14
by @aishatouuu
_Aiahatou_
***
______________
"Oho Safiya ce dai ta tafi kuma in sha Allahu ta tafi ke nan, ba wa'azi ba in kaso ka sauke Kur'ani, duk rashin daɗin zama dani kuma nida kai mutu ka raba." Dije tayi maganar a ranta tana barin wajen tayi cikin gida ranta a ɓace.
Bayan tafiyar Dije Mai Kano ya rinƙa bawa Aramma haƙuri tare dayi masa bayanin abinda ya faru suke da ba komai ya faɗa masa ba, Aramma yaji kan zancen sai abunda dije tayi yayi masa ciwo, sai kuma tausayin ɗan nasa ya kama shi da irin uwar da Allah ya basu.
Sosai ya kwantar masa da hankali ya kuma yi masa nasiha tare da addu'ar alkhairi, anan Salisu ya zo ya same su shima yaji babu daɗi dajin abinda ya faru, ya tausaya wa ɗan uwanshi, ya sake karfafa masa kuwa da cewa.
"Kayi haƙuri Yaya Mai Kano Iya bata da daɗi mu kanmu da muke zaune tare wallahi haƙuri kawai muke da ita, Allah dai ya raba mu lafiya."
Nan suka haɗu sunata hira har lokacin Sallar la'asar yayi suka yi alwala suka fice masallaci.....
Shigowar dare sukayi saboda basu baro ƙyauye da wuri ba, Nana ta samu gidan babu datti ko ƙura irin wacce mace kan samu in ta kwana biyu bata gidan ta saboda Mai Kano kullum saiya share gidan kanya fita haka inya dawo da yamma, kan ya kwanta kuma saiya gyara ɗaki da inda zai kwanta.
Ɗan abinda baza'a rasa ba kawai Nana ta sake gyara wa ta kunce musu dambun da suka taho dashi suka ci suka kwanta.
Mai Kano kuwa tunda suka taho sabgar gaban sa kawai yake Nana ko kallo bata ishesa ba komai zaice saidai yayi wa Ni'ima magana saboda haushin ta yake ji har yanzu.
Washegari bayan sun karya wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe ya ɗauki Nana a bayan mashin suka tafi Bamfai dan shi kansa ya fiso a tsorata masa ita sosai kan Husna ta dawo gidan inba haka ba komai na iya faruwa nan gaba, saboda yasan halin ta farin sani bajin magana take ba.
Bai samu matsalar shiga ba dan sun yi magana da Yaya Ja'afar kanya taho.
Tunda suka fito Nana a tsorace take ai batayi asalin tsorata ba saida suka shiga cikin Bamfai taga taron ƴan sanda tako ina, ga yara ƙanana da manya masu lefi wasu an kawo su hannu sanye cikin handcup, wasu yan uwan su sun zo neman beli suna kukan neman taimako, wasu kuma sun zo ganin nasu babu dama.
Gaba ɗaya jikin Nana saiya kama rawa cikin ta ya kulle, to sashen masu manyan lefika na Bamfai suka shiga kuma wajen ne da ko Namiji ya shiga in yaga yadda wajen yake dole zuciyar sa tayi rawa hankalin shi ya tashi bare mace, macen ma irin Nana da bata da wayewar rayuwa bata taɓa experiencing abu makarancin wannan ba, matar da bata taɓa zuwa ko gaban mai anguwar garin su ba yau ita ce a cikin tsakiyar Bamfai tsamo tsamo ai dole taji tsoro.
A ranta kuwa ta tsinewa Zahira da shawarwarin ta yafi cikin carbi, duk halin firgicin data shiga Mai Kano yana kula da yanayin ta yana mata dariya a ƙasan ransa, wallahi yau fes yake jin zuciyar sa dama da gangan ya roƙi Yaya Ja'afar a tsorata ta da kyau yadda kashe din zai shiga kunnen ta da ƙwaƙwalwar ta ya zauna sosai ba tare daya sake nina mata shiba, in ba haka ba kuwa nan gaba sai baƙin halinta yasa ta tayi kisan kai taja masa masifa.
