi yana murmushi ya amsa mashi

“Yeah I know, and am grateful.”

Patting bayanshi Lee keyi yace

“It’s fine…now can we pls eat, yunwa nakeji.”

Kai Ayaan ya gyada tare da cewa

“Theek hai.”
(Ok)

Shima kan ya gyada mashi yana cewa

“Theek hai.”

Daga haka suka shiga cin abincin, duk da shi dai har yanzu hankalinshi na kan ’yarshi ne, to yanzu idan bata tashi taci abincin ba fa?…ai dai bai kamata ta kwana da yunwa ba ko?…amma idan abincin ya ƙara choking ɗinta fa?…

Sai da gabanshi ya faɗi duk da cewa tunani ne kawai, nan da nan yayi watsi da tunanin ya maida hankali kan abincin da yake ci don ko kaɗan baya son wannan over thinking ɗin nashi.

Shi kanshi yasan he over thinks alot especially kan duk wani abu da ya shafi Kiara.




Rano✨