Yaya Ja'afar na haɗa su da Abokin aikin shi Asp Zawaciki wanda Case ɗin yake hannun shi ya fito yabar musu office ɗin dan baya so yayi Case ɗin da kansa haka baya so ayi a gaban sa.
Nana da Mai Kano suna zaune a gaban Asp Zawaciki ya ɗago fuskarshi babu rahama da sauƙi ko kaɗan yace "ke ce kika yiwa yar kishiyar ki dukan mutuwa ko?"
Nana da ta riga ta kama tsorata ta daga kai da sauri.
"Magana zaki buɗe baki kiyimin ba body language ba." Ya faɗa a tsawace, jikin Nana ya sake ɗaukan rawa kar.....kar...kar...sai kuma ta fashe da kuka.
"Yallaɓai nice a gafarceni wallahi sharrin shaidan ne da zuciya."
"Zakiga sharrin shaiɗan randa kika sake koda dungurin tane." Zawaciki ya faɗa yana danna kira a wayar sa, yace "Eh shigo dasu sannan ka karɓo File ɗin Case ɗin Asma'u Abdullahi Mai Kano a wajen Mai Shinkafa." Yana gama bada umarnin ya kashe wayar yana kallon Nana dake kuka har yanzu yace "will you keep quiet my friend?"
Nana ta sake rudewa dan bata san mai yace ba, Mai Kano ya dube ta yace "Kiyi musu shiru basa son haya niya anan." Gum Nana ta rufe bakin ta da tafin hannu.
Ba'a jima ba aka kawo File ɗin Nana da ƙyar ta iya saka hannu a inda aka nuna mata saboda rawar da jikin ta keyi, a tsume Asp Zawaciki ya sake karanta mata abin da file ɗin ya ƙunsa da abinda ta sawa hannu bakin ta na rawa tace ta amince.
"Bazan ma sake ba in sha Allahu." Nana ta faɗa tana sharce zufa.
Da kin taimaki kanki." Zawaciki yayi maganar sai kuma ya maida hankalin sa kan Mai Kano. Saida suka yi magana sosai sanna ya sallame su.
Suna fitowa daga office ɗin Nana tayi ido biyu da wata mata da batafi shekarun taba ƴan sanda biyu sun taso ƙeyarta hannunta cikin handcup tayi firi....firi tana rusa kuka da magiya bakin ta yaƙi mutuwa fadi take.
"Dan Allah karku maida ni cikin wajen nan, wallahi tsautsayi ne bada gangan na jeho ta daga saman bene ba, ita ce ta fara tsokana ta, wayyooooo Allah jama'a ku taimake ni zasu kashe ni, na shiga uku." Haka matar nan take kurma ihu tana tsalle tana dara kamar doki babu mai bi takan ta bare ya saurare ta, to wajene da kowa ta kanshi yake, ƴan Sandan da suka rakota ɗaya a cikin su ya falla mata mari tare da faɗin.
"Keep quiet. a zafafe.
Wannan abu da Nana ta gani ya sake firgita ta har suka zo gida jikin ta rawa yake.
Suna zuwa gida kuma zazzaɓi mai zafi ya rufe ta saboda firgita da tayi, tun Mai Kano yana mata dariya a ɓoye tare da faɗin "Allah ya ƙara." harta koma bashi tausayi, dan sosai cikin ta ya saki ta rinƙa gudawa, daga karshe dai dole saida aka kira Aunty Nurse tazo tasa mata ruwa da allura.
*****Yau Husna ke cika sati biyu a gidan Kakanin ta tuni ta warke tayi fes da ita, kusan kullum sai sunyi waya da Maman ta, haka Babanta na zuwa dubata kullum, duk ciwukan jikin ta sun warke sai tabbunan da ko zasu ɓace dole sai a hankali.
Gaba ɗaya yanayin Husna ya canja yanzu bata da walwala da sakewa kamar da, dawowar yayan ta Baffa cema tasa taɗan ware.
Lokacin da Baffa ya samu labarin Maman su da Baban su sun rabu kuka ya saka duk da bawai an bashi labarin asalin abinda ya faru bane, amma shiba yaro bane yanzu yasan mai saki yake nufi dan gaf yake da gama secondary gashi yaro ne ma ilimin addini da nutsuwa, wannan yasa ya fahimci abinda ke faruwa har ma fiya da yadda Momma dake masa bayani tayi zaton zai gane.
"Amma dai Husna ta dawo nan ke nan da zama ko Momma?" Baffa ya faɗi yana duban Momma bayan ya gama jin labarin rabuwar iyayen su.
"A'a zata koma amma bamu san lokacin da za su mai da ita ba sai abinda Kawun ku yace."
Baffa sai yaji zancen wani iri, yace "wanne irin zata koma kuma? Anan ma ai za'a iya riƙe ta, ku dan bakusan baƙin halin waccar Nanan ba ne, bata da kirki wallahi." Baffa yayi maganar ranshi a ɓace sai kuma ya fara faɗin "gaskiya ba zata koma ba, ni zan yiwa Baba magana nasan zai barta muci gaba da zama tare anan tunda mu tamu ƙaddarar ke nan."
Maganar Baffa ta ƙarshe tasa su Momma jin tausayin sa ya rufe su, sai kuma suka bisa da kallon kai yaro ne bazaka gane ba.
Wai a haka ma gwanda Husna dashi da har yau tsawan shekara goma sha bakwai da haihuwar shi ke nan amma ubansa ya juya masa baya yaƙi duban shi a matsayin ɗan cikin sa, danma ƴan uwansa masu zumunci ne sosai suka jashi cikin su, dan tun Baffa yana JS 2 Musa ya kaishi kasuwa, yanzu shekara uku ke nan da fara zuwan sa kwari duk ranar Jumma'a Asabar da Lahadi yake zuwa kasuwa.
Yasha haɗu wa da Alhaji Manu Kwabo (mahaifinsa) amma kallo ɗaya zaiyi masa ya ɗauke kai, gashi komai nasa irin na ubansa ne kamar su ɗaya, kai hatta tafiyar sa irin ta Baban shice, yan kasuwa suyi ta maganar amma shi ɗan Alhaji ne ko? Shi dai baya basu amsa haka su Musa basa cewa komai, indai ba wanda suka san labarin ba to kowa a kasuwar kallon ƙaramin kanin su suke wa Baffa wasu kuma suce irin ƴaƴan ƴan uwan Alhaji Manu ne da yake ɗakko wa ya riƙe.
Dama a rumfar su Musa yake inba hanya ce ta biyo dashi ta wajen rumfar Baban shiba basa haɗuwa, haka shima baya bi ta inda Alhajin ma zai gashi.
Randa Husna ta cika sati uku da barin gidan su Yaya Ja'afar da kan shi ya maida ita gidan Babanta, Mai Kano bai san za'a dawo da ita ba sai ganin su yayi da yake da safe ne yana gida.
Yaya Ja'afar baice masa komai ba ya miƙa masa ita da tarin tsarabar ta ya juya ya tafi ya barta tana kuka da ihun ita ba zata zauna ba, sai kuma ta fara kiran Yayanta dan lokacin da suka taho baya nan ya tafi makaranta.
Wannan dawowar da aka yi da Husna saida ya haddasa rigima tsakanin su Aunty Maimuna da yayun su Maza dan sosai suka haɗe kai suka ce baza'a maida ita ba, Baba Habu kuma yace sun yi kaɗan wannan yasa suka yiwa gidan yaji tsawan sati biyu ke nan babu wacce ta sake leƙa su Momma sai dai su kirasu a waya.
A gidan Alhaji Ƙadiri kuwa rigima ce ta tashi sabuwa bayan dawowar Baffa gida ya samu labarin an mai da Husna gidan su, nan fa yayi tsalle yace saiya je ya ɗakko ta, saida Abdussamad yayi masa kaca-kaca sannan ya haƙura, sai kuma ya fara haɗa kayan shi yana kuka yace shima gidan Yayan sa Musa zai koma da zama ba zai zauna a gidan Alhaji ba tunda suka maida Husna.
....... Mai Kano ya samu Malam Idrisa maƙocin sa suka yi magana dashi sosai akan Husna, yayi masa godiya tare da roƙon shi dan Allah suna kusa Umman Bishira ta taimaka masa ta rinƙa sa masa ido akan ta shima kuma duk abinda ya gani naba daidai ba dan Allah ya faɗa masa tunda shi ne a kusa da gida.
Malam Idrisa ya jinjina kai bayan ya gama jin duka bayanan maƙocin nasa yace.
"Karka damu Malam Mai Kano in sha Allahu komai zai wuce, Allah ya kara rufa mana asiri."
"Amin ya Allah."
A haka suka yi sallama kowa ya shige gidan sa.
Lokacin da Baban Bishira yake faɗa wa Umma yadda suka yi da Baban Husna sai tayi murmushi tace "Ai munyi waya da Safiya washegarin tafiyar Husna mantawa nayi ban faɗa maka ba, kasan munyi zanje duba jikin ta ko?"
"Eh anyi haka."
"To danaje ai ban same taba sai su Momma suke cemin ta koma gidan Babban wansu Lagos, to anan mukayi waya da ita ta roƙe ni dan Allah na taimaka nasa mata ido akan Husna."
Malam Idrisa yace "Allah sarki wannan bayin Allah sunga jarrabawa, wallahi duk bakiga Mai Kano ba ya rame."
"To Malam damuwa ai bata da daɗi."
Haka Umma da mijinta suka yi ta tattauna wa akan matsalolin rayuwa.
Wannan karon sosai Mai Kano yasa ido akan Husna ya koma dawowa gida da wuri kamar yadda ya saba, haka sosai Nana ke dannar zuciyar ta, saidai yadda Mai Kano ke kula da Husna fiya da da abin naci mata rai, dan yanzu ko fuska yaga ta canja ya rinƙa tambayar ta meya same ta me take so? Kome ya kawo kuwa da kanshi yake rabawa ya bata nata ya bawa Ni'ima nata sauran kuma ya miƙawa Nana ko taci kota zubar matsalar ta.
A wajen kwanciya ma an samu canji, yanzu tare suke kwanciya da Ni'ima, da farko Ni'ima taso ta hanata kwanciyar Nana ta rufe ta da faɗa.
"Karki jamin masifar da bazan iya fita daga ciki taba, Ni'ima wannan yar da kike gani masifa ce a gidan nan."
Haka suke kwana tare saidai babu dama tayi juyi ta taɓa jikinta saita haure ta da ƙafa kota ɗaka mata duka, wannan yasa dole Husna ta koyi haɗe jikin ta waje ɗaya.
Satin farko Abdulgaffar ne yazo duba Husna ya same ta babu lefi duk da gyaran dai sai a hankali amma kuma babu ƙazanta a jikin ta, ya kawo mata su Popcorn biskit da yawa ya bata leda daban yace ta bawa su Bishira inji Maman ta, ai kuwa da gudunta ta shige gidan su Bishira ta kai musu Umma nata godiya. Abdulgaffar yaɗan jima da ita kanya tafi, tana shigowa gida da nata kuma ta ɗibi tsaraban da Kawun ta ya kawo mata ta bawa Ni'ima.
Da farko Ni'ima taso taƙi karɓa sai kuma ta amsa tana kallon Husna Nana ta taɓe baki.
Akace wai hali zanan dutse barin hali sai mutuwa, Nana ta gaji da kallon Husna tana yin abinda taga dama bata da damar hanawa, kullam inta ganta a sake zuciyar ta zafi take wannan yasa ta canja salon mugun ta.
Mai Kano na fita kasuwa to duk wani aiken gidan Husna ke yi saidai in tana makaranta wacce ita ma ta rasa yadda zatayi ta hanata zuwa ne amma ba'a son ranta take tafiya ba, wanke wanke da shara kuwa tun tana buja-buja yanzu harta fara iya wa.
Tsawa da mugun zagi tuni Nana ta dawo dasu akan sai dai duka tanayi ne a bayan idon Mai Kano, in yana gidan cikin sanyin rai zakaji tana yiwa Husna magana.
Wanka kuwa tuni yafi ƙarfin yinta kullum, dan kuru-kuru Nana take hana ta wanka tace zata yi mata wasan ruwa.
Umman Bishira tana ƙoƙari sosai wajen duba Husna dan yanzu kitso ma itake mata da yake ta iya, tana zuwa Boko da islamiyya saidai karatu da ƙoƙarin ta yaja baya sosai, homework kuwa duk wanda ta gane take yi wanda bata gane ba kuma ta barshi, to dama Yayanta ne ke koya mata homework da hadda yanzu kuma babu shi, Baban ta kuma bashi da cikakken lokacin yi mata duka wannan, Islamiyya ma yanzu ba koda yaushe take iya bada hadda ba tun ya Sayyadi yana dukanta akan bada hadda harya daina.
Watan daya wuce kuɗin hayar gidan su Husna ya ƙare, Mai Kano yaje biyan kuɗi mai gidan yace ya bashi notice gidan zai siyar....
Tun daga lokacin yake neman gidan da zasu kama amma har yanzu da suke gab da cinye notice din ba'a samu gida ba.
"Na faɗa maka ka koma gidana muci gaba da zaman mu tare amma kaƙi, kaga yanzu ni ba mata gare ni ba zaman kaɗaici dama ya ishe ni, Amma Mai Kano in kana kusa ai kaga zan najin daɗi ko? Kuma ma kace min cikin shekarar nan kake son fara naka ginin kaga shi kenan kana kusa kana ganin abinda ake yi zaifi maka sauƙi ma" Sale ya sake maimaita wa Mai Kano Ƙudirin sa nasan ya koma gidan sa da zama bayan ya gama jin ƙorafin shi akan neman gida da yake tayi bai samu ba.
"Shike nan zanyi tunani in komawar cance tafi saimu dawo, amma kaima Sale ya kamata kayi aure zuwa yanzu lokaci ya fara ja, gashi Maman su Abba ta doshi shekara da rasuwa."
"Hmmmm! In sha Allah zanyi amma babu Wani tunani da zakayi Malam kawai ku fara haɗa kayan ku daga yau."
Sale ya tari numfashin sa da sauri yana ɗan sakin murmushin jin daɗi.
"Ai shike nan tunda ka dage saimu koma ɗin."
Bayan Mai Kano ya dawo gida yaci abinci ya huta yake faɗa wa Nana ta fara haɗa kayan ta cikin satin nan zasu tashi, tace "A'a an samu gidan ne?" Kai ya girgiza mata.
"A'a Hotoro zamu koma gidan Aminina Sale can ƴandodo." Nana taji daɗin maganar dan tasan Sale sosai mutumin kirki ne.
A cikin satin Kuma suka tashi Umman Bishira bata da labari tunda basa shiri da Nana saboda tace ita munafukar Safiya ce, sai da mota tazo ɗiban kaya sannan taji.
Umman Bishira taji babu daɗi sosai da tashin su dan sosai su Bishira suka saba da Husna, jikin Umma a sanyaye ta koma cikin gida tana tunanin koya rayuwa zatayi da Husna kuma nan gaba.
Da malam Idrisa ya dawo Umma ke faɗa masa tashin su Husna, tace "sosai nayi mamaki Malam tashi babu sallama sai ɗazu dana fita ana kwashe kayan Baban Husna ke yimin godiya a bakin shi naji ashe Hotoro zasu koma can inda suka fara zama."
"Eh wallahi kwanaki ya faɗa min zai tashi amma shaf na manta na faɗa miki, ai gidan abokin shi daya taɓa zama zasu koma." Umman Bishira tayi shiru tana juya Maganar sai kuma a hankali tace "to Allah ya basu zaman lafiya, ni wallahi Husna nake taji."
Malam Idrisa yace "Babu komai kiyi mata addu'a akwai Allah."